Showing 45001 words to 48000 words out of 79094 words

Chapter 16 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4660

take shiryawa ne*😳🤭


*Rahma Ce*
[8/9, 5:48 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *22.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


Da misalin k'arfe uku na dare, Basma ta tashi ta gabatar da sallan Nafila, Addu'a tayi da niman yardan Allah akan abinda take shirin yi, haka ta zauna tayi ta tasbihi, har gabanin sallan Asubahi, kana ta k'ara yin alwala tayi raka'atanil fijri, sannan ta gabatar da sallan Asubahi, azkar ta karanta, sai ta tashi ta nad'e sallaya, idonta a rufe ta fad'a gado, murmushi ta saki, a ranta tace


"ashe ma Yaya Shureym mugun wawa ne, da nasan haka yake da saukin kai da tuni nasan abinyi, wai su sun d'auka da gaske period nake, hmm kana tunanin cin zarafin da kayi min da sharrin da kamin kasha ni masilla ne, wlh saina d'auki fansa mafi muni a gareka, azzalumi kawai" tsaki taja saita gyara kwanciya, cikin k'ank'anin lokaci barci mai nauyi yayi gaba da ita.


Sai k'arfe goma na safe ta farka, wanka tayi ta shirya cikin riga da sket English wears, ba wani makeup da tayi, fitowa tayi taga su Yaya Shureym suna Karin kumallo, murmushi ta sakar musu saita k'arasa wurin taja kujera ta zauna, gaishe su tayi suka amsa cikin kulawa, tace
"kuyi hak'uri na makara ban tashi da wuri na had'a mana breakfast ba" murmushi Safeena tayi tace
"Basma kenan, karki damu ai nice da girki, nasa kuku ya had'a mana tunda ni gaskiya bana girki" Basma harta kai hannunta zata jawo food wormer sai ta janye hannunta jin Safeena na fad'in kuku yayi musu breakfast, da sauri tace
"gwara da ban zuba ba, dan bazan iya cin girkinsu ba" mik'ewa tayi ta wuce d'aki, shi dai Shureym saurarensu yake yi yana kai loman abinci, a ransa yana yabawa Basma


"yanda take k'ok'arin yin abinci da kanta duk irin matsayinta da take dashi na 'YAR SHUGABAN K'asa, amma ita Safeena ba 'yar kowa ba sai iyayin tsiya, k'ilama bata iya bane, dan Ni ban tab'a cin girkinta ba"


Maganar Basma shine ya dawo dashi daga zancen zuci da yake, tace
"Yaya Shureym bari naje naci abinci" kallonta yayi sama da k'asa yace
"amma kinsan yanzu ba zan yarda da wannan fitan naki ba ko" marairaice fuska tayi tace
"yaya takeway kawai zanyi na dawo" d'aure fuska yayi yace
"ni bawai fitan bane damuwa na, kawai bana so ki had'u da d'an iskan saurayinki d'in nan ne" idon Basma ya ciko da kwalla bata ce komai ba, saita juya zata koma d'aki, dakatar da ita yayi yace
"kije amma na baki minti talatin, in kika bari ya wuce, to kinfi kowa sanin hukunci na, bawai na bari bane sanyi kawai nayi" bata tanka mishi ba, ta wuce abinta tana kissima abinda zata aikata mishi.


Tana fita studio ta wuce, wayarta ta basu ta nuna masu hotunan da take so a wanke mata, tana gama musu bayani ta wuce siyan abinci. Cikin sauri ta dawo ta basu kud'insu ta karb'i hotunan da wayarta, ta adana su a jaka, kana ta fita cikin sauri, taxi ta tara ya sauketa a gida ta shiga da sauri.


