Showing 30001 words to 33000 words out of 79094 words

Chapter 11 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

5149

wurin mahaifinku, nayi mamaki sosai da yanda kuka shigo cukinmu kuka zauna damu duk girman matsayinku, kun rungume mu tamkar jininku" saita k'arasa maganar da kuka, Deeja ma kuka ta soma yi, falon ne yayi shuru na 'yan dak'ik'a, sai Abba yace


"Hajiya kuyi hak'uri ai wannan ba abin kuka bane, kai Aryan ba wai na maka wannan kyauta bane domin ka fansar min da soyayyarka ba, nayi maka ne saboda Allah a matsayin d'an cikina, taso ka amshi wannan takardun, na gidan Hutun Basma ce da kuma takardun motanta guda uku, ni na baka su halak malak, ina so kafin lokacin Biki Ku tare a gidan" Yaya Ahmad ne ya matsa danya Amsa takardun, sai Abba yace
"shi nake so ya amsa da kansa, domin shima d'ana ne" jikin Aryan ne yayi sanyi, haka ya mik'e yaje ya amsa tare dayi masa godiya. Momy itama tayi masa Addu'a da Allah ya bashi mata tagari, har a zuciyarta taji tana son Aryan, taso ace ya zama sirikinta. Ammi kuwa ta gama k'ulewa kamar zata fashe dan haushi, Meena da Leema sun shaida Aryan kuma sun yaba da kyawunsa lallai sun dace da Basma, Yaya Naufal da yake yasan Aryan ya tayashi murna, amma har a azuciyansa baya son ya auri Basma domin tafi k'arfinsa.


Nan Umma tayita godiya, Abba yace
"Hajiya ya isa haka Allah ne ya baku, ina 'yata Khadija?" Kanta a sunkuye tace gani, Abba yace
"Masha Allah, Allah ya muku Albarka yasa Albarka a aurenku" ya kai dubansa ga Momy yace
"Hajiya Maryam gafa surukarku nan, matar Ahmad" ai sai Momy ta fad'ad'a murmushinta tace
"Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi, ai tunda tazo ma ba zasu tafi da ita ba, zata zauna anan domin ayi mata gyaran jini dasu Leema gaba d'aya" Abba yace
"To shikenan, Abu yayi kyau, bari na fita ana jira na" nan yayi musu sallama ya fice, Ammi ce ya mik'e da sauri tace


"Ahmad yanzu ka rasa matar aure sai wannan yarinyan, to ka sani ba da yawuna ba, dan bataimin ba" tana gama fad'an haka ta fice, da mamaki duk suka bita da kallon, Ahmad cike da tashin hankali yace ma Momy,
"Momy kinji abinda Ammi tace ko, dan Allah ki shawomin kanta" Momy tayi murmushi tace
"karkaji komai zata sakko ne" ta kai dubanta gasu Umma tace
"Hajiya kuyi hak'uri rashin fahimta ne" Murmushin yak'e Umma tayi domin abin ya bata haushi tace
"ba komai ai" nan Yaya Ahmad yace su tashi ya rakasu gidan da Abba ya basu, Basma ta mik'e tace
"Yaya Ahmad zani" hararan wasa yayi mata yace
"kinsan dai yanzu bakwa fita, kiyi hak'uri kiyi zamanki a gida" marairaice fuska tayi tace
"tom zanyi magana da Yaya Aryan" da sauri Aryan ya juyo yace
"a'a Basma magana a tsakani mu ya k'are" yana gama fad'an haka yayi waje da sauri, ai da gudu Basma ta bi bayansa tana kwala masa kira.


Ya kusa kaiwa gate, sai ya tsaya tsak amma bai juyo ba, ta cimmasa ta tsaya a gabansa tana haki, kallonta yayi ya kauda kai, hawaye ke sauka bisa kuncinta tace cikin sark'ewan murya
"Yaya Aryan guduna kakeyi na zama abin gudu ko, ko ka daina sona ne?" Runtse idonsa yayi ya bud'e su, sun rine sunyi ja yace
"Basma dole na gujeki domin ke yanzu ba tawa bace, Basma kin haramta a gareni, magana a tsakaninmu bai dace ba, domin zai tado min da mikin dake zuciyana wanda mai gama warkewa ba, ina Sonki Basma baya musaltuwa, amma ki sani soyayyan da mukayi dake kisa aranki tamkar mafarki ne, ki cireni a zuciyarki kiyiwa iyayenki biyayya" yana gama fad'an haka ya matsa ya cigaba da tafiyan, Basma durkushewa tayi a gurin ta saki wani kuka mai tsuma zuciya, Aryan shima da kuka ya fita gidan, yana fita ya tsaya gefen wani dakali ya durkusa agun ya shiga rera kuka tamkar k'aramin Yaro.


