Showing 3001 words to 6000 words out of 79094 words

Chapter 2 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4655

d'insa na diploma, ya koma Abuja lokacin Deeja ta shiga jss3 a secondary.


Wata rana Aliyu ya wayi gari da matsanancin ciwon ciki Abu kamar wasa, zuwa yamma yace ga garinku, wannan family sun shiga tashin hankali sosai da rashin Mahaifinsu, karma ace maka Aryan da yayi mugun sabo da mahaifinsa, mutanan Gombe suka zo saida akayi arba'in sannan Inna ta tafi, sun so su Umma su tattara su koma Gombe amma Alhaji Sani yace su barsu anan, yana so Aryan ya cigaba da aikin Mahaifinsa, haka suka amince badan ransu yaso ba.


Aryan ya fara zuwa aiki a company Alhaji Sani, tunda ya fara zuwa ya fara samun matsaloli, wasu daga wurin aikin suka sanya masa ido saboda sunga yanda Alhaji sani ke nan-nan dashi. Daga karshe suka yi masa sharri bayan shekaransa guda da fara aiki Alhaji Sani ya koreshi.


Aryan yayi kuka sosai rayuwa tayi musu k'unci abinda za suci wuya yake musu cikin k'ank'anin lokaci duk suka rame suka lalace, Khadija ta daina zuwa makaranta domin ba kud'in school fees, Allah yasa ba haya suke ba domin da gidan su kawai suka tsira. Dole yasa Aryan ya fara bige-bige, Umma kuma ta soma wankau a gida da haka ne suke samun abincin da zasuci, Aryan yayi yawon niman aiki Amma bai samu ba, wani wurin inya je sai suce mai Digree suke nima, ba suda kud'in da zai koma karatu dole yasa ya soma dako a kasuwa. Allah ya taimakeshi ya samu baro yana amfani dashi wajen dakon. Da wannan kud'in baron ne ya samu ya kafa runfa a cikin kasuwa yana biyan kud'in hayan wurin, ya fara saida kayan miya, abu kamar wasa sai sana'ar ya amshe shi, da haka Deeja ta koma makaranta ya cigaba da biya mata school fees, Umma kuma ta daina wankau saboda sanyi ya fara mata illa, sai ta samu jari ta fara dafawa Deeja kwai tana saidawa, in ta dawo makarantan boko saita fita tallan kwai, da yake duk sunyi saukar Al'Qur'ani, boko kawai take zuwa.


A daddafe Khadija ta kammala secondary school, tunda ta gama Aryan yaso nima mata school of health ta cigaba amma ba kud'i, burin Khadija ta zama babban likitan mata amma ba hali. Samari sosai take da su amma Yaya Aryan ya hanata hira, saida Umma ta sanya baki ya fara barinta tana fitan ma wani malaminsu na ialamiyan da ta gama mai suna Musa. Soyayya sosai suke yi, sun fara zancen Aure Iyayen Musa suka hana shi aurenta saboda akwai yarinyar da suka zab'an masa, wannan dalilin ne ya kawo k'arshen soyayyan Dija da Musa. Tun daga nan Dija ta tsani soyayya burinta yanzu bai wuce ta samu ta cigaba da karatu. Aryan yazame mata uba duk abinda 'ya budurwa take buk'ata Aryan ya tsare mata shi, ta maida hankali sosai wajen tallan kwai.


Aryan runfansa ya rufta tun daga wannan ranar komai ya dagule masa cinikinsa yaja baya, wata biyu kenan da rushewan rumfansa. Ana cikin hakane mak'ocinsu Malam Lawal yaje ya kafa tashi rumfan kusa dana Aryan da hakane Malam Lawal ya kwashewa Aryan customers, ya zamana Aryan saiya fita kasuwa ya dawo gida baiyi cinikin kirki ba.


Aryan saurayi ne matashi mai cikar kamala, yanada tsayi amma dai-dai misali, yanada kauri, kuma fatarsa mai haske ne, yanada dogon hanci da dara-daran ido, bakinsa dai-dai da fuskansa, Namiji ne mai cike da kwarjini ga faffad'an k'irji, suman kansa luf-luf yake tamkar d'an India, in ya d'auki lokaci baiyi aski ba gashinta yana taruwa wanda zai iya kamawa da ribom, gashi da santsi sosai. Hakane kesa kullun Kansa da Hula baya son sumansa na fitowa, ba kowa yasan sumarsa haka yake ba saboda baya fita ba hula, sai dai in yaje masallaci wurin yin Alwala sai mutane su gani.


