Showing 60001 words to 63000 words out of 79094 words
Chapter 21 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt
faruwar lamarin tun daga farko har k'arshe, kukan su Meena ne ya k'aru a falon, Malam ya nisa yace
"lokacin da Ameena ta aiki Khalil kasuwa, har yamma bai dawo ba" daganan ya cigaba da basu labarin yaruwansu gaba d'aya bayan ba Khalil, Umma ta d'aura itama da irin rayuwar da suka yi da Abban su Aryan, har zuwa had'uwar su da Basma da irin taimakon da tayi musu, har Auren su Deeja da Ahma, babu abinda ta rage hatta soyayyan Basma da Aryan ta bada labari, tana gama labarin ta cigaba da kuka.
Falon ne yayi shuru na tsayin minti, Umma ta taso wa Basma da mikin rabuwa da Aryan, ta mik'e ta isa wurin Umma ta d'aura kanta misa cinyarta, ta cigaba kuka mai kashe zuciya.
Abba yace
"Alhamdulillah, Basma kece silan komai, sanadin ki gashi dangi mun had'u, Allah ya muku Albarka gaba d'aya" duk suka amsa da "Amin".
Abba ya gabatar da duk Familynsa masu Malam Faffa, sai suka sanyawa zuri'a Albarka. nan dai suka cigaba da hira, yara suka fita zuwa farfajiyar gidan, suka baje kolinsu a acan, Aryan dai yana tare da Ahmad suna hira, su kuma su Yaya Naufal b'angaren hiransu daban dasu Yaya Shureym, matan kuma duk suna tare, harda Safeena yanzu ta zama 'yar gida.
*Da Yamma*
Mai Martaba da Abba, Dady da Malam duk suna hira gaba d'aya, Mai Martaba ya kalli Abba yace
"Alhaji Muktar nifa naga iri ina so in za'a bani" Abba ya kalle shi cikin rashin fahimta yace
"ban fahimce ka ba" Mai Martaba yayi murmushi yace
"K'anuwar Ibrahim nake bara ko zaku bani aurenta" cike da farin ciki Dady ya kalli Abba yace
"kasan me yake nufi kuwa? Aishatu Mahaifiyar su Aryan yake maga fa" Abba yace
"Alhamdulillahi, abu yayi kyau, ai ga malam nan a kusa sai muyi magana" cikin kawaici na Manya Malam yace
"wannan ai maganarku ne, Aishatu k'anwarku ce ku zaku yanke hukunci, ni nawa sai dai nasa Albarka" farin ciki ne ya rufe su dajin kalaman Malam, nan suka yanke hukunci hatta sadaki suka yanke, suka sanya rana mako mai zuwa in an sakko Sallan Juma'a a masallaci, Abba yace
Zuwa gobe in Allah ya kaimu, sai mu kirata mu tattauna da ita dan ta sani, nasan ba zata k'i amimcewa ba".
*Washe gari*
Haka duk suka had'u suka ci abincin safe, da yake su Umma sun kwana gidan president, bayan sun kammala, Abba ya kira Umma yana so suyi magana, ba musu Umma tabi yansa, suka zauna a falonsa na sama, Umma na k'asa gefe, Abba na zaune bisa kujera, Dady ne ya shigo shima ya zauna, ta kuma gaishesu, Abba ya nisa yace
"wata magana ce zan sanar miki ban sani ba ko zai miki dad'i, mun yanke shawara ba tare da saninki ba, Mai Martaba yazo mana da wata magana akan yana son ya aureki"
Da sauri Umma ta d'ago kai tare da dafe kirjinta tace
"Ni kuma?" Dady yayi dariya yace
"meye abin firgita, ke d'in fa, kuma mun amince har ya bada sadaki, mun yanke Juma'a mai zuwa zamu d'aura auren ku bayan an sakko Sallan Juma'a" sun kuyar da kai tayi cike da jimami dajin kunya tace
"shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa" Abba da Dady suka had'a ido tare da sakar ma juna murmushi suka ce "Ameen" Abba yace
"tunda kin amince, mungode Allah ya miki Albarka, zaki iya tafiya" mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta musu godiya ta fito.
