Showing 9001 words to 12000 words out of 79094 words

Chapter 4 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

5143

yace
"in kika je ne har kika bigeta?" gefe ta koma ta samu wuri ta zauna, shima binta yayi ya zauna, nan ta bashi labarin yanda ya faru. Ya girgaza kai yace
"Allah ya kyauta gaba, amma meyasa kikayi driving da kanki" murmushi tayi tace
"Yaya Ahmad wlh kawai hakanan naji ina sha'awar tuka kaina" Dariya yayi yace
"hmm su Basma rikici, kije gida kawai saiki turo Shugaban mai kula da sashin Ammi Baba kulu tazo ta zauna da ita, tunda ke yau nasan kinada baƙo ya kusa sauka ma", murmushi tayi tace
"tom Yaya Ahmad bari naje anjima zan dawo insha Allah"
"ok sai kin dawo, ki kula da kankifa"
"insha Allah Yaya zan kula" suka rabu cikin farin ciki.


Tana isa gida taje ta samu Baba Kulu ta sanar da ita saƙon Yaya Ahmad, driver zai kaita, cikin sauri Baba kulu ta tafi.


Basma tasa masu aikin Kicin na ɓangaran Ammi ta sanar musu abincin da za suyi mata na tarban baƙonta. Sai ta nufi sashin Momy ta samesu zaune da Ammi suna magana ta gaishesu kana tace
"Momy na kai mata saƙon tace za kuyi waya" Momy tace
"ok, amma naga kin daɗe ko kin biya gidan hutun naki da kika saba?" murmushi tayi tace
"a'a Momy wallahi a kan hanyar dawowa na gida, na bige wata, yanzu haka tana asibity, na tura Baba Kulu ta zauna da ita zuwa anjima zan koma" cikin tashin hankali Ammi da Momy suka hada baki
"subhanallah da fatan dai abin da sauki" murmushi tayi tace
"da sauki kamar yanda Yaya Ahmad ya sanar dani shiyasa na taho ma" Ammi tace
"to Allah ya bata lafiya ya kuma tsare na gaba" duk suka amsa da "Amin". Saita shiga ɗakinta dake sashin Momy.


Tana Shiga ta faɗa makeken gadonta wayarta ta jawo ta duba taga miss call ɗin su Meena, kiranta tayi bugu buyu ta ɗauka, Meena bata jira Basma ta yi magana tace
"wlh Basma ba kida kirki, jiya ko ki kiramu kiji ya muka sauka" cikin natsuwa tace
"Afwan ya habibty, nima Momy saida tamin faɗa, haushin haka yasa ban kiraku ba" Nan dai suka shirya, Basma ta bata labarin accident ɗin da tayi, Meena ta mata Allah ya kyauta na gaba kana suka kashe wayar.


Basma ta kuma kiran Leema itama mita tayi mata ƙorafi kamar yanda Meena tayi nan ta bata haƙuri suka yi hira kana suka yi sallama.


Bayan sallan asri Basma tayi wani wanka ta sanya baƙar jallabiya mai ɗauke da kwalliya pink color, tayi rolin da gyalen abayan, saita fito, abinci ta ɗauka a baske kamar yanda Momy tasa aka dafawa mara lafiyan, saita shiga mota driver ya jata zuwa asibity.


Ta nufi ɗakin da aka sauyawa mara lafiyan, ta shiga ta sameta zaune jingine da pillow, idonta a lumshe da alama tana hutawa ne, Baba Kulu ta amshi kwandon abincin tace
"sannu Basma" cikin fara'a Basma ta ce
"yauwa Baba Kulu, ya mai jiki,
"da sauki, ta farka tun ɗazu amma fa kuka take tayi min, wai ita zata tafi, da kyar na lallashe" cikin kulawa Basma ta kai dubanta ga mara lafiyan, wuri ta samu gefen gadon ta zauba ta kama hannun mara lafiyan tace cikin sanyin murya
"baiwar Allah ya jikin da fatan dai babu wata damuwa" idonta cike da hawaye tace
"lafiya lau ni naji sauƙi, ni dai ku taimaka ku kaini gida, wlh nasan hankalin Umma na da Yaya a tashe yake in basu ganni ba" cikin nutsuwa Basma ta kuma cewa
"kiyi hakuri, ya sunanki?" cikin damuwa tace
"Khadija" girgiza kai tayi a laman gamsuwa tace
"kiyi haƙuri kici abinci zan kira likita yazo ya bamu sallama saina kaiki gida" cike da fara'a tace
"nagode Hajiya" Basma tayi murmushi tace
"sunana Basma ba Hajiya ba" itama Khadija murmushi tayi kawai batace komai ba.