'yan Matan unguwansu Aryan sun rud'e sosai akansa, suna haukan sonsa, shi kuma bai san ma suna yi ba. Shekarunsa Talatin (30yrs) a duniya har yanzu baida budurwa, baima kallon mata balle ma su birgeshi, shiyasa ranar da sukayi ido hud'u da Basma gabansa ya fad'i domin shi Sam baya kallon mata, amma fuskan Basma ya kasa b'ace masa a ido saboda wulak'ancin da tayi masa. A yanzu kullun burinsa bai wuce ya samu kud'i ya farantawa Ummansa rai da k'anwarsa abin sonsa.


*Cigaban Labari...*


Malam lawal ne ya kwad'a ma Aryan sallama, firgigit ya farka daga dogon tunanin da ya shiga, cikin sark'ewan murya yace
"Naam Malam Lawal ashe harka iso" cikin dariya Malam Lawal yace
"tun d'azu nazo, nayi maka magana naga gaba d'aya hankalinka ya yi nisa ince dai lafiya?" murmushi yayi yace
"lafiya lau Malam Lawal, ya kwanan iyalin?"
"Lafiya lau, d'azun nan naga Deeja zata aiken Ummanku, sai na tambayeta ko ka wuce? sai tace aika fita da wuri"
"eh wallahi na fito da wuri, da yake na biya wajen saro kayan miya"
"Ok, Allah ya bamu sa'a da kasuwa mai Albarka"
"Ameen Malam Lawal". Nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar kasuwan.


B'angaren su Queen Basma sai goma na safe suka farka, ko wacce ta fito cikin shigan mu ta Hausawa, Leema ta sanya leshi riga da zani rafa, Meena ta sanya shadda doguwar Riga, Basma kuma ta sanya atamfa super, d'inkin Riga da siket, ba k'aramin kyau sukayi ba, ko wacce da gyale a kanta, hakan da suka yi sai suka bani mamaki, gaba d'aya kamar ba sune jiya suka yi shigan dogayen riga sai kace ba 'ya'yan Musulmai ba, suka tafi zuwa club.


Queen ce tace
"Ni zan tafi gida domin a yanzu haka ana jirana domin yin breakfast, in kuma za kuje tom sai mu tafi tare" Leema ta yatsine fuska tace
"Ni bazani ba saboda Momynki akwai takura gwara-gwara Ammi, dan haka hotel d'in da muka sauka ni da Meena zan wuce" Meena tace
"kai Leema kiyi hak'uri muje kawai kinga fa sunsan muna garin nan bai kamata muje wani guri ba tunda duk Family ne mu ba bare ba" Queen ta yi hanyar fita tace
"ban takurawa kowa ba, in kun so ku fito mu tafi in kuma kun k'i ko wacce ta kama hanyar inda zata, yau dai ba mai kwana min a wannan gidan, nima gidan Ubana zani na kwana" tana gama fad'an haka tasa kai ta fice, tsaki Meena tayi tace
"In kina tak'ama da mulki muma fa gidanta muka fito, kinga Leema mu wuce gidan President d'in inya so in munyi two days sai ki koma Kano ni kuma na wuce Kaduna, domin wallahi ina missing Family na" Murmushi Leema tayi tace
"hmmm wallahi nima hankalina ya koma gida fa, yanzu fa iyayenmu sun d'auka yau ne zamu dawo daga Dubai da muka tafi, bacin yau satinmu d'aya da dawowa, muna biyewa Queen bayan ita iyayenta sun ga dawowarta a ranar, muko munyi k'arya sai yawo muke bamu nan bamu can" Dariya Meena ta kwashe dashi tace
"kefa saboda Jalal kika tsaya anan" hararan wasa Leema tayi mata tace
"Ke kuma saboda mashayarku kika tsaya, saboda kinsan in kika koma gida Yaya Jamal zai takura miki ba shiga ba fita" duka Meena ta kaiwa Leema saita goce ta fice da sauri tana dariya. Haka su dukansu suka d'unguma zuwa babban gidan Shugaban k'asa.


*WACECE QUEEN BASMA?...*


_*Rahma Ce*_
[8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *3.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


*WACECE QUEEN BASMA?*


'Yace a wurin Alhaji Mukhtar Bukar Bulama, wanda yake shugabancin k'asarmu Nigeria a yanzu. Asalin Mahaifinsa d'an Maiduguri ne Kanuri, mahaifiyarsa kuma mai suna Asma'u 'yar Gombe ce Fulani, Alhaji Bukar Bulama babban d'an kasuwa ne, yana fita k'asashen waje sosai, ya jima baiyi aure ba saboda yanayin kasuwancinsa, Mahaifin Asma'u Alhaji Salis, abokinsa ne k'ud da k'ud wanda a sanadin kasuwanci abotansu ya had'u, ganin Ahaji Bukar Bulam baiyi aure ba yasa Alhaji Salis ya bama Alhaji Bukar auren 'yar tilo d'aya Asma'u.


