Showing 18001 words to 21000 words out of 79094 words

Chapter 7 - YAR SHUGABAN KASA COMPLETE DOCUMENT BY Rahma Kabir .txt

29 Nov 2024

5156

kuka tace
"haba Yaya Aryan kayi hak'uri muje ba zamu dad'e ba" ganin zata fara masa kuka yace
"to muje".


Nan suka shiga mota suka fara tafiya, ta sanya wak'ar larabawa yana yi a hankali, ta juyo tace
"Yaya Aryan kayi kyau amma abu d'aya ya b'ata wankanka" murmushi yayi bai tanka mata ba, ai bai aune ba sai yaje ta janye hulan kansa ta b'oye a dayan gefenta, da sauri ya juyo yace
"wai ina wasa dake ne?" tuni Basma ta shagaltu da kallon sumansa saura kad'an ta buga motan dake gabansu, da sauri ta gyara tuk'in ta mai da hankali kan hanya, Yaya Aryan ya kwashe da dariya yace
"Yarinya taga suma ba irin nata ba ta rikice" dariya kawai tayi bata ce komai ba har suka isa wurin shak'atawa.


Parking suka yi duk suka fito, suka jera ba tare da sunce ma juna komai ba, shi dai binta kawai yakeyi, sun isa wani wurin da aka zagayeshi da furanni masu k'amshi, wuri sanyi ga iska mai dad'i, kujerune a ciki da table a tsakiya duk suka zaune, weta ne ya zo da sauri ya tambayesu abinda za a kawo musu, Basma tace
"ice cream da shawarma da kuma drink" ta kalli Yaya Aryan tace
"Yaya me za'a kawo maka" yace
"duk abinda zaki ci shi zanci" murmushi tayi ta gaya ma weta ya tafi kawo musu.


Suna fuskantan juna Yaya Aryan yace
"dama nan wurin zaki kawoni" dariya tayi tace
"eh, saboda in dan saka ka waye, dan naga kamar baka waye ba" hararanta yayi yace
"kece dai baki waye ba da kike sanya k'ananun kaya ki fito ko ajikinki wai irin kin had'u" da sauri ta kalli jikinta tace
"Yaya kana nufin banyi kyau ba ne?"
"eh baki kyau ba saboda shigan bata dace dake ba" tace
"Yaya Aryan, na sanya ne saboda naga a mota nake" riga da wando ta sanya sun kamata sai dai rigan ya sakko har gwiwanta amma duk shape d'in jikinta ya fito sai ta yi rolling da gale a kanta ta rufe gashinta" yace
"eh, ai ba shiga bane na musulunci mace tayi ta fita" jikinta ne yayi sanyi tace
"To insha Allah bazan sake yin shigan na fito ba, amma zan rik'a sanyawa a gida" murmushi yayi yace
"da dai yafi miki" tace
"Yaya Aryan sumanka tayi maka kyau, meyasa kake rufewa?" ya kalleta suka had'a ido sai da suka kalli juna na tsayin minti uku, kana ya sauke ajiyan zuciya yace
"Basmaaa" sai duk jikinta ya mutu ta sunkuyar da kai k'asa, sai taji ta cigaba da magana,
"bana son barin suman, kuma yawan askewa yana k'ara yawansa, shiyasa nake yawo da hula, saboda in mutane suka gani suna yawan min magana akai" murmushi tayi tace
"Yaya Aryan dan Allah karka aske, zan siyo maka mayuka na maza, da zaka rik'a gyarawa, wlh har sheki zai rik'ayi, ba kaga yanda mazan India suke yi bane" murmushi yayi yace
"ni Basma bana son sumar dan a takure nake" marairaice fuska tayi tace
"to ko zaka aske, karka aske duka ni ina son ganinka dashi" hararenta yayi, kan yayi magana an kawo musu shawarman.


Sai wayar Basma ce ta d'auki k'ara, da sauri ta d'auka ta kara a kunne, tace
"My Shureym" saita shagwab'e fuska ta fara shagwab'a,
"bayan kasan ina missing d'inka, shine duk yau baka kirani ba ka manta dani" ta b'angaren Shureym kuwa ya shiga lallashinta.
Aryan zuciyansa ne ke dukan uku-uku hankalinsa ya tashi, amma saiya dake, ya cigaba da cin shawarman, amma abin mamaki kamar yana cin magani sam baya jin dad'in sa, sunkuyar da kai yayi k'asa, zuciyansa nayi masa zugi, numfashinsa yana fita da k'arfi, dakiya kawai yayi. Basma sun d'auki tsawon minti sha Biyar suna wayan, daga bisani suka yi bankwana ta kashe wayar.


