Showing 123001 words to 126000 words out of 133697 words

Chapter 42 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8525

kuma bai dawo ba,zuwa tayi har gaban sa tana faɗin " ina so ka fahimce ni Please, duk abun da ka ga ina faɗa maka ina faɗa maka tsakani na da Allah ne"


"naji hidaya, ai na ce maki kije gaki ga shazim ba shikenan ba"


" am dr......... "
"please ya isa haka bana son jin komai daga bakin ki"


" saboda mi"
"saboda duk abun da zai fito daga bakin ki ba alkairi ba ne a wurina, dan haka ni kawai ki fita ki barni da abun da ya ishe ni pls" ya ƙarasa maganar haɗi da haɗe hannuwan shi wuri ɗaya,kan sofa ya koma ya zauna

" shikenan zan fita na baka wuri" tana faɗa ta buɗe ƙofar office ɗin ta fice, wurin su maryam ta nufa , tun kafin ta ƙara so maryam ke jefan ta da harara
"lafiya wai ki ke hararata?" hidaya ta faɗa yayin da take samun wurin zama ku sa da maryam ɗin


"kinfi kowa sani"


"ni babu wani abu da na sani "
"yayi kyau " maryam ta faɗa, fira su ke ɗan taɓawa jefi jefi, suna nan zaune har aka fara kiran sallar zuhur, dr kabir ne ya fito daga office ɗin shi ya shiga na shazim, yana shiga ya same shi yana tattara files ɗin da ke kan table ɗin alamar ya tashi sai kuma wani lokacin.
Sallam kabir yayi mashi haɗi da shi gowa ciki, kallon shi shazim yayi yana amsa mashi sallamar
"Autan momy lafiya dai?" shazim ya faɗa dan ganin kabir da yayi duk sai a hankali ga idanuwan shi a kumbure kamar na wanda ya sha kuka
"lafiya lau, mi ka gani?"
"bakomai" shazim ya bashi amsa
"mu tafi ko " shazim ɗin ya sake faɗi saboda ya gama haɗa duk wani kayan shi, gaba kabir yayi shi kuma ya bi bayan shi su ka nufi masallaci, da aka gama sallah shazim sallama yayi ma kabir saboda shi zai wuce Abnoor kabir ma cewa yayi shima da anyi sallar asr gida zai tafi hakan ce ta faru ana gama sallah bai daɗe ba shima ya kama hanyar tafiya gida.


_*FEENAH*_


......... zaune take bakin gado a ɗakin su ita da kairiyya, wayarta da ke kan bedside drawer ta ɗauka number innah ta shiga dialing bugu biyu innah ta ɗauka tana faɗin
"sai yau kikayi lokacina?"
"kai innah daga kiran ki zaki fara da complen"
"oho ni kike cema haka ko"
"innah ai kece daga kira sai ƙorafi"
"to naji , miyasa kika kira ni dan na san ba dan Allah kika kira ni ba"
"haba dan Allah innah"


"ba wani haba, ƙarya na faɗa tun da nake da ke kin taɓa kirana haka nan kawai da sunan ki gaishe ni tun da kika kama ƙafa kika koma lagos da zama "


"naji ni dai innah, kima tsaya ki saurari mi ke damuna amma sai wani faɗa kike man"


"to naji, yanzu faɗa man mike damunki da yasa kika kirani "


"dama ba komai bane, yaushe su Abbah su ka tsaida ranar Auran mu da ya shazim, dan ni nagaji da wulaƙancin da yake man ga wannan munafukar kairiyya a gefe "


"wannan ko ƴar banyar yarinya a nan ɗin ma sa maki ido take ke nan "


"Ai wallahi innah sai ma abun da ya cigaba jiya har da wani tsare ni zata yi man wa'azi saboda naje part ɗin ya shazim ya mare ni "


"mi?, mari fa kika ce?"