Leema, Meena da Deeja ne suka zo suka d'aga Basma, suka wuce da ita part d'in Momy. Umma suka fita itama tana kwalla, a haka suka cimma Yaya Aryan ita da Yaya Ahmad da kuma Yaya Naufal, dafashi Yaya Ahmad yayi, ya d'agoshi ya shiga share masa hawaye tare da gaya masa kalamai masu sanyaye rai. A haka ya sanyashi a mota ya wuce dasu gidan da Abba ya basu.


B'angaren Shureym kuwa Mami ta aika Sarkin Gida da wasu mutane garin Yola, an basu auren Safeena, sun kai musu akwati da komai da Shureym ya siya, anyi shagulgulan Biki lafiya an d'auko Amarya. sun sauka a gidanta dake garin Kano wanda Shureym ya gyara shi sosai, komai na jin dad'i akwai a gidan. Sun gama bikin auren sirri, wanda daga Mami sai Shureym sai wanda suka je nema masa aure sune kawai suka sani. An bar Amarya da Ango suna cin Amarci.


Momy ta samu Ammi akan batun Auren Yaya Ahmad da Deeja, tayi mata bayani mai gamsarwa, Ammi ta sauko, tace ta hak'uri amma tana son Ahmad ya zauna da matar anan cikin gidan President, ta da sanyawa Auren Albarka, Momy taji dad'in haka sosai, tace zata Sanar ma President domin a gyara part d'in da Ahmad zai zauna.


*Biki saura mako guda*
Anata shirin biki ta ko ina, mutanan Kano sun tattaro sun wuce Abuja, mutanan Kaduna ma haka, gidan president ya cika da dangi da abokan arziki, kowa kagan shi yana cikin farin ciki.


Amare kuwa sunsha gyara sai kyalli suke, a zuwa yanzu su Yaya Naufal da Yaya Jamal sun sauko da k'in da sukewa su Meena, yanzu burinsu bai wuce a d'aura aure ba susha amarci, sai dai a Kasan zuciyan Yaya Jamal yayi alkawarin sake aure da sabuwar budurwa domin shima ya mori aure, dan yasan Leema saura zai samu agunta.


Basma ta saduda sosai tayi sanyi, tana tsayawa tayi hira da Yaya Shureym amma a k'asar zuciyanta Aryan yana nan, kullun dare saita yi kuka na rashinsa, Shureym sai rawan jiki yake yi, yana nunawa Basma kuwala ta musamman, dan burinshi bai wuce yaga an d'aura Auren ba, domin yana cike da tsananin sha'awarta, yasan duk k'insa da take yi da an d'aura zata bada kai bori ya hau.


B'angaren Safeena, Yaya Shureym ya sanar mata da komai na aurensa da Basma, ta nuna rashin damuwa akan haka, sun tawo Abuja a tare, ya kama mata d'aki a hotel har a gama bikin su wuce America, Safeena burinta bai wuce ana gama shagalin biki ba su wuce America, ta juya Basma yanda ranta keso, domin Shureym ta gama dashi a tafin hannunta yake, sannan tayi alkhawarin Shureym bazai tab'a tarawa da Basma ba in dai tana raye.


Amarya Deeja tayi kyau tamkar ba ita ba, hatta Ammi da take k'inta ta yaba da yanda ta sauya, fatarta tayi kyau, kamannin ta da Meena ya fito sosai, a hankali taji ta kwanta mata arai saboda yanda Deeja take mata biyayya da kuma nuna kunya a gareta a matayinta na mahaifiyan mijinta, cikin k'ank'anin lokacin ta nima k'iyayyar da take mata ta rasa, har wautan kanta take gani akan meyasa ta nunawa Yarinya tsana haka. Deeja ta koma gida, ta samu su Ammi a sabon gidansu, domin a nan ne za'a d'aukota a kawota gidan president.


