Showing 21001 words to 24000 words out of 79094 words

Chapter 8 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

5158

raina ya b'aci" gabanta ne taji ya fad'i "dammm", hakanan taji maganar da yayi bai mata dad'i ba, tace
"Yaya Aryan ba mijina bane fa kawai dai saurayina ne" murmushin yak'e yayi yace
"Amma ai aure za kuyi" yana gama fad'an haka yayi gaba ya barta a tsaye, Basma ji tayi zuciyarta ya mata ba dad'i, hawaye ne ke son zubo mata, da sauri tabi bayansa tasha gabansa tace cikin shagwab'a.


"Yaya hawayen zai zubo" dariya ta bashi Amma ya dake, yace me ya kawo hawaye, keda kika gama shan soyayya da mijinki" ai tuni hawayen ya soma zuba, sam bata k'aunar Aryan na fad'an haka, matsawa yayi gab da ita cikin salon muryansa mai kashe jiki yace
"wlh karki kuskura hawayenki ya sauka k'asa, domin saina mugun sab'a miki, hawayan Basma mai daraja ne a gun yayanta Aryan." Da sauri ya tara hannunsa biyu yace
"duk lokacin da kike jin kuka koda bama tare ki rik'e kukan, sai mun had'u kiyi shi akan hannnu na, domin in maida shi cikina".


Murmushi tayi tace
"tom na bari Amma saika daina cemin Yaya Shureym shine Mijina" dariya yayi sosai yace
"dama a kan shi zaki min asaran hawayanki tom karki k'ara" yatsansa yasa ya lakuto hawayenta ya sanya a baki yasha, saida ya raba fuskan da hawaye kana yace
"muje gida".


Sun kama hanyan zuwa gida, Basma tace
"Yaya Aryan wlh da za'a barni dana kwana a gidan ku" Murmushi yayi yace
"saboda me zaki kwana mana a gida?"
"saboda kawai in tashi inga Yaya Aryan, in nayi kuka ya shanye min hawayena" dariya yayi sosai yace
"tom bazan k'ara sha ba, kuma mun b'ata" fuskar tausayi tayi yace
"wlh bamu b'ata ba, muna nan a tare, Yayana ba fad'a" duk suka kwashe da dariya. Cikin farin ciki da nishad'i suka isa gida, a wannan rana kamar karsu rabu ko wanne yana jin kewar d'an Uwansa.


Tun daga wannan rana Yaya Aryan da Basma suka d'inke, rana d'ai-d'ai ne basa fita wurin shak'atawa. Aryan ya kama aiki gadan-gadan wanda a sanadin zuwansa company ya k'ara hab'aka, Deeja kuma tana ta zuwa makaranta, a yanzu soyayya take sosai da Yaya Ahmad a waya, wani lokacin yakan zo hira, Basma ta rako shi, itama dan su sha hira da Yaya Aryan.


Umma da Yaya Aryan sun san soyayyan Yaya Ahmad da Deeja, abinda ke basu tsoro shine, kar gaba iyayen su Basma suk'i yarda ya aureta, domin su talaka ne, Yaya Ahmad ya gyarawa su Deeja gida, anyi fenti an gyara gidan yayi kyau, an zuba musu sabon furniture's. Yaya Aryan ya siyan musu kaya da komai na abincin, da kud'in albashinsa na farko dana biyu, yanzu ko sun fita da Basma shi yake musu siyayya, ya sauya waya ya mai dama Basma nata.


Shak'uwa mai k'arfi ya shiga tsakaninsu, Basma ba tada abokin hira sai Yaya Aryan, video call, charts da kuma zuwa wurin shak'atawa, duk tare suke komai, gaba d'aya ta sauyawa Yaya Shureym, wayansa da kyar take d'agawa, shima da yake yanada wacce yake so sai ya daina damuwa da ita, dama shi abinda yasa ya rik'e wuta, ko zai tusa mata son shi ya samu yana rage zafi da ita.


Bayan wata uku Basma da Yaya Aryan lamarinsu ya wuce tunanin kowa, basu tab'a furtawa juna kalmar So ba, Amma kuma idanun su, sassan jikinsu, jini, b'argo, da tsoka sun gama zama d'aya, sun tabbatar da in ba d'aya ba rayuwa, amma duk da haka zuciyansu yak'i ya basu damar yarda da abida jikinsu ke fad'a musu.


