Showing 66001 words to 69000 words out of 79094 words

Chapter 23 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

4647

aiki har k'asa, tayi matuk'ar kyau, su Deeja sai kallonta suke cike da burgewa.


B'angarden Ango kuwa suna can sunata hada-hada da Mutane, Yaya Shureym shima ba'a barshi a baya ba ya mance komai ya kama Matarsa Safeena, dashi aketa hidimar bikin, Ango yana tare da Abokai da 'yan Uwa sunata hira.


*_Da k'arfe takwas na dare_*


Kowa ya gama shirin zuwa Dinner, Amarya ta sanya wani leshi mai matuk'ar kyau da tsada, mai kalan pink da fari sai rashin bak'i a jiki, ta kalmi da pos bak'i, head fari ta sanya, Ango yasha shadda fari anyi mata aiki da bak'in zare yayi kyau sosai, hula bak'ar dara da takalmi bak'i ya sanya.


Ango yana bayan seat aka fito da Amarya aka sanya ta a kusa da Yaya Aryan, Yaya Ahmad shine ke mazaunin driver sai Deeja a gefenta, Walid ta barshi wuri Momy. Suka kama hanyar Wajen Dinner.


Tunda Basma ta shigo Motan, gaban Yaya Aryan ke bugawa ya nima natsuwansa ya rasa, kansa ne ya soma sarawa nan da nan idanunsa yayi ja, Basma kuwa farin ciki ya cika ta matsawa kusa da shi tayi ta kamo hannunsa, da sauri ya runtsa idonsa saboda azabar da kansa yake masa, Basma ta matsa da bakinta kusa da kunnensa tace


"myn yau ba magana ko?"


Murmushi yayi ya juyo ya kalleta suka had'a ido, a razane tace


"Yaya Aryan meya samu idonka yayi ja haka?"


Murmushi ya mata yace
"Missing d'inki ne yasa haka"


Kunya ne ya kama ta sai ta jaye jikinta ta koma gefe, ajiyan zuciya ya saki a hankali, ambaton Allah ya shiga yi a hankali ya soma dawowa hayyacinsa, lamarin ya fara damunsa tsakanin jiya da yau, kuma hakan bai damunsa sai Basma na tare dashi. A ransa yace


"Me yake shirin faruwa dani ne?" babu amsa, dole ya kauda tunanin a ransa.


Sun isa wurin dinner. Wurin ya tsaru sosai, mutane sun hallara zuwan Amarya da Ango ya rage, haka suka fito ya sakala hannunsa cikin nata nan take ciwon kai ya dawo, d'aurewa yayi har suka isa mazaunin su kana ya zare hannunsa a nata.


Taro ya kayatar kuma anci an sha anyi hotuna, anyi rawa an zubda Naira. Matan *sirrin ya mace group* sai rarraba ido suke yi, haka ma manan *Yar Shugaba novel Fan's group* suma sun cashe sosai. Haka aka gama taro kowa ya koma gida cike da farin ciki.


*Washe gari*


Da misalin k'arfe Hudu na yamma gaba d'aya iyayen suka had'u a falon Abba, Basma na gefe kusa da Kaka Ma'u, Aryan yana gefen Kaka Malam, nasiha sosai iyayen suka yi musu akan zamantakewar Aure, Basma kuka take yi mara sauti, shi kuma Aryan jikinsa ne yayi sanyi sosai, bayan sun gama Abba yace


"Hajiya Fatima ina so da ganan ku wuce da Basma gidanta" Ammi tace
"to Yallab'ai"


Nan ta kama hannunsa Basma su Ummi na biye dasu suka wuce wurin motocin gidan, Momy dai part d'inta ta wuce ko waiwaye batayi ba, hawayen farin ciki ke fita a idonta, saboda Basma ta auri wanda take so tasan tabbas zata samu natsuwa. Umma ma bata bisu ba tabi bayan Momy.


Basma kuka take da kyar suka sanyata a mota kamar wannan ne aurenta na farko, gaba d'aya motocin gidan suka kwashe su aka wuce kai Basma gidanta.