Baba Kulu ta sanya mata tuwon semo miyar agushi, ga wani plet ɗin ta sanya mata farfesun kayan ciki ta kuma zuba mata drink na 5alive a cup, a kan gadon ta jera mata, cikin kulawa Deeja tace
"nagode Baba" dama da ɗan yunwanta ta fito zuwa wurin saro kwai, bata kaiga siyo bane Basma ta bigeta, saita buɗe ciki ta kwashi girki Basma sai kallonta take yi, a zuciyarta tana yaba kyawun khadijan sai dai a irin shigan da taganta dashi ya tabbatar mata masu ƙaramin ƙarfi ne, hakanan taji Kadijan ta kwanta mata a rai saboda ta lura tanada sauƙin hali, bayan ta gama cin abincin suka kawo mata wurin wanke hannu ta wanke kana ta kalli Basma tace,
"Hajiya au, kince sunanki Basma ko" ta gyada mata kai alaman eh, ta cigaba dacewa
"ke nake jira ki kira likita in tafi gida, wlh Ummata zata damu da Yaya Aryan, murmushi Basma tayi mata ba tace komai ba a zuciyarta tana maimaita sunan Aryan, hakanan taji sunan tayi mata daɗi.


Wayarta da ɗauka ta kira Yaya Ahmad bai ɓata lokaci ba yazo, yace
"Basma ashe kin dawo?"
"eh Yaya Ahmad na dawo, dama Patient ɗinka ce tace a sallameta zata gida" dubansa ya kai wurin Khadija yayi mata murmushi yace
"haba dai kiyi haƙuri ki kwana gobe zaina sallamaki" Deeja ta zaro ido waje tace cikin tsoro wlh Ummata nake ji da Yaya Aryan, kuyi hakuri Ku sallameni" shima Yaya Ahmad cikin zolaya ya zaro ido yace
"tafɗi, ni bazan sallameki ba sai gobe in Allah ya kaimu" ai sai Deeja ta fara fidda kwalla, Basma tace
"Yaya kaga kuka take yifa, ka sallameta kawai sai a bata magunguna, in yaso ni da kaina zan dawo maka da ita sai ka kara dubata" cikin fara'a yace
"Basma rabu da ita wasa nake mata, dolena na sallameta kafin ta nima hanyar guduwa" dukansu sai suka sa dariya amma banda Deeja da ta sunkuyar da kai ƙasa tana murmushi.


Yaya Ahmad ya rubuta mata sallama yace
"Basma zaki dawo da ita nan da kwana biyu"
"OK Yaya insha Allah zan dawo da ita". Nan Yaya Ahmad ya kira driver ya kwashi kayan su yasa a mota, ya kalli Baba Kulu yace
"Baba kuje gida ni zan kaisu Basma", cikin kulawa Baba Kulu tayi godiya kana ta tafi.


Ya kai dubansa ga Basma yace
"muje ko, da fatan ta sanar miki da inda take"
"Ok, Yaya ba damuwa zan tambayeta a mota".


Sai suka kama hanya, Yaya Ahmad ya shiga dasu shopping complex ya siya mata kayan ciye-ciye, kana suka ɗauki hanyan gidansu Deeja.


Aɓangaren su Umma kuwa Yaya Aryan zaune yake a gidan yayi jugum, Umma ma tayi tagumi tace
"wlh hankali ya tashi har yanzu ace bata dawo ba? ban taɓa aiken Deeja ta dad.ɗe haka ba, gashi kaje har wajen masu kwai bata ba labarinta, sunce ma bata jeba, Allah yasa ba sace min 'ya akaya ba" ta ƙarasa maganar tana matsar kwalla, Yaya Aryan cikin damuwa yace
"Umma kiyi haƙuri insha Allah za'a ganta, bari na ƙara fita in duba ko Allah zaisa muji wanda yaganta" ya miƙe tare da cewa
"Umma saina dawo" ta amsa da
"to Allah yasa a dace".