Ta kalli Yaya Aryan tace
"Yaya kayi hak'uri na d'auki waya ban nima izini ba" d'agowa yayi idonsa ya kad'a ya d'anyi ja, sai yayi mata murmushin yak'e yace
"karki damu bakomai" murmushi ta mayar masa, ta mik'a hannu ta d'auko sauran shawarman da ya rage ta soma ci ko ajikinta. Sam bata lura da sauyawan yanayin sa ba, saida ta gama tace
"Yaya Aryan" ya d'ago ya kalle, tace
"bari muyi salfee mana?" murmushi gefen baki yayi yace
"ni bana hoto" shagwab'e fuska tayi tace
"ni dai dan Allah muyi" bata jira me zaice ba ta mik'e ta zo bayanta ta tsaya, shi kuma yana zaune, aiko ta kashe musu photo har uku, shi dai fuskansa ba yabo ba fallasa, gaba d'aya zuciyansa a takure yake, tace
"gaka kuwa yanda mukayi kyau?" ta nuna masa, ya kalla shima kanshi hoton ya ma kyau yace
"yayi kyau" tace
"Yaya muje gida yamma yayi sosai".


Bayan sun kama hanya, ta ciro hulansa ta bashi tace
"Yaya Aryan, gobe in Allah ya kaimu zanzo mu k'ara fita" murmushi yayi yace
"Allah ya kaimu" haka ta sanya wani wanka da music na soyayya, sai bin wakar take, shi ko kwantawa yayi a bayansa yana sauraren wak'ar da muryarta ,gaba d'aya ya shiga wani duniya wanda shi kanshi bai san wani irin duniya ya lula ba.


Ta sauke shi suka yi sallama, kana ya wuce cike da damuwa a zuciyansa, itama ta wuce cike da farin cikin a zuciyarta mara misaltuwa.


Da dare misalin k'arfe goma da rabi, Basma ta kira Yaya Aryan, yana kallon kiran yak'i d'auka, ta kira shi ya kai sau goma amma yak'i d'agawa, haka nan yaji ba zai d'auka ba, domin shak'uwar da zuciyansa yake da Basma, ya fara bashi tsoro kuma ga dukkan alamu ya soma shiga wani hurumi da ba nashi ba, dole ya d'auki matakan kaucewa damuwa.


Basma kuka ta shiga yi hawaye wannan na bin wannan, iyaka damuwa ta shiga, da kyar barci da d'auketa. Haka ma ta b'angaren Yaya Aryan, k'arshe ma tashi yayi ya gabatar da sallan nafila yayi Addu'a akan, Allah ya k'are masa zuciyansa da irin abinda ya soma raya masa game da Basma.


*Washe gari*
Basma da ciwon kai ta tashi, ta samu ta karya tasha magani sannan ta koma barci. Ta wurin Yaya Aryan kuwa ya samu sassauci game da abinda yake ji, ya shirya ya tafi kasuwa kamar yanda ya saba kullun, amma a k'asan zuciyansa yana tuna masa hiran Basma da Shureym sai damuwa ya ziyarce shi.


Da misalin k'arfe biyar ya dawo daga kasuwa, da sauri yayi wanka ya shirya ya fita, unguwar ya bari gaba d'aya saboda baya so su had'u da Basma. Ta b'angarenta kuwa ta zo tayi parking in da suka had'u jiya, tayi ta kiran wayan ba'a d'auka ba, kuma ta jira shi bai zo ba har kusan k'arfe shida na yamma, abinda bata sani ba Aryan yana hangen motanta ya b'oye a wani shagon aski, hakanan yaji tausayinta kamar ya fito sai kawai ya basar, haka ta hak'ura zuciyarta na mata zafi ta tuka motan a hankali, idonta na zubda hawaye, ta shiga damuwa na rashin zuwan Yaya Aryan, a haka ta isa gida kamar mara lafiya.


Shima Aryan cikin damuwa ya wuce gida bayan tafiyarta, koda Umma ta ganshi ta tambaye shi ko lafiya? yace mata kansa ke ciwo, sai tayi masa sannu.


Yau da wuri ya dawo gida ya kwanta, yau ma yak"i d'auka wayarta, a haka ko wanne ya kwana cikin damuwa.