"eh kawai dan na taɓa shi, fuskata fa duk ya kumbura man ita hannuna har da targaɗe kuma da Ammy tace ya duba ni ƙinyi yayi, shiyyasa na kira ki kisa su Abbah su tsai da ranar Auran mu nasan dai ya Aure ni ƙarya yake yace zai dake ni "


"amma kin bani haushi feenah, bana hanaki taɓa sa ba ke mi yasa baki jin magana ne, yanzu da ya illata ki da ya kenan, shi bai da asara saboda daman ba sonki yake ba"


"ai bazan ma ƙara ba, dan wallahi ba ƙaramar azaba na sha ba jiya da ana gyara man hannuna "


"to dadai ya fiye maki, dan shi ba ruwan shi dan ya yi maki illa"


"to innha yanzu yaushe zaki sa a sa ranar bikin mu "


"kar ki damu ki barni da su ni na san mi zanyi "


"yawwa innha ta shiyyasa nake sonki "
"kar ki ji komai, kawai ki bi abun da na ce maki "


"to insha Allah "


"sai anjima, na manta in faɗa maki mansoor na nan zai zo nace ya barki ya dawo da su sa'ada amma na san halin shi duk yanda zai yi karki saki ki biyo shi kinji na faɗa maki "


"insha Allah innha bazan biyo shi ba"
"yawwa, sai anjima "


innah ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran


faɗawa tayi saman gado tana faɗin


"yawwa innha shiyyasa nafi kowa sonki don baki bari na zubar da hawaye "


_*a dai juri zuwa rafi feenah wata ran tulu zai fashe*_


_*✨KATSINA✨*_


...... Abdallah ne ya shigo wrin su mom dake kitchen ita da ummah da baaba larai ya nufa, da sallama a bakin sa ya shiga kitchen ɗin, amsa mashi mom tayi tana faɗin


"wai da kai baka bi su abie ɗinka ba?"
"eh naje na dawo ɗaukar takardun su Aairah ne , makarantar ta fara ba da addimisson yanzu wani abokin uncle Ahmad ya kira shi yake sanar da shi Ameerah ta samu , shine uncle Ahmad yace na zo na ɗauki na su Aairah na tura ma Abokin na shi wanda ya duba ma Ameerah sai suma ya duba masu suma"


"masha Allah kace ƴan biyu na sun kusa tafiya school ƙwanda ta kwanta, kullum na huta da mom wai yaushe ya Abdallah yace za'a fara ba da addimisson kullum maganar su ke nan "
Ummah tace " ai gara su da Ameera, yanzu hankalina ya kwanta tunda Allah ya sa ansamu addimisson yanzu hankalina zai kwanta "


"ai yaran nan idan ka bari suka ta so ka gaba kaga ta kanka " mom ta faɗa
Ummah tace " Allah dai ya shirye su " da Ameen su ka amsa Abdallah ya ce
"ni zan wuce"
Mom tace
"yaushe Abie ɗin naku yace za su iso"
"sai ɗan anjima ka ɗan yanzu ma ni su ke jira "
"Ok sai kun dawo, su kuma Allah ya kawo su lafiya"
"Ameen, sai na dawo" ya faɗa haɗi da ficewa ya bar kitchen ɗin.


Su Aairah ne su ka shigo da gudu daga garden Ameera na riƙe da wayar Aairah Aairah na biye da ita tana faɗin
" wallahi Ameera ki bani waya ta kafin ranki ya ɓaci "
"wallahi ban badawa kin bi duk kin ishi mutane, ban badawa idan kina da ƙarfi ki zo ki karɓa " Ameera ta faɗa tana ma Aairah gwalo, sai zagaye parlor su ke Aaimah na tsaye tana masu dariya tana faɗin
"wallahi karki bata "
"Aaimah ban san wulaƙanci dan mi zaki ce karta bani "
"ai wallahi ko bata ce haka ba bazan baki ba dama kin daina bi na " Ameerah ta faɗa sai haki take, awannan yana yin ne Abdallah ya fito daga part ɗin shi ya gansu, tswa ya daka masu yana faɗin


