Showing 63001 words to 66000 words out of 79094 words

Chapter 22 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4645

jiyo a fusace, da sauri ta k'ara so ta fusge wayan ta kara a kunnenta, ita kuma Jidda lokacin tace masa


"My Aryan ka yadani, pls ka soni ko kad'an ne, nima na bar k'asar Monaco na dawo Abuja, ka gaya min inda zamu had'u akwai maganar da zan maka ne"


Basma bata bari ta kai aya ba ta daka mata tsawa tace


"kee ki kiyaye ni ki fita hanyar Mijina, wallahi in ba haka ba sai na miki abinda baki tab'a tsammani ba, Yaya Aryan nawa ne ni kad'ai, babu wata 'Ya Mace data isa ta shiga gonata" bata jira me zata ce ba saita kashe wayan.


Rahma ce
[8/13, 4:09 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *32.*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


Yaya Aryan d'aure fuska yayi cikin sigar wasa, itama ta d'aure fuska kamar za tayi kuka, tace


"bana buk'atar sanin ko ita wacece, ga wayata kayi amfani da shi in kana buk'atan kiran su Umma, dan nima ina da contact d'in kowa har nasu Kaka Malam, Wayanka kuma sai na d'auki mataki akanta sannan zan dawo mana da shi"


Mamakinta ne ya bayyana k'arara a fuskansa, bai yi tsammanin abun har zai kai haka ba, cikin d'aure fuska yace


"Malama me kike nufi ne? yanzu fa kika gama ce min baki sona, to meye ne dan wacce take sona ta kira ni, kawai ki bani wayata ki rik'e taki, dan ban yarda da wannan salon naki ba"


Ya tsine fuska tayi tace
"Yaya Aryan wallahi bazan baka wayan nan ba yanzu" tana gama fad'a ta aje masa wayarta a gefen wani kujera
"gashinan in ka tashi tafiya sai ka d'auka" ta wuce fuuu cikin fushi kamar guguwa.


Dariyan da yake dannewa ne ya kwace masa, ya shiga dariya harda rik'e ciki, Basma ta kara k'uluwa, tafiya take ranta na suya kishi ya gama rufe mata ido, hawaye ke fita a idonta tana sharewa, a ranta tace


"wai wani irin So nake wa Yaya Aryan ne haka? har da zan kasa controlling kaina". Haka ta isa part d'in Ammi, sashinta ta wuce ta kulle kanta, kiran wani security tayi a waya tace


"zan turo maka wata number yanzu kaje MTN office a bincika min waye mai number, kuma da cikakken address d'in mai number".


Cikin girgamawa ya amsa da to sai ta kace wayan. Ta jawo wayan Yaya Aryan, ta d'auki numban Jidda ta turawa security d'in.


Yaya Aryan ya d'auka wayan Basma cike da nishad'i, ji yayi duniyan yayi masa dad'i saboda yanda ya gano babu abinda ya rage Sonsa a zuciyar Basma.


Ammi na daga window d'akinta dake sama duk tana hangen abinda ya faru tsakanin Basma da Aryan, bata jin abinda suke cewa, Amma ta fahimci soyayya ta dawo, murmushi tayi tace a ranta
"masoya Laila da Majnun, dole zan sanar da president domin a zo ayi bikin nan kowa ya huta tunda Basma ta gama idda".


*Washe Gari*


Ammi suna hira da Momy tana gaya mata labarin su Basma, Momy dariya tayi tace


"Aiko wallahi wata ran zaki ga abinda idonki sai kasa gani in dai yaran nan ne"


Itama dariya tayi tace
"bari kawai, naje rufe window d'in ne fa, shine nayi arba da su, so nake Anjima naje na samu President nayi masa magana, don a sanya bikin da wuri ayi a gama kowa ya huta"


Momy tace
"aiko gwara dai ki gaya masa dan ni ba ruwana a ciki kunfi kusa, dan yaranki ne" nan dai sukaita tattaunawa.


Da yamma misalin k'arfe biyar Basma ce ta fito cikin shirin fita, Yaya Ahmad da Yaya Aryan sun jero suna hira da alama fita za suyi, da sauri Yaya Ahmad ya k'arasa wurin Basma Aryan na biye dashi a baya yace


"Queen sai ina haka kuma haka?"