*Ana gobe biki*


Mutane sun gama hallara, ta wajen su Umma mutanan Gombe sunzo, sai dai mahaifinta Malam ba shida lafiya, dan haka Innarta basu samu zuwa ba sai danginsu, sunata shirye-shirye cikin kwanciyar hankali.


Yaya Aryan ya bar K'asan ana saura kwana uku biki, ya wuce K'asar Manaco domin yaji ba zai iya tsayawa bikin ba, koda ya isa k'asar ya kashe duk wayoyinsa ya soma Harkan karatunsa, Basma tana ransa, shi kad'ai yasan irin k'unan da zuciyansa yake ciki, kullun saiya kalla hotunanta da wanda take ita kad'ai da wanda suka d'auka tare a cikin system d'inshi, wani yayi murmushi wani yayi kuka, ya saba da haka, harya zame masa jiki.


*Ranar daurin aure*


Angwaye sun fito sunyi fas sai shek'i suke yi, ta b'angaren amare kuwa tsayawa fad'an kyawunsu b'ata lokaci ne, Basma koda tana cikin damuwa tayi kyau, tasha kwalliya amma bai haka zuban hawaye a fuskanta ba, duk wanda ya ganta saiya tausaya mata, ta k'ara tsukewa ta rame, ko tayi dariya yake tayi, sam bata farin ciki da wannan auren, Addu'a take Allah ya bata hak'uri da juriya akan auren.


Bayan sun idar da Sallah Juma'a limamin masallaci ya sanar da d'aurin Auren yaran President da Gomnan Kaduna, da kuma Sarkin Kano. Biki na 'yayan gata.


An d'aura auren
Yaya Ahmad da Khadija
Yaya Shureym da Basma
Yaya Jamal da Haleema
Yaya Naufal da Ameena
Yaya Adam da Munaya 'yar wazirin Sarkin Kano.


Anyi addu'o'i kana aka wuce taron walima a babban hol dake fadar Shugaban k'asa, anci ansha kowa ya shaida wannan aure, na 'yayan manya ne kuma masu gata.


Basma tana jin an d'aura ta shiga d'akinta ta kulle kanta, kwantawa tayi a gadonta ta fara kuka mara sauti, hoton Aryan a wayanta take kallo tace
"shikenan an rabamu, Yaya Aryan ina sonka Allah ya rabamu, Allah kasamin juriya da hak'uri azuciyata, Aryan na je soyayyarka a zuciyata, zan yi kok'arin yin biyayyar aure ga mijina, Allah ya had'a fuskokinmu yasa na zama matarka a aljanna" saita b'alle da sabon kuka. A haka barci mai nauyi ya d'auketa, ba ita ta farka ba sai bayan sallan La'asar. Wanka ta tayi, ta canza wasu kayan zuwa leshi marun mai fulawa fari, tayi makeup tamkar ba Basma ba, ta b'ata lokaci sosai wajen kwalliya, kana ta aza gwagwaro Fari, ta sanya takalmi mai tsini, turaruka kuwa kamar wanka tayi dasu. Kallon kanta tayi a madubi, ita kanta ta yaba da Kyan da tayi. Ta fito a Queen Basma.


A can kuwa cikin gidan hankalin kowa ya tashi ba'a ga Basma ba, an duba duk inda ya kama ta amma ba'a ganta ba, gaba d'aya gidan ya hautsine cikin tashin hankali, a cikin wannan yanayi ne Basma ta fito cikin taku na k'asaita, yau Queen Basma ta fito a sunanta, ai sai kallo ya koma gunta cike suke da mamakin ganinta a rinin wannan shiga, nan take suka fara murna, Basma tayi kyau sosai, masu d'aukan hoto suka fara d'aukanta, Ammi ce ta tawo da gudu ta rungemata tace
"Basma ina kika shige ne haka?" dariya tayi tace ina d'akina, nayi bankwana da Yaya Aryan shine barci ya d'aukeni, yanzu na kimsha nace bari na fito a cigaba da shagalin Biki dani" ai baki bud'e Ammi ta bita da kallo tana mamakinta tare da tausayinta.


