Showing 33001 words to 36000 words out of 96302 words

Chapter 12 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt

shima ya sha kukan nan ko zai samu mai rarrashinsa, da kyar Aziza ta zare hannunta daga na Hajja ta fice da sauri jin wani kukan na shirin cewa a ba shi hanya, Hajja kuwa tuni ta sake saka wani kuka tasa hannuwanta a fuska, saurin ficewa Baffa ya yi jin hawaye ya fara bin fuskarsa, yana fita babu b'ata lokaci suka hau doki, da Baffa da Baffa Mandi da Arɗo sai Aziza, suna hawa doki suka dauki hanyar yankin ja'o ba tare da bata lokaci ba.








🐍🐍🐍🐍🐍


Tun bayan da Azima ta bar yankin kwana take aikin tafiya ba tare da ta gaji ba dan bata jin gajiya a tattare da ita, hakika tana shan tafiya, dan kuwa ace mutum wanda yake ba aljani ba idan zai fita daga yankin kwana zuwa cikin garin kafin ya iske titi a kan doki sai ya shafe sati biyu, shiyasa su haka suke ba a shigo musu su ma kuma basu shiga gari dan nan ne rayuwarsu a kauyensu mai cike da abun burgewa da albarkatun korayen shuke-shuke, a kwana daya Azima ta yi rabin tafiya abunka da ba tafiyar mutane ba.






🍃🍃🍃🍃


Sai kusan gaff azahar su Baffa suka isa yankin ja'o ba tare da bata lokaci ba aka musu iso izuwa ganawa da Malam Shadi, suna shiga bukkarsa Malam Shadi na haɗa ido da Aziza ya hau salati yana sanar da Ubangiji nan gaban Baffa ya bada dammm! amma ya daure suka zauna ana gaisawa cikin mutunci da mutuntawa, Malam Shadi ya kalli Baffa ya ce
"Ohh Allah Magaji Mazan fama kana raye? Yaushe rabonka da yankin nan? Inaji fa tun sadda wan can muguwar mayyar ta sakamu a gaba kazo ka rabamu da ita ban sake ganinka ba sai dai kayi aike" Baffa ya yi murmushin boye damuwa ya ce
"Wlh kuwa Malam Shadi,tun sadda na daina shige-shige naji komai ya fita a raina"
"Allahu Akbar" cewar Malam Shadi yana kallon Aziza da ta dukar da kai gabanta na faduwa, ya kalli Baffa cike da al'ajabi ya ce
"Magaji Bawa ina ka samo *MACIJIYA!?*" juyawa Baffa ya yi ya kalli Aziza da ta rakube ta dukar da kai kasa kamar ma kuka take yi,sannan ya maida kallonsa ga Malam ya ce
" 'yata ce Malam, na kawota ne wajanka dan ka duba min ita, Banju da na kashe yace zai dawo shine ya dawo daukar Fansa a kan yarana, yanzu haka dayar ta bar yankin kwana kwata-kwata, ita kuma wannan ka ganta nan, shine nace bari na kawosu wajanka dan a san ta yadda za a rabasu da su,bana so gwagwarmayan da nayi ya shafe yarana"
"Shafa kuma ta nawa magaji? Ai shafa kam an gama shafansu tunda gasu nan a macizai" cewar Arɗo, Malam Shadi ya gya ɗa kai yana fadin
"Ya Hayyu Ya Qayyum Ya Zuljalalu wal'ikram, hakika Banju mugun aljani ne, Banju mugu ne fiye da tunanin me tunani, amma Magaji kai ma zaka iya yiwa yaranka magani ai"
Girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"Zan iya sake kashe Banju, amma abunda nake tsoro shine Banju na rayuwa ne a cikin Azima yana tafiya ne da kafafunta, yana aiki ne da hannuwanta,yana gani ne da idanunta,yana motsi ne da motsinta, sannan a binciken da nayi Azima a sume take a jikin Banju, idan har na kashe Banju to tabbas Azima ma ta tafi, na duba na ga ita Aziza rabata da Bahula ba wata damuwa ba ce, amma kuma tashin hankalin a nan shine,ko Bahula ta bar jikin Aziza, Aziza ba zata samu lafiya ba dan Banju ya maidata Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinta ba" jinjina kai Malam Shadi yayi bayan Baffa ya gama yi masa bayani, Baffa ya kuma cewa
"Ina da bukatar taimako dan bana so na salwantar da rayuwar yarana! Jumala ba zata yafemini ba,sannan nima bazan yafewa kaina ba Malam Shadi"