"wai ku wane kalar yara ne kun girma amma kwata kwata baku san ciwan kanku ba, wallahi ko ku natsu ko ranku yayi mumunnan ɓaci sakarkaru kawai "
"yaya wayata fa ta amsa Aaimah na ce mata wai karta bani "Aairah ta faɗa tana turo baki
"na dai faɗa maku " Abdallah ya faɗa haɗi da ficewa ya bar parlorn , suna ganin ya fita kamar yace su cigaba sai kace ƙananan yara haka su kai ta zagaye parlor duk sun cika gidan da hayaniya.


_*✨Airport✨*_


Mutane ne ta ko ina suna kai kawo, kowa da baun da yake, masu jira jirji da masu jiran ƴan uwan su, motar su Abie ce ta shigo cikin Airport ɗin Abdallah ke driving motar da su Abie suke ciki yayin da uncle mustafa ke driving motar shi, parking lot su ka nufa haɗi da yin parking su ka shiga fitowa, Abie da uncle Ahmad ne su ka fara fitowa sai uncle mustafa sai ya Abdallah, cikin Airport ɗin su ka nufa abie da su uncle Ahmad suna ɗan fira sama sama, wani ƙyatattce wuri su ka nufa zama su kayi kan chair's ɗin da ke wurin , su abie kaɗai ne su ka zauna ya Abdallah kuma can gefan su ya samu wuri ya zauna wayar shi ya ciro yayi dialing number fatima,bakin ta ɗauke da sallama tayi picking call ɗin tana faɗin
" ni nayi fushi, sai yanzu daga bari na dawo "
" da ya dr ki kayi fushi?" ya faɗa cikin sigar tamabaya
"ai duk laifin shi ne, ya bar ƙanwar shi tana ta jiran shi" a shagwaɓea tayi maganar
"kin san dai idan ba wani abu ya tsare ya dr ba bazai bar ƙanwar shi tana jiran shi ba "
"shikenan tun da haka kace "
"haka ne fah ba wai nace ba "
"kana ina yanzu?" fatima ta tambaya
"ina airport"
"ya dr ba dai wani wuri zaka je ba?"
"zanyi tafiya ne, kina so na zo maki da wani abu ne"
nan take yana yin muryarta ya canza, rai a ɓace tace
"bana so, sai ka dawo" ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, murmushi ne ya suɓuce mashi yana faɗin
" fatima manya " tashi yayi daga inda yake zaune ganin su Abie sun ta shi, bin bayan su yayi.


Wani kyakyawan matashin saurayi ne ke saukowa daga mata ƙalar benen jirgin da ya sauka, fari tas da shi hannun shi ɗauke da madai daicin trolly sanye yake da baƙin cargo trouser sai t_shirt wacce ita ma ta kasan ce baƙa da p_cap red color da ɓakin glass, ba ƙaramin fito da kyawun shi da na fatarshi kayan su kayi ba,saukowa yake cikin natsuwa yayin da wani dattijon mutum ke bayan sa jikin sa sanye da kayan mu na hausawa riga da wando na yadi mai taushi,shima fari tas kyakyawan gaske zai su yi sa'annin juna shi da Abie duk da yawan shekarun shi haka bai hana kyauwun shi fitowa ba, tafiya su ke shi da matashin har su ka iso inda mutane ke tsai tsaye,


Abie ne ya ƙara so da sauri wurin su fuskar shi ɗauke da tsantsar farin ciki,su uncle mustafa na bayan shi, yaan ƙarasowa yayi hugging ɗin wannan dattijon yana faɗin " masha Allah, barkan ka da zuwa ƙasar ka, barka da dawowa " murmushi shima dattijon yayi yana faɗin "nagode" raba jikinsu su kayi su uncle Ahmad ma matsowa su kayi kusa da shi hannu su ka miƙa mashi su kayi musabaha, suna mashi barka da zuwa, ya Abdallah matsawa yayi wurin wannan matashin yana faɗin