Yau ya kama Lahadi, Yaya Aryan da Basma suna zaune bisa dadduma a wurin shak'atawa, hira suke na nishad'i, wayar Basma ya d'auki k'ara, cikin rashin damuwa ba tare da ta duba mai kiran ba saita d'auka tare da sanya hands free, muryan Yaya Shureym taji yace


"My Basma nazo yanzu ance kin fita kina ina ne? ni fa yau na zo muyita ta k'ara, gaba d'aya kin sauyamin kin shareni, kin barni da missing d'inki, Basma ina cike da shauk'inki mai yawa, dan Allah Basma ki bani had'in kai ko da sau d'aya ne muyi rayuwa, wlh bazan bari kowa ya sani ba, kuma kinga Aure za muyi, inma kina tsoro miyu a k'asar nan saimu fita England muje can mu huta"


Tsoro, fargaba, damuwa ne suka ziyarci Basma, wani zafafan hawaye ke fita a idonta, jikinta ya d'auki rawa, sam bata zaci abinda zai ce mata ba kenan har tabar wayan a hands free, Yaya Aryan mik'ewa Yayi da sauri ya fizge wayan ya bugata da k'asa, komai na waya ya tarwatse, Basma toshe kunne tayi saboda k'aran fashewan wayan, Yaya Aryan sai huci yake kamar wani zaki, sanya takalmi yayi ya fara tafiya, ya rasa ina zai sanya ransa yaji sanyi, ya d'anyi nisa a tafiyan ya shiga cikin mutane, da gudu Basma ta ruga ta rungumeshi ta baya tana kuka, tace


"Yaya Aryan wlh ban tab'a yin wani Abu ba, Yaya Shureym ya sha kawo min farmaki da irin wannan maganar amma nak'i amincewa da k'udurinsa, wlh tun lokacin ya fara fita a raina ni sam bana Sonsa"


Aryan ya b'abb'are hannunta daga jikinsa, ya juyo da ita gabanshi ya tsinketa da kyakkyawan Mari guda biyu, nan da nan hankalin mutane ya dawo gunsu, Ya matsa gab da ita yace
"Basma kalli ido na ki gayamin abinda kika gani a ciki yanzu" idonta na zubda hawaye ta dafe kumatunta tace
"Yaya Aryan kayi hak'uri wlh ban aikata komai ba" cikin fushi da fad'a ya daka mata tsawa yace
"Basma me kika gani a idona ki gayamin" tace
"idonka yayi ja" yace
"Basma kukan zuciyana ne ya bayyana a idona, kina son ki kasheni ko" ya k'arasa maganar muryanshi na rawa, ido ta zaro waje tace
"Yaya Aryan ni bazan kasheka ba" lumshe ido yayi ya bud'e, cikin kasalalliyan murya da rauni yace
"Basma ina sonki, ina k'aunarki" idonsa ne ya kawo kwalla yana gabda zubowa, sai Basma ta tara hannunta tace cikin kuka
"Yaya Aryan nima ina sonka, ina k'aunarka, kaine rayuwata, karka min asaran hawayenka, wanda ban tab'a ganinsa ya fitaba sai yau, ka gau-gauta mayar min da sauran ka adana min su, sai lokacin farin ciki ka fiddamin su" sai hawayen ya d'iga a hannunta, bakinta takai ta shanye su, hannunsa ta kama tana jansa suna tafiya, Yaya Aryan binta yayi da kallon mamaki, gaba d'aya Basma ta bashi mamaki da maganarta. Mutunan dake gurin sai suka fara tafa musu, lallai sun bada salo da kowa yayi sha'awarsu, haka suka bar wurin su ko ajikinsu, kowa na fad'an albarkacin bakinsa.


