Showing 72001 words to 75000 words out of 79094 words

Chapter 25 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4662

da sassafe zata je ta gaya wa su Ammi.


*Washe Gari*
Da misalin k'arfe takwas na safe, Deeja ce a tsaye a bakin k'ofa, Yaya Ahmad ya rufe d'aki yana ta masifa akan ba zata fita ba, ita kuma ta kafe saita fita, Waya ya ciro a aljihunsa ya kira Yaya Aryan, yana d'auka suka gaisa yace


"Aryan dan Allah kuzo part d'inmu kaida Basma yanzu pls" bai jira mai zai ce ba ya kashe kiran.


Cike da mamaki Aryan yake bama Basma labari, ba shiri suka fito suka nufi part d'insu Deeja. Nocking su kayi, ya bud'e musu suka shiga suka zauna, sun samu Deeja sai kuka take yi, Yaya Ahmad ya karanto musu abin da ke faruwa, Yaya Aryan ransa ya b'aci sosai cikin damuwa yace


"Khadija ina kika koyi wannan halin, ba irin wannan tarbiyan Umma ta baki ba, Wallahi kin bani mamaki, Allah ya baki kyauta ki raina, wasu na can suna nima da kud'insu ido rufe amma Allah bai basu ba, karki zama mai budulci mana, babu abinda kika rasa a wajen Mijinki, in kuma dan Walid ne ai ke Doctor ce kinsan babu wani illa akan haka, karki sa in raina wayonki"


Ya k'arasa maganar cikin hasala, Basma ta koma gefen Deeja ta dafa ta tace
"Kawata kuma 'yar uwata, don Allah ki sanyawa ranki ruwan sanyi, in dai kula da Walid ne matsalan, na d'auki Alkhawarin zai dinga yini a hannu na, Nono kawai zan kawo shi ya sha, kuma ni zan siya masa abincin yara da ake dama musu kullun dare zan bashi ya rik'a kwana a wurina har ki yaye shi, amma in kin yarda"


Deeja ta rungume Basma tace
"Na yarda kuma na janye kud'urina zan raina cikin, dama ba wai dan bana so bane sai dan ina tausayin Walid"


Nan dai su Yaya Aryan su kayi ta mata nasiha jikinta yayi sanyi, har sai da taji tsanar kanta akan b'atawa Yaya Ahmad rai da tayi tsakanin jiya da yau, tunda suka yi aure basu tab'a samum sab'ani ba, ta mik'e da gudu ta fad'a jikin Yaya Ahmad tana kuka tace


"Ka yafe min Mijina wallahi sharrin shaid'an ne da yaso cin galaba a kaina, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba"


Cikin farin ciki Yaya Ahmad yace
"Ni banyi fushi dake ba, dama burina ki gane gaskiya, kuma Alhamdulillah tunda kin gane, na yafe miki Deeja na"


"Nagode Mijina" sai ta mik'e tace
"Basma taso muje mu had'a breakfast, tunda kunzo, nasan kuma baku d'aura komai ba k'ilama mu muka tadaku a barci"


"A'a, mun tashi ban dai d'aura komai bane" sai ta mik'e suka shiga kitchen.


Yaya Ahmad ya yiwa Yaya Aryan godiya sai suka cigaba da hira, anan Yaya Aryan ya sanar masa da zancen Organization da yake so su Basma suyi, Yaya Ahmad yayi na'am sosai da abun, kuma hakan ya sashi farin ciki sosai, sai suka yanke bayan sati biyu mai zuwa za suyi zaman Meeting, Aryan yace zai kira su Shureym da Jamal ya sanar musu da komai.


Sai wajen k'arfe Goma suka kammala had'a breakfast d'in, suka jera a kafet d'in tsakiyar d'akin, nan suka baje suka yi hani'an, daga bisani Basma ta d'auki Walid a hannu ta suka wuce part d'in su dashi.