*Washe gari Monday*


Basma da sassafe ta fito tazo gidansu Deeja, ta samu Deeja ta shirya suka gaisa da Umma, Aryan yana d'aki yana jinsu amma yak'i fitowa, dauriya Basma tayi tak'i tambayar ko yana nan, suka yiwa Umna sallama suka wuce University dake cikin Abuja, da yake ansan da zuwansu basu sha wani wahala ba wajen yin registration d'in, kuma dama president yasa hannu, Deeja an d'auke ta ba tare da zana wani exam ba, ta samu Medicine b'angaren mata (gynecology). Zuwa k'arfe biyu sun gama komai, sai suka kama hanyar gida.


B'angaren Yaya Aryan, ya tafi company su Basma, ya had'u da Yaya Naufal kamar yanda Yaya Ahmad ya gaya ma Naufal d'in, Yaya Naufal yayi masa interview, ga mamakinsa duka Yaya Aryan ya amsa masa, gashi dai ba digree gareshi ba amma ya amsa masa duk tambayoyinsa. Ya duba takardunsa sosai, cikin k'asaita da mulki yace


"sunana Naufal, a yanda na gwadaka kuma na duba takardunka gaskiya komai yayi yanda muke so, mun d'auke ka aiki, sannan bayan kamar watanni zamu turaka ka k'aro karatu kayi degree da masters, ga wannan kud'in kuma ka samu ka siya kaya na zuwa office, dole ne ka rik'a shiga mai kyau domin zaka rik'a ganawa da manyan mutane, office d'inka shine na b'angaren computer, kai ne mai shigar da komai in an fitar da kaya ko an shigo da su, da fatan ka fahimta"


Yaya Aryan cike da farin ciki yace
"na fahimta, nagode Allah ya saka da alkhairi" duk wannan bayanin cikin harshen turanci suke magana, kana Yaya Naufal ya rakashi katon office d'insa, mai d'auke da kujeru na alfarma da katon table, ga AC, ga fridge, kai har toilet akwai a ciki, komai dai normal, Yaya Naufal ya gama nuna masa komai ya fice, Yaya Aryan ya zauna kan kujeran table d'in ya juya yana kallon kud'in da aka zubama office d'in, sai hawaye ya soma zarya a kuncinsa, farin ciki da begen son ganin Basma ne ya bijiro masa, ba dan Allah yasa sanadin ta ba, da ba zai tsinci kansa a irin nan wurin ba.


Suna isa Basma ta fad'a d'akin Yaya Aryan ta kwanta bisa katifansa, cikin kankanin lokacin barci ya d'auke ta. Deeja ce ta shigo taga tana barci, taso tashinta ta koma d'akin su, amma saita kyaleta ta cigaba da barcin, ta koma wurin Umma tace
"Umma Basma fa barci takeyi, da zan tasheta ta koma d'akinmu saina barta" Umma tace
"kyaleta ta kwanta ta gaji ne, kinsan yaran masu kud'i basu saba da wahala ba, kuma ma ai d'akin Aryan yafi namu gyaruwa zata fi jin dad'in barcin anan". Khadija tace
"hakane kuma" sai suka cigaba da aikin su na girki, Umma na rangad'a musu, tuwon shinkafa miyar kub'ewa d'anya wanda yaji nama.


Da misalin k'arfe uku da rabi, Yaya Aryan ya dawo gida daga company su Basma, ya zauna bisa tabarma a tsakar gida, ya gaisa da Umma, kana yace
"Khadija kun gama registration d'in?" tace
"eh, Yaya mun gama komai, Monday mai zuwa zan fara zuwa d'aukan lectures" yace
"masha Allah, Allah ya taimaka" duk suka amsa da "Ameen", Umma tace ya kuka yi ne a wurin da kaje?" murmushi tayi yace
"Umma komai Alhandulillah, an min interview, kuma na ci, musamman suka bani office nawa ni kad'ai, nine zan d'inka shigar da komai na company" kud'i ya ciro daga aljihunsa yace
"wannan kud'in budi D'ari biyu ne, sun bani na siya kayan sawa kawai na zuwa office, saboda zan d'inga ganawa da mutane, masu amsan yakan company" baki Umma ta bud'e tace
"ikon Allah, wannan Abu haka, gaskiya ba abinda za mucewa Basma da Yayanta sai Allah ya saka musu da gidan Aljanna" duk suka amsa da "Amin"


Yaya Aryan yace
'gobe insha Allah zan fara zuwa aiki, albashi na kuma dubu d'ari biyu duk wata" ai Umma sai kabbara, ta yiwa annabi salati s.a.w, hawayen farin cikin ta soma fiddawa, Deeja tace
"Umma ba kuka za kiyi ba, waraka Allah ya kawo mana dan haka saimu gode masa".


