Showing 75001 words to 78000 words out of 79094 words

Chapter 26 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4651

tana zubar da kwalla, murmushi yayi mata tare da matsawa kusa da ita yace "Babynmu yana nan yace ba zai sa Momy da Abbanshi kuka ba" Murmushi tayi, ya taimaka mata ta zauna, sai a sannan ne ta lura da Yaya Ahmad a wurin kunya ce ta rufeta tace "Au ashe Yaya Ahmad kazo?" Dariya yayi yace "Ina zaki san ina wurin bacin ta Unborn Baby d'inki kike" Rufe ido tayi da tafin hannunta tana dariya. Gida suka wuce. Tun daga ranar kowa yasan Basma tana da juna biyu, aiki kuma bata komai sai dai taci ta kwanta, tayi b'ul-b'ul da kyau, soyayya kuma tsakanin Basma da Aryan sai abinda yayi gaba. A haka har cikinta ya kai wata tara, cikin yayi k'ato ta kubbura, Haihuwa ko yau ko gobe, Yaya Aryan yak'i yarda Basma ta koma gida shike jikilan komai nata.


*Rahma Ce*
[8/20, 9:16 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *39.*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


*Cikin Basma Wata Tara Da Sati Biyu*


Basma ce a cikin kitchen tana zuba Peppe Meat a plet, fitowa tayi tana jan k'afa da alama cikinta yayi mata nauyi sosai, zama tayi akan kushim ta fara ci tare da cuna baki alamar yaji ya dame ta, haka tayi ta ci tana gumi tare da shan Gwaba juice, haka ta cinye tas tare da lashe hannu, da alama bai isheta ba sai ta kwalawa d'aya daga cikin masu aikinta kira
"Uwale, Uwale" da sassarfa ta fito ta risina tace
"Hajiya gani"
"Yauwa k'aromin peppe Meat d'in nan, ki zuba min da yawa sannan ki d'auko min goran ruwa da cup ki kawo min"


Jiki na rawa Uwale ta wuce kitchen ta kawo mata gaba d'aya duk abinda take so, zama ta gyara ta cigaba da cin kayanta tanaci tana shan ruwa saboda bala'in yaji data zuba a ciki.


Sallaman su Meena da Deeja ne ya katse ta, ta amsa musu, zama duk suka yi suna yi mata tsiya
"kullun in muka shigo sai mun ganki da wani abun kina ci, acici mala'kan tauna" Meena ce take fad'an haka.


Dariya kawai tayi musu ta cigaba da cin abin ta, hira suke sosai suna tattaunawa akan taron daya gudana a garin Katsina wanda Basma bata samu zuwa ba, hak'ik'a taron ya k'ayatar kuma sun tattauna akan Matsalolin masu yima Yara k'anana fyad'e, Basma tace
Wallahi nayi missing taron kuma ba haka naso ba"


Deeja ta lura da yanda Basma take yatsine fuska cikin kulawa tace
"K'alli yadai naga tun d'azu kina ta yamutse fuska kodai abin yazo ne?"


Murmushi kawai tayi tace
"inda yazo kya ganni ina d'irkan abinci"
Dariya suka yi mata, Meena ta mik'e tace


"Kinga bari naje na shirya Yaya Naufal ya kusa shigowa kunsan da an sakko Sallan Juma'a suke dawowa"


Deeja ma mik'ewa tayi tace
"Hakane 'Yar Uwa, nima bari naje na shirya kinsan yau akwai yini a gidan Abba bayan Sallan La'asar" Nan suka yiwa Basma Sallama, sai tace


"Uhum masu Maza to sai ku tafi kan k'uda ya riga ku" Dariya suka kwashe dashi suka fita.


Basma ji tayi cikin ta yayi mata hak'e-hak'e da kar take numfashi, gyara zama tayi ta jingina jikin kushim, a fili tace
"Ya Rabb ka rabani lafiya da abinda ke cikin nan, kayi masa albarka da kyakkyawan Albarkanka, Ameen, yau dai cikin nan ya d'aure min sosai to Allah gani gareka"


Bata rufe baki ba cikin ya fara tsingulinta, da sauri ta mik'e tana jan k'afa ta shiga d'aki ta d'auko key na Motanta, fitowa tayi ta bama masu aikinta order akan abinda take so suyi mata, sai ta fita tana nishi, gaba d'aya ciwon mara ya soma damunta, driver ta kira yazo ta mik'a masa key Motarta tace
"Kaini Asibiti" ba musu ya amsa cikin girmamawa.