*Bayan Sati Biyu*


Su Aryan ne zaune a falonsu, gaba d'aya sun had'u don gudanar da Meeting d'in su. Yaya Ahmad ne yayi Sallama tare da gabatar da bayanai akan musabbabin had'uwarsu, Yaya Aryan ya d'aura da bayanai masu ma'ana, nan duk su Yaya Adam suka yi Na'am da lamarin. Suka yanke shawaran za suyi k'ok'arin Registration d'in k'ungiyar, sannan zasu sanar da Iyayansu akan abinda suka yanke, sun san tabbas zasu samu goyen baya sosai. Sun tsara Ranar taro k'arshen wata a Kaduna, a Babban filin Murtala Square dan K'addamar da k'ungiyar da kuma fara bada Tallafi ga Mahalarta Taron. Yaya Shureym yace "Na d'auki Alkwarin samo Ma'aikata Masu Ilimi wanda suke niman aiki, kuma Masu gaskiya har Mutane Talatin ta b'angaren Kano" "Yaya Jamal yace "Nima zan kawo Mutane Talatin ta b'angare na, kunga an samu Ma'aikata Sittin kenan, sai mu yanke musu Albashi Dubu d'ari-d'ari, sannan zamu ware Mutane Talatin wanda zasu rik'a bincika mana halin da Mutane suke ciki na ko wani Jaha, ta kafafen gidan TV, Radio, 'yan jarida, da kuma sarakuna, dakatai. Mai Anguwa da sauransu. Mutane Talatin kuma za su rik'a had'a mana bayanai ta na'urar Computer, a Manyan Office da zamu bud'e Kano, Abuja, Kaduna. A hankali zamu bud'e Offisoshi a sauran Jahohin" Cikin farin ciki suka tafa masa raf-raf-raf. Yaya Ahmad yace "Alhamdulillah wannan Abu yayi kyau, amma ya kamata a samu Mutane Ashirin wanda za su rik'a supplying kaya daga Kasuwanni, Abinci, kayan masarufi, sutura, keken guragu, keken d'inki dana sak'a, da duk kayan amfani wanda Mutane zasu amfana dashi, sannan a samu Mutane Goma Drivers wanda za su rik'a zirga-zirga a duk States d'in da muka shirya bada Tallafi" Nan ma suka yi mishi tafi, Yaya Aryan yace "Da fatan sunan Organization d'in yayi muku? *QUEEN BASMA ('YAR SHUGABA) FOUNDATION*" nan duk suka had'a baki da hakan yayi musu, domin Basma ta cancanci haka. Yaya Adam yace "Wato ni kun maidani sectary mai shigar da bayanai, to ga bayanan dana d'aukar mana gaba d'aya, amma karku manta akwai wanda tallafin kud'i suke nima, wasu kuma na karatu, wasu aiki, wasu Sana'a da dai sauransu, ya zamuyi dasu?". Yaya Ahmad yace "Wow, wannan magana taka yazo akan gab'a, akwai companoni da Abba yake k'ok'arin bud'ewa a ko wani Jaha a fad'in Nigeria, ina ganin zamu bada sanarwa a ko wani taro in za muyi, don masu niman aiki su turo applications d'in su ta email d'inmu, Ma'aikatan mu masu shigar da bayanai sune zasu rik'a dubawa suna zaban wanda suka can-canta" Yaya Aryan yace "Gaskiya ne, kuma zamu duba duk buk'atan Mutane sai muyi musu akan abinda suka raja'a akai, amma bada Sadakar Abinci wannan wajibi ne a duk taron da zamu yi sai mun bada shi" Nan dai suka k'are magana da yin Addu'a akan k'udirinsu. Sunyi Murna sosai gaba d'ayansu, suka ci suka sha da ciye-ciye,. Daga nan suka d'unguwa zuwa gidan Abba dan yi masa bayanin abubuwan da suka tattauna. Iyayan nasu sunyi matuk'ar murna, sun kuma goya musu baya wanda daga K'aramin organization ya koma Babba, don Abba yace za su sanya hannu a cikin lamarin, hatta makarantu za'a bud'e ta k'ark'ashin k'ungiyar, sannan kuma akwai Scholarships da zai bayar, zai tafi a k'ark'ashin *Queen Basma ('Year Shugaba) Foundation* donmin Tallafawa marasa k'arfi zuwa K'asashen waje don cigaba da karatunsu. Mu samman Abba ya k'ara yanke ranar Meeting gaba d'aya Family akan K'ungiyar, kafin k'addamar da taron k'ungiyar. Su Yaya Aryan sunyi murna sosai kamma Basma da ake komai dominta, sun k'ara Mutane Goma wanda za su gudanar da aiki Akan wanda zasu fita k'asar waje karatu in sun samu Scholarship. Ma'aikatan nasu sun zama guda d'ari kenan, Nan suka watse cikin farin ciki kowa ya koma gidansa. Yaya Aryan da Basma suna zaune a dinning suna cin abinci, Yaya Aryan yace "Babyna kinga yanda k'udurinmu yake ta bunk'asa ko?" Ta d'ago tare da kai loman abinci bakinta tace "uhum ai Yaya Aryan Yau farin ciki ne ya rufe ni, Alhamdulillah Ala Kullu Halin, babu abin da zancen sai Allah ya barmu tare, Myn kai Haske ne a rayuwata" Tasowa yayi ya rungumeta ta baya yace "Allah ya miki Albarka Babyna, ya bamu Zuri'a d'ayyiba yasa Aljanna ta zame mana makoma" Ta amsa da Ameen tare k'ank'ame hannunsa a k'irjinta. Amai ne taji ya taso mata ba shiri, da sauri ta toshe bakinta tana yunk'uri, da sauri ya d'uketa ya kaita toilet dake falo, sai da ta amayar da abincin da taci duka har sai da ta fara kakari babu abinda ke fita sai majina, nan da nan ta gala baita, d'auraye mata jiki yayi ya dawo da ita falo, d'aki ya shiga ya d'auko key mota, ya yafa mata gyale ya kama ta suka fito waje, suka shiga mota Mai Gadi ya bud'e musu Gate ya fice da gudu zuwa Asibiti.


