Showing 24001 words to 27000 words out of 133697 words

Chapter 9 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8488

kamar wacce a ka koro, bed din mom ta nufa ta haye hadi da jan blanket ta rufe jikinta tana cigaba da kuka
kusa da ita mom ta ƙaraso tana fadin " ke kuma lafiya kamar an koroki, mikike ma kuka ne"
"Mom ya abdallah ne zaiman allura"
"Yau ni naga takaina ni kubrah, shine kika shigo kamar an koroki "
Mom bata rufe baki ba sai ga ya abdallah yashi go hannun sa rikeda leda, yaje dakin su bai sameta ba
tada Aairah mom tayi magani yafara bata da kuwa zai mata allura sun sha buduri har Mom , sai da yayi mata jan ido tukun a ka samu a kayi allurar dama haka yake fama dasu ita da Aaimah Indai a kace basu lafoya tofa sai sun kusa tara masu mutane a gida saboda allur kawai, amma kullum Iƙirarin su shine su zama likitoci
Kuka Aairah tasha Banida kuka ba, sai dai ta kwana dakin Mom Aaimah ma nan ta dawo ta kwanta saboda bata iya kwana dakin su ita kadai...


WASHE GARI...


Alhmdllh tatashi da jikin da sauki sosai bedroom dinsu ta koma tayi wanka tasa kaya mara sa nauyi
ko da Aaimah ta shigo tana tambayar ta ya jikin
"da sauki sosai"
"to Allah ya Kara sauki, hajiyar allura "
harara ta bugama Aaimah, ita kuwa mi Aaimah zatayi inba dariya ba tana fadin "wlh sister duk mijin da ya aure ki zai sha fama musamman idan shi likita ne, dan wlh nasan tara mashi mutane zaki rikayi muddin baki da lpy yace xai maki allura"
"kice duk mijin daya aure mu dai, sai kace kema allurar kike so zaki wani tasa ni gaba kina man dariyar banza"
"ai wlh kinsan gara ni dake wllh"
"wlh karya ne bawani nan"
"to uwayen musu da safiya zaku fara ma mutane musun tsiya da kuka saba, ba kamar ke Aairah daga samun sauki harzaki fara dan banzan surutun da kuka saba"
Mom ta fada wacce shigowar ta kenan tasame su suna ta gaddamar da su ka saba "ke kinyi wankan kokodai sai kungama musun sannan"
"A'a yanzu zanyi" Aaimah ta fada hadi da nufar toilet ta shiga, kusada Aairah Mom ta matso tana fadin "ya jikin, duk dama kinji sauki tunda gashi harkina musu"
murmushi tayi hadi da daura kanta saman kafadar Mom tana cewa"da sauki Mom, Aaimah ce da raini wayau waini take ma sharrin bana son allura saika ce ita ma so take" murmushi kawai mom tayi tana fadin Allah ya shirye ku "ameen Mom" Aairah ta fada


✨VICTORIA✨


sanye take da uniform din ta, fita tayi daga office din su direct lifter ta nufa numbobi ta danna kofar lifter ce ta bude wasu nurses ne ciki shiga tayi ciki itama
Lifter na tsayawa kowa ya fice alamar sun kawo inda zasu, fita tayi itama direct office din Dr Shazim ta nufa saida ta zo bakin kofar office din tukun ta tsaya, waige waige tashiga yi alamar rashin gaskiya
saida ta tabbatar ba mai ganin ta tukun ta sanya key din dake hannun ta ta bude office din da sauri ta shige ciki saboda jin alamar kamar mutum na tunka ro office din