*Rahma Ce*
[8/7, 8:33 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *15.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


*Da dare*


An shirya kayataccen Dinner a katon hol mai d'aukan mutane dubu, manyan mutane sun halarci wannan Dinner, harda wasu yan k'asashen waje sun halarta, Amare da Angwaye sunsha kyau, ko wanne zaune yake da Amaryansa, Safeena na zaune cikin mutane ranta ya gama b'aci, zuciyarta yana mata zafi dan tsananin kishi, tunani ta shiga yi, ita fa Auren sirri aka mata sam ba'ayi irin wannan shagalin ba, haushi ya k'ara cikata, amma tasan matakin da zata d'auka akan Shureym, dan taga yana ta rawan jiki akan Basma.


Kowa ka ganshi a wannan lokacin yana cikin farin ciki, amma banda Basma da take cikin damuwa na rashin ganin Aryan agun, dan batasan yayi tafiya ba, sai kuma Safeena da take jin haushi akan mijinta. Anyi taro lafiya an watse lafiya, cikin farin ciki da kwanciyar hankali.


*Washe gari*
An kai ko wace Amarya gidan Mijinta da misalin larfe hud'u na yamma, Deeja an kawota gidan president a side d'in mijinta, haka Meena ma an ajeta acikin gidan president, part d'insu na gefen nasu Yaya Ahmad, Leema kuma an wuce da ita Kaduna zuwa gidan Jamal da Dady ya siya masa, sai Yaya Adam an wuce da matarsa Munayah, an kaita part d'inta dake cikin gidan Sarki, Basma ita ce tayi saura a gida, itama part d'inta yana gidan Sarki kusa dana Yaya Adam, kasantuwar Yaya Shureym bai gama aikin da suka d'aukeshi ba na shekara biyu, yasa zasu wuce America, su cikasa sauran shekara d'ayan daya rage. Sauran baki kuma suna nan basu soma tafiya ba.


Sai Washe gari ko wani Ango ya shiga d'akin matansa, suka fud'e faifan sabon rayuwa cike da So da K'auna.


Da safe su Basma suka wuce airport, da kyar aka raba Basma da jikin Ammi, tasha kuka kaman ranta zai fita, Shureym kuwa sai wani kamata yake yana lallashi, sun shiga jirgi Basma na d'agawa iyayenta hannu, ji take kamar in ta tafi bazata dawo ba, haka suka zauna wuri guda, sannan aka rufe k'ofar jirgi, ana rufewa Shureym ya tashi kusa da ita ya kowa gefen hagunsa, kusa da Safeena ya zauna, ta cika ta batse dan haushi, Basma ta bishi da kallo ganin ya zauna kusa da wata mace cike da mamaki, bata iya cewa komai ba, Safeena ce da taga Basma na kallonsu, sai tayi saurin sakin fusha ta juyo fuskanta tana kallon Shureym, sai ta had'a bakinsu guri guda, ai da sauri Basma ta kauda kai, zuciyarta na dukan uku-uku, bakinta na fad'an
"Inalillahi wa inna ilaihir raji'un" kwantar da bayanta tayi jikin kujera, ta runtse ido, tsananin radad'i zuciyarta yake mata, bawai kishin Yaya Shureym taji ba, tsabar bak'in ciki da irin tsanar hayayyansa take, a tunaninta k'aruwansa ce, Safeena tana ganin Basma ta kauda kai, sai ta janye jikinta ta fara magana k'asa-k'asa tace


"Baby wlh ka b'ata min rai cikin kwanakin nan, naga sai wani rawar jiki kake akan wancen yar iskan Yarinya, to wlh ka sani bazan tab'a raba kwana da ita ba, alkwari ka d'aukan min cewa kai mijin mace d'aya ce, dan haka kai nawa ne ni kad'ai, tunda kace had'in zumunci ne shiyasa na yarda da auren, dan haka da kanta zata gaji da zaman gidanka, harta nima saki tayi gaba"


Gaban Shureym ne ya fad'i, hankalinsa ya tashi, amma sai ya dake ya wayince yace


"Love ke kad'ai ce a guna, me zanyi da Basma, had'in zumunci akai mana dan bana sonta"


Cike da murmushi tace
"yauwa Babyna, kamin alkwara ba raba kwana da ita" murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace


"na miki alkawari, ai bana son b'acin ran ki, ko me kike so zan miki domin in saki farin ciki" Safeena farin ciki ya rufeta, take nan ta manta da b'acin rai data shiga.


Basma kuwa kuka ta shiga yi mara sauti, a haka har barci ya kwasheta.