Ta taddasu a falo,
"sannunku da hutawa" tace, kana ta nufi d'akinta, Yaya Shureym ya dakatar da ita, damm taji gabanta ya fad'i, amma saita dake ta juyo, kallonta yayi yace
"amma kinsan kin d'auki kusan minti arba'in ko, daga siyan abinci shine zaki d'auki wannan lokacin" marairaice fuska tayi tace


"haba Yaya Shureym, kasan k'asar nan bafa Nigeria bane, duk yanda na tadda layi sai an sallami wanda suka rigani kafin a bani, su ba ruwansu da cuwa-cuwa, kuma bada motan gida na fita ba, da taxi ne"


Kallonta yayi a takaice kana ya d'auki telephone ya kira masu gadin gidan, tare da duk ma'aikatan gidan, bayan sunzo yace tare da nuna Basma
"karku sake ku bar wancen ta fita a gidan nan sai in na baku izini" duk wannan bayani a cikin harshen turenci yake musu, cikin girmama suka amsa masa kana ya sallamesu suka fita, mik'ewa yayi ya zo inda ta tsaya kana ya amshi ledan take away d'in, yace
"muje na taya ki ci" gabanta ne ya shigo dukan uku-uku, burin ta karya buk'aci ganin abinda ke cikin jakarta, haka suka jera suka shiga cikin d'akin, Safeena wani bak'in kishi ne ya tirnik'eta, tsaki taja tace


"ni sam bana burin wata mace ta rab'i Shureym, amma shegiyar yarinyar nan ta zame mini k'arfen k'afa, bari mu koma Nigeria saina raba wannan Auren, dan in ba haka ba, Shureym ya sameta kashina ya bushe, dan na shiga uku, dani da banza duk d'aya ne a gunsa" mik'ewa tayi ta wuce d'akinta cike da damuwa.


Suna shiga ya fincikota, a tsorace ta kalleshi, jakanta ya amsa, ai Basma Addu'a ta fara yi a cikin ranta domin ta gama tsorata, duk tunaninta bud'e jakar zai yi, da mamaki sai taga ya aje akan dressing mirror din ta, wani ajiyar zuciya ta saki a hankali, dawowa yayi wurinta, hannunta ya kama suka zauna kan kujera, jawota yayi kan jikinsa wanda har tana jin saukar numfashinsa a gefen kuncinta, juyo da fuskanta yayi, suka kalli juna ido cikin ido, sha'awar Basma ce kwance a kwayar idon Shureym, itama kuma tsana ce kwance a cikin kwayar idonta, bata ankara ba saita ji ya had'e bakinsu, ya soma sumbatar ta, duk yanda taso kwace kanta ta kasa, k'arshe hak'ura tayi sai da yayi iya ka yinsa kana ya saketa, kuka taso yi amma saboda karta nuna damuwa saita shanye su, mik'ewa yayi yace
"daga yanzu wannan ne irin hukuncin da zan rik'a miki, in dai kika sab'awa umarni na" sai ya fice.


Da gudu ta mik'e ta shiga bayi, brush ta soma yi tana dirjan harshenta, tana yi tana kuka, takai kusan minti Sha biyar tana aikin abu d'aya, sai da taji bakinta ya soma yi mata zafi kana ta dena brush d'in, wanka tayi ta fito ta sanya kaya marasa nauyi, saita rufe k'ofarta, ji tayi bata jin yunwa, abincin da ta siyo saita sanya a fridge, d'auko wannan jakar tayi ta ciro diary d'inta, ta shiga rubuta labarin fitanta da Bilal, da harya kawo mata ice cream data manta a motansa, Yaya Shureym kuma daya ganshi ya kulla mata sharri, dama ta rubuta labarin tun farkon had'uwarta da Bilal a cikin diary d'in, saita d'aura da labarin bayan dawowarsu daga Nigeria, haka ta rubuta komai abinda ya faru, sai ta sak'ala hotunan data d'aukesu a cikin diary. Maida shi tayi majiyansa, saita mik'e ta dumama abincin da ta siya a microwave, bayan ta gama ta gabatar da Sallan Azahar sai ta bi lafiyan gado.


*Kasar Monaco*
Jidda ta matsawa Aryan wanda duk iya wulakanci yayi mata, amma tak'i rabuwa dashi, k'arshe dole ya sakko suka cigaba da mutunci kamar yanda ya buk'ata, don ya sanar mata shi sam ba zaiyi soyayya da ita ba, Aryan yayi waya da Umma ya sanar mata saura wata Uku ya dawo Nigeria, tayi masa Addu'a sosai kana tayi masa fad'a da nasiha akan jin tsoron Allah, yayi mata godiya yace "Umma inna dawo zanje Gombe na dawo dasu Malam da Inna su dawo wurinmu mu zauna dasu" Umma tayi farin ciki sosai tace "gaskiya ne, tunda Allah ya bud'a mana yanzu sai su dawo kusa damu, in ya so duk bayan lokaci sai mu rik'a zuwa Gombe muna gaisawa da sauran dangin mu". Nan suka yi sallama tana sanya masa Albarka.


