Showing 51001 words to 54000 words out of 79094 words

Chapter 18 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4643

Addu'a tayi Allah ya bashi mata ta gari. K'arasawa tayi wurin tace
"Deeja ni zan tafi in Ahmad ya dawo ki gaishe shi" Deeja ta kwab'e fuska kamar za tayi kuka tace
"kai Umma baki dad'e ba fa, kuma da kin jira sun kusa k'ara sowa ma" murmushi tayi tace
"haba Deeja baki ganin Yayanki ya dawo ne, so nake inje in had'a masa abinci dan nasan da wuya inya karya ma" Murmushin jin dad'i Yaya Aryan yayi yace
"kinsan kuwa Umma nayi missing d'in Abinci ki, kuma akwai yunwa a tare dani, ki tafi kawai nima ina bisa hanya" dariya tayi tace
"yauwa Aryan saika tawo" nan tayi sallama da Deeja ta wuce ta shiga mota driver ya jata sai gida.


Aryan suna zaune a wurin Yace
"Deeja lafiya naga gidan naku da taron mutane?" murmushi yak'e tayi tace
"lafiya lau, president ne yayi umarni da duk a taru anan, mutanen kano da Kaduna duk sunzo, yanzu jiran isowarsu muke daga America" yace
"to Allah yasa lafiya, Nima ina ganin bari na gudu ba zan iya jiran su dawo ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu zanzo na gaishesu" bai rufe baki ba, motoci suka fara shigowa cikin haraban gidan, Deeja tace


"laaa gaka sun dawo ma muna zancen su" murmushi kawai yayi baice komai ba, yana kallon mototcin da suke shigowa, da sauri ya mik'e lokacin yaga su Yaya Ahmad sun fito ya isa wurin yana dariya, suka kama hannun juna cike da farin ciki a fuskokinsu Yaya Ahmad yace
"Aryan saukan yaushe?" cike da dariya yace
"yau na sauka"
"to kai da mu kayi waya kace sai nan da wata uku zaka dawo" murmushi yayi yace
"wlh naji hankali na yayo gida burina in ganin a Nigeria" gaban yaya Ahmad ne ya fad'i amma saiya dake, ya mayar masa da murmushi yace
'lallai fa kace kana kewarmu"
"kwarai kuwa nayi"


Nan ya wuce wurin President ya risina zai gaisheshi, Abba shafa kansa, ya kama hannun Aryan suka wuce babban falonsa.


Falon ya cika da dangi, Dady, Abba, Mai Martaba, da duk iyalensu, Ammi, Mami, Momy, Umma, Hajiya Murja, Duk suka gaisa, suna cikin wannan zaman ne sai ga sallaman Yaya Shureym a birkice ya shigo, Safeena na biye dashi a bayansa, Mami na ganinsu gabanta ya fad'i damm, a razane ta mik'e tace
"Shureym lafiya na ganka haka wurjanjan" zuwa yayi ya rungumeta ya soma kuka wiwi, duk mamaki ya cika mutanan falon banda su Abba dasu suka san komai.


Yaya Aryan yana gefen Yaya Ahmad suna hira k'asa-k'asa, Dady ne yayi gyaran murya yace
"Kai Shureym samu wuri ka zauna, da fatan duk kun san musabbabin taruwan mu anan, akan Shureym da Basma" ai yana furta Basma Yaya Aryan ya d'ago fuskansa gabansa ne ya shiga dukan uku-uku, mutanan falon yabi da kallo amma baiga Basma ba, dama tun d'azu yake raba ido ko zai ganta, amma shuru ba alamunta, kamar zai tambayi Deeja amma saiya fasa.


Abba yasa Yaya Ahmad ya karanta lettern da Basma ta rubuta da kuma diary d'inta, nan ya shiga karantawa iyayen sai salati suke yi dama su Mai Martaba basu san komai ba sun dai je America sunga Shureym da mata, Mai Martaba jikinsa yayi sanyi, yace a ransa
"lallai shureym yaci amanansa" k'arin tashin hankalinsa yanda Shureym ya maida Basma tamkar baiwansa.