Nan ya mik'e ya shiga d'akinsa, ai sai yaci karo da Basma tayi d'ai-d'ai bisa godonsa, gashin kanta ya baje a bayanta, da gani barcin gajiya take yi, murmushi kawai tayi yace a ransa
"Basma rigima, wato ba tad'a wurin barci sai d'akina" Wasu kaya ya d'auka, ya fito ya shiga bayi, Basma da tun shigowarsa ta farka tabi bayansa da kallo tana murmushi.


Bayan ya fito daga wankan ya wuce d'akin Umma ya sauya kaya, masallaci ya wuce dan yin sallan La'asar, suma su Umma suka gabatar da nasu sallan. Basma ta fito tayi alwala ta shiga d'akin Umma tayi sallah, anan Deeja ta kawo masu tuwo suka ci tare, bayan sun gama ta shirya zuwa gida ta yiwa su Umma sallama ta fito, Deeja ta rakata mota ta wuce.


Tafiya take a hankali zuciyarta cike da son ganin Yaya Aryan, aiko tana yin kwana ta hangeshi tsaye inda ta d'auke shi rannan, farin ciki taji a zuciyarta kana ta d'aure fuska tamkar ba ita ba, ta k'arasa tayi parking mota, ba tare da ta ce masa uffan ba ya bud'e motan ya shiga, yana shiga ta tada motan suka wuce ba wanda wace wani Abu, ko wanne da abinda zuciyansa ke saka masa. Yaya Aryan ya katse shurun yace
"Basma" juyiwa tayi ba tare ta tace komai ba, sai hawaye ya fara zuba a idonta, ta juga ta cigaba da tukasu....


*Hmmmm wannan abu ya fara bani tsooloooo😉😂 koya zasu kwashe...🤔*


*Rahma Ce*
[8/4, 5:19 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑


_page_ *10.*


_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾


Wani wajen shak'atawa ta kaisu ba wancen na farko ba, sun samu k'asan wata bishiya suka zauna kan kujeru, ga table a tsakiya, an kawo musu drinks ne da ruwa, Basma ko kallon Yaya Aryan batayi ba kuma tak'i magana, jikin Yaya Aryan yayi sanyi sai ya kwantar da murya yace
"Basma fushi kike dani?" kallo d'aya ta mishi a fak'aice sai ta kauda kai gefe, murmushi yayi yace
"haba k'anwata ki daina fushi dani mana, bana son ganin b'acin ranki, burina in saki farin ciki har k'arshen rayuwana" d'agowa tayi suka had'a id, idonunta fal da hawaye suna gabda zubowa, da sauri Yaya Aryan ya tara hannunsa a fuskanta domin hawayen ya sauka bisa tafin hannunsa, cikin wani irin murya wanda shi kanshi baisan yanada ita ba, mai dad'i da zak'i yace
"Basma karki min asaran hawayenki ya kai ga zuba a k'asa, ba tare da na sharesu ba, ki yafe ma Yayanki, ba zai zake b'ata miki raiba" murmushi tayi na jin dad'i, saita runtse idonta hawayen suka sauka bisa hannunsa, Yaya Aryan ya koma ya zauna, suna kallon juna ya d'aga hannunsa zuwa bakinsa ya lashe digon hawayen ya shanye, Basma saita tafa masa rap rap rap, cike da farin ciki tace
"wow, Yaya Aryan yau kawai na tabbatar da cewa ka d'aunke ni jinin jikinka kuma 'yar uwanka" murmushi yayi yace
"ke ce baki sani ba amma tun ranar da kika bani hak'uri na d'auke ki a haka, kawai dai na d'an nuna miki ni din Namiji ne" hararansa tayi na wasa tace
"ohoo dama shiyasa ka ke basar dani domin kaga rauni na ko, amma ba komai tunda ka fahimci yanda na d'auke ka" dariya yayi yace
"sosai na sani, Basma kin zama haske a rayuwana da Ahalina, sanadinki Umma da Deeja da Ni kaina muna farin ciki, kin mana abinda ban san dame zan biya ki ba face Allah ya baki miji nagari, ya kuma baki Aljannah" murmushi tayi najin dad'in abinda yace har cikin taranta, Abu d'aya ne taji ya mata wani iri lokacin da ta tuno da Yaya Shureym, tambayar kanta ta shiga yi,
"yanzu inna yi aure shikenan Yaya Shureym ya rabani da Yaya Aryan kenan?" Nan danan taji zuciyarta ya mata wani iri, ganin ta lula duniyar tunani, sai Yaya Aryan ya matso da fuskansa ya hura mata iskan bakinsa, nan take ta dawo hayyacinta, sai duk suka zubawa juna ido, suna baiwa junansu wasu sak'onnin cikin kwayar idonsu, suna karantar wa juna sirrin zuciyansu, sun d'auki tsawon minti biyar kana Yaya Aryan ya kashe mata ido d'aya, da sauri ta sunne kai k'asa alaman jin kunya, a gaskiya duk wanda ya gansu a wannan yanayin, babu abinda mutum zaice illa Aryan da Basma masoya ne.