*Rahma Ce*
[8/20, 9:15 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *38.*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


Koda suka isa Asibiti direct d'akin Likita suka nufa, nan take aka fara mata tests da sauran gwaje-gwaje, Likita ya tabbatar musu tana d'auke da juna biyu harna tsawon wata biyu, Yaya Aryan farin ciki sosai ya kama shi, hatta ita kanta Basma farin ciki ya rufeta, nan take Likita ya rubuta musu Magani suka siya a pharmacy na Asibiti suka kamo hanyar Gida. Suna tafi bisa hanya Aryan tuk'i yake a hankali kwance cikin natsuwa, wani irin nishad'i suke ji mara misaltuwa, hannunsa ya d'aura kan cikinta, da sauri ta kalleshi sai ya kashe mata ido d'aya cikin wani salo na murya yace


"Ki kula min da kanki da Unborn Baby d'inmu plss"


Murmushi tayi ta gyara zama tace cikin shagwab'a
"Uhum Ni fa nayi k'arama da Haihuwa dan bazan iya ba Haihuwa ba ance da wahala, tsoro nake ji"


Waro ido waje yayi yace
"To me kike nufi"
"Ni dai tsoro nake ji amma ina son cikin sosai"


Dariya yayi yana buga sitiyarin mota yace
"wow My Basma rikici, bafa wani wahala da kinyi nishi shikenan fa"


Hararan wasa tayi masa tace
"ai su Meena sun bani labarin wahalan da suka sha wajen Haihuwa, ni dai ka tayani da Addu'a kar ya bani wuya Myn" ta k'arasa maganar cikin shagwab'a. Shafa gefen kumatunta yayi yace


"Babyna kullun cikin Addu'a nake miki karki damu, insha Allah zaki Haihu lafiya dashi" murmushi tayi ta amsa da "Ameen". a haka suka isa gida cike da farin ciki.


*Bayan Kwana Biyu*
Suna kwance Basma tayi pillow da hannunsa tace


"Baby ina so karka gayawa kowa ina da ciki, nafi so su ganshi in ya fito"
"Saboda me" ya jefa mata tambaya.


"Kunya na keji"
"Uhum su kunya ko, in ya fito zanga yanda za kiyi"


Mirginawa tayi ta kwanji samansa, ido cikin ido suke kallon juna sai ya sakar mata Murmushi, murgud'a masa baki tayi saiya sanya hannu ya kama bakin, kukan shagwab'a ta fara sai ya saki yana dariya, tace


"Baby ina son shan agwaluma"
"What, ya fad'a da k'arfi, Na manta shi ma"


kuka ta shiga rerawa ita lallai fa zata sha agwaluma, marairaice fuska yayi yace
"Baby ina zan sameshi bama lokacinsa bane fa"


Tashi tayi ta zauna ta fara tsotsan bayan hannunta, a dole tayi fushi, tashi yayi ya zauna shima ya jawota jikinshi, hab'arta ya d'ago yace
"Babyna ki fad'i wani abun wanda kika san bazan sha wuyan nima ba pls" murgud'a masa baki tayi tace
"Farar k'asa da yalo"