" safwan manyan ƙasa yau dai gaka a nigeria, ina tsoron naka ya tafi "


murmushi safwan yayi haɗi da cire glass ɗin dake idon shi yace
"Abdallah ka raina ni, wani ya ce maka ina tsoro ne "
"sosai ma kuwa tsoro kake, in ba tsoro ba mi yahana ka zuwa tun tuni sai yanzu"
"saboda kai ma baka zuwa "


"ba wani nan tsoro ne ya hanaka zuwa "
"haka ka ce "
"eh haka na ce "
"zamu gani ai ni da kai wake tsoron" safwan ɗin ya faɗa haɗi da matsawa wurin Abie ya shiga gaishe da su.


Ɗunguma su kayi zuwa parking lot in da su kayi parking ɗin motocin su, safwan shi da Abdallah su ka shiga motar shi yayin da Abie da uncle Ahmad su ka shiga motar uncle mustafa, barin airport ɗin su kayi ba su nufi ko ina ba sai gidan Dadi.


Horn su kayi a bakin gate ɗin gidan dadi, mai gadi ne ya buɗe masu ciki su ka shiga,parking lot su ka nufa haɗin da yin parking, fitowa su ka shiga yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun gama fitowa ciki su ka nufa, abie gaba ɗaya a cikin farin ciki yake da zuwan wannan bawan Allah, da sallama a bakunan su suka shiga ciki, parlorn tsit yake kamar ba kowa, Aunty Rabi ce zaune kan sofa tana karatun al'qur'ani mai girma,sai da ta kai aya sannan ta tsaya haɗi da amsa masu sallamar da su kayi, ciki su ka ƙara sa haɗi da samun wurin zama kan sofa's su ka zauna, gaishe da wannan dattijon ta yi tare da yi mashi barka da zuwa ,cikin kulawa ya amsa mata, da fara'a a fuskar safwan ya gaishe da ita, amsa mashi tayi tana faɗin " safwan yau dai gaka ga nigeria, ya gajiyar hanya "
"lafiya lau Alhmdllhl" safwan ya faɗa
"masha Allah , ya ka baro momyn ka "
"tana lafiya ta ma ce a gaishe da ku "
"muna amsawa "
abie ne yace " ina mama, ko tana ɗaki?"
" eh yanzu ta shiga bari naje nayi mata magana" ta faɗa haɗi da tashi ta nufi ɗakin dadi,wannan dattijon ne ya kalli abie yace
" sai dai ban gane nan ina ne ba?"
"nan gidan mama mahaifiyar mu"
"oho Allah sarki " mutumin ya faɗa
Aunty Rabi ce ta fito ita da dadi,ƙara sowa wurin su su kayi wuri dadi ta samu kan sofa ta zauna tana kallon wannan mutumin, ta sowa yayi ya dawo kusa da ita yana faɗin " mama ina wuni " wani iri dadi taji jin ya kirata da mama, duk sai ya bata tausayi, shikenan waɗannan mutanen sun cuce shi yanzu baya iya tuna komai da ya shafi rayuwar shi ya manta ko shi wanene ya manta iyalan shi da ƴan uwan shi.
Kallon Abie yayi yace "naji tayi shiru ko ba ita bace mamar ba?"
"ita ce bata ji ka bane" abie ya faɗa
"lafiya lau nake, ya hanya" dadi ta faɗa fuskar ta da ɗan murmushi wanda da ka ganshi kasan na dole ne
"Alhmdllh " mutumin ya faɗa, fira suka shiga taɓawa shi da dadi kamar ɗan da ta haifa da cikinta, tun bata saki jiki da shi ba har ta saki jiki su ka sha fira duk da firar ba wata bace tambayoyi ma da yake mata duk sunfi yawa.