*Nigeria*


Abba ya tattauna dasu Ammi da Momy akan zancen Basma, ya bama Momy hak'uri akan abinda ya faru, sun sasanta kansu kana ya gargad'i kowa akan kar abari su Meena suji komai, kamar yanda suka yanke da sauran iyayen kafin su tafi. Haka aka rufe maganar ba tare da sun fitar dashi ba.


Deeja ta damu Yaya Ahmad akan ya sanar mata abinda ke faruwa, hak'uri ya bata yak'i gaya mata, duk yanda su Meena suka so jin abinda ke faruwa amma ba suji komai ba a wajen mazajensu, k'arshe hak'ura suka yi da niyyar tambayar Basma, sun kira ta, itama tak'i gaya musu tace "ku kwantar da hankalin ku, za kuji komai nan gaba kad'an" dole suka hak'ura badan sun so ba.


*America*
*Bayan kwana Hud'u*


Ya kama yau kwana biyar kenan da dawowar su Basma, cikin dare Basma ta tashi ta d'auki Jakar da diary d'inta ke ciki, ta gama sanya duk abinda ya kama, ta sanya wayar da take amfani wajen d'aukansu Yaya Shureym a ciki, ta barta a kunne, sai ta sanya dukkan gwala-gwalan zinarinta a ciki da hayan amfaninta, saita ta kulle jakar. Tashi tayi ta shiga had'a kayanta gaba d'aya a cikin trolley guda uku, hatta takalmanta bata bari ba, bayan ta kammala tas, sai ta sanya duka trolley d'in a cikin kitchen dinta ta kulle, Sallan Nafila ta gabatar, ta shiga kwararo Addu'a akan abinda take shirin aikatawa, Allah ya bata sa'a ya taimaketa, Sallan Asubahi aka kira ta gabatar da raka'atanil fajri, sannan tayi Sallan Asubahi tayi azkar na safe, saita tashi ta sanya sallayan a cikin d'aya daga cikin trolley, gado ta fad'a ta kwanta ta soma sharb'an barci.


*Da safe*


Misalin k'arfe tara na safe, Yaya Shureym yazo yana buga mata k'ofa, kamar bazata bud'e ba saboda barcin da take ji, zuwa tayi ta bud'e k'ofar tace "Yaya Shureym lafiya kake buga min k'ofa? wlh barci ke damuna" cikin murmushi yace "Lafiya lau, ina so ki d'an had'a mana breakfast kafin mu dawo daga asibiti, zan kai Safeena ne ba ta jin dad'in jikinta, daga nan za'ayi mata awon ciki" murmushi tayi tace "tom Yaya Allah ya bata lafiya" fitowa tayi ta tadda Safeena a falo sannu tayi mata saita amsa a yatsine, murmushi Basma tayi tace a ranta "kisha kuruminki Malama, yau zan bar miki mijinki" a fili kuma tace "d'an Baba yana baki wahala, Allah dai ya raba ku lafiya" ta amsa a takaice kana suka wuce. Kitchen Basma ta shiga, ta gayawa kuku Breakfast d'in da take so su had'a musu, kana ta koma d'aki da sauri, ta shiga fito da duk trolleyn ta falon, ta aje a bayan kujera, saita rufe su da wani zani. Wanka ta tayi, ta sanya doguwar riga bak'a mai aiki purple, sai ta yi rolin da farin gyale tayi kyau sosai, d'akinta ta bud'e ta fita farfajiyan gidan da gudu a tsorace tana ihu, da sauri duk ma'aikatan gidan suka fito, cikin harshen turanci ta shiga gaya musu "wani Abu ne a d'aki na Ku taimakeni Ku ciremin" suka tambayeta "me ta gani" tace "Ni bazan gane ko miye ne ba" Da sauri duk suka shiga falon suka soma dubawa, d'akinta suka shiga su duka, da sauri tabi bayansu, k'ofar ta jawo da k'arfi ta sanya key ta rufe su, cikin sauri taja trolleyn kayanta har waje, ta bud'e gate ta fitar dashi, a haka harta fidda kayanta duka, su Ema sai ihu suke akan ta bud'e su, kyalkyacewa tayi da dariya ta d'auki hand bag dinta ta fice abinta, tana fita ta samu taxi ya kwashe mata kayanta sai airport. Suna isa ta ja kayanta, zuwa minti sha biyar an gama checking kayansu sun shiga jirgi, minti goma da shigansu jirgi ya daga zuwa k'asarmu Nigeria.✈