Ajiyar zuciya ya saki ya mata kiss a goshi sannan ya sauka bisa gadon yace
"zan fita yanzu na nimo miki, inna siya zan bama driver ya kawo miki domin yau ina da aiki sosai a office"


Bata ce masa kala ba ya shige toilet dan ya watsa ruwa, itama mik'ewa tayi tabi bayanshi, ta iske shi a bawo yana wanka zuwa tayi itama ta shige ciki, dole ya aje nashi wankan yayi mata sannan ya d'aura mata towel ta fito, Murmushi yayi yace
'Wannan unborn Baby ya sa Basma rikici, in da banyi mata wankan ba ta fara kuka' duk a zuciya yake wannan maganar.


Bayan ya idar da nashi wankan ya fito ya taddata ta sanya atamfa d'inkin riga da sket, tayi makeup kamar ba ita ba tayi kyau sosai, tsayawa yayi yana kallonta ta juyo fuska tana dariya tace
"Ya aka yi ne ka zuba min ido ko na sauya maka ne?" girgiza kai kawai yayi ya soma shiryawa, dama ta ciro masa kayan da zai sanya, k'ananun kaya ne da suit, zama yayi ta shirya shi, ta sanya masa riga da wando ta d'aure masa belt ta kuma yi sitokin d'insa, ya d'aura neck tie ta santa masa suit, turarukan sa ta shiga fesa masa har saida ya amshe yana fad'an


"Ya isa haka ko so kike ki k'arar mini Madam rikici"


Murgud'a baki tayi ta matsa ta d'auko gyalenta da hand bag, ta sanya takalmi mai tudu ta d'aura igiyan ta d'auke key motan Yaya Aryan tace
"Muje aikin ko"
Sakin baki yayi yana kallonta, murmushi ta sakar masa ta kanne masa ido d'aya tare da kama hannunsa tana jaaa, suka fito falo masu aikinta ta basu oder duk abinda take so suyi mata, kana ta cigaba da Jan hannunsa suka fice. Bud'e motan tayi ta zauna mazaunin driver bai iya furta komai ba ya shiga gefenta ya zauna ta sanya key ta tada mota ta fice abinta.


Lumshe ido yayi ya kwanatar da kanshi a bayan seat, saida su kayi tafiya mai nisa, tayi parking juyowa tayi a shagwab'e tace


"Baby ko baka so in raka ka zuwa wurin aikin?"


Juyowa yayi ya kalleta sai ya d'aure fuska cikin sigar wasa baice komai ba, hawaye ne ya ciko idonta cikin rawar murya tace


"Don Allah ka yafe min kar fushinka ya in kasance cikin tsinuwar Allah, bana fatan in b'ata maka rai"


Hannunta ya kamo yace
"Waye yace kin min laifi? nasan fa duk Baby d'inmu yasa ki wannan aiki saboda baya son Momyn shi da Abbanshi su rabu" ya k'arasa maganar yana dariya tare da lakace hancinta, itama dariya ta saki ta tada mota suka wuce wurin aikinsa.


Yau dai Basma da Aryan a tare suka yi aiki sai yamma lis suka tashi, kasuwa suka wuce sai da Aryan ya siya mata, farar kasa, yalo, da agwaluma harma da magarya duk ya had'a ya siya da yawa. Cike da farin ciki suka dawo Gida.


*Karshen Wata*
Ana gobe taronsu gaba d'aya Matasan Maza da Matansu suka had'u a Kaduna gidan Dady suka sauka, shirye-shirye suke wanda a lokacin sun gama samun Ma'aikata sun bud'e manyan office a Kaduna, Kano, Abuja.


A Ranar taro anko suka yi Maza fararen shadda Matan kuma atamfa mai ratsin yallow, green da fari. Filin Murtala Square ya cika da mutane domin wannan taro na k'addamar da k'ungiyar *QUEEN BASMA ('YAR SHUGABA) FOUNDATION.* Manyan Mutane Mata da Maza sun halarta da yake abin na 'ya'yan Manya ne, hatta Dady yaje wurin da muk'arabansa, Mai Martaba Sarki shima yaje da Sarkin Zaria ya harta, Abba bai samu halarta ba saboda yayi tafiya, sunyi taro cikin farin ciki da lumana, an baza jami'an tsaro har aka gama babu wani tashin hankali ko hatsaniya, sun raba abubuwa da dama kama daga Abinci, Suturu, Kud'ad'e ga talakawa da nak'asassu, ba k'aramin farin ciki suka sanya a zuk'atan Mutane ba, kowa ya tafi Gidansa yana mai sanya musu Albarka.