Suna kaiwa dama gate d'in abud'e yake haka su kaita parking suna fitowa, falon suka shiga sun tadda su Deeja, Meena, Leema, Safeena, Munayah Matar Yaya Adam, sun kintsa komai na gidan, sun zauna suna jiran zuwan Amarya, Ammi ta wuce da ita d'akinta, ta ajeta kan gado, wani k'aramin kofi ta dank'a mata a hannu tace mata a kunne,


"bayan sallan Magrib ki tabbatar kin sha wannan, Allah ya baku zaman lafiya"


Basma ta k'ara fashewa da kuka tace
"Ammi karki tafi dan Allah" Dariya tayi
"A'a Basma, aiko tafiya ya zama dole kuma ai wannan ba shine aurenki na farko ba balle kice baki saba ba, nan da kwana biyu zamu dawo"


Sai ta janye jikinta daga na Basma ta wuce tana share hawaye, haka suka tafi suka bar su Deeja, sai dare insu Yaya Ahmad sun kawo Ango sannan zasu tafi tare dasu.


*Wai Yaya Aryan yadai?*🤔


*Rahma Ce*
[8/13, 4:11 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *34.*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


*Bayan Sallan Isha'i*


Su Yaya Ahmad sun kawo Ango Aryan, tunda suka shigo gabansa ke fad'uwa ya rasa natsuwan sa, nan su Yaya Ahmad suka yi musu d'an tunatarwa game da aure sannan suka yi musu sallama, da kyar Basma ta saki Meena sai kuka take yi, haka suka tafi tare da yi mata sallama. Yaya Aryan ya rakasu har mota saida yaga wuce wansu kana ya koma cikin falo ya zauna ya cire hulan kansa yana fifita dashi domin duk sanyin AC dake d'akin gumi yake yi, maida hulan yayi ya mik'e ya nufi d'akinsa, ruwa ya watsa tare da d'auro alwala ya sanya farar jallabiya ya fito falo, ya shiga kitchen ya d'auki plet tare da cups, hannunsa rik'e da ledoji ya nufi d'akin Basma.


Ya sameta zaune gefen gado fuskarta rufe da mayafi, zama yayi kusa da ita yaji kansa ya sara d'aurewa yayi ya yaye mayafin, d'ago fuskarta yayi cikin murya k'asa-k'asa yace


"Amaryata kinsha k'amshi, anya zaki rik'a barina ina fita kuwa? dan k'amshin ki kawai zai rik'a riki tani in kasa fita".


Murmushi tayi tace
"anya kuwa myn?"


Murmushi yayi shima yace
"Eh mana, tashi ki d'auro Alwala muyi Sallah"


Cikin murmushi tace
"ina da alwala ban dad'e da idar da Sallan Isha'i ba"


"ok tashi ki mu gabatar da Nafila" ba musu ta mik'e.


Sun idar da Sallan Nafila Raka'a biyu ya kama kanta ya mata Addu'a'o'i, kana suka yi Addu'a gaba d'aya suka shafa, kayan ciye-ciye ya zuba a plet d'in sannan ya zuba mata yoghurt a cup ya kai bakinta kamar ba zata amsa ba, ta bud'e bakin a hankali tana sha, haka ya ciyar da ita komai da hannunsa har sai da ta ce ta koshi kana ya rabu da ita yaci nashi.


Bayan sun kammala ya kwashe kayan ya maida kitchen ya rufe ya koma d'akin ya tadda Basma ta sauya kayan barci ta kuma shiga bayi ta wanke baki, kwanciya tayi akan gadon taja bargo tana dariya k'asa-k'asa tace


"Myn saida safe"


Murmushi yayi yace
"ok Allah ya tashe mu lafiya" sai ya zauna gefen gadon ya dafe kansa, tunani iri-iri yake yi amma ya gaza sanin ina hankalinsa ya dosa, jallabiyansa ya cire ya za gaya d'ayan side d'in gadon ya kwanta, kansa yana ta sarawa d'auriya kawai yake yi, cikin k'ank'anin lokaci idonsa yayi jaaa, hakanan tsoro yaji ya diran masa, Addu'a ya shiga yi dan neman yardan Allah, cikin lokaci kad'an ya samu rangwame ga yanda yake ji.


Jawo Basma yayi tana k'ok'arin zillewa ya d'aurata bisa kirjinshi, gam ya rik'eta suna jin bugun zuciyan juna, cikin rad'a yace mata a kunne


"Rashinki yasa dare ya zame min rana bana iya barci, na shiga k'unci da damuwa, ya zanyi in misalta miki Son da nake miki ki fahimci zuciyana, my Queen kin zama b'angare na jikina bazan iya rayuwa ba ke ba"


Hawaye mai zafi yana fita a idonsa kansa nayi masa tsananin ciwo, Basma ta d'ago kanta tana kallon fuskansa, cikin kasala da damuwa tace


"Myn ka daina min asaran hawayenka, wannan ranar muke jira tazo, dan haka farin cikinka nake so ka nuna min a yau da mai cike da so da k'auna".