*Su Basma an shuka tsiya😂😜, koya cakwakiyar zai kasance sai kun jini a next page...*


*Rahma Ce*
[8/10, 5:30 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *23.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


Jirgin su Basma ya sauka lafiya, drop ta d'auka taxi, ya kaita asibitin da Yaya Ahamd yake aiki, nan ta bufa, ta ciro trolley d'inta guda biyu da kuma wannan bak'ar jakar da diary ke ciki, ta jasu zuwa cikin asibitin, gefe ta tsaya ta samu d'aya daga cikin masu gadi yana ganinta ya washe baki dan ya ganeta suka gaisa tace
"aam Baba Dr Ahmad yana ciki kuwa? cikin ladabi yace
"yana ciki, motansa yana cikin wancen barandan yayi parking d'inta"


Murmushin jin dad'i tayi sai ta ciro wata farar takarda mai d'auke da wasik'a a ciki tace
"Baba Dan Allah ka taimaka ka kai masa wannan kayan, sauri nake jirgi na jirana, ka gane ni ai?" cikin dariya yace
"kwarai Hajiya na gane ki" murmushi tayi ta k'irga dubu Ashirin ta bashi tace
"Baba ga wannan saika ci goro ko" jiki na rawa ya amsa yayita shi mata da albarka, kiran wani matashin saurayi yayi d'aya ne daga cikin drivern asibiti, yayi masa umarni daya d'auki d'aya daga cikin trolley, shi kuma Baba yayi mata sallama ya sanya wasik'ar a aljiunsa, kana ya d'auki d'ayan trolley da kuma bak'ar jakar suka shiga cikin asibiti.


Basma binsu tayi a baya har saida taga sun isa k'ofar office d'in Yaya Ahmad, kana tadan tsaya, tana ganin sun Shiga sai ta juya cikin sauri ta isa bakin gate, taxi ta koma ta shiga, da gudu suka bar unguwar.


Mai gadi suna Shiga, Yaya Ahmad ya kalle su cike da mamaki yace
"Malam wannan kayan fa daga ina?" da dariya a fuskansa yace
"Uwar d'akinta tace na kawo maka" cikin mamaki yace
"wace uwar d'akin naka?" yace
"Basma mana, ita tace na kawo maka domin tace tana sauri ne ana jiranta, tace in baka wannan wasikar ma" saiya mik'a masa, cike da tsoro da mamaki Yaya Ahmad ya mik'e yace
"Basma kuma?" da sauri ya fita a office d'in, Baba mai gadi da d'ayan saurayin suka rufa masa baya, gate ya nufa yana hangen ko zai ga Motan da tazo a ciki, babu kowa bamu alaman wata mota, Baba mai gadi yace
"kaga ikwan Allah sun riga sun tafi, acan fa na hangi mota taxi wanda ya kawo ta, nima nayi mamaki dana ganta a cikin taxi" ajiyar zuciya Yaya Ahmad yayi ya shiga wasi-wasi da damuwa, komawa office yayi ya Shiga bud'e jakukunan, tabbas kayan Basma ne a ciki, bak'ar jakar ne ya nima bud'ewa amma arufe take babu key a jiki, zama yayi kamar wanda yayi aikin gajiya, dan jikinsa duk a mace yake, da kuma tsananin fargaba da zuciyansa yake ciki, bud'e wasik'ar ya yi, ya soma karantawa kamar haka...