Bayan sun kama hanyan gida Yaya Aryan yace ta samu guri tayi parking za suyi magana, bata masa musu ba ta samu guri tayi parking, yace
"Basma ina so ki sani tun ranar dana fara tozali dake da kika tofamin miyau, wani Abu ya d'arsu a zuciyana akanki, a da ina tsammanin k'iyayya ne, sai daga bata na gane ashe So ne, ban tab'a jin d'an d'anon So akan wata mace ba, sai akanki Basma, dan Allah Basma ki kulamin da kanki da rayuwanki, domin kece rayuwata"


Farin ciki ne ya lullub'e Basma, yau ta gasgata abinda gan-gan jikinta yake gaya mata akan Yaya Aryan, tace cikin jin kunya


"Yaya Aryan karka damu, insha Allah zan kula maka da kaina da kuma mutunci na, kai ne rayuwata nima, kai kad'ai nake gani a idona na kasance cikin farin ciki, dan Allah ka rik'e min Amanar zuciyata, domin kaine mutum na farko da ya bud'e shafukan So da K'auna a ciki, kuma har abada kai ne mutum na farko kuma na k'arshe ba na biyunka"


Murmushi yayi yace
"Kinsani farin ciki Murmushi na, amma fa ina da kishi, sai ki san yanda za kiyi da Shureym" murmushi tayi tace
"my Aryan karka damu zan gayawa ya Ahmad komai".


Cikin farin ciki suka k'arasa gida, yau Yaya Aryan ji yake ya sauke wani abu mai nauyi a zuciyansa, haka ma Basma yanzu ta tabbatar Aryan nata ne.


*Da dare*
Basma ta tafi wurin Yaya Ahmad ta sameshi yana aiki a system d'insa, sai ta gaishe shi, kana ta samu guri ta zauna tace
"Yaya Ahmad nazo muyi magana ne" cikin kulawa yace
"ina jinki Basma" gyara zama tayi ta soma gaya masa duk abinda Yaya Shureym ke gaya mata, hankalinsa yayi matuk'ar tashi, nan ya shiga niman number Shureym, amma bai shiga ba, cikin yanayi na damuwa ya shiga yi mata fad'a akan meyasa bata gaya da wuri ba, fad'a da nasiha yayi mata sosai kana yace
"ina ganin zan gayawa su Momy a sanya bikin kawai ayi kowa ya huta" da sauri Basma ta kalli Yaya Ahmad bakinta har yana rawa tace
"Yaya Ahmad wlh bana sonsa bazan aureshi ba na tsaneshi" ta k'arasa maganar cikin damuwa...


_*Su Basma da Aryan an shiga lanbun masoya, gaskiya fa salon soyayyanku ya bada kala, koya kuka ce masu karatu...*_


*Rahma Ce*
[8/5, 6:45 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *11.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


Yaya Ahmad yace
"Basma auren ki da Shureym dole za'ayi shi, tunda iyaye sun riga sunyi magana, kuma da an d'aura shikenan zai daina wannan iskancin nashi" hawaye ne ya sauka a kuncinta tace
"Yaya Ahmad bana fatan auren Yaya Shureym ni ina da wanda nake so, kuma in ba a bani shima wlh Yaya zaku rasani, domin zan mutu" a razane ya kalleta yace
"Basma kina da hankali kuwa? waye kike So haka? waye shi kuma d'an gidan waye?" Cikin kuka tace
"ni Yaya Aryan nake so, kuma in ban aureshi ba zan iya mutuwa" a razane Yaya Ahmad ya mik'e tsaye yace cikin kad'uwa,


"a'a Basma, a'a Basma, karki ce za kiyi sanadin rabuwar family d'inmu, kinsan yanda Shureym yake a wajenmu, yaron Yayan Ammi ne, karki ce za kiyiwa Ammi haka, plss ki d'auka mafarki kike da sanin Aryan, ki gaggauta cire Aryan a ranki" a razane ta d'ago ta mik'e tsaye tace
"Yaya Ahmad bazan iya ba, wlh Yaya Aryan nake so" da gudu ta fita daga d'akin tana kuka, lanbun gidan ta nufa taje ta zauna, kuka take kamar ranta zai fita ba tare da sauti sosai ba, Yaya Ahmad cikin sauri ya isketa a gun, dan yasan tabbas ba zata koma part d'in Ammi ba a haka, zama yayi gefenta ya kama hannunta shima a zuciyarta yana gasgata lallai Basma da Aryan ta dace, domin Mutumin kirki ne ga Addini da sanin yakama, a d'an zaman da yayi dashi baiga wani aibu a gunsa ba, sai dai matsala d'aya ne, su Ammi ba zasu yarda Basma ta kawo wani Mijin ba, sai Shureym, sannan kuma Aryan ba d'an kowa bane shi, baya tunanin su Ammi zasu yarda ta auri talaka.