Murmushi tayi tace
"Yaya Ahmad Momy ta aike ni zanje yanzu na dawo" Aryan ne ya kalleta yace


"Bani waya ta in d'auki wani number"


ta kalle shi a tak'aice tace
"Gaskiya ban gama abinda nake da shi ba inna gama zan baka"


"ok, shikenan amma ba ke kad'ai zaki fita ba ko?"


"Ni kad'ai zan fita ko akwai matsala ne?"


"Awkai saboda ban yarda kina fita ke kad'ai ba, in dai kina son fita to lallai sai dai driver ya kaiki"


Bata tanka masa ba, ya mik'a hannunsa Alaman ta bashi key d'in motan, tana turo baki ta mik'a masa, driver ya kwalawa kira ya tawo da sassarfa, Yaya Ahmad na kallon ikwan Allah, Yaya Aryan ya mik'a ma driver key yace


"ga tanan ka kaita duk inda zata je, kuma ka tabbatar magriba ta muku a gida"


Jiki na rawa ya amsa da to, sannan suka wuce. Ahmad yana mata dariya ciki-ciki dan abin nasu ya bashi dariya sosai.


Basma kamar yanda security ya samo mata address d'in Jiddah haka tayi ta ma driver kwatance har suka kai, driver yayi parking tace
"ka jirata nan".


Cikin natsuwa ta isa bakin gate d'in gidan, turawa tayi k'ofar ya bud'e sai ta shiga, mai gadi na zaune a kan kujera Basma tayi masa sannu, sannan tace


"dan Allah ko nan ne gidansu Jidda?"


cikin sauri yace
"kwarai nan ne, bata dad'e da dawowa daga anguwa ba"


Kud'i Basma ta ciro a jakarta wanda bata san adadinsu ba ta bashi, jikinsa na rawa ya amsa yana mata godiya da Addu'a, haka ta shiga cikin gidan hankali ta kwance ba tare da fargaba ko damuwa ba.


K'ofar falon ta tura ta shiga, k'aton falo ne mai d'uke da kujeru da kayan alatu, dai-dai gwargwado sunada kud'i suma ba laifi, wata Mata ta amsawa Basma sallama, cikin natsuwa Basma ta k'arasa ta samu guri ta zauna, Matar ta kafawa Basma ido domin bata wayi fuskanta ba, Basma ta sirinar da kai k'asa ta gaisheta, cikin fara'a Hajiya ta amsa, Basma tace


"Momy Jidda na nan kuwa?"


"tana nan, bari na kira miki ita" nan take ta bud'e murya ta shiga kwalawa Jidda kira, cikin sauri ta fito sanye da k'anun kaya sun matseta tace


"Mama kaya nake sawa fa yanzu na fito wanka"


"To bak'uwa kika yi gata nan, shine dalilin kiran naki"


Da sauri ta karasa falon ta zauna cike da kallon mamaki tak'ewa Basma, cikin murmushi Basma tace


"nasan baki waye ni ba, Amma inna ce miki Queen Basma ce k'ila ki iya sani na"


Washe baki Jidda tayi tace
"laa kece dama Queen Basma Yar shugaba? ai ina jin sunanki, to ya kike?"


"Lafiya lau, dama nazo muyi magana ne akan Mijina Aryan"


Damm zuciyan Jidda ta buga, cikun k'arfin hali tace
"ban fahimceki ba?"


Murmushi Basma tayi ta kai kallonta ga Maman Jidda tace


"Momy nazo wurinku ne badan rigima ba sai domin inyi magana da Jidda ta fita hanyar Mijina don Allah"


Mamaki ya kuma kama Jidda da Mama, Mama tace
"Jidda ko yaron da ki kika min bayanin shi?"


"Eh shi take magana"


"Basma ta cigaba da cewa
"tun jiya bayan munyi waya dake baki fasa kira ba kuma wayar tana hannu na, to na rok'eki da ki fita hanyansa in ba haka ba duk abinda na miki ke kika ja"


Ta d'auki wayan Aryan ta kashe, ta zare sim d'in ta cigaba da cewa
"wannan shine abinda yake had'a ku kuke magana ko? To bari ki gani" sai ta karya sim d'in tayi masa gutsi-gutsi, kana ta ciro sabon layi data sanya aka yi masa regista tare ta sanya masa duk nombobinsa a ciki, na Jidda ne kawai aka cire, sai ta sanya ta kunna tace
"na sauya masa layi"


Jidda mutuwar zaune zayi domin yau ta had'u da wacce ta fita son Aryan. Basma ta mik'e ta ciro bandir d'in kud'i na dubu d'ai-d'ai taje ta aje gefen Mama tace
"Mama ga wannan kici goro na gode" Mama tace


"Allah ya miki albarka, nagode ki gaida manyan"


Jidda ta mik'e ta bi bayanta har suka fita farfajiyan gidan, hak'uri ta shiga bama Basma da kuma alk'awarin komai ya wuce ba zata sake shiga hanyar Aryan ba, dama ita ke sonsa bashi ba. Nan dai suka rabu lafiya har mota Jidda ta raka ta, kana ta koma gida cike da damuwa.