"Matso nan kusa dani Aziza karki ji tsoro" Malam Shadi ya fada yana kallon Aziza, a hankali ta taso ta matso kusa da shi ta duka, wani magani ya ɗiba a kasko ya watsa mata a fuska,ihu Aziza ta saka tana furta "Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Baffana zafii!!" abun tausayi, hawaye ne ya cika a idon Baffa yana ji kamar ya tashi ya fita amma ina ba hali, Malam Shadi yasa hannu ya damƙi goshin Aziza da karfi, murkususu ta hauyi tana son kwacewa amma ta kasa,rintse idonsa ya yi yana gane-gane da hange-hange, ya dau lokaci yana riƙe da goshin Aziza wacce ke murkususun azaba har sai da ta suma kafin Malam Shadi ya saketa, Baffa ya yi saurin taro 'yarsa ta fada jikinsa,jikinsa na rawa hawaye na zuba a idonsa ya d'ago ya kalli Malam Shadi yana fadin
"Malam me ya sameta?"


"Haba Magaji! Sai kace baka san yanayin aiki ba,ka kwantar da hankalinka zata farfado, amma gaskiya akwai babbar matsala wanda ba zan iya ce muku komai a kai ba, akwai aikin da nake so nayi cikin dare ina so na bincika na ga taya za a rabasu da mugun nan Banju, sannan Babban tashin hankalin shine 'yar uwarta Banju ya jata sun bar al'ƙaryan nan,ina take? Ina za a ganta? Duk babu wanda ya sani" Arɗo da Baffa Mandi suka sharo zufar tashin hankali, Malam Shadi ya ɗora da cewa
"Babban damuwar shine abunda Banju zai ja Azima ta aikata,amma zanyi bincike a kai yau In sha Allah,ina dai a nan zaku kwana?" Baffa suka amsa da eh, sannan Malam Shadi ya kira wani almajirinsa yace ya kawo masa tarbama wanda yake na kara ne, bayan an kawo ya ce a shinfiɗe Aziza a kai, bayan Baffa ya kwantar da Aziza Malam Shadi ya kunna mata hayaki, sannan suka fita waje suka zauna suna tattauna yadda zasu yi a kan lamarin.






🍃🍃🍃🍃


Sarki Chubado ne da mai unguwan kwana ori suke tattaunawa a kan batun Azima da Aziza Macizai ne,suna ta alhinin lamarin, su biyu suke magana a kan cewa suna tausayawa Baffa, a garin yaya sai ga Salti ɗan gidan Jauro mai maganin yankin kwana yazo wucewa caraf a kunnensa, dan Salti ba dai gulma ba,nan yaji duk wani tattaunawa da Sarki Chubado da Ori ke yi a kan lamarin har da tafiyar da su Baffa suka yi yankin ja'o, da gudu Salti ya kwasa yana fadin zai je ya gayawa Baffansa dan yasan zai yi farin ciki da wannan labarin da zai kai ma sa.






🍃🍃🍃🍃🍃




Comments
Vote
By
Momyn Ahlan
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)


MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


🍃🍃🍃🍃🍃


*INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN........BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU*






*PAID.*
🅿️==3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣






Sarki Chubaɗo cikin fushi ya kalli mutanen da suke wajan ya ce.
"Amma wallahi kun bani mamaki! Kuma kunji kunya! Yanzu akwai masifar da zata samu Magaji wanda har zai sa ku juya masa baya? Idan har ku wa inda ku ka zo bayan shekara ashirin baku san gwagwarmayen da Magaji ya yi ba, to ku wa inda ku ka zo kafin bayan shekara ashirin zaku ce kun manta da wannan halaccin ne? Dayawanku a nan wasunku basu da dangi kaff Banju ya kashesu! dabadin Magaji ba babu ko da ƙwaro da zai rage a wannan yankin!!" Sarki Chubado ya karasa da tsawa idonsa jajur dan ransa ya b'aci matuka
"A ce ina sarkin fulanin yankin kwana amma Jauro ya ja ku ba tare da sanina ba ku zo yiwa Magaji rashin mutunci da dibar albarka! Jauro ne sarkinku!! Na ce Jauroo neee sarkinkuuu!!!?" shuru jama'a suka yi masu zare ido da masu tsilli-tsilli da ido suna yi, Mai Unguwar yankin kwana bayan Sarkin fulanin kwana Chubaɗo ya dasa ayar tasa shima ya karbe da cewa
"Jauro dai mai maganin yankin kwana ne kamar yadda ku ka sani, amma a da kun san waye GARKUWAN YANKIN KWANA KAFIN A ƊORA GARKUWA NA YANZU!! TO GA SHI NAN SHINE DAI! *MAGAJI BAWA!!* kafin ya sauke duk wata baiwa tasa ya binne bayan yasha wahalan kama aljanu da mayu ya kullesu!! Ya sauka ne a kan matsayinsa da yake da shi bayan ya kashe Banju! Amma har kwanan gobe! kai ba ma kwanan gobe kawai ba! HAR GABAN ABADA BABU WANI GARKUWAN FULANIN YANKIN KWANA SAMA DA MAGAJI! SANNAN BABU WANI MAI MAGANI SAMA DA MAGAJI! Har ta Garkuwan fulanin yankin kwana na yanzu da Magaji yake tunkaho"