*ASSALAMU ALAIKUM*


*Yaya Ahmad da fatan duk kuna lafiya, nasan zaka yi mamaki da ganin kayana ba tare da na bari mun had'u ba, Yaya Ahmad ina cikin damuwa na tsani rayuwar dana ke ciki, dan haka zanyi nesa da kowa ko zanji saukin abinda ke damuna, Yaya Ahmad kafi kowa sanin bana son auren da a kayi min, amma na hak'ura nayi biyayya gasu Abba, na d'auki alk'awarin yiwa Yaya Shureym biyayya in zauna dashi, amma kash sai dai shi a gunsa akwai mugun nufi a zuciyansa game dani, a ranar da muka shiga jirgi zuwa garin America lokacin aurenmu, anan cikin jirgi Yaya Shureym ya fara shayar dani ruwan bak'in ciki, wanda har yau ina cikin shansa, Yaya Ahmad na so gaya maka komai a wancen lokacin, saina ce bari nayi hak'uri bai kamata in fara kai k'ara ba, kuma ma duk abinda zan fad'a ba mai yarda dani akai, sai kai kawai nasan zaka yarda tunda kai kasan halinsa, d'aurewa nayi tun daga ranar dana tafi na bar gida har zuwa yanzu, Yaya Ahmad bari na tak'aice maka bayani, duk kan k'arin bayani da kuma labarin zamana a America yana cikin wannan diaryna na rubuta shi, da kuma wasu hotuna a ciki wanda zasu zame min shaida, duk a cikin wannan bak'ar jakan, akwai kuma wayata a ciki wanda akwai wasu hotuna a ciki, ga system d'ina ka aje min shi, key d'in dana baka rannan ka aje min shine mabud'in wannan jakar, ina so ka kai gida ka bayyana wa su Abba komai dake cikin jakar nan, tare da karanta musu wannan wasik'ar da kuma abinda ke cikin diary na, Yayana nagode da kulawanka, nasan kaida Momy ne zaku fi kowa shiga damuwa, dan Allah ka bama Momyna hak'uri, kuma nayi muku alk'awari duk inda nake zan kula da kaina zan kare mana martaban gidanmu da mutunci na, insha Allah zan kiyaye duk kan hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akaina, kuma zan kare igiyar Aure na.*


*Hawayena ba zasu daina zuba ba, har sai naji a raina kun yafe min laifin dana yi muku akan tafiya da nayi na barku, Ina sonku duka dangina. Abbana ku yafenin Ammi na kar kuyi fushi dani, zan dawo amma ba nan kusa ba, hasalima a yanzu bansan ina na nufa ba*😭.


*Bissalam*🙏
'Yarku Basma...


Kafin ya gama karantawa, hawaye ya gama wanke masa fuska, tashin hankali ya shiga mara misali, da sauri ya share hawayensa ya sanya wasik'ar cikin aljiunsa, kiran wani mai goge masa office yayi, ya taya shi fita da trolley, mota ya sanyasu, ya shiga mota zuwa gida cike da tashin hankali.


Basma suna isa airport ta biya mai taxi, ta ja trolley d'inta wanda ya rage guda d'aya, saita shiga ciki, ba wani b'ata lokaci suka shiga jirgi sai zuwa k'asar Etopia, jirgunsu na d'agawa taji gabanta ya fad'i, kewar family d'inta ya cika mata zuciya, ji tayi dama jirgin zai tsaya ta sauka, runtse idonta tayi tace a ranta


"Anya na yiwa iyayena adalci kuwa? anya na yiwa kaina adalci? shin ya za suji in suka ji labarin na tafi, Allah sarki Yaya Ahmad ban kyauta muku ba"


Ajiyar zuciya tayi tace
"Shureym kaine silan komai, dole in yi nesa da kai da kuma mugun nufinka a kaina, na tsaneka ba zaka tab'a cimma burinka a kaina ba, kuma so nake ka gane kuranka kasan cewa ni Basma 'yar halak ce" saita ja tsaki ta gyara zamanta.


Tsarbi counter ta ciro a hand bag d'inta, ta shiga salatin Annabi s.a.w, nan take taji natsuwa ya ziyar ceta, murmushi tayi saita lumshe idonta kamar mai barci.


Yaya Ahmad yana isa gida yayi parking, da sauri ya fito ya kwalawa wani driver kira, cikin sauri yazo, jakan ya ciro ya ce ya d'auki d'aya, shima ya d'auki d'aya ya rik'e da bak'ar jakar, falon Abba ya wuce dasu, suna shiga suka aje, ba kowa a falon sai ya sallami driver. Zama yayi dirshen a k'asan kafet, ya rafka ta gumi tunani yake ta ina zai fara, wayansa ya ciro ya kira Amminsa cikin tashin hankali yace "Ammi kina ina? ki zo ina falon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login