Da misalin k'arfe biyu na rana, Dady suka shirya tafiya, yace lallai dasu Malam zai tafi, haka suka shirya hard'asu Umma dasu Aryan, duk suka tafi Kaduna, Deeja banda ita da Meena saboda suna jego, harda kuka lokacin da zasu tafi suka yi, Leema tabi Mijinta Yaya Jamal, Kaka Ma'u ma ta bisu don ta samu K'awa Inna, tace ba zata zauna Abauja ba. Mai martaba ma ya tafi da iyalinsa, domin yin shirye-shiryen bikinsu da Umma, Yaya Shureym ma ya tafi da Safeena Kano.
Gidan kowa ya watse, sai su Ammi da Yaransu. Washe gari Abba ya wuce Germany domin halarta wani taro a k'asar.
Basma ta koma part d'in Ammi, hankalin kowa yanzu a kwance yake, Yaya Ahmad ya cigaba da zuwa aikinsa, Yaya Naufal ma haka, Meena kuwa anata jego.
*Da dare*
Yaya Ahmad yana zaune da Basma suna cin abinci a plet d'aya, ya kalleta yace
"Basma wannan irin santi da haka, ashe Deejana ta iya girki sosai?"
Murmushi tayi tace
"wallahi Yaya Ahmad ta iya sosai, kuma kasan haka Umma ta iya girki fa, fried rice d'in nan yamin dad'i, yau zan cika cikina sosai"
"ki dai ci a hankali kar kici ki kasa tashi da yin numfashi, kin san ance ana so a kasa ciki kashi uku ne, kashi na farko na abinci, kashi na biyu na ruwa, kashi na uku kuma na numfashi" murmushi tayi tace
"hakane kuwa Yaya Ahmad, nima wasa nake maka dana ce haka" nan suka cigaba da cin abincin har suka kammala.
Yaya Ahmad yace
"Queen Basma" da sauri ta d'ago ta kalleshi tana murmushi tace
"ya a kayi ne Yayana" yace
"kawai naji kiran sunanki ne, ina so ki gayamin yaushe zaki koma gidan Shureym" a razane ta mik'e tace
"komawa gidan ya Shureym kuma?" yace
"yes, mako guda aka baku, ku sasanta kanku, kuma week d'in ya kusa k'arewa, ina tunanin kun gama sasantawa ai"
Hawaye ne ya sauka a kuncinta, ta koma ta zauna bakin gadonta tace
"Yayana wallahi bana son zama dashi, amma in har abinda iyayenmu suke so kenan, zan koma in dai ransu zai yi musu dad'i"
Yaya Ahmad ya nisa yace
"zanyi wani abu akai" da sauri ta d'ago kai tana girgiza kai tace
"a'a Yaya Ahmad kar kayi komai akai, haka Allah ya tsaramin rayuwata, kuma ni yanzu bana son Yaya Aryan ma" sai ta k'arasa maganar tana kuka.
Murmushi yayi yace
"me Aryan ya miki da har zaki daina Sonsa lokaci d'aya?"
Cikin kuka ta bashi labarin abinda yayi mata, dariya Yaya Ahmad yayi sosai yace
"Basma har yanzu ke Yarinya ce" b'ata fuska tayi tace
"Dariya ma kake min ko?" ta k'arasa maganar cike da shagwab'a, toshe bakinsa yayi yace
"nayi shuru, na daina dariyan yi hak'uri yar k'anwata, kinga bari naje na kwanta dare yayi, da safe kisa masu aiki su kawo mana tire d'in abincin nan"
"to Yaya Ahmad Allah ya bamu alkhairi" ya amsa da "Ameen" ya wuce.
*Ranar Juma'a*
An d'aura auren Sarki Abdallah da Aisha (Umma) bisa sadaki dubu Hamsin, sun dawo gida, an yi walima da ciye-ciye, kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Hajiya Sa'a tak'i zuwa saboda bak'in kishi, Hajiya Murja kuwa da ita aka zo Abuja dan shagalin Biki, gidan Umma cike yake da 'yan Uwansu na Gombe, ko da suka ji labarin ganin Dady sunyi murna sosai.