Garkuwan fulanin kwana na yanzu ya fito ya ce
"Tabbas hakane, da taimakon Magaji Bawa na zama Garkuwan fulanin kwana shi ya maidani mutum, gaskiya baku kyauta ba" wasu ne jikinsu ya fara sanyi ganin haka yasa Jauro ƙara tattaro sauran munafurcinsa dan shi baya so ace mutane su banzartar da maganarsa idan ba haka ba ba zai cika burinsa ba,baya so yaji sunan Magaji na daukaka! yafi so duk yankuna yadda ake kiran sunan Magaji Bawa! Magaji Bawa! ya kasance shi Jauro Mai Maganin yankin kwana shi ake kira ba wani Magaji Bawa ba, ace shine shahararsa ta kai inda yake so kuma yake bukata, saurin cewa ya yi
"Babu wani borin kunyar da za ayiwa mutane an dai cutar dasu! Wa inda aka kashe musu yara su ce mai? Sannan tunda daɗewa Magaji yasan yaransa Macizai ne amma ya boyewa mutane bai gaya musu dan yanzu yana da mugun nufi a ransa!"



"Magaji baya da masaniya a kan cewa *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* taya idan ya sani har zai barsu su yi kisan kai!? Da kake maganar su na kisa Aziza bata taba kisa ba,akasari ma ita dabi'un Magaji ne tattare da ita, ku a tsammaninku da Azima ce har kwa fara yi mata abunda ku ka yiwa Aziza? Inaaa! Da kafin mu iso wlh sai dai gawawwakinku!" cewar Baffa Mandi, jauro ya ce
"Owoohh! Kenan da saninku ma kamar yadda na faɗa! Jama'a kuna dai ji ko? An zalinceku an munafurceku an kashe muku! Kuma ta yadda zaku gane Magaji ya san yaransa Macizai ne shine basu zuwa bikin gargajiya ta al'adun fulani wanda ake gabatarwa duk shekara, sabida sun san a lokacin ana amfanin da magungunan macizai! Sannan......"




"Ya isheka haka Jauro!!" Baffa ya katse Jauro jikinsa na rawa, ya tako ya zo gabansa ya ce
"Da ace da sanina yarana macizai ne da tuni na dauki mataki wani zancan 7ake yi yanzu ba wannan ba, a da nace maka muddun ka gano yarana macizai ne nina maka lamuni ka kashesu! Amma tunda na gano cewa ku ɗin ba mutane bane dabbobi ne wanda shanu ma sun fiku hankali ko da Azima da Aziza sun dawo yankin kwana duk wanda ya yi gigin taba min yara a lokacin zan basu umarni su kashe min koma waye!! Sannan ka zuba ido ka gani, zan maida yarana mutane ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyar mutuwata, a yau kuna zaginsu macizai kuna ci min mutunci, amma ku sani ko nace kai jauro ko sani, MAGAJI BAWA KAFIN ALLAH NE BA KAFIN MUTUM BA! KO DA ACE MISALI BANA RAYE! AZIMA DA AZIZA SAI SUNANSU YA BUGA TAMBARI A YANKUNA BA MA IYAKAR YANKIN KWANA BA! KAMAR YADDA NA MAHAIFINSU NI MAGAJI BAWA NAYI! NA MAKA WANNAN ALKAWARI! BAIWA DA FARIN JININMU DAGA ALLAH NE KA ZUBA IDO KA GANI JAURO!!!" Baffa na gama faɗi ya bar wajan tare da daukar Hajja suka yi gida yana tunanin tashin hankalin da Hajja zata farka da shi, da fari yara macizai yanzu kuma babu su ma kwata-kwata, amma ya zata yi dole su rungumi kaddara.






Bayan Baffa ya bar wajan Sarki Chubaɗo ya kalli Jauro ya ce
"Ka dai ji kunya wlh! Da ace nima tsoron kar nayi abun kunya ba wlh da yau a yanzu na koreka daga yankin kwana, ku kuma idan dai Jauro ne gaku ga shi,in dai ba a mutu ba to ba shakka ba a daina kallo ba, ba fata nake muku ba amma na tabbata akwai jarabawa,sannan Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wani abunda ya sameku karku sake kuce zakuje wajan Magaji ya taimaka muku! kuje wajan Jauro ya taimaka muku, wannan umarnina ne a matsayina na sarkin wannan yankin!! Idan kuma na ga akasin abunda nace mutum zai fuskanci mugun hukunci!" Chubaɗo na gama faɗi ya yi gaba ya bar su a tsaye a wajan, wasu jikinsu yayi sanyi inda nadama ta kamasu wasu kuwa zuciyarsu kamar busashshen itace!.