Kafin sukai Asibiti ciwo ya tsananta salati kawai take yi, da sauri Driver ya kira Nurses suka zo suka shiga da Basma cikin Asibiti d'akin Haihuwa suka wuce da ita, Nurse Sa'a ta dubata tana 8cm, da alama ta jima tana nakud'ar a tsaitsaye inji Nurse d'in, Basma nak'uda ta taso sosai Aryan take kira tare da Abbanta, hawaye ya na zuba, Addu'a take da niman sassauci a wurin Allah.


Yaya Aryan yana gun Aiki ji yayi Kansa ya sara masa, gabansa ne ya fad'i, a lifi ya furta Basma, da sauri ya mik'e yabar abinda ya keyi ya soma had'a kayansa, jaka ya d'auka ya sanya hularsa ya fito, Massinger ne yace
"Yallab'ai akwai masu jiranka suna wurin Alhaji Naufal"
Yana tafiya yace
"kace su dawo ranar Monday wani uziri ya taso min".


Mota ya shige ya kamo hanyar gida, wayar Basma yaketa kira amma bata d'auka ba, Basma a gida ta bar wayan, hankinsa ne ya kuma tashi, wayar Deeja ya kira ya tambayeta Basma tace


"Ban jima da fitowa daga part d'inku ba ina ganin tayi barci ne" Cikin damuwa yace "ok" ya kashe wayar.


Basma ta cika 10cm haihuwa ta taso amai ta fara yi, haihuwarta mai fayar baki ne, amai take sosai tana yunk'uri, bayan ta gama aman sai nak'udar ta lafa a hankali barci ya fara fizgarta, hutun minti biyar tayi nak'udar ya dawo, cikin ikwan Allah bata k'ara minti goma ba ta haifo d'anta Namiji mai kama da Aryan sak. Yaron kato sai ihu yake Hamdala Basma ta shiga jerowa da yiwa Allah Tasbihi.


Yaya Aryan ya shiga kan layinsu kenan wayarsa ya d'auki k'ara, Likintansu ne ya kira shi ya d'auka suka gaisa sai Likita yace
"Madam tazo ita kad'ai Asibiti ba tare da kowa ba sai Driver, yanzu haka tana Labour Room, muna so a kawo kayan Baby"


Da k'arfi Aryan yace
"ta Haihuwa ne?"


Likita yace
"A'a tana gab, ku kawo kayan da sauri"


Godiya Yaya Aryan yayi masa, sai ya juya akalan Motansa ya nufi Asibiti, wayar Deeja ya kira yace mata
"Ki shiga part d'inmu ki had'o kayan Baby, da wanda Basma zata canza, da duk kayan da ake buk'ata a Asibiti sai ku tawo" bai jira amsar da zata bashi ba ya kashe.


Farin ciki ne ya rufe Deeja ta fito da sauri, Allah yasa ta idar da Sallah kenan tasa kaya. Had'a kayan tayi ta shiga wajen Meena tare suka tawo suka kira su Momy a waya suka sanar dasu.


Basma an ciro Mahaifa an gyara mata jiki, kaya ya rage a kawo ta sauya, Baby ma haka, Yaya Aryan a sittin ya shiga d'akin Haihuwar bai jira an bashi izini ba, Nurse Sa'a ta dakatar dashi


"Dan Allah Kaje waje mu gama tukuna saika shigo"


Ko saurarenta bai yi ba ya isa wurin Basma ya kama hannunta gam yace cikin muryan tausayawa


"Babyna Allah ya saukeki lafiya" tare da matsar kwalla. Murmushi Basma tayi sai ta kai hannunsa wajen cikinta tace


"Babynmu baya cikina yanzu dan ya fito" ware ido yayi ya shiga waige-waige, hango gadon Yaron yayi ya isa wurin, ya ganci a cikin towel an k'udun-dune shi, hannunsa na rawa ya kai ya d'auko shi, farin ciki ya sanya shi fitan kwalla, ya shiga jero masa Addu'a tare da godewa Allah, Basma na kallonsu tana murmushin farin ciki cike da so da k'aunar su.


Nurse Sa'a ce ta amshi Yaron don su sanya masa kayansa da su Deeja suka kawo, Basma ma sanya kayanta tayi Aryan ya d'auketa cak ya kaita d'akin hutawa na masu Haihuwa. Meena da Deeja suka rufa musu baya, dai-dai lokacin Ammi tazo tabi bayansu. Momy tak'i zuwa saboda kunyar 'Yar fari.