Suna zama a cikin garin Kaduna a Unguwar Rimi, Alhaji Bukar an sanshi sosai, Mutum ne mai tausayi da taimakon talakawa, yaransa biyu a duniya Mukhtar da Halimatus Sadiya, sun taso cikin gata da kulawa kuma Asma'u tayi k'ok'ari sosai wajen basu tarbiyya mai kyau.


Mukhtar yana gama primary mahaifinsa ya turashi karatu k'asar Germany a can ya fara secondary school d'insa. Tafiya ya kama su Alhaji Bukar zuwa Gombe sanafin rasuwan mahaifiyar Asma'u, bayan sunje basu dawo ba har akayi Addu'an bakwai kana suka kamo hanyar Kaduna, basu fita daga Gombe ba akan hanyarsu suka bige wani yaro, cike da tashin hankali suka nufi Asibiti dashi, aka karb'esu emergency, an samu yaron ya farfad'o, amma baya iya magana sai zaro idonsa yake waje, Likita ya basu tabbacin yaron ya samu Matsala a kwakwalwansa, hankalin Alhaji Bukar yayi masifar tashi, sunyi iya bincike ganin an gano iyayan yaron amma shuru ba a gano ba, da haka ya d'auki yaron ya wuce dashi Kaduna da nufin in ya samawa yaron lafiya ya maidashi wurin Iyayensa.


Alhaji Bukar suna dawowa da kwana biyu ya shirya zuwa kasar Germany da iyalensa domin duba lafiyan Yaron daya bige, wanda baya iya magana. Da isarsu da kwana biyu cikin ikon Allah Yaron ya soma magana, sunan shi kad'ai ya iya tunawa Ibrahim, amma banda haka bai tuna komai ba, Likitoci suka tabbatar musu da Yaron ya samu mancewar kwakwalwa (loosing Memory). Abin ya damu Hajiya Asma'u sosai hakan yasa Alhaji Bukar ya bar Ibrahim a wajen Mukhtar ya fara karatu shima, sai suka tarkato suka dawo Nigeria.


*Bayan shekaru mai tsawo*


Su Muktar sun dawo Nigeria wanda dukkansu sun gama karatunsu sun samu aiki, har zuwa lokacin Ibrahim bai dawo cikin kwakwalwansa ba. Sadiya kuma tana karatu a KASU, tun dawowar su Mukhtar Allah ya daurawa Sadiya son Ibrahim, Abu kamar wasa har mahaifiyarsu ta ganeta saita kwab'eta, abinda basu Sani ba shima ta wurin Ibrahim d'in ya kamu da son Sadiya, daga bisani ya bayyana mata zuciyanshi suka fara soyayya.


An sanya bikin su Ibrahim da Sadiya ba b'ata lokaci, wanda Alhaji Bukar yace ta cigaba da karatunta a d'akin mijinta, Mukhtar shima yana soyayya da k'anwar Sarkin kano mai suna Fatima, soyayya tayi k'arfi wanda hakan yasa aka had'a bikin su duka a kayi. Anyi biki sosai na manyan Attajirai, ko wacce ta tare a sabon gidanta da Alhaji Bukar ya siya musu a unguwar sunusi.


Wata rana Alhaji Bukar ya shirya tafiya k'asar Dubai shida Mahaifin Asma'u, domin kula da kasuwancinsu dake can, a hanyar dawowarsu jirginsu yayi hatsari suka rasu. tashin hankali ba'a sanya masa rana, wannan Family sun shiga cikin damuwa da k'unci na rashin jigonsu, Hajiya Asma'u ta zama ba Uwa ba Uba ba Miji sai sauran danginta da yaranta. Hakan ya girgizata wanda haka yasa ta samu ciwon hawan jini. Su kuma su Mukhtar sun rasa Bango abin jingina watarsu. Ibrahim yayi kuka matuk'a domin da bazar Alhaji Bukar yake taka rawa, har yau baisan shi waye ba ko danginsa, yasan dai su Hajiya Asma'u basune iyayensa ba, ya kasa tuna komai na danginsa.


Bayan Addu'an Arba'in duk dangi suka watse, an rab'e musu gadonsu, Muktar ya had'a duka dana k'anwarsa Sadiya dana Ummansu ya cigaba da kasuwanci dasu sannan yana aikinsa. Shi kuma Ibrahim sun bashi wani kaso mai tsoka daga dukiyar nasu kamar yanda mahaifinsu ya rubuta a cikin dairy d'insa, Ibrahim ya amsa yana godiya harda kukansa, daga nan shima ya cigaba da business.