*Washe gari*
Yaya Ahmad ya samu Mai Martaba a side d'in da President ya ware masa, ya zauna ya gaishe yace
"Baffa nazo wurin ka ne muyi wata magana" Mai Martaba ya gyara zama yace
"ina jinka Ahmad" Yaya Ahmad ya risina kansa k'asa yace
"Abba akan batun auren Basma da Shureym ne, a gaskiya Abba Basma bata son zama da Shureym saboda tana da wanda take so, tun farko Abba ya matsa mata akan sai ta auri Shureym, to ni ina niman Alfarma dan Allah Baffa kayi wani Abu a kai, domin itama ta samu farin ciki a rayuwarta kamar yanda kowa yake rayuwan farin ciki, nasan Basma ba zata tab'a cewa a raba auren nan ba, saboda yin biyayya a gareku, amma kuma Baffa wallahi tana cikin damuwa" ya k'arasa maganan cikin fuskan tausayi.
Mai Martaba ya jinjina lamarin yace
"ai dama munce suje su sasanta kansu, gashi mako gudan ya cika, kaje karka damu zanyi wani abu akai" Yaya Ahmad ya risina yayi masa godiya kana ya fita.
A ranar aka wuce da Umma kano gidan Mai Martaba Sarki, gaba d'aya Matan gidan suka tafi Kano, Mazan ne kawai suka bari, Dady ya koma Kaduna, president ya cigaba da gudanar da ayyukan sa.
Umma ta samu tarba sosai wajen dangin su Ammi, anyi taro an watse mutanan Kaduna sun koma, na Abuja ma haka, Aryan dole ya dawo Abuja, Abba ya bashi wani part da zai zauna saboda gidansu ba kowa a ciki sai masu gadi, Malam da Inna suna kaduna, Umma kuma ta koma Kano. Aryan baiso dawowa gidan ba, saboda yasan Basma tana nan.
*Rahma Ce*
[8/12, 7:13 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*
_page_ *31.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*
Mai Martaba ya had'a duk kan iyalinsa ya gabatar musu da Amaryansa Umma, sai kuma ya gabatar da Matar Shureym Safeena, Hajiya Sa'a k'iri-k'iri ta nuna kishi sosai akan Umma, Mai Martaba ya ja mata kunne sosai da gargad'i, dole ta shiga taitayinta dan tasan halinsa sarai.
Shureym ya zauna a cikin gidansu na sarauta kusa da part d'in Yaya Adam, d'akin Safeena yana kallon d'akin Basma wanda ya dad'e a kulle bata tab'a zama a ciki ba, Shureym kullun yana sanyawa a gyara d'akin Basma tamkar tana zama a ciki tsaf yake.
*Bayan sati biyu*
Komai yana tafiya yanda ya kamata, Umma ta soma sabawa da zaman gidan sarauta, suna shiri sosai da Hajiya Murja, Mami ganin ba Sarki sai Allah dole ta sauko suka had'a kai suna zaman lafiya. Mai martaba yaji dad'i yanda suka had'a kai, mulki kuma yana tafiya yanda ya kamata.
*Da dare*
Mai Martaba ya kira Yaya Shureym domin suyi magana, Mai Martaba yace
"na kira ka ne akan maganar Basma, wai shin kun dai-daita kuwa? dan yanzu ana niman wata guda kenan dana ce na baku sati d'aya"
Sunkuyar da kai yayi k'asa ya soma sosa k'eya, yace cikin inda-inda
"am am Baffa muna kan dai-dai tawa dan ina waya da ita" cikin nuna ko in kula Baffa yace
"Kira ta yanzu a wayanka inji, ka kuma sanya min a hands free"
Gaban Shureym ya buga damm, cikin tsoro yace
"Baffa a k'ara bani lokaci yanda zamu samu damar fahimtar juna" wani kallo Baffa yayi masa sai da cikinsa ya kad'a, cikin d'aure fuska yace
"Nace ka kira min ita" jikinsa ya d'auki rawa ya ciro wayar ya danna number ta, Kiran farko taki d'auka harya katse, acan kuwa Basma tana kallon kiransa tak'i d'auka, ya sake kira cike da Masifa ta d'aga ko sallama babu tace
"Wai Yaya Shureym meye damuwanka da nine? dan Allah ka rabu dani ka fita rayuwata, baza ka tab'a samun yanda kake so ba dan kasan bana Sonka, Abu d'aya zai za na koma d'akin ka, shine in su Abba sun nuna suna son haka, dan bazan tab'a bijirewa buk'atansu ba" saita fara kuka, jikin Yaya Shureym yayi matuk'ar sanyi, bai iya furta mata komai ba ya kashe wayar.