Mama ta kalleta cikin kulawa tace
"ai kinga yanzu kya bari Bashir ya fito auren ki, k'iri-k'iri Yaron nan na Sonki, kika mak'ale ke kina da wanda kike So to yau kin gamu da wacce ta fiki sonshi, dan haka yanzu kya shiga hankalin ki, ni naji dad'in zuwanta ma dan yamin riba, dubu d'ari tabani bashi a rubuce"


Marai-rai ce fuska tayi tace
"Mama ai yanzu ma hak'uri na bata don mu rabu lafiya, bazan iya ja da 'yar President ba, dama can nayi tunanin Aryan yafi k'arfina, baki ganshi bane Mama gayen ya had'u"


"Tafi can ki bani wuri, ni dai ki bama Bashir dama ya fito a yi biki nan ko na huta". Murmushi tayi tace


"Mama kenan, to ki kwantar da kankalin ki nima na saduda".


Basma tana komawa gida taje part d'in Yaya Ahmad ta same su a can, zama tayi suka gaisa ta ciro wayan Aryan ta mik'a mishi tace


"ga wayanka nan na sauya masa layi, kuma numbers d'in dake wancen nayi nasa duk an maida maka su, number Jidda ne kawai bai ciki, kuma nasa an tura ma duk contact d'inka text da cewa wannan shine sabon layinka, MTN office naje acan suka min komai"


Yaya Ahmad yace
"biri yai kama da Mutum d'azun naga text magana ne kawai banyi ba"


Aryan murmushi yayi ya amsa wayan, amma yak'i mika mata nata, tace
"ka bani nawa"


Hararanta yayi yace
"ba yanzu ba" mik'e wa tayi ta ce


"shikenan ka rik'e tunda burina dai ya cika, dan na gama yin abinda nake so, Jidda ce kuma ba zata sake kiranka ba dan nayi tattaki zuwa gidansu" nan ta kwashe labari tas ta gaya musu sannan bata jira me zasu ce ba ta fice tana gunguni.


Dariya duk ta basu Yaya Ahmad yace
"Basma rikici, to kai aiki ya same ka"


Dariya Aryan yayi yace
"zata gama borinta ta daina" nan dai suka cigaba da hira suna dariya.


Da dare Yaya Aryan ya kirata a d'ayan wayanta kamar ba zata d'aga ba, sai taji bazata iya share shi ba, d'agawa tayi tare da yin sallama, ya amsa, sannan suka yi shuru, can k'asan murya yace


"My Basma ina part d'in Yaya Ahmad kizo za muyi magana"


"barci nake ji"
"to shikenan bari naje gidansu Jidda nasan ita zata saurareni"


Da sauri ta mik'e cikin masifa tace
"gani nan zuwa wallahi karma fita" dariya ya kwashe dashi sai ya kashe wayan.


Ta same shi tana d'aure fuska, a hankali ta saki saboda irin soyayya da hira da yake mata cikin farin ciki suka rabu.


Ammi ta samu Abba sunyi magana akan zancen su Basma, Abba yayi farin ciki nan take ya kira Dady da Mai Martaba yayi magana dasu.


*Washe Gari*
Duk zuka zo suka had'u suka yanke sadaki da ranar biki sati biyu mai zuwa, Mai Martaba shine ya biyawa Aryan sadaki, Dady kuma shine zaiwa Basma kayan d'aki, da kuma gyaran gidan da zasu zauna, Abba kuma shine zai had'a masa akwati.


*Rahma Ce*
[8/13, 4:10 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *33.*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


Sun fara shirye-shiryen biki ba kama hannun yaro, Musamman Ummi ta kira wata 'yar Uwarsu daga Maiduguri tazo gyara Basma, an tsumata da turaruka sosai da dilka, dasu kayan k'arin ni'ima, Basma ta k'ara kyau sosai duk in da ta gifta k'amshi ke tashi, in ko ta zauna a wuri sai yayi damshi, an gyara mata sumanta ya k'ara bak'i, silb'i da shek'i yayi kyau sosai.


