Showing 33001 words to 36000 words out of 79094 words
Chapter 12 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt
ruwan tea ta dafa, ta zo ta diba cin-cin d'in data tawo dashi a plet, ta zauna taci kana ta d'aura da danbun Namam kaza, bayan ta gama sai ta kwanta akan doguwar kujera, ta runtsa idonta ta shiga tunanin wani irin rayuwa zatayi yanzu, kuma wani mataki zata d'auka akan Yaya Shureym da Safeena wacce yake ik'ira rin matarsa ce, hawaye ne ya sauka a kuncinta, a fili tace cikin kuka
"babu wanda ya jamin wannan rayuwa sai ku Abbana, dan haka ba wani matakin da zan d'auka ma, domin ko me ya sameni kune sila"
Ta goge hawayenta, ta d'auko wayanta ta shiga kiran Momy, ta sanar da ita sun sauka lafiya, nan sukayi sallama, ta kira President ta sanar masa da sun sauka lafiya shima, haka kuma ta kiranl Ammi ta sanar mata da sun sauka lafiya itama, bayan ta gama wayan, sai ta tuna da Umma, sai tayi murmushi, itama ta kira ta suka gaisa, Umma tayi mata nasiha sosai akan biyayyan aure, kana suka yi sallama, saita kashe wayen gaba d'aya ta gyara kwanciya, bata dad'e ba barci ya d'auketa.
*A Nigeria*
Mutanan Biki duk sun watse sai dai-dai da suka rage, ta b'angaren Amare kuwa sunata cin Amarci hankalin su kwance, kowa yana cikin farin ciki. Ta b'angaren Yaya Jalal ya samu Leema ta yanda bai yi tsammani ba, domin gaskiya tasha gyara wajensu Momy, duk da dai bata isa ta maida mudurcinta ba, amma dai ya gamsu sosai da ita, Leema ta kasance cikin murna da yanda Jalal ya saki jiki da ita, tamkar babu wani abin da ya faru a baya.
*A K'asar Monaco*
Yaya Aryan ya cigaba da rayuwa shi kad'ai, da Umma kawai yake waya su gaida, da sun gama saiya kashe wayan. Kullun soyayyan Basma k'aruwa yake a zuciyansa, yanzu da baya ganinta yafi shiga tashin hankali da damuwa, ya k'ara ramewa sosai, burinsa yanzu bai wuce Basma ta kwantar da hankalinta ba, tayi rayuwan Aure cikin farin ciki da annatsuwa. Ya duk'ufa sosai wajen karatunsa, yana k'ok'arin kafa sabon rayuwa.
*Bayan mako guda*
*A America*
Basma tunda ta kulle kanta a d'aki, bata kuma bud'ewa ba har tsawon mako guda, komai a cikin d'akinta take yi, hatta girki da kanta take yi, taci ta wanke kayan data b'ata, tun yin aikin na bata wuya kasantuwar bata saba yi ba, har ta fara sabawa, Allah yasa ta iya girki, domin Momy ta koyawa Basma girki dan gaba zai mata amfani, kamar yanda yanzu ya soma mata amfani.
Yaya Shureym suna falo suna hira, Safeena tayi pillow da cinyansa, hankalinsa na kan k'ofar d'akin Basma, hira take mishi amma sam baya tare da ita, sha'awan Basma na d'awainiya dashi, sannan ya fara damuwa da rashin ganinta da baiyi ba, tun ran da suka zo, bai sake tozali da ita ba, Safeena ganin baya tare da ita ya barta tana ta surutu, sai ta d'ago kai tana kallon direction d'in da yake kallo, gabanta ne ya fad'i cikin jin haushi tace
"Baby tunanin me kake yi haka? Ko ka fara sonta ne?" Firgigit ya farka, cikin inda-inda yace
"ba komai, me zanyi da Basma, Allah ya kyauta" cikin fushi tace
"k'arya kake yi, d'akinta fa kake kallo, kana ce min ba komai" murmushin ta kaici yayi domin ya soma gajiya da yawan k'orafinta, kawai ba yanda zaiyi da ita saboda yana sonta, kuma baya son b'acin ranta yace
"kedai kin cika kishi, kawai ina tunanin yarinyar nan ne, akan tunda muka zo ban ganta ba, ina tsoron kar wani abu ya sameta, domin in wani abu ya sameta wlh zamu shiga cikin matsala, kinsan *YAR SHUGABA* ce, gwara na rika duba lafiyan ta domin president ya bani amanarta, ko ba komai kuma 'Yar Uwata ce"
Safeena cikin nuna ko in kula tace
"wannan kaita shafa" tana gama fad'an haka ta mik'e ta shiga d'aki tana jan tsaki, binta yayi da kallo yace a fili
"Safeena sarkin kishi" sai ya mik'e ya nufa d'akin Basma...