*Bayan Sallan La'asar*
Aka basu Sallama suka wuce gidan Abba gaba d'aya. A side d'in Ammi Basma suka sauka tare da Babynsu. Nan fa kan ace miye gida ya soma cika da 'yan barka sunata zuwa, Anty Husnah ma da sauri tazo gidan dan ganin idon Basma an zama Mama, tasha tsiya wurin su Deeja, amma kuma sun yabama k'ok'arinta da juriya data iya kai kanta Asibiti. Abba yayi Murna da ganin jikinsa ya amsa Yaron yayi masa Addu'a tare da hud'uba. Duk sun sanar da dangi wanda suke nesa, da yawansu sun d'aura d'amaran zuwa Abuja a washe gari, kuma in suka zo sai anyi suna zasu tafi. Leema kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Abuja don Murna, haka ma Safeena ta k'osa Gari ya waye su kamo hanya, Shureym sai da yaji wani iri aransa yace "Da yanzu wannan Yaron nawa ne, Allah Sarki, na amshi wannan k'addaran tawa, ka yafe min dukkan kuskuran dana aikata". Nima na tayaka da Ameen.


*Ranar Suna*
Yaro yaci sunan *Aliyu* Mahaifinsu Aryan, Suna kiransa da *Hydar*, ba k'aramin shagali suka shirya ba, wannan hidima ya tara Manyan Mutane Sarakuna da Manyan 'Yan Kasuwa. An shirya k'ayataccen Walima bayan Sallan Isha'i a babban hol dake Abuja, hatta Abba dasu Mai Martaba, Dady duk sunje wurin, har Momy da take kunyar 'yar fari taje wurin, su Kaka Ma'u, Inna, Malam kawai suka bari a gidan, Wata Babbar Malama suka gayyata tazo ta bada Fatawa akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*.


Da farko Tarbiyyan Yara sun rataya akan Uba da Uwa wanda aka samu wannan D'a daga Jikinsu. Uba dole ne ya samarwa 'Ya'yansa Uwa Tagari haka itama Uwa dole ne ta samawa 'Ya'yanta Uba Nagari, Tarbiyya yana farawa ne tun daga ginshik'in Neman Aure. Ma'aurata dole ne a yayin saduwa suyi Addu'a kamar yanda Monzon Allah s.a.w ya koyar damu kafin iyaye su kaiga saduwar Aure, kunga kenan an fara samar da D'an ta kyakkyawa hanya, daga nan lokacin da aka samu cikin wannan d'a, Uwa dole ne ta zama mai hak'uri tare ya yawaita Addu'a don samun d'a Nagari, Uba kaima yana da kyau ka sanya ido ka bata kulawa sosai tare da Addu'a har Allah ya sauketa Lafiya.


Wasu Iyayen sukan fara da tsinewa ciki tun kan yazo Duniya, sai kuji Uwa na cewa 'Wannan shegen cikin ya isheni da muntsili' 'Na k'osa wannan jarababen cikin nan ya fito na huta' Wannan cikin kaza-kaza, tun d'a na ciki wata Uwar ke fara lalata shi kafin ya fito Duniya, dan haka jan kunne garemu Mata Ku kula sosai yayin irin wannan halin da kuka tsinci kanku, mugun furuci yana lalata Tarbiyyar Yaro, ki zama mai hak'uri da juriya domin a wannan lokacin kina cikin wani jarabawa ne mai dinbin lada, ki zama mai yin Addu'a da niman sauk'i a wurin Allah yayin da cikin ya dame ki.


Sannan bayan an haifi Yaro, Uba zai masa kiran Sallah da hud'uba da sunansa, a wannan lokacin d'a zai hanasu barci wani Uban yaita tsaki yana zage-zage, wata Uwar kuma ma kaji tace 'wane kaza ka cika shegen kuka ai Allah wadaran wannan rikici naka', to wallahi dole sai mun kiyaye fidda mugayen kalami akan Yaranmu. Duk abinda Uwa zata yi dole sai kin sanya ido da hak'uri da kuma Juriya, kuma dole sai kin fara gyara halayyarki kafin ki fara kafa tubalin Tarbiyyan Yaranki. Domin wasu Yaran yayin tasowarsu sukan fara koyan wasu halayya da Uwarsu keyi, koda ace mara kyaune a ganinsu mai kyaune tunda sun ga Uwarsu tayi. Dan haka dole mu Iyaye Mata muna sanya ido a kan Yaranmu domin Mune Makarantar farko ga Yaranmu. Sannan da zarar yaro ya taso nuna masa yin Ibada akan lokaci, koyar dashi Addu'an safe da maraice, na shiga bayi, fita gida da sauran Azkar, kasance mai jansu a jiki kina tunatar dasu Tsoron Allah, ki sanyawa d'anki Tak'awa da kuma Tauhidi, nuna masa yanda Azabar Allah yake a ranar gobe k'iyama in suka sab'a masa, ki tsawatar musu in suna wasa da Sallah, ki jasu a jikinki a nan ne zaki rik'a jin dukkan matsalolin su, rik'a duba takardunsu na makaranta kina ganin abinda yara ke ciki game da karatunsu.