*America*
Bayan sun kai, mota biyu ke jiransu, d'aya wanda zai d'auki kayan su, d'aya kuma wanda zasu shiga, Basma jikinta a mace ta bud'e k'ofan bayan mota zata shiga, sai Yaya Shureym ya daka mata tsawa yace
"Karki kuskura ki shiga nan, ki shiga gaba ki zauna da driver, ko baki ga ina tare da matata bace?" cikin tsoro Basma ta bar jikin mota cike da tsiwa tace
"Matarka ko Karuwa?" Ai bata rufe baki ba ya tawo da sauri ya wanketa da mari, a razane ta dafe kuncinta tace
"Ni ka mara akan wannan yar iskan, to Allah ya isa mugu fasik'i kawai" tana gama fad'an haka tabar wurin da gudu, ta shige gaban motan daya d'auki kayansu ta zauna, driver ya tukasu suka wuce. Cike da k'unar rai Yaya Shureym ya girgiza kai yayi kwafa, iya ka k'uluwa Safeena tayi, amma ta share suka shiga mota tana sake-saken irin matakin da zata d'auka akan Basma, Lallai dole saita fahimtar da ita cewa ita matar Shureym ce.


Suna isa gidan, ta shiga babban falon gidan Driver ya shigo musu da kayansu, d'akuna uku ne a cikin falon, ko wanne da kaya aciki wanda President yasa aka sanya musu komai na buk'ata aciki, Basma ta zauna akan kushim tana jiran su Shureym su shigo, koda suka shigo sai suka zauna suma, Yaya Shureym ya kira wani kuku, sai gashi da gudu yazo, da yake gidan ai'nahi anan Shureym yake zama, ya Umarcesa daya kawo musu ruwa, da sauri yaje ya kawo musu ya dire musu goran ruwa biyu da cup, yaje zai aje goran ruwa a gaban Basma, sai Safeena ta dakatar dashi cikin turanci tace
"kai zonan" jikinsa na b'ari ya isa gurin ya risina, tace


"daga yau Ni zaka rik'awa aiki amma banda wacen 'yar iskan, domin Mijina ni kad'ai yake aure" tana kaiwa nan tayi shuru, jiki na rawa Kuku ya amsa mata yabar gurin.


Cikin ko in kula Basma ta mik'e tace
"Yaya Shureym ina ne d'aki na?" Hararanta yayi yace


"ban sani ba mara kunyar banza, wlh nan ba Nigeria bane da zaki min iskanci na d'auka, koda kika ga ina lallab'a ki, dama ina yi ne dan ayi auren, saboda kar in b'atawa Iyayena rai, kuma ki sani bana son ki, biyayya ga Iyayena yasa na aureki"


Gaban Basma ne ya shiga bugawa da sauri, saboda tashin hankali, ya cigaba da cewa
"kinga wannan sunanta Safeena, itace zab'ina, kuma munyi aure da ita wata guda daya wuce cikin sirri, ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai Mami na data goya min baya, dan haka in kina son zaman lafiya a gidan nan, to dole sai kin bita sauda k'afa, inba haka ba wlh na lahira saiya fiki jin dad'i"


Basma durkushewa tayi a gurin, saboda k'afafunta bazai iya d'aukanta ba, ta shiga rera kuka wiwi, sai ya kwashe da dariya yace
"wawuya nasan kin d'auka son ki nake ko, tashi dalla ki bani wuri, ki wuce d'akinki shine na gefen hagu, na tsakiya kuma nawa ne, na gefen dama na Safeena ce, kuma na haramta miki shiga d'akina" yana kaiwa nan ya mik'e ya kama hannun Safeena suka wuce d'aki.


Basma cikin tashin hankali taja trolley kayanta, ta shiga d'akin daya gaya mata, katon d'akine mai d'auke da katon gado, sai daga gefe an jera kujeru set, sai bayi da kicin a ciki, kalan d'akin da kayan ciki purple da ash color ne, rufe d'akin tayi da key, ta shiga wanka, kanta ta sanyawa ruwa sosai, saboda zafin da yake mata, tayi kuka kamar zata shid'e, daga bisani tayi wanka ta d'auro alwala ta fito, kaya ta sanya mara nauyi, ta sanya hijab ta tada sallah, sai da ta rama duk Sallolin da ake binta kana tayi Addu'a, ta mik'e ta shiga cikin d'in d'akinta, komai data ke buk'ata akwai aciki, dan akwai k'aramin store a ciki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login