*Rahma Ce*
[8/7, 8:34 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑
_page_ *16.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_
Yana isa d'akin ya shiga bugawa, kwance take bisa gadonta tana kallon tv, koda taji bugun k'ofan, ta d'auki kusan minti uku kafin ta mik'e ta nufi k'ofar ta bud'e, tsaye ta ganshi yana k'are mata kallo, miyau ya had'iye da k'arfi, gaba d'aya hankalinsa ya tashi da ganin Basma cikin k'ananun kaya, hararansa tayi cikin tsiwa tace
"Malam lafiya ko da matsala ne"
guntun murmushi yayi bai ce komai ba, sai yabi gefenta ya kutsa kai cikin d'akin, zama yayi kan kujeran zaman Mutum d'aya, ya shiga k'arewa d'akin kallo yana shakar kamshin d'akin, wanda ya saukar masa da kasala had'e da tsananin sha'awar Basma, ita kuma tura k'ofan tayi ta koma cikin d'akin ta zauna gefen gadonta ta cigaba da kallon tv, sun kai minti biyar a haka ba tare da wani yace wani abu ba, Yaya Shureym ne ya katse shurun yace
"Basma meyasa bakya fitowa falo ki zauna?"
Cikin nuna ko in kula tayi banza dashi, yace
"magana nake kinyi banza dani" Cikin yatsina fuska tace
"naga cewa wannan ba matsalan ka bane, ka je ka cigaba da zama da karuwanka, don ni ban yarda aure ku kai ba, kyamarka nake ma, da zaka taimaka ka tashi ka fita da ka kyauta min"
"Iya b'acin rai ransa ya baci, mik'ewa yayi da sauri zai isa inda ta zauna, ai da sauri itama ta mik'e tana ja da baya harta isa jikin bango, kankame jikinta tayi ta runtse ido domin yanda taga ransa ya b'aci ta sadakar zai duketa, gabda ita ya tsaya wanda hartana jin hucinsa, hannunta ya shiga b'amb'arewa a jikinta, a razane ta bud'e ido tana kallonsa, ba tayi aune ba ya rungumeta da k'arfi ya matseta a jikinshi, tirjiya ta shiga yi tana k'ok'arin kwatar kanta, ganin ya rik'eta gam yak'i sakinta, saita gantsara masa cizo a damtsan hannusa, da sauri ya saketa yana yarfe hannu, saita maza ta matsa a gun, yana jiyowa ya nima k'ara kamota, da sauri ta ruga, guje-guje suka fara a cikin d'akin, yana k'ok'arin kamata tana kaucewa.
Safeena shiganta d'aki da tayi, tana tsammanin Shureym zai biyo bayan ta, sai taji shuru, ganin haka yasa ta lek'a falo sai taga wayam baya gun data barshi, cike da masifa ta fito ta nufi d'akin Basma, tana bud'e k'ofa sai ta cimmusu suna wannan wasan guje-guje, ai sakin baki tayi tana kallonsu, shiga ciki tayi rai b'ace, Shureym yana ganinta yayi sauri ya tsaya yana sosa k'eya, mugun kallo Safeena tabi shi dashi bata ce masa uffan ba, sai nuna masa hanyar waje tayi alaman ya fita, sum-sum ya fita yana murmushi k'asa-k'asa, yana fita ta gyara tsayuwa tana kallon Basma tace
"A hir d'inki da Mijina domin ba sa'anki bane, in kuma ke mayya ce to Mijina yafin k'arfinki, ki shiga taitayinki domin wlh inna kuma ganin haka zan d'auki tsastsauran mataki mafi muni a gareki" tsaki Basma tayi tace cikin fad'a
"ai ko wlh da kinga yanda zanyi k'asa-k'asa dake, ke d'in banza ke wacece da zaki zo ki nima shiga tsakanina da Mijina kuma d'an Uwana, kefa ba kowa bace face karuwa mara lasisi mara mutunci, ki gaugauta fita sabgata domin had'uwata dake bazai yi kyauta, kibar ganin ina miki shuru-shuru, jaka kawai"
Ai tuni Safeena ta cika ta b'atse, magananun Basma sun tunzurata, bata san lokacin da tayi kukan kura ba ta nufi Basma gadan-dagan, Basma na ganin tayo kanta sai ta shige bayi da gudu tare da sanya key, tana maida numfashi, iya tsoro ta tsorata da Safeena, dan ta girmeta kuma ta fita girman jiki, tace a fili
"ko banza nasha dakyar muguwa kawai" Safeena tana ganin ta shige bayi sai tayi kwafa, ta fita da sauri.