Kaima Uba ka ja 'ya'yanka a jikinka banda d'aure fuska, ko daka dawo daga aiki su rik'a gudu suna tsoron fad'anka, zauna dasu tamkar abokanka kayi wasa dasu ka tunatar dasu hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akan su. Ka sanya su a makaranta masu kyau, karka zama me kyashin biya musu kud'in makaranta.
Sannan mu sani yawan duka baya shirya yaro sai dai ya kangarar dashi, mu rik'a musu fad'a da Nasiha, karmu gaji. Insha Allah duk abinda ya gani na sabon Allah zai guje shi, zai kasance mai gudun B'acin ranku, zai zama kamili nagari abin sha'awa gun kowa, Mutane za su rik'a kwatantaku cikin sawun Iyaye Nagari, haka yaron za'a rik'a kwatance dashi a cikin 'Ya'ya Nagari. Allah ya bamu ikwan Tarbiyyan tar da Yaranmu bisa tafarkin Al-Qur'ni da Sunnah. Ameen ya Rabb


Sai k'arfe Goma na dare aka gama wannan Walima, kowa ya koma Gida lafiya. Walimar ya burge Mutane sosai game da yanda Malamar ta bada bayani akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*. Anan Mami ta gane cewa tayi kuskure wajen Tarbiyyan Shureym, ta kuma d'auki Alkhawarin niman gafaransa, da gyara kuskurenta akan jikokinta.


*Bayan Wata Guda*
Deeja itama ta sullub'o 'Yarta Mace kyakkyawa mai kama da Basma, ranar suna taci sunan Umma 'Aisha'. Kamar yanda aka yi taron sunan Hydar haka akayi na Aisha, an shirya Walima kyatacce akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*


Anyi taro lafiya aka watse lafiya. Inna itace ta zaunawa Deeja har zuwa tayi Arba'in.


*Rahma Ce*
[8/20, 9:17 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *40.*


*_Final page_*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


*Bayan Kammala Wankan Jego*


Basma ta gama wanka, zaune take tasha kwaliya cikin d'inkin riga da sket na atamfa, Baby Hydar yana gefenta ta kwantar dashi, wayarta ce a hannunta tana latsawa da alama charting take yi, Sallaman Yaya Aryan shine ya katseta ta d'ago cikin murmushi tare da kallon so ta amsa masa, isa yayi kusa da ita ya zauna tare da rausayar da kai gefe yace


"Babyna kinga yanda ki kayi kyau kuwa, kamar Baby Hydar bai fita a jikinki ba, meye sirrin?"


Murmushi tayi wanda ya bayyana farin cikin ta tace


"Myn bafa komai, Ni ce dai yanda ka sanni sai dai fa na samu kyakkyawan kulawa wurin Ammi dan haka ita zaka tambaya sirrin"


Hararan wasa yayi mata yace
"Kinsan dai babu wannan tsakanina da Ammi, a bakinki ya kamata naji komai, yanzu dai mu bar wannan maganar yaushe zaki dawo gidanmu, ina missing d'inki Baby love, da kyar nake iya barci fa" ya k'arasa maganar cikin muryar tausayi.


Kanne masa ido d'aya tayi tace
"Uhum Myn nifa sai nayi wata biyu zan dawo"


Ido ya zaro waje yama kasa magana, da gudu ta mik'e ta bar wurin tana kwasan dariya, girgiza kai yayi ya d'auki Baby Hydar yabi bayanta, d'akinta ya sameta ya kwanar da Baby Hydar ya matsa wurin ta yace


"Babyna ko so kike in shiga wani hali?"


