Showing 36001 words to 39000 words out of 96302 words
Chapter 13 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt
miƙe yana murna ya fice,Jauro ya dungule hannu yana dukar iska ya ce
"Lokaci ya yi da zan fatattaki Magaji Bawa, ka fi ni a komai kyau,martaba,baiwa,kyakkyawar mata Jumala,ga kuma yara kyawawa! kai kana gani ka fi kowa ne! zargin da nake yiwa yaranka ya tabbata, wato ma har b'oye-b'oye ake yiwa mutane ana munafurtarsu kar a gaya musu gaskiya, to ni nan zan bayyanawa jama'a su waye Azima da Aziza!" ya faɗa yana murmushin mugunta.
🍃🍃🍃🍃
Kamar yadda Malam Shadi ya faɗa da daddare ne ya yi bincike mai zurfi dangane da matsalar su Azima da Aziza,inda ya hangi gagaramin matsala mai rikitarwa inda tausayin yaran ya kamasa dan kuwa da wuya a samu maganin warakarsu.
Da washe gari bayan sun idar da sallar asuba ana gaggaisawa bayan sun gama gaisawa Malam Shadi ya kalli Baffa sai kuma ya duƙar da kai, Baffa ya yi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo ya ce
"Malam Shadi karkiji komai gaya min ko ma miye ne,ni musulmi ne kuma nayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, ka gaya min kawai"
Jinjina kai Malam Shadi ya yi ya ce
"Tabbas ni shaidan hakane Magaji, wato a gaskiya ba zan boye maka ba, samun lafiyar Aziza yana tattare ne da Azima, domin kuwa wanda yake da alhakin abun ya ja Azima basu yankin kwana balle a musu magani, kai ko da Azima bata bar yankin kwana ba da wuya a samu wanda zai yi jahadin taimaka musu" goge gumi Baffa ya yi ya ce
"Malam Shadi ka gaya min kai tsaye kawai zan fi ganewa,dan a yanzu ji nake kamar kirjina zai tsage zuciyata ta faɗo kasa"
Malam Shadi ya gyara zama ya ce
"Dole sai sunyi aure kafin Banju ya rabu dasu, barin ma Azima ita ce wacce take bukatar taimakon gaggawa, sannan wannan miji da zai auresu sai ya sadu da Azima kafin Banju ya fita a jikin Azima, idan Banju ya bar jikin Azima a cikin kaso dari mun yaƙesa kaso sittin, idan aka yi sa'a idan Banju ya fita a jikin Azima, Aziza zata iya samun lafiya,idan kuma bata samu ba ita ma dole sai wanda ya aureta ya kusanceta kafin makarin sihirin da Banju ya mata na siddabarun maidata macijiya ya karya"
"Ma'asabamun musibatin Qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innallahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" shine abunda Baffa da Baffa Mandi da Arɗo suke iya nanatawa suna fifita da hannunsu,Arɗo ya girgiza kai ya ce
"Tabdijam kawai Allah ya jikan Azima da Aziza, dan kuwa na tabbata babu namijin da zaiji cewa su macizai ne ya taimaka ya auresu har mu sa ran zasu samu lafiya"
"Kuma dole wanda zai aure su zai fuskanci ƙalubale kafin ya kusancesu,sannan bayan ya kusancesu zai iya kamuwa da mugun ciwo amma ba ina nufin ba zai warke ba amma tabbas zaiji a jikinsa,idan an samu damar hakan zaka iya kara kashe Banju a karo na biyu" hawaye ne Baffa ya hau yi yana kan tasbihi ga Ubangijin talikai, Baffa ya ce
"Tabbas da ace na dinga ganin tashin hankalin nan na b'arna da ta'adin da Azima ke yi da ni da kaina zan kasheta! to amma yanzu tana ina? Me take yi? Su wa da wa zata kashe!? Akwai tambayoyi dayawa a raina wanda babu wanda zai amsamin" Baffa ya hau kuka Arɗo da Baffa Mandi suna rarrashinsa, Baffa Mandi ya kalli Malam Shadi ya ce
"Malam Shadi, yanzu ya maganar raba Aziza da Bahula?"