Ta tada Shureym a d'akinsa, ta shiga surfa masa masifa shi dai uffan bai ce ba, da ya gaji da jin haya niyarta sai ya shige baya danyin wanka ya barta tsaye baki na kumfa, a ransa yace
"Safeena akwai masifa, ta dage ta hakikance akan abin da yake halal d'ina, gaskiya bazan d'auki wannan sakarcin ba, domin ko ban son Basma ai ina feeling d'inta, balle ma ina sonta kawai kauda kai nake ina miki biyayya, saboda ina tsananin sonki, amma nasan hukuncin da zan d"auka"
Basma sai da ta tabbatar ta fita a d'akin saita fito da sauri ta rufe k'ofarta, ta haye gado tana kwasar dariya, ko ba komai ranta ya mata dad'i tunda ta bak'anta ran Safeena, Jakarta ta jawo na kayan gurinta, lollypop ta d'auko, ta bud'e sweet ta sanya a baki tare da lumshe ido dan dad'in ya fara ratsa ta, nan take ta tuna da sunanta Queen Basma 'yar rawa, tashi tayi ta kunna radio tare da sakin sauti, ta shiga cashewa son ranta tare da tuno rayuwanta na makaranta cike da nishad'i.
Yaya Shureym ya fito zai fita, jin wakar da Basma ta sanya yasa shi girgiza kai, a fili ya furta
"Basma dangin k'uruciya" sai ya fice, Safeena ma fitowa tayi cikin shirin fita tabi bayansa da sauri ta taddashi harya kunna mota zai wuce, da sauri ta cimmasa ta bud'e gaba kusa dashi ta zauna, tana mai kallonsa cike da shagwab'a tace
"haba baby shine zaka tafi ka barni" murmushi yayi yace
"ai naga fushi kike dani shiyasa nayi shirin fita in je in wayata kona sarara" kamo hannunsa tayi tace
"sorry Baby, d'azu raina ne ya b'aci bazan sake ba" gyad'a kai kawai yayi alaman ya gamsu, sai suka fice daga gidan.
*Washe gari*
Shureym ya tashi da sassafe yayi shirin office, haka ma Safeena tayi shirin fita, nan suka had'u suka fice a gidan.
Basma tana jin k'aran fitan motansu, saita bud'e k'ofa ta fito, d'akin Shureym ta shiga ta gama kallon komai, yanda akayi decoration d'akin yayi mata kyau, kalan fentin coffee brown da milk color, haka ma kalan furniture d'in, d'akinsa ba kitchen sai dai akwai toilet babba wanda yafi nasu Basma.
D'akin Safeena ma yanayin d'akin Basma ne, sai dai itama ba Kitchen sai toilet kamar na Basma, kalan fentin d'akin ash da pink ne hakama furniture d'inta, fitowa tayi ta shiga cikin babban kitchen na falo, nan ma ya tsaru sosai, kuku guda biyu ta gani a ciki, cikin ladabi suka gaisheta tare ta tambayan abinda take buk'ata, da murmushi tace
"bata buk'atar komai" shiga tayi store d'in ta shiga diban abinda ba tada shi ta kai kitchen d'akinta, kana ta fice farfajiyan gidan, baya ta nufa inda shukoki na furanni suke, ta tsak'i iskan wurin sai taji dad'i a ranta, nan take ta tuno da wurin shak'atawan da suke zuwa ita da Yaya Aryan, idonta ya ciko da kwalla, zama tayi kan wani kujera na katako mai lilo, runtse idonta tayi ta shiga duniyan tunanin Aryan, ta kai kusan rabin awa agun kana ta bud'e ido, ta shiga rera kuka, istigfari tayi ta nima yafiyan Allah akan tunanin da tayi na Aryan Alhalin tanada auren wani akanta, tashi tayi ta nufi d'akinta ta fad'a bayi dan watsa ruwa, ko jikinta zai mata dad'i.