tsi office din yake alamar ba kowa a cikin sa , sai ac dake aiki
wurin freezer dake office din ta nufa.
- to fa nace mi Victoria ke shirin yima dactor A office ne🤔-
bu dewa tayi, cike yake da drinks kala kala, gani nayi ta dauko kwalin daya daga cikin drinks din ta a jiye saman wani dan ƙara min table dake kusa da fridge
Sannan ta sake dauko wani, a ta kaice dai sai da ta ɗauko kusan kowace color dake ciki sannan ta maida ta rufe.
Hannu tasa cikin aljihun wandon kayan ta, ta fito da wani gari cikin wata yar ƙara mar ruba fari tas dashi , buɗe marfin kowane kwali na drinks din tayi sannan ta dibi wannan garin ta zuba ta girgiza, daya Bayan daya sai da ta tabbatar ta girgiza kowane ya girgizu sannan ta mai da ta rufe
maida su tayi ciki ta jera su kamar yanda ta same su, rufe fridge tayi sannan ta kama hanya ta fice ta nufi lifter ta sake danna numbobi kamar dazu sai ga kofar ta bude
sai da gaban ta ya fadi saka makwan ganin hidaya da maryam da tayi ciki tasan dole suyi zargin wani abu saboda a wannan floor din daga office din dr shazim sai na dr kabir sauran wuraren ɗakin marasa lpy ne da inda patient ke zama dan ganin likita in sun zo, kuma gashi lokacin da patient ke zama bai yi ba, an dai bu ɗe offices domin sharewa da moping. dan doctors babu wanda yazo
kallon kallo suka shiga yima juna itada hidaya dan ita maryam harara kawai ta bita da ita
Itama harar maryam din tayi hadi da tsaki ta shige cikin lifter fita suka yi dama nan suka nufo
"Aikin bazan harara a cikin duhu, yar wahala kawai" maryam ta fada hadi da jan hannun hidaya suka wuce , itama tsakin tayi hadi dacewa "oho dai dr ne dai saina rabata dashi, kuma kema zan dawo kan kine inna gama da ita"
Haka dai taita ban baminta a banza har ta kai inda zata sauka


A chan kuma hidaya ce ke ce ma maryam "nifa kinsan gani nake Victoria kamar bata da gsky,"
"mikika gani? "Maryam ta tambaya
"bakiga tana ganin mu ba duk tawani sha jinin jikinta, bayan haka ma mita zo yi floor ɗin su Dr yanzu ba lokacin fara aiki ba, ni sai nake ganin kamar wani abun tayi"
"Uhmm haka ne kumafa hidaya, ke ita ta sani chan taje taji da rashin gaskiyarta, si Allah na sama yana kallon duk wani abu da zatayi, koma mi tayi dan kanta hidaya ita da Allahn daya halicceta"


"Wlh kuwa ita da mahaliccinta" hidaya ta fada abun da ya kawo su suka shiga yi, suka ture zan chan Victoria gefe


Tana shiga office din su destiny ta samu da wasu daga cikin nurses din da suke zama office din
wurin destiny ta kara sa tana fadin "sister shigowar ki kena? "
"Eh yanzu nazo, nama yi tuna nin bakizo ba sai da naga ka yanki a locker sannan, amma daga ina haka.? "
"Mufita daga waje na fada maki, nan kinga mutane, kuma kinsan su da bakar gulma yanzu zakiji magana wani wuri."
"hakane kuma" destiny ta fada hadi dajan hannun Victoria suka fice daga office din
sai da suka shiga wani dan corridor ku sada office din su sannan Victoria tace"daga office din dr nake"
"kai da gaske kike"
"da gaske nake mana, kaji destiny na taɓa maki wasa ne, daga chan nake"
"Amma ina fatan ba wanda ya ganki ko, kuma kinyi yanda gurutu yace muyi"
"Sosai ma kuwa, ai kamar yanda yace nayi haka nayi"
"Yawwa yanzu sai dai mu tsaya jiran saka mako kawai"
"hakane kam, kinga mu koma office kar wanima ya fito"
"kumafa haka"
Office din suka koma dumin shirin fita dan da suka shiga office din ba kowa ciki duk sun fita , suma basu wani jima ba suka fice..