Hawayensa ta goge masa, rungumeta yayi tsam ajikinsa tare da sakin ajiyar zuciya. Daga nan kuma salon ya sauya, suka lula duniyar masoya, soyayya suke nunawa juna mara misaltuwa, sun gama kamuwa sosai, Aryan yana k'ok'arin kai ga biyan buk'atansa jikinsa ya soma rawa, nan da nan zazzab'i ya diran masa kansa yayi zafi kamar wuta nan take kwayan idonsa ya sauya kala yayi jaa kamar garwashin wuta, cike da tashin hankali ya ja jikinsa yana haki, Basma ta kamo hannunsa domin ta kama kamuwa dan maganin da tasha suna matuk'ar aiki a jikinta, fincike hannunsa yayi da k'arfi ya mik'e jallabiyansa ya maida ya koma gefen gadon ya zauna tare da dafe kai.


Kuka Basma ta fashe dashi tanata juyi a kan gadon, kukanta ya k'ara tayar masa da hankali, cikin mutuwan jiki ya mik'e da nufin barin d'akin, jiri ne ya kwashe shi ya zube akan gadon yana rawar sanyi, Basma hankali ta yayi matuk'ar tashi, cikin k'arfin hali ta mik'e ta matsa kusa dashi, a can k'asan mak'oshi Aryan ke fad'in


"Basma dan Allah ki matsa a kusa dani mutuwa zanyi, in kina kusanto ni azaba nake ji"


Kuka Basma ta fashe dashi da k'arfi tana fad'in
"Innalillahi wa inna ilai hir rajiu'n". mik'ewa tayi ta shiga bayi ta d'auraye jikinta tare da yin Alwala.


Al'Qur'ani ta d'auko ta zauna nesa dashi ta soma karantawa a nutse tana kuka, dafe kunnuwansa yayi bai son jin karatun amma bai hana karatun na shiga kunnensa ba, a hankali ya soma samun natsuwa, da k'arfi ya saki ajiyan zuciya, juyowa yayi yana kallon Basma hawaye na zuba masa, daina karatun tayi ta aje Al'Qur'ani ta dawo gefensa, fuskanta d'auke da murmushi tace


"Myn sannu ya jikin da fatan baka jin komai yanzu ko"


Murmushi ya mayar mata ya share hawayensa, mik'ewa yayi yana tangad'i, ta mik'e zata kamashi ya daga mata hannu cikin dishewan murya yace


"Kina tab'a ni ciwon zai dawo" ido ta zaro waje tare da toshe bakinta hawaye na fita a idonta, haka ya fita zuwa d'akinsa, wanka yayi ya sauya kayan ya fad'a gado sai barci mai nauyi ya d'auke shi.


Basma zama tayi gefen gado tana kuka wiwi ba mai taimakonta, tunani barkatai take yi amma ta gaza fahimtar komai, mik'ewa tayi ta gyara shinfid'ar gadon ta kwanta, cikin k'ank'anin lokacin barci ya d'auke ta.


*Washe Gari*


Basu suka farka ba sai bayan k'arfe takwas na safe, cikin sauri Basma ta fad'a bayi tayi wanka tare da d'auro alwala, ta gabatar da Sallan aAsubshi tayi dukkan Azkar na safe kana ta tashi ta shirya cikin Riga da sket na atamfa ta d'aura d'ankwali, ba wani make-up tayi ba ta fito falo ta samu Yaya Aryan yana zaune, ta k'arasa falon ta zauna nesa dashi kanta a sunkuye ta gaishe shi, cikin fara'a ya amsa


"My Queen hop kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau Myn, uhum ya jikinka?"
"da sauk'i ai na warware"
"tom masha Allah, Allah ya k'ara afuwa, amma ka tashi da wuri shine baka tashe ni ba?"
"Wallahi naso tashin ki, dan harna isa k'ofar d'akin sai naji gabana na fad'uwa sai na dawo kawai"


D'ago fuska tayi ido cike da hawaye tace
"amma Yaya Aryan a da baka jin irin haka, meyasa yanzu haka ke faruwa?" tana zubda hawaye.