Yaya Shureym yana office amma ya kasa aiwatar da komai, gaba d'aya tunanin Basma ya cika masa kai, burinsa bai wuce ya samu Basma ba, agogan hannunsa ya duba yaga k'arfe 11am na safe, mik'ewa yayi da sauri ya d'auki wayansa, jakansa da key d'in mota ya wuce gida.
Basma ta fito wanka d'aure da towel a k'irjinta, tana zaune gefen gado cike da damuwa a ranta, tunanin iyayenta da family d'inta takeyi, tunawa tayi da tun ranar da suka sauka ta kashe wayarta bata kuma waiwayan sa ba, murmushi ne ya sub'uce mata data tuna dasu Meena, tunanin ya sukaci amarci ne ya fad'o mata, tace a fili
"guys nayi missing d'inku sosai, anjima zan bud'e waya muyi chart"
Tana gama fad'an haka taje kusa da dressing mirror ta soma Shafa mai, jin motsin k'ofa tayi sai ta juya da sauri, dan shaf ta manta bata rufe ba d'azun, Yaya Shureym ne tsaye yana jefo mata mayen kallo, gabanta ne ya shiga fad'uwa sam bataji k'ugin motansa ba, takowa ya fara yi yana mata wani shu'umin murmushi, Jada baya ta shiga yi, k'ok'arin isa Waldrop d'inta tayi da nufin d'auko hijabi dan ta sanya, da sassarfa ya cimmata a gurin, jikinta ne ya soma b'ari, hannu ya kai saman k'irjinta inda ta d'aura towel d'in, ta rik'e gam ta shiga kuka tana cewa
"meye haka Yaya Shureym dan Allan ka fita"
Murmushi kawai yayi ya sanya k'arfinsa ya fisge towel d'in, da sauri ta zukunna k'asa ta shiga kuka da k'arfi, d'aukarta yayi ya jefata kan gado, zanin gadon ta jawo ta rufe jikinta dashi, cire kayansa ya shiga yi, vest da gajeran wandon kawai ya rage a jikinsa, sai ya hau kan gadon, Basma ganin haka ta kuma rushewa da kuka, bai hanashi fasa k'udirinsa ba, zanin gadon ya shiga yayewa amma Basma ta cukukuye jikinta da shi, wani wawan mari ya sakar mata, sai ta tsandara uban ihu, duk da haka baisa ta saki ba, cikin fushi yace
"wlh ko ki so ko kar kiso yau saina karb'i hakk'i na"
Wani marin ya kuma sakar mata, duk da haka tak'i saki, da k'arfi ya finciko zanin gadon, sai ta k'ank'ame hannunta a k'irjinta, kuka take kamar ranta zai fita, magiya ta shiga yi masa cikin kuka
"Yaya Shureym dan Allah ka kyaleni karka kasheni, me nayi maka ne da zaka yi min mugunta"
Bige mata baki yayi, bakin ya fashe sai jini, abinda yake son aiwatarwa bai fasa ba, Basma kuwa gunjin kuka take yi, a wannan lokacin tariga ta sadak'ar, cizo ta ganna masa a kunne sai ya saketa ya kai mata naushi a baki, ya shiga dukanta ta ko ina
Basma wani wahalanlan ihu ta saki wanda yayi dai-dai da shugawar Safeena falon, dama ta shigo falon da mamaki, saboda ganin motan Shureym da tayi a gida, da sauri ta nufi inda take jin kukan, harta isa d'akin Basma, ta tsaya a bakin k'ofar, dai-dai lokacin Shureym yana k'ok'arin kai ga cika k'udurinsa Basma ta saki wani wawan k'ara, ai da k'arfi Safeena ta tura k'ofan ta buga garam, ta fad'a d'akin ta tuna huci....