✨Hidaya✨


Zaune suke ita da maryam da sauran nurses din asibiti fira suke yi kafin doctors su shigo kowa ya kama gaban sa zuwa inda yake nasa aikin
suna nan zaune dr shazim ya shigo shi da dr kabir da Noraiz, yana gaba su Noraiz na bayan shi
gaishe da su nurses din su kayi Noraiz da Dr kabir ne kawai suka smsa masu Shazim kuwa hannu kawai ya iya daga masu
Suna zuwa bakin office din shi briefcase dinsa dake hannun Noraiz ya amsa
saboda shi Noraiz office din Dr kabir zai wuce
Office din ya shiga, ko ina fes an gyara sai kamshin fresheners
tarkacen sa ya ajiye saman table hadi da zama kan chair dinsa laptop dinsa ya jawo ya fara aiki a ciki, nocking aka yi "Come in" ya ba da izin, hidaya ce ta shigo bakin ta dauke da sallama, hannun ta riƙe da file,amsa mata sallamar yayi "GM Dr, dama nace zan iya fara turo patient"
kai kawai ya daga mata alamar eh "ok" ta fada hadi da ficewa ta koma wurin patient
wurin 12:00 ya gama ganin patient din dazai gani time din har Noraiz ya dawo office din ,
"Yaya wai baka da wani abun cine a office dinnan"
Noraiz ya fada yayin da yake bude fridge dake office din "to a cici ni bana aje komai daya danganci abinci a eko , zaka iya bari Sai munje abnoor tukunnan" kwalin lemu ya ɗauka sannan ya
rufe fridge ɗin , yana fadin "bari nasha wannan kafin mu tafi " wurin zaman shi kan sofa ya koma ya zauna hadi da bude marfin lemun, Dr kabir ne ya shigo da sallama a bakin sa hannun shi ɗauke da basket din abinci yana cewa "wlh Momma har yanzu kallon yaro take man, wai abinci tasa aka biyo ni dashi saboda kawai banyi breakfast na fito ba"
"dama ai kai yaro ne" shazim yafa da yana murmushi "haba dai kai ka san wanene yaro wlh"
"ai duk auta yaro ne"da yake kabir shine auta a wurin momman shi
"lallaima Shazim wlh ka rainani" maganar Noraiz ta katse su yana cewa
"wlh Momma ni ta tai maka kamar tasan yunwa nake ji" kallon shi Shazim yayi yana girgiza kai da fadin
"wlh Allah ya shiryaka Noraiz, duka ƙarfe 12 amma sai wani complain din yunwa kake, sai kace wani karamin yaro"
"Yaya kasan fa ina fama da ulcer" ya fada yana shafa cikin sa
"bawani ulcer kawai ragon cine"
Shi dai dr kabir binsu kawai yake da idanu yana murmushi
"to yanzu dai ku kale wannan musun, kai Noraiz zo ka zuba abinci kaci" Dr kabir ya fada
dawowa Noraiz yayi kan sofar da Dr kabir yake , plate ya dauka da serving spoon ya buɗe food flask farar shinkafa ce, zubawa yayi sannan ya bude dayar flask din wacce pepper soup ce ciki, duka dai y
sai da ya buɗe kowane flask dake cikin basket din sannan ya koma gefe yana ci, Dr kabir ya zuba ma Shazim yana cema noraiz "wato ɗan tsako sami ka ki dangi ko"
dariya kawai Noraiz yayi
"Ok bakin maganar ya mutu kenan" Dr kabir ya fada yana murmushi, shima dai Shazim murmushi yayi yana cewa "baka san waye noraiz ba a kan abinci" daga nan su kayi shiru kowa na aikin bama cikin sa
sai da suka gama Dr kabir ya nufi fridge ya dauko masu lemu da ruwa
Shi noraiz ruwa kawai ya amsa saboda ya dauko lemu tun dazu sai da suka gama tsab sannan suka tashi shazim Duka tarkacen sa ya haɗa saboda da sun dawo sallah abnoor zasu wuce shida Noraiz.......