Yace
"Basma nima ina son ki auri Aryan, amma kin san hakan bazai yuwuba a wurin su Ammi" cikin kuka tace
"Yaya zai wuyu tunda ina sonsa, kai zaka taimaka na aureshi kamar yanda zan taimaka maka ka auri Deeja" nisawa yayi yace
"karki damu zanyi wani Abu a kai, ki bani lokaci" sassauta kukan tayi ta share hawayenta tace
"Nagode Yaya Ahmad, Allah ya mana jagora"
"Ameen" yace, kana ya rakata part d'in Ammi ya koma d'akinsu cike da tunani barkatai, da damuwa fal zuciyansa. Lallai yana tausayin Basma kuma yana sonta fiye da kansa. dole yayi k'ok'arin sama mata mafita, da wannan tunanin har barci ya kwashe shi.


*Bayan kwana biyu* Basma sun cigaba da soyayyansu, wanda a yanzu basa b'oyeta ko a gaban waye, Umma ta kad'u sosai data fahimci haka, kiran Yaya Aryan tayi, ta masa fad'a akan yabi a hankali Basma ba tsaran aurensa bane, dole ya iya takunsa, hankalin Aryan ya tashi yace
"Umma wlh ina son Basma ki mana addua, domin Addu'anki yana da matuk'ar tasiri a garemu" Umma tayi ajiyar zuciya, ta sanya musu Albarka, can kasan zuciyarta tana tausayawa yaranta, domin tasan iyayansu Basma ba zasu yarda da auren su Deeja ba, saboda su d'in ba kowa bane, talaka ne futuk.


Haka Yaya Shureym ya k'araci zama a gidansu Basma bai samu fuska a gunta ba, ko ya kirata bata d'agawa, haka ya tattara ya koma Kano.


*To bari na waiwayi wajensu Leema da Meena.*


Leema tana kano a takure take, domin bata samun sakewa sosai kullun tana gida, in zata fita saida kuyangi da dogarai, hakan yasa taji duk zaman Kano ya gundureta, ta fata tunanin komawa Abuja, in sha'awarta ta motsa kamar za tayi hauka, wataran a sace take fita tayi b'adda kama taje su had'u da Jalal, su gama shek'e ayarsu ta dawo gida a gau-gauce. A daddafe ta iya kaiwa har wata hud'u a Kano, yanzu ta gama shirya kayanta da yawa domin komawa Abuja, in kuma ta koma bata tunanin dawowa, sai dai ta rik'a zuwa tana gaishe da iyayenta.


Haka ma b'angaren Meena, Alhaji Ibrahim mahaifinta mutum ne mai sanya ido sosai kan yaransa, hakan ne yasa Meena bata fita saida dalili mai k'arfi, Yaya Jamal ya sanya mata ido shima domin yaga take-takenta akwai rawar kai, Meena in son shan syrup ya motsa mata, rufe kanta take yi a d'aki taita kuka tana buk'atar abinda zata sha, dakyar barci ke d'aukanta, in ta farka shikenan ta dawo dai-dai, hakan yasa ta samu wani shed'ani d'an unguwarsu, suka tsadance yana siyo mata syrup a sace ya kawo mata, sai ta bashi kud'i mai yawa, haka zatai ta maneji dashi harya k'are, gaba d'aya zaman Kaduna ya gundureta, saita soma had'a kaya dan komawa Abuja gaba d'aya, ita sam ba zata zauna a Kaduna ba, waya sukayi da Leema, suka gayawa juna matsalansu, nan take suka yanke shawaran barin gidan iyayensu a gobe in Allah ya kaimu, domin ci gaba da rayuwan freedom da suka fara a England.


*Washe gari*
Da safe Meena tayi sallama da iyayenta, dama ta riga ta sanar musu zata koma Abuja, jirgin k'asa tabi, daga gidan president aka aiko mota ya d'auke ta. Leema ma haka ta sauka a airport, mota daga gidan President yazo ya d'auketa.