Yaya Ahmad ya gama karantawa, Aryan gumi ya gama jik'ashi, kamar shine yayi karatun, falon ne yayi shuru, Ummi tace
"ai biri yayi kama da Mutum, kazo ka kawo k'aranta harda yiwa Yarinya k'azafi, ni dama ban yarda ba, ashe kai ne ke cutar da ita"


Mai Martaba yace
"ka kyauta Shureym, yanzu amanar da muka baka kenan, kaci amanata da zumuncinmu ban tab'a tsammanin haka daga gareka ba" cikin kuka Shureym yace
"Baffana ku yafe min sharrin shaid'an ne" Mai Martaba ya katse shi yace
"yi min shuru mutumin banza kawai, yanzu ya akai kayi aure har ban sani ba, wasu iyaye ne ka samu suka jagoranci auren?"


Cikin tashin hankali Shureym ya basu labarin yanda aka yi aurensa da safeena, jikin kowa ne yayi sanyi jin cewa Mami itace ta goya masa baya wajen yin aure, Ammi cikin fad'a tace


"ai dama Hajiya Sa'a na dad'e da sanin Yayana bai yi sa'an mata ba, kin cika kyakkyawar makira mai raba kan zumunci, ina ce kece kika matsa kika hura wuta dan ganin Shureym ya auri Basma, ashe da mugun nufi a ranki, sannan har kina goyawa d'anki baya ya auri wata, tun farko da ya nuna baya son Basma me yasa zaki matsa ya aure ta, da munsan da haka wlh da ba zamu tab'a bari ya auri Basma ba"


Mami ne cikin tsiwa da makirci tace
"ya ishe ki Hajiya Fatima, ba zan d'auki cin fuska ba" Mai Martaba ne ya daka mata tsawa yace


"Mutumiyar banza, dama duk cikin gidana kece mai bani matsala, kuma kisani kamar yanda kika had'a auren Shureym da wancen Yarinya to tamkar kin datse igiyar aurenki ne, saboda kinsan ba na son zama da munafuki mara tsoron Allah"


A firgice Mami yace cikin kuka
"haba Mai Martaba tuba nake, dan Allah karka min haka, nasan nayi kuskure bazan kuma haka ba, ka k'ara hak'uri dani, dan Allah ka gafarta min zan gyara halina"


Saita kai kallonta ga Shureym ta cigaba da cewa
"Kai Shureym maza ka saki Safeena don Mai Martaba ya maida aurena" cikin fad'a Mai Martaba yace
"karka kuskura ka furta saki akanta domin wlh saina sab'a maka, aure dai ka riga kayi, sai ka san inda zaka aje musu Yarinya kuma ba dai gidana ba, sannan in kika sanya Shureym ya saki Yarinyan mutane wlh saina tsinke duk igiyar aurenmu dake wanda yayi saura"


Abba ne ya katse shi da cewa
"haba Mai Martaba, in rai ya b'aci hankali karya gushe, dan Allah ka maida aurenka da Hajia Sa'a ka kuma yafewa shureym, kuskure dai an riga anyi, sannan ni dai zan tsare Shureym har sai anga Basma, dan alkawari na d'auka akan haka"


Dady yace
"ni dai duk kowa yayi hak'uri a sulhunta, aure dai ya riga yayi, dan haka sai mu jira dawo war Basma, in tace zata zauna da mijinta shikenan, in kuma tace bazata zauna dashi ba, to ba mai yi mata dole"


Kuka Momy take wiwi, tace
"ni dai Ku aje duk wannan bayani, ku tashi ku nimo min Basma, ba zan jure rashinta ba"


Kuka Shureym yake tare da sambatu
"Dan Allah Basma ki dawo gareni wlhi ina son ki, bazan jure rashinki ba, Basma nayi miki kuskure ki yafemin"


Su Meena ne suke hararanshi shike da jin haushinsa, Yaya Adam ya daka masa tsawa,


"Dalla yi mana shuru mutumin banza, haka kawai ka tada zaune tsaye, ana zaman lafiya, duk abinda ka dauko insha Allah kanka zai tsaya, kuma babu abinda zai tab'a zumuncinmu"


Aryan ya mik'e tsaye fuskanta a tamke cike da damuwa, baicewa kowa komai ba, ya nima fita daga falon, Yaya Ahmad yace
"Aryan ina zaka ka tsaya mana" waigowa yayi idonsa na fidda kwalla, ya bud'e baki zaiyi magana, sai kawai waji wani abu ya tokare masa k'irjinsa, jiri ne ya dibeshi sai ya fad'i k'asa da k'arfi, da gudu Yaya Ahmad ya isa wurinsa, Deeja ce ta saki wani k'ara tace
"Yaya Aryannnn" cike da firgici duk suka isa wurinsa, cikin tashin hankali suka wuce dashi Asibiti...


