Showing 78001 words to 79094 words out of 79094 words

Chapter 27 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4653

k'alubale a wurin wasu Matan nasu da zarar Mace ta haihu, ita kullun ba data lokacinsa, wata ma ta daina yin kwalliya, wata kuma tsafta ma ta rage, wata kuma yin abinci ma sai dole, babu wani kyale kyale da Miji zai gani a wurin Matarsa da sai sashi sha'awarta. Da ance wance kaza kin daina abubuwa kaza kin sauya, saita ce hidimar Yara sune suke hanata. Hakan kesa Mazan suna sha'awar Matan dake waje masu kwalliya da kyale-kyale, da ya samu mai sonsa saiki fara damuwa Mijinki ya sauya miki, ke kaza-kaza, bacin kece kika bashi k'ofar yin hakan.


Shi dai haihuwa bazai sanya ki zama k'azama ba ko ki zama mara kwalliya da gyaran jiki ba, sai in dama kin sanyawa ranki sangarci, lalaci, son jiki da kuma rashin tunani, dan haka Mata mu kula sosai, dan da wayan matsalolin da wasummu suke fuskanta a gidan aure muke fara bada k'ofar aukuwarsa.


Namiji kamar Yaro yake jin kansa, yana buk'atar kulawa da tarairaya, 'yar soyayyan nan ko 'Ya'ya nawa ki kayi baki tsufa da yinshi ba, a kullun kina gyara kina tsafta Mijinki zai rik'a miki kallon yarinya ce".


Basma shuru tayi, gaba d'aya jikinta ya mutu tace
"Momy yanzu kina nufin da safe kafin in fara indimar Hydar na Babanshi zan fara?"


Momy 'yar dariyarsu ta Murmushi tace
"kwarai kuwa, ba da safe bama a ko wani lokaci ma, in har Mijinki mai fitan safiya ne dole ki tashi ki fara masa hidima kafin ya fita ki tabbatar ya fita da farin ciki a ransa wanda in ya tuna zai rik'a Murmushi da farin ciki, kinga kin samar masa farin ciki wanda ko ya fita hankalinsa da tunaninsa yana wurinki zai rika Allah-Allah ya dawo gida.


Ki zama mai kwalliya, canza shiga iri-iri, karki nacewa shiga guda d'aya, k'amshi karya rabu dake ki zama mai amfani da turaruka masu sanyin k'amshi, kuma kala-kala, karki yarda Mijinki ya fahimci k'amshin ki guda d'aya ne, ya zamana daban-daban, kuma ki tanada masu taushin k'amshi na wanciya barci ne wannan kawai. K'amshi yana d'aya daga cikin sirrin mace wanda zata mallaki zuciyar mijinta cikin sauki.


Sannan ki rik'a wa Mijinki Addu'a a fili da kuma a b'oye, in zai fita bishi da Addu'a tare da tarairaya wanda in ya tuna ki ya saki murmushi. Kuma karki kuskura ki sakarwa 'yar aiki hidimar mijinki dan wasu matsalolin daga nan yake farawa, sai jiki ance 'yar aiki ta aure mijin matar gida, wannan duk sakacin matane akan kula da hakk'in Miji. Nasan duk kin sannan wannan abubuwan tuni dai nake miki".


Ajiyar zuciya Basma ta saki mai k'arfi tace
"Momy nagode sosai, hak'ik'a duk Macen da tayi amfani da shawarwarinki zai mata amfani matuk'a sosai, Allah ya saka Miki da Aljanna yasa ki gama da duniya lafiya, ina alfahsri da samunki A matsayinki na Uwa a gareni, love u much Mom" ta k'arasa maganar tana matsar kwalla.


Momy tayi Murmushi tace
"Ai Basma lokacin ma yayi mana kad'an, domin na lura da *Anty Rahma* ta k'osa ta gudu ta barmu, ta koma labarin Jannat na cikin sabon littafinta *MAI HAK'URI (shi ke da riba)*.


Dariya Basma tayi ta mik'e tace
"Momy Anty Rahma tana k'ok'ari sosai ina jinjina mata matuk'a"


Momy ta wuce d'aki ta had'o mata wasu magunguna ta bata, Basma ta amsa tana murmushi cike da jin kunya tayi mata Godiya.