Dukansu suna zaune a falon Ammi suna shan farfesun kifi, Ammi ne ta fito tace
"Leema wai ku baza ku zauna guri d'aya ba, baku nan baku can, ni dai naga alama aure kuke so, bari anjima zan samu president in sanar masa, sai a sanya rana mu fara shiri kowa ya huta" bata rufe baki ba Leema tace
"taf wlh Ammi aure ba yanzu ba, munyi k'anana" Meena tace
"gaskiya kuwa aure sai mun kai 30yrs" Basma dai murmushi tayi kawai domin ita a yanzu auren take so amma fa da Aryan d'inta, Momy ce tace
"lallai yaran nan da sauranku, wlh baku isa mu zuba muku ido ba har kukai lokacin da kuke so, aure kam kuma fara shiri" tana gama fad'a ta mik'e ta wuce d'aki, turo baki su Meena sukayi, su a dole basa so, Basma ce ta kallesu tace
"dama dai kun bar wannan shirman, domin dai aure shine riban ko wace mace" tana gama fad'a ta mik'e ta wuce d'aki tana murmushi, kallon mamaki suka bita dashi, daga bisa ni suka tafa Leema tace
"nifa Basma ta sauya, ko ke baki ga a lama ba? Sam ba ji da kai, ba shan k'amshi, duk wani mulki ta aje, anya babu wani abu a k'asa kuwa?" Meena tace
"ita ta sani dai, dan ni ba zanyi aure yanzu ba" haka suka mik'e tare, d'akin Basma suka Shiga sun sameta bisa gado tana chart, ba wanda ya kulata suka haye gadon suka fara hiran yanda suka yi missing zuwa clup, yau sunyi masa shiri na musamman, Basma na jinsu bata ce musu k'ala ba.


Bayan sallan la'asar suka shirya sai gidan hutun Basma, Basma bata bisu ba, sun wuce tare da escot, ita kuma ta wuce wurin masoyinta, suka had'u a in da suka saba had'uwa, suka wuce wurin hutawa domin su samu yin hira mai dad'i. Sai misalin k'arfe shiga na yamma suka yi sallama da Yaya Aryan ta wuce gidan hutun da sauri, domin tana son yin wanka a swimming pool, dan ta kwana biyu bata yi ba.


Tana isa ta samu su Meena a wajen, haka itama ta shiga ta soma wankanta, Leema ce tace
"Besty wai yane naga duk kin sauya ne, ko akwai abinda ke damunki ne?" murumushi tayi a ranta tace
"soyayyan Aryan ya sauya ni" a zahiri kuma tace
"Me kika gani besty, ina nan a Queen Basma kamar yanda kuka sanni" Meena ce tayi caraf tace
"ba wani nan, da akwai abinda ke going wanda bakya so ki gaya mana, sam ban gane sauya wanki akan zancen aure ba, ko kuma soyayyar Yaya Shureym ke fizgarki" nan take Basma ta b'ata rai, bata ce komai ba, ta cigaba da wankanta, Leema da Meena suka had'a ido sai suka kwashe da dariya, hiransu suke bata tanka musu ba, harta gama ta bar su ta nufi d'akinta. Magrib ya gabato ba halin yin rawa, shiyasa ta wuce d'aki dan gabatar da Sallah akan lokaci.


Bayan k'arfe takwas na dare kamar yanda suka saba fita, yau ma cikin shirin doguwar riga masu fidda tsiraici su Leema suka sanya, Basma harta d'auko wata yalolon riga wanda duk rabin cinyarta a waje yake, sai zuciyarta ya karaya saboda da tunawa da tayi da Yaya Aryan, dole yasa ta maida ta d'auko wata doguwar riga mara tsagu, kuma mai kauri ta sanya, duk da haka tana jin wani iri, zuciyarta na gaya mata kamar taci amanar Yaya Aryan, haka dai ta shirya, ta taje sumanta ta sakeshi a bayanta, ta d'aura hular Queen, sai ta fito a Queen Basma tamkar yanda take a da, tayi kyau sosai, haka sukaita d'aukar photo kafin nan suka wuce.


Kamar yanda suka saba, Leema dama Jalal yana Abuja, cikin k'ank'anin lokaci ya bayyana, yazo suka tafi cikin hotel, Leema kuwa cikin group d'in su na mashaya ta nufa, nan suka soma ihu da kalamai masu dad'i, da irin missing d'inta da suka yi, Basma dai yau a d'arare take ta kasa sakin jikinta, duk hankalinta yaki kwanciya gani take kamar Yaya Aryan zai bayyana a gurin, dakewa tayi ta mik'e ta nufi saman step da abokan rawarta, suka fara cashewa cikin salo mai ban sha'awa.


A can gida kuma, Momy ta shiga part d'in Ammi domin ta kira su Meena, zata sanya su aiki a system d'inta, koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login