"A gaskiya Mandi ni a ganina a shawarce, kar a raba Aziza da Bahula, tinda bata cutar da ita, sannan ko an raba Aziza da Bahula Aziza fa ba zata taba komawa mutum ba, ni a ganina tunda Banju yana son kanwarsa Bahula sannan yasan cewa tana rayuwa a jikin Aziza dole wata rana zai dawo, karku manta kamar yadda Azima da Aziza suke 'yan biyu haka ma Banju da Bahula suke 'yan biyu, zamu iya samun dawowa da Azima gida ta hanyar Bahula dake jikin Aziza,ni a ganina kar a raba Aziza da Bahula a barsu tare idan ya so aka samu wanda zai yi jahadin aurensu bayan an raba Azima da Banju sai a raba Aziza da Bahula"
"Tashin hankali wanda ba a sa masa rana" cewar Arɗo yana kan rarrashin Baffa dake kuka wi-wi, da kyar suka rarrashi Baffa ya samu ya tsaida hawayen idonsa sannan ya miƙe yana yiwa Malam Shadi godiya ya ce masa zasu wuce yau, Malam Shadi ya ce
"Ba damuwa Magaji,karka damu Allah zai shiga cikin lamarin" Baffa bai iya ya kara cewa kala ba, Malam Shadi ya miƙa masa wani ganyen magani ya ce
"Wannan idan ka je ka haɗawa Aziza,ita kuma Azima Allah ya dawo da ita cikin gaggawa, bari nasa a kira muku Azizan sai ku wuce" su Baffa Mandi da Arɗo suka yiwa Malam Shadi Godiya sannan suka fito a tare,bayan an kira Aziza ta fito Baffa ya kama hannunta idonsa jajur ya ɗorata a kan doki, Aziza tunda ta ga yanayin Baffanta tasan cewa kwai gagarumin matsala, haka sukayi sallama da Malam shadi cikin amince suka kama hanyar yankin kwana.
🍃🍃🍃🍃🍃
Sai da lokacin sallar azahar ya gauta kafin suka iso yankin kwana kai tsaye gidan Arɗo suka nufa, Hajja na zaune tayi zugum Yawuro ta ajiye mata kwaryan nono a gabanta amma haka nonon ke kallonta, Yawuro ke fadin
"Haba Jumala! Dan Allah ki sa wani abu a cikinki mana, ga jikinki da zafi, kiyi hakuri mana haba dan Allah" hawaye Hajja ta goge ba tare da ta cewa Yawuro Uffan ba, sallamarsu Baffa ne yasa Hajja ta dago da sauri ta sauke idonta a kan Aziza da ta shigo kanta a sunkuye, duk irin kunya na Hajja amma da sauri ta tashi ta rungume Aziza wacce itama ta saki kuka take ji a ranta da ace kisan kai ba haramun bane babu abinda zai hanata bata sha guba ta kashe kanta ba, kuka sukeyi sosai sai da Inna wuro ta dakatar dasu, sannan Inna wuro ta hau tambayarsu ya suka yi a can yankin ja'o ɗin, Baffa Mandi ya ce "babu amfanin a boye muku, gwara a gaya muku gaskiya" Ardo ya ce "tabbas dan wannan ba abun boyewa bane" nan Arɗo ya kwashe yadda suka yi da Malam Shadi ya gaya musu, wani mahaukacin zare ido Aziza ta yi jin bala'in da suke ciki wai sai sunyi aure an sadu dasu kafin su warke! Wa ma zai auri macizai!? Barin ma wanda zai auri Azima ya ji labarin kisan da Banju ya yi tayi a jikinta ai ma babu mai aurensu,in kuwa dole sai hakane sun zama annoba a cikin jama'a barin ma yanzu da Azima bata nan.
Sallallami su Inna wuro da Yawuro suke yi suna tafa hannuwa yayinda Hajja ke girgiza kai tana fadin ita a maido mata da yaranta tana wani irin kuka, Arɗo da Baffa Mandi suka ce Baffa yazo su je wajan Sarki Chubado da mai Unguwa Ori su gaya musu halin da ake ciki, a tare suka fita aka bar Hajja da kuka ita da Aziza, su Inna Wuro suna rarrashinsu.