✨Aairah ✨


Alhmdllh jiki yayi sauki sosai dan yanzu haka zaune take parlor suna fira ita da Mom da Aaimah wacce taki zuwa school saboda Aairah bata je ba abie ne ya shigo daga masallachi sallar zuhur wurin su ya nufa zama yayi kan sofar da Aairah take yana faɗin "ah lallai jiki yayi sauki Masha Allah" hadi da shafa kanta
Mom tace"Jiya kana part ɗinka da ka ga budirin yin allura"
abie yace "Allah dai ya shirya yaran nan da dan bazan tsoron allura, a haka zaku zama Drs din da ku ke so kuna tsoron allura"
Aaimah tace"duk da haka abie muna iyawa Allah"
abie yace "to Allah dai yasa"
Aairah tace "ameen abie"
sun jima suna fira har wurin ƙarfe 3:00 sannan suka tashi


✨ Shazim ✨


Yau da wuri suka bar abnoor saɓanin kullum da sai yayi sallar magrib da isha sannan ya ke ko mawa gida, duk da yanzun ma ba gida suka nufa ba gidan malam suka nufa domin sukara duba jikin sa
Zaune suka same shi a parlorn shi yana duba littafi, sallama su kayi hadi da shiga cikin , cikin parlorn amsa masu sallamar yayi yana tambayar su ya aiki, da alhmdllh suka amsa mashi
Shazim ya ce"ya ƙarfin jiki"
"Masha Allah jiki alhmdllh , yanzu ko ina ina iya zuwa alhmdllh "
"Masha Allah Malam Allah ya ƙarl sauki da Nisan kwana mai amfani"
"Ameen ya Rabbi"
"Malam kodai lokaci ne yayi, muyi shirin cin gumba" noraiz ya fada yana dariya
dakkuwa malam yayi mashi "lallai nuraddeen ni kake ma fatan Mutuwa koh, to sai dai mahaifiyar ka ta mutum amma bani ba, ja irin banza"
dariya Noraiz ya kwashe da ita yana fadin "yanzu nan malam baka san mutuwa"
Shazim dai na gefe yana jin su in ban da murmushi ba abun da yake
"mutuwa na kan kowa nuraddeen , yaushe musilmin kwairai zai guji mutuwa, kawai dai ana tsoron mi za'a riska in an je chan"
"haka ne kam Malam, Allah dai yasa mu mutu muna masu Imani"
da Ameen suka Amsa su duka , nan mlm ya shiga yi masu nasiha a kan ruƙo da gaskiya da kuma aiki da ita da tsare mutuncin kai, sannan ya ƙara yima shazim fada a kan ya fitar da mata yayi Aure shekarun sa ƙaruwa suke ba raguwa ba, kuma mahaifiyar su bata da wani buri daya wuce taga ta aurar dasu baki daya shine kwanchiyar hankalin ta, saboda dangin mahaifin su gani suke kamar ita da malam suka hana shi yin aure, "Shazim ko baka so naga jikokin jajirtaccen jika na ne" duƙar da kanshi yayi ƙasa yana cewa "ba haka bane Malam, Insha Allah zanyi kokari nayi nan kusa"
"to Allah ya yarda, ya kuma za ba maka mace tagari kai da ɗan uwanka, itama fatima Allah ya bata miji nagari"
da ameen suka amsa su duka har da ummy wacce shigo war ta kenan parlorn taji suna adu'a shine itama ta amsa da ameen.gaishe da ita su kayi , cikin kulawa ta amsa tana tambayar su ammy, shazim maganar kasuwancin shi da yake son noraiz ya cigaba da kula da su yayi ma malam da noraiz ɗin kan shi, "eh wannan shawara ce mai kyau,dama ya kamata ka rage ma kanka wasu abu buwan,"
"hakane, dama jiran dawuwar sa nake
na tattara komi na miƙa masa "
"yayi hakan Allaha ya tai maka,amma ko da noraiz ɗin ya amsa ka bar hameed su cigaba da kula tare, duk da noraiz abun da ya karanta kenan, zai ƙara samun wasu daba ru wurin hameed"
"eh daman shawarar da na yanke kenan"
"to Allah ya tai maka"da ameen suka amsa
sun jima sosai gidan malam dan sai wajen Karfe 10 na dare sannan suka tafi gida , mlm ya sha maganin sa , kuma yana sa shi bacci .
Suna shiga gida parlorn Ammy suka nufa inda anan suka sameta ita da Fatima zaune sallama suka yi , amsa masu Ammy tayi tana cewa "nayi tuna nin baba ya rike ku chan ku sai kwana, ashe zaku dawo"
"Wlh kuwa zamu dawo, ya gida"
"gida alhmdllh gashi nan"
fira suka ɗan taba Ammy nace masu ga dinner din su chan kan dinning suka ce sun koshi dan sun ci dinner gidan malam
basu jima ba kowa ya nufi dakin sa saboda dare da yaja sosai.....