*Rahma Ce*
[8/11, 6:16 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *26.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


Bayan sun kaishi asibiti likita ya duba shi, ya tabbatar musu da damuwa ce ta haifar masa da suma
"amma yanzu ya farfad'o, nayi masa alluran barci domin kwakwalwansa ya huta, zuwa anjima inya farka, komai zaiyi dai-dai insha Allah"


Bayanin da likita yayiwa su Yaya Ahmad kenan sai ya wuce, zama suka yi suna ta zancen zuci, Yaya Ahmad, Yaya Naufal, da kuma Yaya Jamal sune suka kawo shi asibiti.


A can gidan kuma sun k'ara shiga damuwa fiye da damuwar rashin Basma, Dady ya shiga tunanin ina ya san Aryan, lallai fuskansa tayi masa kama da wanda ya sani da dad'ewa, amma ya kasa tuna komai, matsantawan da yayi ma kansa da tunani ne ya haifar masa da ciwon kai, dole ya yakice abin a ransa dan gudun matsala.


Awa biyu Yaya Aryan ya farka, sai dai bai iya furta koda kalma d'aya ba, idanun sa sun masa nauyi da kyar yake iya bud'esu a hankali ya rufe, hawaye mai zafi ya gangaro masa a kefen idonsa, Yaya Ahmad ya matsa kusa da gadon cikin sanyin murya da tausasa zuciya yace,


"Aryan kayi hak'uri duk kan tsanani yana tare da sauk'i, dan Allah ka sanyawa zuciyanka salama, insha Allah komai zaiyi dai-dai, ka rik'a Addu'a a zuciyanka zaka samu sassauci, yawan damuwa baida amfani domin zai rik'a cutar da lafiyanka"


A hankali ya bud'e idonsa, ya fud'e baki zai yi magana amma ya kasa, Yaya Ahmad ne ya dakatar dashi ya d'aga masa hannu yace
"karka furta komai, ni dai kayi amfani da shawaran dana baka". Haka suka cigaba da zama a Asibiti sai yamma lis likita ya sallame su. Suka wuce dashi gida tare da magungunansa, suka gaisheda Umma, kana suka yi musu sallama.


Umma ta kawo masa abinci faten Irish da naman kaza a ciki, da kyar yaci kad'an kana ta zauna kusa dashi ta dafa kafad'ansa tace


"Aryan ya kake abu kamar ma tsatson musulmai ba, banji dad'in yanda kake nuna rashin tawakkalin da kake yi, koda nasan zuciya ba tada k'ashi, daman dalilin dawowarka kenan kazo kaga abin bak'in ciki, amma haka Allah ya rubuta, ni dai ina k'ara jan kunnenka ka cire Basma a ranka, kayi tawakkali da lamarin Allah yanda yazo maka, Basma dai da auren wani akanta dan haka ka cireta a rayuwanka, in dai baso kake ka sanyawa kanka wani ciwon ba, a kullun ina maka Addu'a Allah ya baka mata tagari mai tsoron Allah"


Aryan rungume Umma yayi ya soma kuka wiwi, yace
"Umma ina k'ok'arin cireta a rayuwata, abinda naji ne ya d'aga min hankali, yanda Shureym ya azabtar min da Basma, yayi mata mugun rik'o, Umma ba zan samu natsuwa ba har sai Basma ta dawo cikin koshin lafiya ta cigaba da rayuwan farin ciki kamar kowa yake yi, dan Allah ki yafemin Umma na, son Basma a jini na yake, cireta a zuciyata abu ne mai wahala, sai dai na miki alkawarin kiyayewa akan haka".


Umma ta kwantar da Kansa bisa cinyarta, ta shiga lallashinsa har saida yayi shuru yana ajiyar zuciya.


*Makkah*
Basma ta sauka lafiya ta kama d'aki a hotel dake kusa da harami, wanka tayi ta kwanta domin ta huta, tunanin rayuwarta takeyi, hakanan taji gabanta na fad'uwa, Aryan ne ya fad'o mata a rai, hoton fuskansa ke mata yawo a cikin kwayar idonta, hawaye ne ya soma zarya a idonta, bata hanasu zuba ba domin hakan ne zaisa taji sanyi a ranta. Takai kusan rabin awa a cikin wannan yanayin daga bisani ta mik'e tayi shirin fita ta wuce cikin masallaci.