@@@@@@
Bayani dalla-dalla suka yiwa su Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori yadda Malam Shadi ya shaida musu, Sarki Chubado ya ce
"Tashin hankali, gaskiya Banju ya mana illa dayawa, amma ina da shawara mai zai hana a gayawa mutanen gari halin da ake ciki, idan ya so sai a nemi wanda zai auresu ko da ba zai zauna dasu ba dai da sun samu lafiya sai ya sake su!"
"Nima na fara wannan tunanin a raina ranka ya dade,amma abun dubawan a nan shine wa zai auresu?" cewar mai unguwa Ori, tattaunawa suke yi sosai ta yadda za a shawo kan matsalar amma duk inda aka dafa babu mafita, su na nan suna kan shawara sai ga Sanda da mugun gudu kamar wanda yake gudu a iska yana zuwa gabansu sarki Chubaɗo ya zube yana haki, Sanda jika ne ga Yawuro, Arɗo ya ce
"Sanda mahaukacin ina ne kai? Wannan gudu da ka zo a haka sai kace an kawo mana farmakin yaƙi miye haka? Meke faruwa?" kasa magana Sanda ya yi illa hanyar gida da yake nunawa da kyar ya furta "ADDA AZIZAAA!!" da sauri Baffa ya ce
"Me ya samu Azizan?" ya fada yana miƙewa tsaye, Sanda ya ce
"Baffa Jauro ne ya gayyo duka mutanen yankin nan wai zasu kashe Adda Azima da Adda Aziza wai macizai ne sune suka dinga kashe-kashe sune suka kashe su Ilu mai maganin Maciji dasu Jarman Macizai da Innu Maciji, yanzu haka ma sun saka wuta a gidan Arɗo ƙarami" da sauri su Chubado suka miƙe suna salati tare da al'ajabin ina Jauro yaji wannan maganar? Baffa Mandi ya ce
"Kafff yankin kwana da kewayenta babu munafuki sarkin gulma sama da ɗan Jauro Salti, to amma taya akayi ya ji wannan maganar?" Sarki Chubaɗo ya ce
"Yanzu babu lokaci maida magana muje kar su kashe Aziza" da gudu Baffa ya yi gaba idonsa har yana rufewa, ya rasa matsalar dake tsakaninsa da Jauro,bai san me ya tarewa Jauro ba a rayuwa da baya sonsa baya kaunarsa sam.
Ko da su Baffa suka isa, sun samu gidan Arɗo karami na ci da wuta, ga Hajja a sheme a kasa an fasa mata kai, Aziza kuwa sun ɗaureta a jikin bishiya sai dukanta suke yi duk sun fasa mata jiki, a ranta take kalman shahada dama su kasheta kawai ta huta da wannan rayuwar, ihuuu Baffa ya yi ganin matarsa kwance a sheme a kasa an fasa mata kai ga 'yarsa da aka yi mata daurin mayu ana dukanta, ihun da Baffa ya yi yasa hankalin jama'a dawowa kansa, Jauro ya yi murmushin gefen baki kafin ya matso kusa da Baffa yana magana yana daga murya
"Hakika bai kamata ace daku za a haɗa baki a munafurci mutanen yankin nan ba, (yana yi da sarki chubaɗo da mai unguwa ori) sannan kai kuma Magaji idan ka manta na tuna maka,kaine kace min duk ranar da na gano *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* kaine wanda zaka bani takwabin da zan kashesu! Dan haka yau sunan Aziza gawa,ita ma Azimar da ta bar yankin nan da ace tana nan da yau gunduwa-gunduwa zamuyi musu" murmushi Baffa ke yi hawaye na zuba a idonsa yana yiwa Jauro wani irin kallo wanda ko idonsa baya kiftawa, Jauro ya kuma cewa
"Shin zaku yarda ku rayu da macijiya mai kisa a cikinku?" jama'a suka amsa da a'a, Jauro ya kuma cewa
"Idan kuwa hakane ku ci gaba da dukanta har sai ta mutu!!" Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suna dakatar da jama'a amma ina kamar kara ingizasu akeyi, wani ne da ya daga wani babbar sanda ya roɗawa Aziza a kai jikake kwasss!! Wani ihuuu Baffa ya kuma yi ganin yadda sandar ta shigi Aziza dan har sai da ta girgiza, Baffa ya kalli Jauro cikin jan ido ya ce
"Karka bari na nuna maka waye asalin Magaji!!"