*Rahma Ce*
[8/8, 5:38 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑
_page_ *17.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾
K'aran bugun k'ofar shine yayi dai-dai da Shureym ya dawo hayyacinsa, da sauri ya sauka akan gadon, cikin jin haushi da borin kunya ya kwaci kayanshi a hannu ya fita a d'akin, da gudu-dugu ya fad'a d'akinsa tare da sanya key. Basma kuka take tana cewa
"Allah ya isa bazan yafe maka ba, mugu azzazulumi insha Allah harka mutu baza ka cimma burinka a kaina ba" furucin Basma na k'arshe shine ya sanya Safeena ajiyan zuciya, dama fargabanta shine ace ya samu Basma, tasan lallai kashinta ya bushe, gashi Basma ta fita komai na kyawun sura, sannan ta tabbatar Basma bata bin maza lallai zai sameta a budurwa, kallo Basma tayi cikin tausayawa, da sanyin murya tace cikin tsoratarwa
"Kad'an kika gani in dai Shureym ne, mugune shi sosai haka yakemin nima, karki k'ara yanda haka ta faru in ba haka ba wataran zai kashe ki, maza tashi ki gasa jiki a toilet, kuma karki sake barin k'ofarki a bud'e, dan Shureym ya wuce yanda kike tunani" tana gama fad'an haka ta fice a d'akin.
Basma wani sabon kuka ta saki, da kyar ta iya sakowa daga gadon, tana bin bango harta shiga bayi, ruwa ta had'a mai zafi ta shiga ciki, ta kai kusan rabin awa tana ciki, kana tayi wanka ta fito, mirror taje ta tsaya tana kallon yanda fuskanta ya kummbura, hawaye ne ya sauka a kuncinta mai zafi, fuskan ta tayi ja sosai, gashi kumatunta ya kunbura da leb'enta, idonta yayi k'anana gaba d'aya ya sauya mata kamanni, hawaye ta share tace a fili
"Abba Ku kuka jamin" kaya ta sanya marasa nauyi ta cire zanin gadon ta ta sanya wani, taje ta kulle d'akinta ta koma gadon ta kwanta cikin k'ankanin lokaci barcin wahala ya d'auketa.
Shureym saida ya samu yayi wanka kafin ya samu nutsuwa, nadama ne ya lullub'eshi akan abinda yayi wa Basma, ga kuma kunyar Safeena da yakeji, wannan dalilin ne ya hanashi fitowa sai kawai ya kwanta har barci ya d'aukeshi.
Safeena kuwa ta kasa ta tsare a falo tana jiran fitowan Shureym, jin yayi shuru bai fito ba saita gyara zama ta kunna tv tana kallo, sai bayan k'arfe biyu Shureym ya fito daga d'akinsa, ya had'e giran sama dana k'asa yana hura hanci duk na borin kunya, Safeena tana ganin shi sai ta kwashe da dariya, dan gaba d'aya ya bata dariya sai wani basarwa yake yi, zama yayi gefenta yace cikin fishi
"meye kika gani na dariya a jikina?" ya mutse fuska tayi tace cikin tsiwa
"wlh Shureym kaji kunya, banda Allah yasa nazo na ritsaka, da ka kashe musu Yarinya, kanata cika min baki akanta, ashe duk burga ce na d'a Namiji, Allah ya kyauta maka, kuma ka sani Basma Yarinya ce imma zaka amshi hakk'inka, to ba da k'arfi zaka amsa ba saika bita a hankali"
Tana gama fad'a ta mik'e ta shige kicin, abinci ta zubo masa ta mik'a masa, murmushi yayi ya amsa tare da cewa
"Tnx my Baby, banyi tunanin zaki saurin saukowa haka ba" hararenshi tayi ta koma ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya kan d'aya, ya soma cin abincin tace
"Shureym ina Sonka sosai, bazan iyi dogon fishi da kai ba, da ace d'azun baka rufe d'akinka ba, har na sameka a ciki, da saina sauke maka kwandon rashin mutunci, amma na sauko, sai dai yanzu na daina yarda da alk'awarinka domin nasan watara saika karya shi" zai yi magana ta d'aga masa hannu tace
"kai dai ci abinci kawai".
Bayan la'asar Basma tayi shigar doguwar riga abaya brown, tayi rolin da gyalen, jaka ta d'auka bak'i ta sanya takalmi bak'i, ta same su a falo bata kalli inda suke ba tayi hanyar fita, da sauri cikin tsawa Shureym yace
"ke ina zaki?" tsayawa tayi cak bata juyo ba kuma bata ba shi amsa ba, saida ya kuma maimaita tambayan, amma shuru ta masa, k'arshema tasa kai ta fice, a zuciye ya mik'e zaibi bayanta, Safeena na rik'e hannunsa tace
"haba Shureym wani irin abune wannan, ka duketa d'azun ka kumbura mata fuska, ka sani ko