Sun shigo Layin su Deeja saita tace
"Ku saukeni a nan in ƙarasa, nagode Allah ya saka da alkhairi" Basma ce ta juyo da sauri, da yake tana kusa da Yaya Ahmad dake tuƙasu, tace
"haba dai Khadija, ki bari mu kaiki har gida mana", cikin dishewar murya tace
"a'a Ku bari kawai na tafi" cikin kulawa Basma tace
"daga nan zuwa gidanku da nisa?" tace
"a'a ba nisa nan sama ne kaɗan" Basma ta kai dubanta ga Yaya Ahmad tace
"Yaya saukemu anan mu ƙarasa, ƙila bata so wasu suga an sauketa a mota ne" cike da kallon tuhuma yace
"kinsan dai ba tare muke da escot ba" Basma ta gyaɗa kai
"na sani Yaya Ahmad, insha babu abin da zai faru"
"Ok, kuje bari na jira ki anan, amma karki daɗe, tace
"Tom Yaya na tnx.


Sun kama hanyar gidan su Deeja, suna zuwa ƙofar gidan Deeja tace
"ga gidan mun kawo" Basma tace
"Ok mu Shiga" Deeja tana shiga ta hango Umma zaune tasha kuka idonta yayi ja, da ganinta tana cikin damuwan rashinta ne, da gudu ta ƙarasa ta faɗa jikin Umma tace
"Umma na dawo" cikin damuwa Umma tace
"Khadija ina kika tsaya tun d.ɗazu kin asamu hankalinmu a tashe?" tace
"Umma tafe nake da baƙuwa" da sauri Umma ta kai dubanta hanyar waje ta hango Basma tsaye tana kallonsu, da sauri ta miƙe tace
"lale sannu da zuwa, ƙaraso ciki mana" da murmushi a fuskarta ta ƙarasa, wuri ta samu ta zauna kan tabarma cikin nutsuwa tace
"Umma ina yini" nan suka gaisa kana ta yiwa Umma bayanin duk abin da ya faru, Umma tayi godiya da kulwanta sannan tace
"sun yafe ba komai, nan dai Basma ta miƙe tayi musu sallama tare da aje musu bandir ɗin 'yan budu ɗai-ɗai har dubu Hamsin, ga kuma siyayyan da Yaya Ahmad yayi mata, Umma cike da tsoro tace
" 'yar nan mun yafe ki d.ɗauki kuɗinki" cikin fara'a Basma tace
"Umma nima 'yar kice, wannan kyauta nayi ma Ummata, kiyi haƙuri ki amsa" da farin ciki Umma tayi mata godiya, sai suka rakata har ƙofar gida, kana ta wuce su kuma suka shiga gida.


Basma ta tafi cike da tausayinsu ganin irin gidan da suke ciki, hakanan taji a zuciyarta tana son ta taimaka musu, amma tana tunanin ta wace hanya zata taimakesu, da haka tayi nisa cikin tunani bata ankaraba taji tayi karo da mutum, da sauri ta ɗago ta kalle shi, ido Huɗu suka yi da juna, nan take zuciyarta ta buga, haka shima nashi ya buga, Aryan sarai ya gane ta, haka itama ta gane shi, cikin yanayi na ko in kula Aryan yace
"Ke ba kida hankali ne zaki riƙa tafiya ba kya kallon hanya, ko makauniya ce ke da kike tafiya bakya kallon gabanki, ko har gefen hanya kina takama dashi ne?" cike da jin zafin abinda ya gaya mata, wato ma ya ganeta ta faɗa a zuciyarta, tace cikin tsiwa
"Kaine ba kada hankali ƙazami kawai, kuma kaine makaho da baka ganin kan hanya" cike da ƙunan zuciya ya d'aga hannunsa ya kwashe ta da mari, abinda bai taɓa yiba kenan ya daki mace, nan fa mutane suka fara taruwa, Basma ta dafe kuncinta tace
"ni ka mara? kasan ko wacece ni?" yace
"Na mareki koke wacece, kiyi abinda za kiyi, kina tsammanin zan mance baƙar fuskarki ne? Mara tunani kawai, dalla ɓace min da gani" ya ƙarasa maganar cikin zare mata ido, nan take tsoranshi ya mamaye mata zuciya, cikin kuka gudu-dugu Basma ta bar wurin tana ƙoƙarin isa wurin motansu. Shi kuma yabi bayan ta da kallo yayi kwafa sannan ya cigaba da tafiya.


Tunda take ba'a taɓa wulaƙanta ta irin na yau ba, tana isa ta faɗa mota, Yaya Ahmad cikin tashin hankali yace
"lafiya Basma me aka miki? meya faru? haka ya jero mata tambaya babu amsa, illa a cikin kuka tace
"Yaya Ahmad muje gida, muje gida". Cikin tashin hankali ya tada mota ya figeta a guje.


