Showing 93001 words to 96000 words out of 133697 words

Chapter 32 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8510

su da abokiyar zaman ta, sosai ruma ke son yaran kusan kullum suna tare da ita dan halimatu ma awurin ruma ta taso, haka rayuwa ta cigaba da tafiya,iyah ta tasa nuraddeen gaba akan dole sai ya saki ruma dan bataga amfanin ta ba tunda bata haihuwa, hankalin nuraddeen da ruma sosai ya tashi, amma bai saki rumar ba, ganin ba shi da niyyar sakin ruma ya sa ta sa aka kira mata shi har gida, tayi mashi faɗa sosai akan ya ƙi bin abun da ta ce har ikirari tayi mashi akan ko dai ya saki ruma ko kuma ta tsine mashi , ba shida wani zaɓi a lokacin bayan ya ai watar da abun da mahaifiyar shi ta ce, haka ya samu ruma yace taje gida sai ya nemeta, hankalin ruma ya kai ƙuloluwar tashi da jin abun da nuraddeen ya faɗa, haƙuri ta shiga bashi ita da maijidda, nuna masu yayi bashi da wani zaɓi ne, kuma ai ba sakin ruma yayi ba, cewa kawai yayi ta tafi gida insha Allah zata dawo idan komai ya daidai ta tsakanin shi da iya, dole ruma ba dan ta so ba ta haɗa kayanta ta tafi gidan iyayen ta, sun sha kuka ita da maijidda san da zata tafi, haka ta tafi gida rai babu daɗi, koda ta tafi gida nan ta samu yayarta bilkisu da ke aure cikin garin katsina ta zo, ran mahaifiyar ruma da na ƴar uwarta ba ƙaramin ɓace yayi ba akan abun da nuraddeen yayi, ko da bilkisu ta tashi tafiya tasa ruma tayi a gaba akan ta haɗa kayan ta su tafi katsina da farko ruma ƙin amincewa tayi akan zata tsaya har sai komai ya dai daita tsakanin ta da nuraddeen, hakan yasa mahaifiyarta ta yi mata faɗa sosai ba dan ta so ba ta bi bilkisu zuwa katsina, bayan tafiyar ruma katsina nuraddeen ya zo gida wurin mahaifiyar ta ya bata haƙuri akan abun da ya faru ya kuma nuna mata bashi da yanda zai yi ne umarni ne daga mahaifiyar shi, mahaifiyar ruma ta fahimci shi ta kuma yi mashi uziri, sannan ta ce yayi ma mahaifiyar shi biyayya ka wai ya saki ruma,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba jin tace wai ya saki ruma, ƙin amincewa yayi, sai ma haƙuri da ya ba mahaifiyar ruma.