"Zan so hakan" Jauro ya fadi yana dariya, ci gaba da dukan Aziza mutane suka yi, wani gurnani Baffa ya yi mai taken muryan zakin dawa, sannan ya rintse ido ya haɗa wani guguwa mai cike da barkono ya kwashi jama'ar da suke dukan Aziza ya watsar dasu, a take ya yi tsalle daya yaje gabanta yasa hannu ya shafe igiyar da suka daureta igiyar ta tsinke, sannan Baffa yasa hannu ya shafe mata inda suka ji mata ciwo ya kamo kafadunta cikin daga murya ya ce
"AZIZAAA!! NA YARDA DA KEEE!! INA SO NE KI BAR YANKIN NAN!! BANA SO SU KASHEKI ALHALI 'YAR UWARKI TA BAZAMA GARI! INASO KIJE KI NEMOTA SANNAN KI DAKATAR DA ITA,IDAN HAR KU KA HADU KIKA GA B'ARNARTA YA YI YAWA NA MIKI IZINI KI KASHETA ITA DA BANJU!! IDAN KUMA KE MA TAKI TA ZO KARSHE DAMA BA ZAMA MUKA ZO YI BA,IDAN KUMA KIN SAMETA KU DAWO! NINA SAN TA INDA ZANYI MAGANIN BANJU!! AZIZA TAFIIIII!!" girgiza kai Aziza tayi tana wani irin kuka alaman ba zata iya tafi ta bar Hajja da Baffa ba, rai b'ace Baffa ya kara cewa bar yankin nan na ce Azizaaaa!! da gudu Aziza ta yankin jeji dan barin yankin kwana, Jauro ya yi yunkurin binta Baffa ya ce
"Kana bin bayanta zan mata umarni ta kasheka! Ka godewa Allah Aziza ce ba Azima ba ce! Da sunanku gawa gaba daya!! Ni zaku yiwa haka! Sabida su waye yanzu nake fuskartar wannan bala'in!!?"
🍃🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN CE✍🏻
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*ASSALAMU ALAYKUM, SAKO ZUWA GAREKU MASU FITAR MINI DA BOOK DA MASU KARANTAWA BASU BIYA BA, DA WA INDA SUKE GANI SUKE KARA WATSATA A DUNIYA,DA FARI ZAN FARA DAKU MASU FITARWA DAN BABU MASU LAIFI SAMA DA KU! HAUSAWA SUKA CE SAI BANGO YA TSAYE KAƊANGARE K......! DAYAWANKU WASUNKU SUN JAHILCI WANNAN LAMARIN NA CEWA WAI KUDINSU SUKA CIRE SUKA BIYA YA ZAMA NASU MALLAKINSU, YAR UWA TA INA LITTAFI YA ZAMA NAKI? LITTAFI HAKKIN MALLAKAR MARUBUCIYA CE ITA DA TA ZAUNA TA TSARA LABARINTA SANNAN TA RUBUTA TA WALLAFASHI TA WATSA SHI HAR KIKA KARANTA SHI,KE KIN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI,KI KARANTA KI BAR WA MARUBUCIYA ABUNTA, KUNA FADIN YANZU MISALI KUJE KASUWA KU CIRE KUDI KU SIYI ABUN SAI ACE MUKU KARKUYI KYAUTA DA SHI KO KU BADA ARO? TO INASO KI SANI AKWAI BAMBANCI TSAKANIN ABU A ZAHIRI DA SOCIAL MEDIA, YANZU NE AKA SAMU CI GABA KINA DAGA KWANCE A DAKI BA SAI KIN SHA WAHALA BA KINJE KASUWA KIN SIYO LITTAFI BA, A DA KAM WA INDA SUKAYI KARANCE-KARANCE SUN SAN TSADAR LITTAFI DARI BAKWAI DARI TAKWAS KAI HAR DUBU DAYA, SANNAN MIYE RIBARKI FISABILILLAHI DAN KIN CIRE DARI! NAIRA DARI KIN BIYA KUDIN KARATUN LITTAFINA SANNAN KI DAUKA KI WATSAWA MUTANE SAMA DA DUBU DARI DA BASU BIYA BA? ANYA KUWA AKWAI ADALCI A