Hajiya Fatima matar Muktar ta haifi d'a Namiji mai suna Ahmad, bayan shekara guda ta kuma samun ciki, bata so ba amma dole ta hak'ura saboda Alhaji Mukhtar yana son abinsa, haka ya d'auki Ahamd ya bama Ummansu ta cigaba da rik'onsa.


Bayan wata tara ta kuma haifo d'anta Namiji mai suna Abubakar suna kiransa da Naufal. Sati biyu da haihuwarta Allah ya azurta Alhaji Ibrahim samun k'aruwa da d'a Namiji wanda suke sanya masa suna Jamal. Sun raini 'ya'yansu cikin Kauna da soyayya, sun basu tarbiya sosai domin kud'insu bai hanasu tsayawa bisa tarbiyyan yaransu ba.


*Bayan shekara biyu*
Hajiya Fatima ta kuma haifo 'ya mace suka sanya mata Asma'u suna kiranta da Husnah. Ta b'angaren Hajiya Sadiya ita bata k'ara haihuwa ba tana rik'e da d'anta Jamal.


Alhaji Mukhtar ya rik'e mukamin Commissioner har kujera uku, soyayyar da ya samu wurin Mutane yasa ya fito takaran gomna, cikin ikwan Allah ya samu. Ta b'angaren Ibrahim shima yana ta samun mukamai a wurin aikinsa dukiyarsu sai hab'aka take ta ko ina.


Alhaji Mukhtar ya k'ara aure da 'yar wani hamshak'in mai kud'i a garin Kano 'yar Alhaji Buba mai Naira itace 'yarsa tilo guda d'aya mai suna Maryam, anyi Biki sosai na manyan Mutane, Alhaji Mukhtar ya tare da ita a gidansa na Gomnati, gida d'aya ya had'asu da Hajiya Fatima, suna zaune zaman lafiya ba tashin hankali.


*Bayan shekara Hudu* yana kujeran Gomna, Hajiya Maryam ta Haifi 'yarta mace k'atuwa ga kyau, suka sanya mata suna Basma, Basma ta taso cikin gata da soyayyan iyayenta, Yaya Ahmad yana sonta sosai tun tana k'arama suka shak'u sosai, bata shiri da Yaya Naufal, Anty Husnah kuwa duk inda zata suna tare, tun tana k'arama ta koma hannun Hajiya Fatima, Nono kawai ke kaita gun Momynta.


Itama Hajiya Sadiya ta k'ara haihuwar 'ya mace aka sanya mata Ameena suna kiranta da Meena, tserayen wata biyu ne tsakanin haihuwar Basma da Meena.


Yaya Ahmad da Yaya Naufal kusan tare suka wuce k'asar Malesia karatu, Yaya Ahmad yana karanta Medicine Yaya Naufal yana karana Biochemistry. A lokacin Anty Husnah tana secondary school.


Basma kuma tana primary. Hajiya Fatima wanda suke kira da Ammi ta gama sangartata duk wani rashin ji ta sani, ga tsokanar fad'a a makaranta, duk wani kiriniya tare suke yi da Meena da yake makarantar su d'aya. A daffafe suka kare primary saboda irin kai k'aransu da iyayen yara keyi, kasantuwar iyayensu manya ne shiyasa ba'a koresu ba.


Hajiya Maryam ta k'ara haihuwar yara Maza 'yan biyu Anwar da Na'im, anyi shagali sosai da haihuwarsu, su Basma kuwa murna har kunne. So tari Hajiyar Maryam wanda suke kira da Momy bata ragawa Basma tayita mata fad'a hakan yasa Basma bata son kwana a b'angarenta sai wurin Ammi saboda Ammi na kula da ita bata son b'acin ranta.


An d'aurawa Anty Husnah aure da Jabir d'an senator, sun had'u a makarantar Abu Zaria inda ta fara karatu, an d'aura auren tana cigaba da zuwa makaranta. A wannan shagalin bikin ne akayi taron da ba'a tab'a yiba, mutanan Gombe, Maiduguri, kano duk sun hallara, matar Sarkin Kano yayan Ammi, Hajiya Murja tazo bikin wanda ta taho da 'yarta mace sa'ar su Husnah mai suna Haleema suna ce mata Leema, tun daga nan su Basma aka samu kawa, da zasu tafi Leema ta kafe saita zauna wurin Ammi, haka mahaifiyarta ta barta mai martaba Sarki Abdallah ya amince Leema ta zauna wurin Ammi domin yasan gidan Gomna Muktar Bukar Bulama akwai tarbiyya.