Aunty Rabi ce ta kawo masu ruwa da lomu, sun jima a gidan sannan abie yace su tafi can gida amma sai wannan bawan Allah yace bazai je ba shi yana nan tare da mama, abie ne yace mashi ai idan sun je zasu dawo dadi ma tace zuwa za kuyi ku dawo to sannan fa ya bisu suka tafi.


Lokacin da suka isa gida su Aairah na nan zaune a main parlor suna kallo, jin sallamar abie ne ya sa su tashi da sauri suka nufe su, suna faɗin
"oyoyo ga abie"
haɗi da gaishe da su uncle Ahmad, ciki su Abie su ka shigo abie na faɗin


"ina su mom ɗin ku sai ku ka ɗai a parlor "
"yanzu su ka shiga ciki" Aaimah ta faɗa
Abie yace " ba kuga uncle sadiq ba " ya faɗa yana nuna wannan mutumin, da sauri su ka nufe shi suna faɗin
" uncle sannu da zuwa, ya gajiyar hanya "
"Alhmdllh, ya kuke "
"lafiya lau mu ke"
"masha Allah " ya faɗa
Wuri su ka samu kan sofa su ka zauna yana tambayar su Aairah ya sunan su, ɗaya bayan ɗaya suka shiga faɗa mashi sunayen su yan jinjina kai.


Ameera ce ta tashi ta tafi kiran su mom , ba ta daɗe da tafiya ba sai gata tare da su mom , ƙara sowa su kayi ciki, nan suka shiga gaishe gaishe, abie na nuna ma uncle su da sunayen su, sun jima anata fira har sai da aka fara kiraye kiyaren sallar magrib sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, su mom ma da su Aairah ɗakunan su auka nufa domin gabatar da tasu sallar, bayan sun kammala ne mom tace su je su jera dinner kan dinning,tafiya su kayi su ka jera komai da ya kamata sannan suka koma kan sofa suna cigaba da kallon da suke yi ɗazu, su abie ba su dawo gidan ba sai bayan da su kayi sallar isha tukun su ka dawo, suna shigowa dining su ka nufa,su Aairah mom tace suje suyi serving ɗin su, su kuma su kawo masu na su abicin nan kan carpet saboda dining ɗin da yayi masu ka ɗan.


bayan sun kammal serving ɗin su kamar yan da mom tace kan carpet su ka kawo masu na su abicin su ka ci.


Bayan sun kammala dinner a nan mai parlor su ka zauna suna ɗan taɓa fira amma banda su Aairah da suka gama dinner bedroom ɗin su suka nufa, Abdallah ma da safwan part ɗin Abdallahn su ka nufa su ka bar su Abie ka ɗai a parlor suna fira.


Sai wurin ten uncle mustafa ya tafi gida uncle Ahmad kuma ya tafi part ɗin da su ka sauka shi da ummah, abie kuma shi da uncle sadiq su ka tafi part ɗin shi.


_har ya manta da yace a mai da shi gidan dadi to kwakwalawa ce ta koma ta ƙananun yara_


bayan sun shiga part ɗin abi, wani bedroom abie ya kaisa wanda ke kusa da nashi, da suka shiga ciki pajamas abie ya ɗauko mashi sannan ya nuna mashi wani corridor da wardrobe ce ciki yace ya shiga ya canza kayan jikin shi , bayan ya canza abie yace ya shiga toilet yayo alwala, da to ya amsa mashi haɗi da nufar toilet ɗin ɗakin bayan 1 minute ya fito jikin shi da danshin ruwa.


Nuna mashi bed abie yayi yace ya zo ya kwanta, matsowa yayi ya hau gadon zaman abie yayi shima kusa da shi sannan yace" zan riƙa karanto maka adu'ar kwanciya bacci sai ka maimaita " to ya faɗa
nan abie ya shiga karanto mashi shi kuma yana maimaitawa har abie ya gama karanta mashi, sannan yace ya kwanta, kwanciya yayi abie yaja mashi blanket sannan yayi mashi sai da safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login