Mik'ewa yayi da sauri ya kamota ta mik'e tsaye, rungumeta yayi tsam ajikinsa, take ya fara jin zafin jiki da ciwon kai, saketa yayi suna kallon juna yace


"Basma bansan me yake faruwa dani ba, tun bayan kwana biyu da suka wuce, duk lokacin da kika zo kusa dani ina shiga cikin mawiyacin hali, kaina ya rik'a min wani irin ciwo tamkar zan mutu, jikina kuma tamkar garwashi, a yanzu haka ina jin abinda nake gaya miki a jikinsa"


Zuba ma juna ido suka yi, tace
"Myn zan kira Yaya Ahmad in sanar masa domin anima maka magani"
Kama hannunta yayi yace
"karki gaya masa saboda kar mu tada musu hankali, yanzu dai ki cigaba damin Addu'a, zo muje mu karya tun d'azu aka aiko mana da breakfast daga gida"


Hannunta ya kama gam suka wuce dinning sunci sun koshi, suna yi suna hira kamar babu wata matsala a tare dasu.


Da midalin k'arfe biyu na rana Mutane suka fara zuwa, Yaya Aryan fita yayi ya basu guri. Basma tana tare dasu Deeja a d'aki sai tsiya suke mata, murmushi kawai take yi dan ita kad'ai tasan halin da suke ciki, kamar ta gaya musu amma saita fasa. haka suka yi mata yini sai dare su Yaya Ahmad suka zo suka kwashe su.


Basma na gefen Aryan yana nishi sama-sama, abinda ya faru jiya shine ya kuma faruwa yau, kuka Basma take yi mara sauti, Addu'a take yi tana tofa masa, a hankali ya samu natsuwa ya hau saman gadon ya gyara kwanciyansa, yau baijin zai iya tafiya ga shi bai wanke jiki ba, haka barci ya d'auke shi mai nauyi. Basma tashi tayi ta wanke jiki ta d'auro alwala Sallan Nafila ta gabatar tare da jero Addu'a, Allah ya kawo musu d'auki cikin matsalan su.
Nima dai na taya su da Ameen.


*Bayan mako biyu*


Su Basma suna cikin wannan halin babu wani sauyi, duk sun rame sunyi haske, d'an kyau da Amare su keyi su sam ba suyi ba. haka suka shirya suka nufi gida dan su gaishe su, sun isa ko wani part sun gaishe su, President yayi tafiya dan haka basu sameshi ba.


Part d'in Yaya Ahmad suka nufa, hira suke sosai Yaya Ahmad ya kalle su yace cikin kulawa


"Aryan, Basma anya babu wata matsala kuwa a tattare daku? kunga yanda kuka yi rama sai haske da kuka yi kamar wanda suka farfad'o daga ciwo"


Murmushi suka yi, Yaya Aryan yace
"Abokina mu da muka yi Auren soyayya ai babu wata Matsala da zai samu damuwa, kawai dai duk cikin Amarci ne muka koma haka, ko ya kika ce My Basma?"


Murmushi tayi tace
"sosai ma kuwa Mijina, hankalin mu kwance yake ba wata damuwa"


Yaya Ahmad yace
"to Alhamdulillah naga yanda kuka sauya ne lokaci guda, dole muyi zargin ko da Matsala"


Yaya Aryan yace
"aiko ba zamu sake zuwa ba sai munyi k'iba sosai, dan d'azu ma Ammi tirkemu tayi, wai me yake damun mu duk mun fita hayyacin mu"


Dariya duk suka saka yaya Ahmad yace
"Allah kuwa duk wanda ya sanku kafin aure in ya ganku yanzu sai anye kunyi rama"


Deeja tace
"raman ma sosai kam, kuma abin mamaki gaba d'aya suka yi raman, Allah yasa dai lafiya"


Harara Yaya Aryan ya watsa mata
"me kike nufi? kina nufin baki gamsu da abinda muka fad'a ba"


mik'ewa tayi da sauri tana dariya tace
"sosai kuwa, ai daga kai har Basma bakin ku d'aya, kuma shegen miskilanci ne daku" tana gama fad'an haka ta bar wurin da gudu dan kar Yaya Aryan ya mata hukunci.


Haka suka gama yinin su sai dare suka koma gida cike da farin ciki, suna isa gida, gabansu ya fara fad'uwa sun riga sun sadak'ar yau ma abinda suka saba fuskanta ne zai faru, sun kuma kasa hak'ura da juna, dan kullun sai Aryan yayi k'ok'arin kusantarta, amma abin yaci tura.


Yaya Ahmad yana kwance a d'aki ya juya ya kalli Deeja sai barci take yi, tunanin su Basma ya kasa b'ace masa a zuciya
"kuma ya kasa yarda da abinda suka gaya masa, yasan wannan karan Basma ba zata tab'a gaya mishi damuwarta ba tunda tana Son Aryan, sannan kuma yasan yanda Aryan ke Son Basma bazai cutar da ita ba, to me yake damunsu su biyun? meyasa su kayi rama haka?"