*Nigeria*
An samu bayanai akan Basma ta shiga jirgin k'asar Etopia, sakamakon binciken da akayi a airport, haka Abba ya tura wasu domin dubata a can k'asar na Etopia. Abba ya sanya an sakaye Shureym a cikin wani d'aki dake cikin gidansa, za'a bashi abinci da komai na buk'ata, fita ne kawai bazai yi ba dan har masu tsaronsa aka aje, har sai anga basma. Safeena duniya tayi mata k'unci, kuma gaba d'aya dangin su Shureym sunk'i amincewa da ita, dole yasa tayi d'amaran komawa gidansu Adamawa, da tsohon cikinta gunin tausayi.


Dady da Abba sun shawo kan mai martaba da kyar, akan ya maida aurensa da Mami, ba dan yaso ba ya maidata d'akinta, duk sun koma gida, an cigaba da Addu'a Allah ya bayyana Basma.


Masu bincike sunyi iya k'ok'arinsu wajen bincika Basma, amma babu nasara, k'arshe hak'ura suka yi suna dawo Nigeria, hankalin su Momy ya kuma tashi, lamarin ya k'ara dagule musu, Addu'a suke kawai da sadaka domin Allah ya bayyana ta.


***
*Bayan wata guda*


Safeena ta haihu 'ya mace, babu abinda ta samu daga dangin mijinta, iyayenta su suka yi komai, koda ta kira Shureym ta sanar masa, yayi murna sosai sai dai ba halin zuwa, ya kira Maminsa ya gaya mata amma ba halin zuwa itama, saboda tana bisa hukuncin Mai Martaba. Ranar suna Yarinya yaci sunan Kausar.


Kowa ya cigaba da harkokinsa, sai dai damuwa yana k'arkashin zuciyansu na rashin sanin inda Basma take, Yaya Ahmad yayi iya k'ok'arinsa ganin an samu labarin gajinta amma abu yaci tura, Momy ciwo riris ya kamata duk tayi bak'i ta lalace, ta b'angaren Shureym kuwa ya zama tamkar zautacce, ba yida magana saina Basma, shi dai burinsa ta dawo ya nima gafaranta su cigaba da zaman aurensu.


*Makkah*
Basma ta murmure ta k'ara kyau, ta samu natsuwa sosai, sai dai zuciyarta yak'i karaya da takoma gida, gani take har zuwa lokacin su Abba basu saduda ba, tausayin Momy take da kuma Yaya Ahmad, sai Yaya Aryan tasan tabbas sune wanda sukafi kowa damuwa akan rashin ta, kayanta ta had'a ta nufi Madina, ta had'u da wata mata yar k'asar Nigeria tana aure anan madina da mijinta, Hajiya Kaltum itace ta bata masauki a gidanta, kullun a masallacin fiyayyen halitta s.a.w take yini, sai dare take komawa makwancinta, tana ibada sosai kuma zuciyarta ta samu kyakkywan natsuwa. Wani lokacin sai taji kamar ta dawo Nigeria, wani b'angare na zuciyarta ke gargad'inta akan ta k'ara hak'uri da sauran lokaci.


***
*Bayan wata guda*


*K'asar Monaco*
Yaya Aryan ya koma ya cigaba da karatunsa, saura masa wata guda ya dawo gaba d'aya, hankalinsa yana Nigeria kullun cikin tambaya yake ko anga Basma, amsa dai d'aya ne ba'a ganta ba. Jidda ta matsawa Yaya Aryan amma duk da haka bata samu yanda take so ba, k'arshe tayi fushi ta daina kula shi.


*Nigeria*
Khadija ta sillib'o d'anta Namiji kyakkyawa mai kama da Yaya Ahmad, gida ya cika da yan barka, wannan haihuwar sai ya rage musu rad'ad'in rashin ganin Basma.


Kwana biyu da haihuwar Khadija Leema itama ta haihu, sun samu d'iya Mace, nan hidima ya k'aru, Leema gaba d'aya aka d'aukota sai Abuja, Kaka Ma'u itace mai yi musu wanka itada da Deeja, farin ciki baya misaltuwa a wannan family, yanzu Meena ce tayi saura, had'a taron suna suka yi, suka k'ara kwana biyu na sunan Deeja aka had'a da Leema, yaron Yaya Ahmad yaci sunan Abba Mukhtar, suna kiransa da Walid, sai Yarinyar Yaya Jamal sunan Ummi taci Sadiya, suna kiranta da Walida, anyi taron suna an watse cikin farin ciki.