Mai martaba yayi ajiyan zuciya yace
"Shureym ka b'ata rawanka da tsalle, da ka rik'eta tun farko da Amana da tuni ta manta da k'iyayyar bata son ka, dan haka yanzu ga wannan farar takardan da bairo, in har na isa da kai kuma ni d'in Uba ne a gareka to ka rubuta mata saki d'aya a ciki, idan da rabon zaku zauna kafin ta fita Idda in ta sauko sai ka maidata".
A razane Shureym ya kalli Mahaifinshi cikin kid'ima yace
"Dan Allah Baffa karka min haka, wallahi ina son ta, zan shiga mawuyacin halin inna rasata, plss Baffa ka tausayamin" sai ya soma zubda hawaye.
Baffa ya tausaya masa amma sai ya danne damuwansa yace cikin Natsuwa
"Shureym na riga na gama magana, yana da kyau itama Basma tayi rayuwar farin ciki, kamar yanda da farko kaje ka auri wanda kake so ba bada sani na ba, dan haka itama a bata dama ta auri wanda take So"
Shureym yana kuka ya d'auki paper da bairo ya rubuta kamar haka
"Basma na sake ki saki d'aya, ba dan bana sonki ba sai dan ki auri cikar burinki, in dai hakan zaisa ki farin ciki, ina son ki Basma Son da babu adadi, da kuma shi zan mutu a raina".
Yana gama rubutawa ya mik'e ya fita daga falon yana kuka, Baffa yana kiran shi amma ina yayi gaba cike da tashin hankali.
Part d'insa ya wuce, ya shiga a birkice, Safeena na ganinsa haka, ta isa inda ya zauna ta shiga tambayansa, kuka yake wiwi yana dafe da Kansa, cikin kuka yace
"Baffa yasa na saki Basma saki d'aya" salati ta saki a fili, a zuciyarta kuma tad'an ji dad'i, wani b'angare kuma ba taji dad'in haka ba, lallashinsa ta shiga yi, da kyar ta samu yayi shuru.
Mai Martaba ya d'aga waya ya kira Dady suka gaisa yace
"Dalilin kiranka shine, Shureym ya saki Basma saki d'aya, ga takardan a gabana, dan haka ka kira Mukhtar ka gaya mishi, domin wallahi kunyansa nake ji" salati Dady ya saki yace
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu duka" nan suka yi sallama suka aje kan wayan.
Dady ya sanar da Abba, Abba bai ji dad'in sakin ba, yaso a lallab'asu su shirya su cigaba da zaman su, Addu'a ya musu da fatan Alkhairi.
Abba ya tara iyalensa a falonsa ya sanar musu da sakin da Shureym yayi wa Basma, nan take farin cikin ya bayyana a zuk'atan su Yaya Ahmad, Ammi da Momy ma ba suyi b'acin rai ba, face suka sanyi fatan Alkhairi akan lamarin, Basma wani hawaye ya sauka kuncinta, a ranta tana jin ba dad'i da kuma farin ciki, abin da ya sata farin ciki saboda ta rabu da Shureym kuma bai samu cikan burinsa akanta ba, na biyu kuma damuwar da ta shiga saboda Aryan ya daina sonta *a nata tunanin kenan.*
Gaba d'aya dangi kowa yasan da mutuwar Auren Basma, Yaya Aryan koda yaji labari murnushi kawai yayi, a ransa yace
"dama nasan zaki dawo gareni, domin insha Allah Basma tawa ce ni kad'ai".
Basma ta fara Idda, koda dai Shureym bai kusanceta ba amma babu wanda yasan haka, kullun tana gida sai dalili kesa ta fita, tunda Aryan ya dawo gidan basu tab'a had'uwa ba saboda yayi duk abinda zaiyi dan kar su had'u.
Yaya Shureym ya lalace yayi bak'i saboda damuwa, Iyayensa saida suka koma suna tausayinsa, hatta Mai Martaba sai da ya tausaya masa, lallashinsa suke tayi da yi masa Addua, a hankali ya soma sabawa da halin da yake ciki ya soma walwala, Safeena na iya k'ok'arinta wajen faranta masa rai, hakan yasa ya dangana ya barwa Allah, amma a ransa bai hak'ura da ita ba gani yake kamar zata kirashi su dai-daita kansu kafin kwanakin cikar iddarta. Lokacin da Iddarta ta cika, a sannan ne yasan tayi masa nisa, sai ya soma k'ok'arin cireta a rayuwansa.