Ammi da Hajiya Murja sune suka tafi Dubai had'o kayan lefen Basma. Akwati dozin guda sha biyu tank'ame da kaya, Ango ma anyi masa nashi akwati biyar cike da kaya.


Yaya Aryan yana ta shirye-shirye, Yaya Ahmad shima ba baya ba tare suke aiwatar da komai. Dady yasa an gyara gidan da Basma zata zauna, komai sabo aka sanya a gidan. Sweeping pool d'in an sauya ruwan ciki, lanbun gidan an gyara shi sai k'amshi ke tashi.


*Biki saura kwana uku*


Gida ya gama cika da dangi, taron Mutane yafi ko wani taron biki da akayi a baya, Mutanan Kano, Kaduna, Gombe, Maiduguri duk sun hallara a gidan shugaban k'asa, ko wanne ya samu masauki.


Hajiya Kaka da Inna suka sanya Basma a gaba suna mata Nasiha, Basma sai kuka take yi, Kaka tace


"Basma, Aryan Yaro ne mai hak'uri dole sai kin ajiye rashin kunya da tsiwan ki in ba haka ba zaki rik'a shiga hakk'insa"


Nan dai su kaita mata, tashi tayi ta mik'e cikin shagob'a tace


"Ni kun tasani a gaba sai mita kuke min, ai shima ya kamata ku kira shi kuyi masa fad'an, ni kunga tafiya ta"


Kaka tace
"kinga ja'ira ko, saina sanya shi ya tsafala min ke mara kunya kawai tafi ki bamu wuri"


Inna tace
"Hajiya bar Yaran yauzu, wataran nan zata zo wurin ki niman tai mako"


Basma tace
"Allah ya kyauta" ta fice abinta tana dariya.


*Ana Gobe Biki*


K'ayataccen walima suka had'a Maza da Mata a wani k'aton hol, aka kira wani Babban Malami yazo ya bada fatawa akan zamantakewar Aure.


Matan *Siirrin 'ya Mace* sun hallara, haka ma matan *'Yar Shugaba Fan's* sun hallara, Matan group d'in *Khaleesat Haydar Facebook* suma sun zo, matan group d'in *M Khady Fan's* suma sun iso, *QueenMamu novel group* suma sun iso, *real maidanbu novel group* suma sun halarto, *S.I Kaduna Fan's club* suma suna wurin, *Sophy an vc novel* duk suma sun iso.


Wuri ya cika ya batse da mutane kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Amarya ta sanya wani material mai kyau da tsada ta d'aura alkebba a sama, haka ma Ango yasha farin yadi mai kyau ya sanya alkebba a sama. Wuri d'aya suka zauna, wurin yasha decoration, Anci ansha taro yayi dad'i da armashi. Sai misalin Sallan Magrib taron ya watse kowa ya koma gida.


Amarya suna hanyar dawowa, zaune suke seat d'in Baya, Yaya Aryan ya matsa kusa da ita ya leka cikin fuskarta, runtse ido tayi alaman jin kunya, cikin murya mai dad'i yace


"Insha Allah gobe In Allah ya kaimu, uwar haka kin zama tawa ni kad'ai"


Murmushi tayi ta bud'e ido sai ya sauka akan nashi, ido d'aya ya kashe mata, sai ta rufe fuska da hannayenta tana dariya, k'unshin da aka mata a hannu ya kurawa ido kamar zai leshe su, dan sunyi masa matuk'ar kyau, cikin kasalan jiki ya kai hannunsa kan zanan, ya shiga binsu a hankali, nan take jikin Basma yayi sanyi kasala ya diran mata, cikin sauri ta cire hannun a fuskanta ta duk'un-k'une su cikin alkebbanta, murmushi yayi mai sauti.


Kansa ne yaji ya rasa masa, runtse ido yayi ya bud'e idonsa sunyi ja, janye jikinsa yayi gefe ya d'aura bayansa jikin kujera, runtse idonsa yayi yana ambaton Allah a zuciyansa, a hankali ya fara samun natsuwa, tunani ya shiga yi
"me yasa nake jin irin hakan kwana biyun nan?" basarwa yayi ya jawo wayansa ya nima wayar Yaya Ahamd suka fara magana akan hidimar biki.