*Ni Rahma nace kunga Iyayen zamani*😉


Ammi itace ta mai da Basma gidanta, sai gabda Magrib ta barota ta dawo Gida.


Yaya Aryan sai bayan Sallan isha'i ya shigo gidan, mamaki ya cika shi yanda k'amshin Abinci ya cika masa hanci daga kitchen, tunani ya shiga yi, yasan tabbas ma'aikatan gidan sun gama aikinsu sun wuce part d'in su, tambayan kansa yake


'Waye a gidan nan?' Dan sam bai san da dawowar Basma ba. Zama yayi a falo yana jiran yaga wanda zai fito, baifi minti biyar da zamansa ba Basma ta fito cikin shiga na English Wears riga da sket, rigar iya cibiya ya tsaya mata, sket d'in kuma iya rabin cinya, gashin kanta ta d'aure shi da ribom ta saki jelan a bayanta, k'amshi take zubawa mai sanyin k'amshi, Baby Hydar ta sab'ashi a kafad'a, shima ta zuba masa nashi kwalliyar.


Yaya Aryan sakin baki yayi yana kallonta harta k'arasa wurinsa, kwantar da Hydar tayi ta koma kusa da shi ta zauna tare da kallonsa tana murmushi ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, hura masa iskan bakinta tayi a idonsa, ya lumshi ya kuma bud'ewa, magana zai yi ta had'e bakinta da nashi suka lula duniyar masoya, sun d'auki kusan rabin awa suna faranta ran juna, daga bisani Basma ta jaye jikinta tace cikin kasala


"Muje kaci abinci" Murmushi kawai yayi ya mik'e ya d'auki Baby Hydar tace
"Ki sameni a d'aki"


Bin bayansa tayi cike da farin ciki tace da k'arfi


"I love u Yaya Aryan"


Sai ya juwo cikin kulawa tare da d'age gira
"Love u too My Queen"


Ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta suka koma suka zauna yace


"Basma kin zamo min haske a rayuwata, sonki halitta ne daga tsatson jikina, zan kasance dake har abada taurauwata, zan cigaba sa shayar dake da ruwan farin ciki wanda yake kwaranya daga koramar masoya"
Ya sumbaci bayan hannunta.


Tace
"in sonka Mijina, Allah ya k'ara mana zaman lafiya da kwanciyar Hankali, ya kauda dukkan shairin Shaid'an, Mutum da Aljan, ya k'ara maka bud'i na Alkhairi ya kuma Albarkaci zuri'anmu"


"Ameen ya Habibty" ya amsa tare da manta mata kiss a baki, daga bisani sai suka mik'e suka wuce d'akinsu, dan cigaba da shayar da juna Zumar Masoya.


*Tammat Bi Hamdillah*


*_Alhamdulillah Ala Kullu Halin_*


Alhamdulillah, Yau Allah ya bani damar kammala wannan littafi mai suna *'YAR SHUGABA*, ina mai godiya ga Allah S.W.A daya bani ikon kammlashi cikin koshin lafiya.


*_MASOYANA_*
_*Bani da bakin gode muku masoyana masu bibiyar wannan labari, kunada yawa domin lissafaku wani sabon littafi zan cika, Allah ya saka muku da Alkhairi ya k'ara mana zumunci ya kuma had'a fuskokinmu a Gidan Aljanna. Ameen. Addu'o'inku yana isa gareni, Nagode sosai wallahi ina sonku sosai, so wanda baida algush😃, so irin da yawan d'in nan, irin totally d'in nan, ina yinku ba adadi Allah ya bar kauna. Ameen😍❤❤*_


*Wannan labari kamar yanda na fad'a a farko k'agaggen labarine, banyishi ko dan wata ko wani ba, hasalima idan muka fuskanci labarin yasha banban da yana yin mulkin k'asar mu da ma sarauta. Na yishi domin ilmantarwa da kuma fad'akarwa acikin siga na nishad'antarwa.*


_Allah ya bamu ikwan Amfani da abinda ke cikin wannan labari, kuskuren dake ciki Allah ya nisantamu dashi ya yafe mana gaba d'aya. Ameen._


_Taku a kullun_
*RAHMA KABIR* sai kun jini a sabon littafina wanda zaizo nan bada dad'ewa ba
*MAI HAK'URI (shi ke da riba)*


*Rahmar Ku Ce*💃😍

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login