Aryan yana tafiya ya fara tunani, a wani ɓangare na zuciyanshi yana farin cikin rama marin da yayi, wani ɓangare kuma yana gargaɗinsa, meyasa ya mareta, nan take wannan tunanin ya rinjayi wancen sai yaji zuciyansa yayi masa ba daɗi da haka ya ƙarasa gida.


*Basmatyyy ansha mari ooo 😉 ko kunga laifin Aryan daya rama? muje zuwa...*


*Rahma Ce*
[8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *6.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


Ya Ahmad saida ya bari sun kusa gida sai ya samu guri yayi parking, ya kalli Basma yace
"Basma ki gaya min me ya faru? dan bazani gida dake a haka ba" share hawayenta tayi ta fara bashi labarin duk abinda ya faru, bata ɓoya masa komai ba tun farkon haɗuwanta da Aryan, saida ta gama tsaf kana ya gyara zamansa ya fuskanceta da kyau yace


"Basma gaskiya baki kyauta ba, domin ke kika ja komai ya faru, meyasa idonki zai rufe saboda samun duniya ki wulakanta Mutum, Allah da kanshi ya karrama ɗan Adam ya fifitamu akan Aljanu, Basma yanzu halittan Allah ya cancanci wulakanci? haba Basma ban san yaushe kika sauya halinki ba, kina taƙama da mulki da kuɗi ko, to wallahi Allah zai iya amshesu daga hannun mu ya bama wasu, ki sani wannan duniyar ba matabbata bace munzo cin kasuwa ne, duk kuma abinda muka shuka shi zamu girba a makomarmu, Basma na lura tunda kuka tafi England ke dasu Meena duk kuka sauya hali"


Jikin Basma ne yayi sanyi sosai, tabbas maganganun sa sun ratsata, cikin mutuwar jiki tace
"Yaya Ahmad wallahi yanzu hankalina ya dawo jikina tabbas ban kyauta masa ba, nagode daka tunatar dani da kayi, lallai na shagala da ruɗin duniya, Yaya Ahmad bansan me ya shiga kaina ba" saita ƙarasa maganar tana kuka, murmushi yayi yace
"Ai shi Allah mai gafara ne, inaso duk lokacin da kika ƙara haɗuwa dashi, to ki bashi haƙuri" tace
"to Yaya Ahmad insha Allah zanyi yanda kace" wannan karan dariya yayi har haƙoransa na fitowa yace
"yauwa ƙanwata farin cikina, yanzu bani labarin yanda kika ƙarasa a gidansu Khadija" murmushi tayi ta soma bashi labari, masha Allah yace, kana ya tada motan suka wuce gida suna hira cikin nishaɗi tamkar Basma batayi kuka ba.


Yaya Aryan yana isa gida ya tadda Umma riƙe da kuɗi tana juyasu a hannunta, da sauri ya ƙarasa yace
"Umma wannan kuɗin fa? Khadija ta dawo kuwa? dan na zaga sosai ban ga mai kamarta ba, na tambaya ba wanda ya ganta" murmushi Umma tayi tace
"Khadija ta dawo yanzu ta shiga bayi, ashe wai wata Yarinya ce ta bigeta a mota suka kaita asibity" nan dai Umma ta labarta masa abinda ta sani, Yaya Aryan ya jinjina lamarin yace
"to Allah ya kyauta nagaba, yanzu duk wannan kuɗin su suka bada?"
"eh su suka bayar, harda siyayya ma suka yi mata na kayan ciye-ciye" kafin yayi magana Khadija ce ta fito daga wanka tace
"sannu da zuwa Yaya Aryan"
"yauwa Khadija" nan suka gaisa itama ta ƙara bashi labari, Umma ce ta miƙa masa kuɗin tace
"ga kuɗin saika gyara runfarka daga nan ka biya kuɗin haya, sauran kuɗin ka siya mana kayan abinci" Amsa yayi cikin natsuwa yace
"Allah ya saka da alkhairi, bari na fita in duba Muntari kafinta sai mu fara maganar gyaran"
"to Aryan saika dawo, Allah ya muku albarka" duk suka amsa da "Ameen" kana ya fice.


Bayan sallan Magrib jirginsu Prince Shureym ya iso, yana sauka a jirgi motoci na jiransa, ya ƙarasa su tafi gidan president.