Yaya Aryan ya d'auko kujeransa ya dawo kusa da ita, da muryansa mai dad'i yace
"k'anwata meyasa ba kya jin kunyar kallon kwayar ido na? ke ce mace ta farko da take iya kallon ido na harta karanta wasu sirri dake ciki, domin ido naya d'aya daga cikin abinda kewa mutane kwarjini" murmushi tayi kawai ba tace komai ba, ya cigaba da cewa
"Amma na fahimci idanunmu sun fara sanin sirrin dake cikin juna, kema haka idonki yake kamar nawa" Basma sunkuyar da kai tayi k'asa, bata tab'a jin nauyi ko kunyar wani namiji ba sai akan Yaya Aryan, wasa take da yatsun hannunta, ta kasa motsi mai k'arfi, gaba d'aya tanajin ta a cikin sabon yanayi da bata tab'a jiba game da wani d'a namiji sai akan Yaya Aryan, a yanzu kunya da kwarjininsa ke tasiri a jikinta, Yaya Aryan ya kira sunansa yace
"Basma kinyi shuru ko yau ba kya jin tsokana ne, magana da kuma fad'a?" murmushi tayi tace
"ai Kaine kake magana, tun d'azu kake wasu bayanai da ban fahimcesu ba" murmushi yayi yace
"kina so ki sansu?" tace
"eh ina so" yace
"to d'ago fuskanki ki kalleni, zaki fahimci abinda nake nufi acikin ido na" ta d'auki minti d'aya kafin ta d'ago fuskanta, suka had'a ido ko wanne fuskansa da murmushi, sakonni suke zubawa zuciyoyinsu, ko wanne idonsa yayi tamkar mangyada aciki, bugun zuciyarsu yana buguwa a hankali, zan iya ce muku suna bugawa kusan a tare, idonun su yana k'eftawa a hankali tamkar ba zasu rufe ba, numfashinsu yana fita a hankali kamar basa cikin duniyarmu, sun d'auki tsawon minti bakwai, kana Basma ta yi ajiyar zuciya ta sun kuyar da kai, shima Yaya Aryan ajiyan zuciya yayi, cikin wani irin murya kamar yana rad'a yace, Basma kin fatimci abinda nake nufi yanzu?" murmushi tayi kawai ba tace komai ba.


Wayar Basma ce tayi ringing, Yaya Shureym ne ya kirata, a wannan lokacin sai taji sam bataji dad'in kiran nasa ba, kamar ba zata d'aga ba, saita d'auka suka gaisa, yau hiran nasu sama-sama suka yi, hakanan taji bata son magana dashi, bayan ta gama ta kashe wayar juyowan da zatayi sai taga ba Yaya Aryan a gun, gabanta ne ya fad'i, ta fara tunanin ko ta b'ata masa raine akan d'aukar wayan, mik'ewa tayi ta hangoshi can yana wasa da ganyen wata bishiya, wurin ta k'arasa tace
"Yaya Aryan" da sauri ya juyo idonsa ya kad'a ya d'anyi ja, kan ta kuma magana ya d'aura hannunsa bida leb'ensa yace
"shiiii, kin gama wayan?" cikin yanayin rashin jin dad'i tace
"eh Amma kayi hak'uri" murmushi yayi yace
"hak'urin me zanyi, ai baki laifi ba, da mijinki kike waya fa to me zaisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login