🍃🐍🍃🐍🍃🐍


Azima kwananta biyu tana tafiya kafin ta fito bakin titi, tana fitowa wani guɗa ta yi da dogon harshenta, duniya sabuwa! Tana nan tsaye a kan titi da lullubi tana tunanin hanyar da zata fara dosa, nan ta yanke shawara kawai ta bi dogon titi ta ga iyakar karewarsa, haka ta hau tafiya a tsakiyar titi tana murmushi, kamar daga sama sai ga wani mota ta yanko da gudu amma sai ganin yarinya ya yi tana tafiya akan titi sai horn yake danna mata amma a banza! Azima kuwa tunda farkon fitowarta kenan ba fahimta tayi ba, da kyar mutumin ya taka burki ya fito a motar gami da daka mata tsawa "keeeeeeee!!" wani tsayuwa Azima tayi tare da ware blue eye dinta, babu wanda ya taba mata irin wannan ihun, a hankali ta kara jan mayafinta ta rufe fuska sannan ta juya a hankali kanta a duke, mutumin kallon sama da kasa ya mata yana yatsine fuska dan ya ganta da shigar fulani ba mamaki irin kidahuman nan ne na jeji dan haka cikin izgilanci ya hau ta da zagi.
"Ke wace iriyar bagidajiya ce da ana miki horn amma da shike kin fito a cikin jeji baki ganewa kwakwalwarki a toshe yake kina tafiya a kan titi banza ballagaza daƙiƙiya ƙidahuma tunkiya!!" hakika zagin ya soki zuciyar Azima, zaro ido ta yi tare da yaye mayafinta rai b'ace cikin hausar da babu sosai a kan harshenta ta ce
"Ba dai tunkiya ba, sai dai *MACIJIYA!🐍**" ta faɗi tare da komawa macijiya ba ta jira ya gama firgita ba ta kai masa sara a wuya nan ya fadi kasa yana shure-shure,komawa mutum ta yi tana dariya ta ce
"Kaina mutum na farko da na fara kashewa daga fitowata,hakan na nufin cewa zan sha jini da yawa kenan sabida mutanen cikin gari basu da ɗa'a,ni kuwa AZIMA MACIJIYA bana daukar wargi!" ta faɗi tana murmushin gefen baki ta leƙa cikin motar ta wargaza ta ga kuɗi ta kwashe duk da bata san amfanin me zasu mata ba, ta ci gaba da tafiya, ta yi tafiya sosai inda ta iske tasha wanda yake cike yake da jama'a a hankali ta ƙutsa kanta cikinsu tana ji ana ambatar sunayen garurruka, garin da taji ya mata masauki a kunneta shine *KANO TUMBIN GIWA KO DA MAI KA ZO AN FIKA!* murmushi ta yi ta kara nanata KANO ranta, sannan ta afka mota ta nemi can baya ta zauna tana murmushi yau burinta ya cika ta bar yankin kwana.




Kuɗi aka fara karba aka zo kanta, ana cewa kawo kuɗinki nan kuwa ta cire ta miƙa ba tare da tayi magana ba ko tasan nawa ta bayar ba,duk da zuciyarta na raya mata da sun isa kanon da zasuje zata kashe mutanen da suke motar!.




Bayan yan wani lokaci ƙalilan mota ta tashi daga tasha ta hau tafiya, inda Azima ta ji ta gaji dan gani take yi motar bata mata sauri,amma ance biyan bukata yafi dogon buri dan haka ta kara rungume hakuri.




Basu da isa kano ba kuwa sai magriba, ganin tsananin girma da faɗi da cikowa irin na garin kano yasa taji ma ta fasa kashe mutanen da tayi niyyar kashesu, ta shagala da kalle-kalle ta ji ana mata magana ta bayanta
"Barka dai 'yar fulani"


🍃🍃🍃🍃🍃🍃




😭😭😭😭


Yau baƙin ciki ne a raina sau biyu ina cin uban typing yana gogewa, Allah dabadin bana son nayi missing update ba da ɗiff zaku jini😭
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)


MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


🍃🍃🍃🍃🍃






*PAID.*
🅿️==2️⃣9️⃣↪️0️⃣3️⃣0️⃣






Ko da Salti ya isa gida ya kwashe kaff yadda yaji su Sarki Chubaɗo da mai Unguwa Ori suka tattauna ya gayawa Baffansa, a hankali Jauro ya mike yana murmushi ya ce
"Salti,tun da kake kwaso gulma baka taba kwaso mai amfani ba sai yau, jeka dole nayi maka kyautar shanuwa daya" da sauri Salti ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login