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wataran dadi wataran akasin haka su Aairah sun fara zana jara bawar gama secondary school har sun kammala, haka zalika fatima ma ta gama Noraiz watan shi 2 da sati 3 da dawowa kenan.


Zaune ammy take bakin bed, wayar tace da ke kan bedside ta fara ringing ɗaukra wayar tayi tana kallon mai kiran, ya ahmad shine mai kiran, dafe kan ta tayi tana faɗin ya salam, Allah ya sa bawani abun bane, picking tayi haɗi da kara wayar a kunne tana sallama, amsa mata sallamar na ciki wayar yayi, gaisawa suka yi, tana tambayar yasu hajiya asiya ds su kairiyya, da lafiya lau ya amsa mata sannan yace"wai aisha mi kuke nufi ke da shazim ne, tun yaushe nake faɗin idan na kira shi bana samun shi"
"kayi haƙuri yaya, tun ranar da kakira na faɗa mashi ya kira ka, na yi tuna nin ya kira"
"yaushe zai kira, kar mi mashi maganar da ya tsana, ko ba mu kai matsayin da za muyi mashi ita ba"
"ba haka bane yaya, dan Allah kayi haƙuri, zanyi mashi magana ya kira ka yau"
"to, daman na kira ne dan in faɗa maki ina son ganin shi shi da ƴan uwan shi cikin wannan watan"
"to yaya, zan faɗa mashi"
"to shikenan, sai anjima"
"to Allah ya kaimu"da ameen ya amsa haɗi da yin rejectin, a jiye wayar ammy tayi tana faɗin" na rasa gane halin shazim, idan har bai jaman abun magana ba wurin su hankali shi baya kwanciya, amma na san maganin shi ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi part ɗin shi, yana parlor zaune, tambayar shi tayi ina wayar shi, "gata nan ammy, lafiya"
"kira ya ahmad yanzu nnan "
"amma ammy mi yasa"
"zaka kira shi kukuwa sai ka gama tambaya ta dalili"
"A'a kawai yace haɗi da ɗaukar wayar yayi dialing number uncle ahmad, tana fara ringing, aka ɗauka, sallama yayi haɗi da cewa "ina wuni uncle "da lafiya lai uncle ahmad ya amsa, sannan ya ɗaura da cewa "shazim laifin mi muka maka da idan mun kiraka baka ɗauka, kuma kai bazaka iya kiran mu ba? "
"bakomi uncle "
"to shikenan, ina son ganin ka abuja kai da ƙannan ka cikin watannan"shiru yayi baice komi ba, uncle ahmad ne yace "baka ji mi nace ba ne "
"A'a naji, amma uncle aiki na ya zanyi da shi"
"Ina sauraron zuwan ku kana ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login