Abdullahi shine ya gaji sarautar gidansu bayan rasuwan Babansu, Yayane ga Hajiya Fatima, uwa d'aya uba d'aya suke, yana da mata biyu Hajiya Sa'a itace Uwar gida tana da yara biyu duk Maza Adam shine babba sai Shureym shine k'arami, sai Amaryansa Murja yarta guda d'aya ce itace Leema, sun d'aura son duniya sun azawa Leema kowa na dangi yana sonta, tun tana k'arama ta taso cikin sarauta, gimbiya Leema 'ya ga Sarki Abdallah.


Hajiya Sa'a Mace ce yar k'arya da son duniya ta shigewa Hajiya Maryam Momyn Basma, amma Momy tak'i sake mata saboda halayyarsu bai zo d'aya ba, Hajiya Sa'a basa shiri Sam da Ammi wato k'anuwar mijinta, hakan yasa Momy tak'i sake jiki da ita.


Hajiya Sa'a ta sangarta Shureym da gata, ta d'aura son duniya ta bashi saboda tana ganin shine zai gaji kujaran Babansu, shiyasa tun yana k'arami take kiranshi da Prince Shureym, hakan yana masa dad'i sosai. Adam shi kuma Mutum ne salihi ba yida hayaniya hakan yasa nasu yazo d'aya da Hajiya Murja, a wurinta yake komai. Shureym yana America yana karatun Engineering, shiko Adam Madina ya tafi karatunsa bangaren Islamic studies.


Basma, Meena, Leema duk makarantar d'aya suke secondary, a part d'in Ammi suka tare domin Ammi ita bata kwab'a musu, Meena ta kwaso kayanta ta dawo gidansu Basma gaba d'aya.


Alhaji Ibrahim Baban Meena ya samu cigaba sosai, wanda yaita samun K'arin girma a wurin aikinsa, ya tura Yaya Jamal karatu inda su Yaya Ahmad suke k'asar Malesia yana karanta Business admin.


Gomna Muktar Bukar Bulama ya sauka a kan kujeran Gomna bayan shekara takwas daya shafe akai, ya k'ara samun kurajeran Sanator wanda ya wuce Abuja, sai weekend yake dawowa gida Kaduna. Dukiyarsu na gado sai hab'aka yake yi.


Su Yaya Ahmad sun gama karatunsu gaba d'aya duk sun dawo, Yaya Ahmad ya fara aiki a babban Asibiti dake garin Abuja, Yaya Naufal kuma ya karb'i kasuwancin Abbansu ya cigaba da juyawa. Yaya Jamal ma dukiyar Dadynsa ya cigaba da rik'ewa.


Ta b'angaren Mutanan Kano kuwa Yarima Adam ya dawo ya fara lecturing a BUK, shi kuma Shureym bai riga ya kammala masters d'inshi ba.


Su Basma an zama 'yan Mata sun gama Secondary School yanzu suna England suna karatu. Basma na karanta Micro Biological, Leema tana karanta Pharmacy, Meena kuma tana karanta Low.


Tunda suka koma England rayuwarsu ta k'ara sauyawa, sun had'u da 'ya'yan turawa da kuma 'yan k'asashe daban-daban, Basma tunda ta soma karatu saita natsu ta zama mara son magana, amma fa akwai tsiwa in aka tab'ota, Meena kuma akwai shegen surutu, Leema kuma akwai ji dakai da kuma k'asaita na Sarauta.


Sunyi farin jini sosai saboda suna da k'ok'ari sosai. Meena ta had'u da wata yar ajinsu ta koya mata zuwa club, abu kamar wasa Meena in bata je club ba bata jin dad'i, tun su Leema na mata k'orafin ta daina zuwa har taja ra'ayin Leema ta fara zuwa.


Abu na farko da suka koya shine Meena ta shiga group d'in 'yan shaye-shaye, tun bata iya ba harta kware sosai wajen zukar sigari da shan kwayoyi.


Leema kuma Mace ce mai yawan sha'awa, in Meena ta jata cikin group d'insu saita kasa sakewa a haka harta had'u da Jalal suka fara soyayya tun bata sakewa harta sake dashi, Jalal ya fara fita da ita yawo kullun sai sun fita. A hankali yayi ta jan ra'ayinta gareshi, tun tanak'in amince masa harta bashi kai bori ya hau. Tun daga nan suka d'inke da Jalal, ya mai da ta tamkar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login