Bayan sun kai ya wuce falon shugaban ƙasa ya gaisheshi, kana ya wuce part ɗin Ammi ya gaisheta, ya shiga wurin Momy itama ya gaisheta, saiya wuce part ɗinsu Yaya Ahmad can ne masaukinsa, yana shiga falon sai ya faɗa wani ɗaki, wanka yayi ya kimtsa saiya gabatar da sallan Magrib, yana idarwa aka kira sallan isha'i, ya tashi ya gabatar, sai da ya kammala gaba ɗaya, kana ya tashi ya fita falon ya zauna, TV ya kunna sannan ya ɗauki wayarsa ya kira Safeena hira suka shiga yi na kewar junansu.


Ɓangaren Basma kuwa, ta sanya aka kawo masa abinci aka jera a kan kafet dake tsakiyar falon, wanka tayi ta sanya doguwar riga na leshi, tayi ɗaurin Maryam Babangida, tayi kyau matuƙa sai ƙamshi takeyi.
Basma doguwa ce kaɗan tanada ƙiba shima kaɗan, sai fatarta akwai ɗan duhu mai haɗe da haske, ita ba baka ba ita ba fara ba, tsaka tsaki, sai kuma tana da Boobs dai-dai da jikinta maca ce mai hips sosai, mazaunanta yayi dai-dai da jikinta, cikinta a ɗame yake tamkar bata cin abinci, Basma akwai shape mai kyau da diri. Fuskarta ɗauke yake da dara daran idanu, bakinta ɗan ƙarami ne pink color, sai dogon hanci da yayi tsini har baka, in tayi dariya dimple ɗinta sai ya lotsa, gashin giranta tamkar anyi mata kabin, Basma tanada yalwataccen gashi har gadon baya, mai silɓi da baƙi sosai, Basma ta haɗu domin ko ba makeup fuskarta a haɗe take, Allah ya gama halitta anan. A fili in ka ganta za kayi zaton za tayi nauyi amma ana ɗaukarta shagwal take, kyau dai ta haɗa na Barebari da kuma Fulani. Masu karatu ya kuka hango kyawun Basma, abin ba acewa komai lol😃.


A hankali take taku, saboda dogon takalmin dake ƙafarta, a haka ta isa part ɗin su Yaya Ahmad, ta same shi yanata waya ganinta ne ya sashi saurin kashe wayar, galala yayi yana kallon halittar Allah, haɗiya miyau yayi a zuciyansa yace
"gaskiya Basma kin haɗu, dole in fara lasar zumanki kan muyi aure, dan bazan jure ganinki haka ba" a fili kuma yace
"walcome my Baby" ya buɗe hannu domin taje tayi hugging ɗinshi, rungume hannunta yayi ta gyara tsayuwa, domin ba zata iya abinda yake nufi ba, miƙewa yayi ya isa gab da ita kamshin turarensu ya gauraye gurin, kama hannunta yayi sai ta runtse ido, ƙoƙarin rungumeta ya shiga yi, da sauri ta janye tace
"miye haka Yaya Shureym, ka bari kaci abinci mana" dariya yayi yace
"afwan gimbiyata ganinki ne duk ya ruɗani, muje ki zuba min" suka je suka zauna, ta zuba masa abincin ya soma ci, yana santi duk a haukansa ya ɗauka ita tayi.


Bayan ya kammala ci, saiya miƙe yaje ya wanke bakinsa ya dayo, ita kuma ta zauna akan kushum tana jiran dawowarsa, daya dawo saiya zauna kusa da ita, hannunta ya kama yace
"Basma ina sonki sosai, gobe ina son zamu fita zaki rakani wani guri da yamma" tace
"ok Allah ya kaimu".
Wasa ya farayi da yatsun hanunta, yana mata magana rad'a-rad'a, janye hannun tayi tace
"haba Prince ka bari mana" sosa k'eya yayi yace
"haba my Basma ya kike yi kamar baki waye ba, ina ce a England kika yi karatu, ai nasan duk kin waye da irin wannan ai" gaban tane ya fad'i tana tambayar kanta
"shin me wannan yake nufi?" a ranta, bata ankara ba taji ya rungumeta yana kokorin yi had'a bakinsu guri d'aya, ai da sauri ta fara kiciniyar kwatar kanta, shi kuma ya rik'eta gam, Sallaman da Yaya Ahmad yayi ne ya shigo, shine yasa yayi saurin sakinta, ita kuma ta mik'e da sauri tayi k'ok'arin barin d'akin da gudu, Shureym ne yake kiranta amma ina ta fece a guje, haka ta isa part d'in Ammi tana haki, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login