Basma ko ta mak'ure gefe d'aya, Allah-Allah take su isa gida ta fita a motan, gaba d'aya hankalinta a tashe yake, abinda Yaya Aryan ya mata duk ta susuce.


"lallai akwai aiki a kaina, bazan k'ara shan wani Magani ba"
Zancen zucin da take yi kenan.


*Washe Gari*


*_Ranar D'aurin Aure_*


Ya kama ranar Asabar Weekend, da misalin k'arfe (10am) na safe, Babban Masallacin Juma'an dake Abuja ya cika da Jama'a, Manyan Mutane ke wurin, hatta daga k'asashen waje Abokan President sun zo d'aura auren su Basma. Unguwar ya cika da motoci da Mutane, Ni kaina na kasa yanda zanyi na shiga Masallacin d'auko muku rahoto, Yaya Ahmad na hango dasu Yaya Naufal d'auke da sink'in goro suna k'ok'arin shiga ciki, da k'arfin na bud'e murya na kira Yaya Ahmad, da sauri ya juyo, mik'awa Yaya Jamal sink'in goron yayi suka shiga ciki, yazo guna da sassarfa yace


"Anty Rahma hala Mutane sun hana ki shiga d'auko abinda ke wakana a cikin Masallacin?"


Murmushi nayi masa nace
"kwarai kuwa, taron Mutanan ne suka min yawa kamar an sauko Sallan idi, yanzu dai bari nabi bayanka ko zan samu hanyar shiga"


Dariya yayi yace
"Ai dole a baki hanya dan in bakya wurin nan d'aurin auren bazai yuwu ba, domin kece jagoran komai, dan haka biyoni a baya".


Haka nabi shi a baya, Mutane na darewa suna bani hanya sai gaisheni suke tamkar sun ga Sarauniya. lol🤪


Muna shiga waliyyan Ango da Amarya suka fara siga, nan take aka d'aura auren


*Aryan Aliyu da Basma Mukhtar Bukar*


Bisa sadaki dubu d'ari lakadan ba ajalan ba, nan a kaita sanarwa a ka soma raban goro da Sweet da dai duk abin da ya shafi Al'adan bahaushe.


A can gida kuwa Yaya Ahamd ya kira Deeja ya shaida mata an d'aura, da sauri ta fita ta shaidawa Mutanan gidan nan fa Mata suka fara sakin gud'a. Amarya na k'urya d'akin Ammi su Meena na tare da ita, ta sha kwalliya tayi kyau har ta gaji, leshi ta sanya Marron da kwalliyan fari, anyi mata d'auri na Amare na head, sarkan gold da dan kunne ta sanya tare da abun hannu sai kyalli suke, k'amshi ke tashi a jikinta, duk inda ta juya sai an kalleta, black beauty yayi fa, nan take suka dinga d'aukarta photo suna turawa a WhatsApp group-group, harda su Instagram.


Fitowa suka yi da ita 'Yan Uwa suka mai mayeta sunata gud'a, masu d'aukarta photo nayi, Basma tunda taji an d'aura Auren wani sanyi ya ratsa zuciyarta, hawaye ne ya sauka kuncinta tana murmushi, Leema ce ta goge mata tace


"Meye haka kuma karki b'ata kwalliyanki"


Murmushi tayi tace
"ko na b'ata za'a sake min wata, ku barni nayi kukan farin ciki na samu cikar burkina"


Juyawa suka ga tayi ta nufi cikin falo, haka suka rufa mata baya, d'aki ta koma ta cire head d'in ta d'auko sanlaya ta shifid'a ta kuma sanya hijab, dama tana da Alwala sai ta kabbarta Sallan Nafila na Walha, raka'a biyu tayi, ta jima a sujuda na k'arshe tana Addu'a, bayana ta d'ago tayi lamuzi tare da sallama. Ta jima a zaune tana yiwa Allah kirari, Addu'a kuwa tayi su da yawa.


Bayan ta idar ta Shafa a'ddu'an tare da goge hawayan da ya sauka kuncinta, farin ciki ya gama rufeta ta mik'e ta maida sallayan da hijab mazaunin su, wasu kayan ta sauya, mai kwalliya ta gyara mata fuska aka kuma d'aura mata wani head d'in, wannan karan shadda ta sanya doguwar riga tasha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login