*Madina*
Basma tana madina tayi sabo sosai da Hajiya Kaltum, Hajiya Kaltum 'yar maiduguri ce kasuwanci mijinta ya dawo dasu Madina, yaransu biyu Nana da Amir. Basma ta fara shirye-shiryen komawa Makka, Hajiya Kaltum ta shiga gyara Basma sosai, dilka dasu gyaran jiki tayi mata, Basma ta k'ara kyau sosai, duk tunanin Hajiya kaltum Basma komawa Nigeria zata yi, shiyasa take gyarata saboda ta sanar mata tanada Aure. Ranar da zata tafi ta bata sauran had'in Magani, harda tsaraba, sannan suka amshi number juna, suka yi sallama cike da kewar juna.


Basma ta koma jiddah, hankalinta ta koma gida, zullumi da fargaba ya cikata akan son sanin ya makomar aurenta yake, da haka tace bari ta k'ara kwana ki ta cike wata uku, kafin ta koma Nigeria.


***
*Bayan wata guda*


Meena ta haihu 'ya Mace kyakkyawa mai kama da ita, farin ciki ba'a magana a gun su, yan barka sunata zuwa, su Leema da Deeja kuma anata wankan jego, gidan ya k'ara cika da mutane, Meena, Leema, Deeja suna zaune suna hira Meena tace


"Allah sarki Queen Basma, wlh inna tuna life d'in da muka yi a baya har kuka nake saboda missing Basma da nayi, gashi yanzu duk mun haihu ita ko nata auren bata ji dad'insa ba, kuma duk tafimu kamun kai, amma Allah saiya jarabceta, ga gata da komai amma bai mata maganin matsalanta ba"


Leema tace
"bari kawai Besty, ai missing ma ba'a magana, naso ace duk wannan shagalin tana nan a kayi, wlh Yaya Shureym ba k'aramin azzalumi bane, bana fatan Basma ta cigaba da zaman aure dashi"


Deeja tace
"gaskiya ne, amma ni kam ina ganin son Basma a idon Shureym fa, kawai yayi rashin hankali ne a kan lamari, kuma Basma tana da sauk'in kai, muzguna mata da yayi ne yasa tayi masa haka"


Leema tace
"kunga dai Yaya Shureym d'an Uwana ne Ubanmu d'aya dashi, Amma wlh koda yana son Basma, ni sai na zugata karta koma gidansa, dan basu dace ba" nan dai suka cigaba da tattaunawa.


*
Yaya Aryan ya sauka a jirgi direct ya wuce gida, ya samu Umma ta yi masa barka da zuwa, abinci yaci kana ya wuce ya watsa ruwa, k'ananun kaya ya sanya, ya fito yace ma Umma ya tafi gidan Abba, zaije yaga yaron Deeja, Umma tace
"a dawo lafiya, ka gaida mutanan gidan".


Yana isa ya wuce part d'in Abba suka gaisa, kana ya je part d'in Ammi nan ya samu Momy duk suka gaisa, sai ya wuce part d'in Deeja yaga Walid sun gaisa sosai na zumumci, Deeja sai murna take da ganin Yaya Aryan, nan ta rakashi part d'in Yaya Naufal yaga Baby, daga nan ya wuce part d'in Kaka Ma'u yaga Baby Walida yarinyar Leema. Suka gaisa saiya musu sallama ya wuce.


Haka nan yau yaji nishad'in son zuwa wurin shak"atawa, yana tafiya a mota a hankali sanyin AC na ratsa shi, wak'ar sudan ya sanya, sautin na duka a hankali. A haka harya isa wurin.


*
Basma ta sauka a jirgi da misalin k'arfe Bihar na yamma, iska mai sanyi yashiga ratsata, gaba d'aya zuciyarta ta cika da tunanin Yaya Aryan, burinta bai wuce tayi tozali dashi ba, taxi ta d'auka drop ta sanya kayanta a ciki, ta shiga ta zauna, lumshe ido tayi taji tana buk'atar zuwa wurin tsak'atawa kafin ta isa gida, har sun d'auki haryan da zai sadata da gida, saita sanya mai motan ya sauya akalan motan, da ya fara kaita wurin shak'atawa.


Suna kaiwa tace wa mai mota,
"dan Allah kad'an jirani ina zuwa" yace
"to hajita sai kin fito" ta shiga cikin wurin a natse, har saida ta kai inda suka saba zama da Yaya Aryan ta samu guri ta zauna, runtse ido tayi ta shak'i iskan dake gurin, nan take taji k'amshin turaren da ba zata tab'a mantawa ba, waige-waige ta soma yi, amma babu alamansa.


Ta b'angaren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login