Bayan komai ya lafa duk suka koma gidan Dady, suka had'a k'aramin walima a gidan da yamma, sun ci sun sha tare da sada hiran zumunci. Washe Gari ko wanne ya kama hanyar garinsu. *Da Dare* Bayan Sallan Isha'i, Basma na zaune a falo tayi dirshen a k'asan kafet tana cin tuwon Dawa miyar Kub'ewa d'anya, Aryan na gefenta yana cin farfesun kayan ciki tare da jelof din cus-cus wanda yaji kayan lanbu. Basma sai surutu take yi tana cin abinci, kuma wannan ba halinta bane, Yaya Aryan tun yana amsa mata sai yayi banza da ita ya daina amsa mata, d'ago kai tayi ta kalleshi tace "Myn shine ka shareni ko?" "To Basma me zance miki, gaba d'aya kin sauya hali, wannan cikin ya sanya miki dabi'u da ba naki ba, cin abinci kike kina surutu, ta yaya abincin zaiyi miki Albarka?" Marairaice fuska tayi tace "To na bari" "Gwara dai ki bari, in ba so kike muyi fad'a ba, kuma ki ci a nutse dan babu mai kwace miki" Ai bai rufe baki ba ta mik'e a zuciye zata bar wurin, da sauri ya kama hannunsa ya soma lallashinta, da kyar ya samu ta sakko, zaman da zata yi ne ya lura da bayan rigarta ya baci da jini, da k'arfi yace "Babyna me ya kawo jini a jikin ki?" A tsorace ta jawo rigan ta gani, kuka ta fara tana fad'an "Shikenan Yaya Aryan cikin ya zube, na bani" A firgice Aryan ya d'auketa ya fice da ita da gudu, mota ya sanya ta ya shiga, a sukwane yabar gidan. Yaya Ahmad ya fito daga part d'in su zai fita, sai yaga fitan Yaya Aryan daga gidan a guje, shima da sauri ya shiga tashi motar ya rufa musu baya a sittin.


*A Asibiti*
D'akin gaggawa aka shigar da ita, a lokacin ciwon mara ya fara damunta, Addu'a take tana ambaton Allah. A waje kuma Yaya Ahmad ya cimma Yaya Aryan yana tambayan sa abinda ya faru, cikin damuwa Aryan ya labarta masa a takaice, mamaki ya kama Yaya Ahmad yace "Dama tana da juna biyu kenan?" Aryan ya girgiza masa kai alaman Eh. Likita yayi k'ok'ari sosai wajen tsaida jinin, sannan ya d'aura mata drip barci mai nauyi ya d'auketa. Likita ya fito Yaya Aryan ya tare shi, hannunsa ya kama suka wuce office d'insa, Yaya Ahmad yana biye dasu. Duk suka zauna suna sauraren Likita yace "Gaskiya da kyar muka tsawo kan matsalan amma Alhamdulillah cikin bai fita ba, dan haka dole a kikaye dan Mahaifarta ba tada k'arfi, zata samu bed rest, komai yi mata za'ayi game da aikin gida, sannan a kiyaye yawan zirga-zirga da ita, ya zama na ta rik'a natsuwa wuri d'aya har sai cikin ya kai wata biyar daga nan ta fita daga wannan risk d'in" Ajiyar Zuciya Yaya Aryan ya saki tare da godewa Allah, Yaya Ahmad yace "Ina ganin fa jugu-jugun taron jiyan nan shine ya haifar mata da wannan matsalan" dan haka sai mu kiyaye fitanta ko ka maida ta gida wurin su Ammi" Da sauri Aryan ya d'ago kai yace "A'a baza ta ko ina ba zan kula da ita" Yaya Ahmad ya dafa shi yana dariya, kunya ce ya kama shi, ya manta shaf Yaya Ahmad Yayan Basma ne, nan Doctor ya rubuta Magani ya basu sallama inta farka su tafi gida. Sai k'arfe sha d'aya na dare ta farka, cikinta ta shafa ta juyo ta kalli Yaya Aryan tace "Ya fita ko?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login