D'ago fuska tayi tana kallonshi cikin ido tace
"Baby nima na kosa na dawo gareka amma bansan ya zanyi ba, bazan iya sanar wa Ammi hakan ba, ka k'ara hak'uri suma sunsan ya kamata na koma karka damu"


Ajiyar zuciya ya saki tare da busa iska mai zafi yace
"ki shirya zanzo gobe Insha Allah zamu fita"


Ido ta zaro waje tace
"ina zamu kuma Myn? kunya nakeji"


Murmushi yayi yace
"Hotel zamu domin ina da buk'atar Babyna in ba so take in fara biye-biye ba"


Da sauri ta had'e bakinta da nashi domin bata son ya k'arasa maganar, sai da suka d'auki minti goma kana ta janye jikinta tare da sauke ajiyar zuciya, cikin kasalan murya tace


"Myn karka k'ara furta kalman da ya fito a bikinka domin kanada ni, Insha Allah zan kasance da kai a koda yau ba zan gaji da kai ba tunda nima inda buk'atarka, zan shirya mu fita amma gidanmu zamu ba Hotel ba, domin in samar maka farin ciki sweet babyna" saita manna masa kiss a goshinsa ta mik'e, tana mai cewa


"bari na kawo maka abinci dan nasan da wiya in kaci na rana".
Bud"e k'ofar da zata yi ne taci karo da Ammi, Ammi tace


"Ina zaki kike sauri haka?" Sosa k'eya tayi tace
"Abinci zan kawowa Yaya Aryan"
"Ok ga wannan ki shanye shi zuwa anjima da yamma" ta amsa goran tana godiya.


*Bayan Sallan La'asar*


Ammi ta sameta a d'aki tace
"Basma je kiyi wa Momynki Sallama yau zaki koma gida, da fatan kin gama shirya kayanki?"


"Eh Ammi na kammala bayan Yaya Aryan ya tafi"
"To madalla" saita fita.


Tana isa part d'in Momy ta sameta zaune saman kushim tana karanta wani Jarida, sallaman da tayi ne yasa ta aje Jaridar a gefe ta amsa mata, Basma ta isa gefenta ta zauna tare da kama hannunta tace


"Momyna sannu da hutawa"
"Yauwa My Basma"
"Nazo muyi sallama ne Ammi tace yau zan koma gida" ta k'arasa maganar cike da shagwab'a.


Hararan wasa ta mata tace
"Basma sai yaushe zaki girma da yin shagwab'a ne?"


Murmushi tayi ta langwab'ar da kai gefe tace
"Uhum Momy ina dake fa kinga kuwa bazan daina shagwab'a ba, ga Abba da Ammi, ga Dady da Ummin kd dasu Kaka Ma'u duk inada ku fa"


Momy tayi dariya tare da lakace hancinta tace
"Ki dai ragewa su Hydar"
Kunya ya rufeta ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi tare da wasa da yatsun hannunta.


Momy ta gyara zama tare da kiran sunan ta, Basma ta d'ago taga babu alamar wasa a tattare da Momy, natsuwarta ta tattaro tace
"Na'am Momy"


Momy tace
"Basma ina son in miki tuni akan hakk'in Mijinki dake kanki, Mata da dama wasu na kuskure akan da zarar Mace ta haihu saita jingine buk'atun Mijinta ta kama na Yaronta kuma wannan ba dai-dai bane, hakk'in Miji shine farko kafin hakk'in 'Ya'ya, A Ranar Gobe K'iyama Allah yana fara tambayan hakk'in Miji ne kafin hakk'in 'Ya'ya, sannan Aljannarki yana k'afar Mijinki inya d'aga ki shiga Aljanna, in kuma ya danne ki auka wuta. Allah yayi mana tsari da wuta Ameen.


Dan haka sai munyi karatun tanatsu sosai, Mata da dama suna jingine need d'in Mijinsu da zarar sun Haihu, wata ma ba tada lokacin wani hira da Miji ko girka masa abinci, kullun itace hidimar yaranta ba ruwanta da farin cikin Mijinta ko b'acin ransa, wata ma saboda d'anta saita hana miji hakk'insa, wai adole ita mai d'a, to wallahi mu hankalta Musani shi Miji yanada matuk'ar mahimmanci dole ne mu rik'a kula dasu muna basu lokutanmu domin samun da cewa.


Ki ware lokutanki kina tsarawa kanki ko wanne ki fita hakk'insa, Miji da kuma Yaranki, su Kansu mazan suna tausayawa Matan akan wasu hidimomin gidan har suke tayasu ma.


"Maza da dama suna fuskanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login