Tambayoyin da yakewa kansa kenan wanda ya zaga samun amsansu sai a bakin Aryan da Basma zai samu, gyara kwanciya yayi da niyyar gobe in Allah ya kaimu sai je gidan da safe yaga abinda ke faru ko ya matsa musu su gaya masa. Da wannan tunanin ne barci ya d'auke shi.


*Lallai Aryan akwai wata matsala a tare da kai, ko meye ne...?*


_*Hmmm yau dai dasan na tarwatsa farin cikin Makaranta wannan littafin, sai dai ince kuyi min hakuri haka na tsara labarin, kuma ina da dalili, insha Allah za kuyi farin ciki a nan gaba. Godiya gareku masoyana da irin Addu'an ku gare ni. Ina sonku sosai irin da yawa d'in nan Allah ya kara zumunci. Ameen*_


*Rahma Ce*
[8/15, 8:44 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*


_page_ *35.*


_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*


*Washe Gari*


Da k'arfe bakwai na safe Yaya Ahmad ya kama hanyar gidan Yaya Aryan. Yana isa yayi hon Mai Gadi ya bud'e masa Gate, yayi parking ya isa bakin k'ofar falon yayi nocking, Yaya Aryan dake kwance a kan doguwar kujera ya mik'e cikin nauyin jiki ya isa bakin k'ofan ya bud'e, sai yayi arba da Yaya Ahmad, sai da gaban Aryan ya fad'i, matsa masa yayi ya shigo cikin falon duk suka samu guri suka zauna, sai suka gaisa, Yaya Ahmad yace


"Ina Basma fa?"


Yaya Aryan yace
"tana d'aki, lafiya na ganka da sassafe haka?"


"Lafiya lau, nazo nayi magana daku ne, dan haka kira min Basma tazo"


Bai ce komai ba ya mik'e ya isa bakin k'ofar Basma, sai ya ki shiga ya tsaya bakin k'ofar yana bugawa tare da cewa
"Basma, Basma ki tashi ga Yaya Ahmad yazo"


Cikin magagin barci ta farka ta mik'e tare da bud'e murya yace "to".


Yaya Ahmad duk yana kallonshi, a ranshi yace
'ko me ya hanashi shiga d'akin oho' Yaya Aryan ya dawo ya zauna.


Basma ta fito sanye cikin doguwar riga ta yane gyale a kanta, zama tayi a one seater ta gaishe da Yaya Ahmad ya amsa cikin kulawa, shuru ne ya biyo baya na tsayin minti Uku, daga bisani Yaya Ahmad yace


"Aryan, Basma nazo domin muyi magana ne, a gaskiya ban yarda da bayanin da kuka min ba jiya, shiyasa na zo Yau dan jiya na kasa barci, Dan Allah karku b'oye min komai"


Basma da Aryan suka kalli juna suka had'a ido, Basma zata yi magana Aryan ya riga ta yace


"ka yarda da abinda muka ce maka mana domin ba komai"


Yaya Ahmad yayi murmushin k'arfin hali yace
"Basma in shi ba zai gaya min ba ke nasan ba zaki b'oye min ba, dan haka gaya min me yake faru?"


Hawaye ne ya soma zarya a idon Basma, ta d'ago ta kalli Yaya Aryan, sai ya fara gir giza mata kai alamar karta gaya, Yaya Ahmad ya kira sunanta sai ta mai da kallonta gare shi yace


"Basma ina jinki"


Basma ta share hawayenta ta gaya wa Yaya Ahmad abinda ke damun Aryan, sai dai bata gaya mishi matsalan da suke fuskanta ba yayin saduwa sai ta boye wannan.


Yaya Ahmad ya kurawa Aryan ido sai ya sun kuyar da kai zuciyarsa na masa zafi, nan take idonsa suka yi ja. Yaya Ahmad yace


"Basma d'auko key d'in motanki ki shirya ki tafi gida"


Da sauri duk suka zuba masa ido, d'aure fuska yayi yace
"Nace ki tashi kiyi abinda na sanya ki" ya fad'a maganar cikin tsawa, jikinta na rawa ta mik'e tare da fashewa da kuka.


Aryan mik'ewa yayi cikin fushi yace
"Me kake nufi da ta tafi gida ba tare da izini na ba?"


Murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login