*BAYAN WATA UKU*
Basma ta kammala Idda, ta zama free ba data nauyin kowa akanta, Yaya Ahmad shine abokin hiranta dasu Meena, kullun suna had'uwa a part d'in Momy ko Ammi su sha hiransu, wani lokacin su sanya waka Basma ta sha rawa ta tuna da rayuwarsu na da lokacin da take Queen Basma.
Yau Basma ta tashi cikin nishad'i, da misalin k'arfe biyar na yamma ta isa wurin shak'awata na cikin gidansu dake can baya, ta zauna wurin furanni da bishiyoyi, system d'inta ta kunna ta fara buga Game, ga lemu mai sanyi tana sha sanyin na ratsata, iskan wurin ya gauraye da kamshin turarenta, sai yana busawa da k'amshi mai dad'i.
Yaya Aryan hakanan yau yaji yana son yaje gurin shak'atawan, dan tunda yazo gidan bai tab'a zuwa ba, ya fito daga part d'inshi cikin shigan k'ananun kaya, ga suman kansa yayi luf-luf, robali yasa ya d'aure gashin ta baya saboda sumar tayi yawa bai aske ba, wani k'amshi yake fita a jikinsa mai dad'i, yayi matuk'ar kyau, a hankali yake tafiya rik'e da goran swan harya isa gurin, da farko bai lura da ita ba yazo zai zauna a wani kujera dake fuskantar na Basma nesa suke da juna, d'ago kan da zaiyi sai idonsu ya had'u dana juna, dama tun isowansa k'amshin turarensa ya ziyarci Basma, ta bishi da kalli har yazo zai zauna shine suka had'a ido, ya tsine fuska tayi ta kauda kanta ta cigaba da Game d'in ta.
Aryan ya zauna yana mai yin murmushi, swan ya bud'e ya kurba ya maida murfin ya rufe, wayansa ya ciro ya fara dannawa yana yi yana satan kallonta, haka ita tunda ya zauna taji ta ta kura a wurin, tana yi ta d'ago kai, ai bata an kara ba ta d'ago kenan ya d'ago suka had'a ido, Yaya Aryan ya sakar mata murmushi, b'ata fuska tayi ta murgud'a masa baki, murmushi ya kuma yi, rufe system d'in tayi ta mik'e a zuciye zata bar wurin.
Da sauri ya mik'e yace da k'arfi yanda zata jishi
"My Baby Basma" cak ta tsaya ta kasa tafiya, hakan taji jikinta ya mutu, a hankali ya isa bayanta ya tsaya yace
"My Lovely fushin me kike dani?" Idonta ne ya kawo kwalla amma saita dake ta juyo cike da tsiwa tace
"kai kuma waye? ko zaka min bayani dan ban wayeka ba"
Yaya Aryan yaji ransa ya b'aci yace a ransa
"wato yarinyar nan ko me a kayi mata saita rama" a fili kuma ya dake yace
"uhum na gane manufarki, kuma banga laifinki ba tunda nine na fara miki haka, amma ni a wancen lokacin akwai dalilin da yasa nayi miki haka" Kallonsa tayi ido cikin ido tace
"wani irin dalili ne Yaya Aryan da zaka nuna baka sanni ba? ai ko da akwai aure a kaina kasan Sonka na raina, abinda ma ya bani haushi da mamaki shine, ka san bana k'asar nan, anata niman ina naje, dawowata kenan zuciyata ta kaini gurin, Kai ne Mutum na farko dana fara had'uwa dashi kafin in isa gida, mai makon kayi murna da gani na amma sai ka kware min, ka nuna baka sanni ba, ai ko albarka cin sanaiya ka nuna min inma ba zaka nuna mun dan soyayya ba"
Ta k'are maganar hawaye na zuba mata, murmushi yayi na rashin jin dad'in abin da yayi mata, yanzu ya gane yayi kuskure, hak'uri ya shiga bata da kalamai masu dad'i, d'aga masa hannu tayi tace
"ba kada kalaman da zaka gaya min har suyi tasiri a raina yanzu, kamar yanda ka daina sona nima na daina sonka"
Juyawa tayi zata tafi, wayar Yaya Aryan ya shiga k'ara, yana dubawa yaga Jiddah ce, da sauri ya d'aga ya bud'e murya yanda Basma ta zaji abinda zai ce, yace
"hello Jidda ya kike kwana biyu"
Ai basma bayi step Biyar ba ta