LAMARIN? DUK TALAUCIN MUTUM MAGANA TA DOMIN ALLAH ZAI CE BAI DA NAIRA DARI DA ZAI BIYA YA KARANTA LITTAFINA NE? BAN TSAULAWA BA SABIDA NA SAN KUNA SON LITTAFIN SHIYASA BANSA TA YADDA BA ZAKU IYA BIYA BA, WLH WLH WLH AZIM DA ACE KUN SAN WAHALAR RUBUTU KO A SHAFI DAYA ZAKU DINGA BA WA MARUBUCIYA DARI BIYAR A DUK SAKIN PAGE WLH BAKU BIYATA BA, BALLE KUMA NI DA NA ZAUNA NA TSARA MUKU LABARI NA CE KU BADA NAIRA DARI KACAL! YAKE MAI FITAR MIN DA LITTAFI INASO KI SANI HAKKINA NE,KUMA DUK HAKKIN DA KA RAINA SHI KE GIRMA YA TSOLE MAKA IDO, IDAN HAR BA ZAKI DAINA TOZARTANI BA TA HANYAR WATSA MIN LITTAFI BA TO INASO KI SANI BA ZAN MIKI ALLAH YA ISA BA, AMMA SHURUN DA NAYI WLH SAI ALLAH YA SAKA MIN, MASU CEWA SAI SUN SATO KUMA SAI SUN KARANTA ALLAH YA BAKU SA'A, A AL'ADANCE SATA SUNANTA MA BABU DADI BARE A ADDINANCE HARAMUN NE! SANNAN WANNAN ALLAH YA ISAN DA KUKEJI MARUBUTA NA FADI BA KARAMAN KALMA BA CE WLH,KE IDAN KINA DA TUNANI KI ZAUNA KIYI NAZARI A KAN KALMAN ALLAH YA ISA! SANNAN NA DAWO KANKU MASU KARANTAWA HARDA TAMBAYAR CI GABA,IDAN HAR KINA KAUNAR ALLAH KINA GANIN GIRMAN DARAJAN ANNABI MUHAMMADU SALALLAHU ALAIHI WASALLAM! KI DAINA KARANTA MIN LITTAFI BAKI BIYA BA,KI NEMENI TA LAMBATA KI BIYA NA SAKAKI A PAID GRP DINA IDAN KUMA KIN SAN ZAKI BIYA NE DAN KI WATSA SHI DAN ALLAH BA SAI KINZO GARENI BA🙏🏻, HAKA KEMA MAI YADAWA DUNIYA INA ROƘONKI DA GIRMAN ALLAH DA DARAJAN IYAYENKI KI BARI! BAKI SIYA BA AMMA IDAN KIKA GANI JIKINKI NA RAWA KI TURAMA WASU KEMA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA, ALLAH YA BAKU IKON FAHIMTAR ABUNDA NA FAƊI, WA INDA BASU SON SU CI HAKKI SAI KU NEMI NAKU!*
*PAID.*
🅿️==3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣
Cikin gari ya nufa inda ya kaita asibiti mafi kusa, yana shiga ya ce a bata taimakon gaggawa,inda wasu nurses suka hau masa iskanci a kan ba zasu karbeta ba, hannu yasa a aljinun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya bude ya ciro ID Card dinsa ya nuna musu, suna gani suka hade gefe suna sorry sir, ya ce
"Baku da tausayi ko kaɗan! haka ku ke yiwa jama'a da haka idan yazo da ƙaran kwana sai marar lafiya ya mutu amma kune sanadi! An san likitoci da tausayi dan haka ku gyara,ina mai wannan asibitin ina son magana da shi idan har yana kusa" jiki na rawa suka ce bari su nuna masa office din, har bakin kofar office ɗin suka kaisa, ya kallesu su biyu ya ce
"Ku fara duba yarinyar nan kar ta mutu ina zuwa bari nayi magana da shi zan zo nayi mata dressing da kaina"
"Ok sir" suka fadi shi kuwa ya shiga ciki da sallama.
Amsawa wanda aka yiwa sallama ya yi, ya kalli wanda ya masa sallamar ya ce
"Bismillah ƙaraso ga waje zauna mana" ƙarasowa ya