Sosai rayuwar ruma ta chanza a gidan ƴar uwar ta, soyayya da kulawa ta ke samu daga wurin ƴar uwar ta da mijin ƴar uwar ta, hakan ya sa ta saki jikinta sosai a gidan ga kuma yaran ƴar uwarta da take kallo kamar ƴaƴen da ta haifa da cikin ta, ko wane lokaci tana tare da su, suma da sun dawo makaranta zaka same su manne da ita, watan ta ɗaya a gidan ta ƙara fresh tayi kyau hasken fatar ta ya ƙara fitowa har yar ƙiba tayi,zazzabin dare ne ya taso ta gaba,sai ta wuni lafiya amma da dare yayi sai zazzaɓi ya rufe ta, ko da bilkisu ta fahimci haka sai ta ce mata ta shirya su tafi asibiti amma ruma ta ƙi, wata rana suna zaune kan dinning zasu ci abinci daga buɗe warmer ƙamshin abincin ya daki hancinta tashi tayi da gudu ta nufi toilet, amai tashiga ƙwarawa kamar zata amayar da ƴan hanjin cikin ta , biyo bayan ta bilkisu tayi tana mata sannu da faɗin "nace muje asibiti amm kin ƙi saboda taurin kai, yanzu ai dole ki shirya mu tafi"
da ƙyar ruma ta buɗe baki tace " ba sai munje ba yanzu da nayi aman na samu sauƙi " ƙin sauraran ta bilkisu tayi sai ma ficewa da tayi ta nufi ɗakin ta tana faɗin " ki shirya kawai mu tafi bana son taurin kai"
tasa ta gaba bilkisu tayi ta shirya suka je asibiti, koda suka je aka yima ruma aune aune anan likita ya shaida mata cewa ruma na ɗauke da ciki tsawan wata uku da sati biyu, zo kaga murna wurin ruma da bilkisu, Allah sarki abun da suka da ɗe suna nema har ake mata gori ake kiranta da juya yau gashi Allah ya ba ta , koda labari ya isa kurfi sunyi murna da jin wannan labari, har gida mahaifiyar ruma ta sa aka kira mata nuraddeen ta sanar da shi, bawan Allah harda kukan shi saboda tsabar farin ciki, yana koma wa gida ya sanar da maijidda, ita ma tayi farin ciki kamar mi, koda iyah ta ji labari ita ma harda kukan ta musamman da ta tuna cin kashin da suka yi ma ruma ita da ƴaƴan ta har suke kiran ta da juya, har gida ta je ta bama mahaifiyar ruma haƙuri akan ruma ta dawo ta haihu ɗaki mijin ta, da farko ƙin amincewa mahaifiyar ruma tayi sai da iya tai ta bata haƙuri tukun ta haƙura kuma tayi mata alƙawari akan rumar zata dawo, iyah taji daɗi kuma tayi ma mahaifiyar ruma godiya, hakan ce ta faru, bilkisu da kanta ta shirya ruma ta dawo da ita gidan mijinta, soyayya da kulawa iyah ta shiga bama ruma tana tattalin ta kusan kullum tana gidan nuraddeen kamar wannane jika na fari da za'a haifar mata, haka shima nuraddeen kamar ba'a taɓa yi mashi haihuwa ba , wani ikwan Allah maijidda sai ta fara jin haushin kulawar da iyah da nuraddeen ke yima ruma, tana ganin kamar sun fi son ruma akanta , ƙi ƙiri ta fara nuna hassadar ta a fili, iyah kuwa da nuraddeen basu ma san tana yi ba, da cikin ruma ya kai watannin haihuwa kamar yanda iyah tayi ma maijidda haka tayi ma ruma ta mai da ta gidan ta da zama, yan da iyah ke son ruma ta ke bata kulawa kamar ta ɗauke mata nauyin cikin haka ta ke ji, saboda cikin ba ƙaramin wahalar da ruma ya ke ba, kullum nuraddeen ya nan manne da ita sai dare yake koma wa gida, sosai ran maijidda ya ƙara ɓaci saboda dawowar da nuraddeen ya ke yi da daddare da kuma wunin daya ke yi wurin ruma, gani take kamar saboda cikin ruma ya banzatar da ita da yaran ta,sosai tsanar ruma ta ƙaru a zuciyar ta duk ta manta rawar ƙafar da nuraddeen yayi lokacin da tana da cikin magaji, cikin ruma sai da ya kai wata goma da satittika bata haihu ba, hankalin nuraddeen ya tashi sosai ganin har tsawan wannan lokacin bata haihu ba, kwantar mashi da hankali iyah ta shiga yi akan ya kwantar ta hankalin shi ana samun irin haka, amma fir ya ƙi amincewa har sai da ya ɗauki ruma zuwa asibiti, ko da likita ya duba ruma anan ya gano cewa bazata iya haihuwa da kanta ba sai anyi mata cs, lokacin da bilkisu ta zo asibitin duk wani abu da ya kamata a yi na cs ɗin nuraddeen yayi har an shiga da ita theater room, bakin theater room ɗin suka tsaya shi da bilkisu suna jiran tsammani, har kusan awa huɗu ta shuɗe amma likitocin ba su fito ba lokacin ana ta kiran sallar asr, masallaci nuraddeen ya tafi ya bar bilkisu, har ya je ya dawo ba'a fito da ruma ba likitocin ma ba wanda ya fito, hankalin nuraddeen ya kai ƙololuwar tashi, sai da wasu awannin suka shuɗe sannan wata nurse ta fito daga ɗakin hannun ta riƙe da jariri cikin towel, da sauri nuraddeen da bilkisu suka nufo nurse ɗin suna tambayar ta jikin ruma,miƙa ma bilkisu jaririn tayi tana faɗin "ana gyarata ne,idan an maida ta ɗakin hutu sai ku ganta" da to su ka amsa mata , amsar jaririn bilkisu tayi tana kallon shi kyakyawan gaske a cikin kamannin ruma babu abun da ya baro kamar tayi kaki, idonun shi rufe da a lama bacci ya ke, barin wurin su nurse ɗin tayi, hankalin nuraddeen duk a tashe so kawai ya ke yayi ido biyu da ruma, sake buɗe ƙofar theater room ɗin aka yi dr ne ya fito yana cire safar hannun shi, da sauri nuraddeen ya ƙarasa wurin shi yana tambayar shi wane hali matar shi ke ciki, " Allah ya bamu ikwan cetan jaririn amma mahaifiyar shi ta sha wahala sosai, yanzu dai munyi mata allurar bacci tana ɗakin hutu,ko da za ku ganta sai zuwa anjima"
"to shikenan dr, nagode "ya faɗa haɗi da miƙa ma mashi hannu su kayi musaba ha, dr yace "babu komi, Allah ya bata lafiya"da ameen nuraddeen ya amsa, wuce wa dr yayi zuwa office ɗin shi,nuraddeen ko ma wa yayi idan da bilkisu take ya amshi jaririn yana kallon shi, ji yake kamar ya mai da shi ciki tsabar yanda ya ke son shi, ruma bata farka ba sai wajen ƙarfe 9, nurse ce tazo ta sanar da su farkawar ruma, ta shi su kayi suka bi bayan nurse ɗin nuraddeen har yan tuntuɓe saboda sauri.


Kwance take kan gadon marasa lafiya, jin an buɗe ƙofa ne yasa ta buɗe idanuwan ta dake rufe, binsu take da idanu ko ɗan ya tsanta bata iya ɗagawa, ba ƙaramin jin jiki take ba, zama nuraddeen yayi kan kujerar dake kusa da gadon, bilkisu kuma ta zauna kan gado, sannu su ka shiga yi mata,bata amsa masu ba sai ma hawayen da ke bin kumatun ta, hannu nuraddeen yasa yana share mata hawayen"ki daina kuka ruma Allah zai baki lafiya" jinjina kai tayi, hankalin nuraddeen duk ya ta shi ganin ko magana bata iyayi, yun ƙurin tashi take zaune,pillow yasa ya tai maka mata yayi ta ɗan jingina da bango sannu kawai su ke mata, kiran sunan nuraddeen tayi , da sauri yace na'am, hannunta ta miƙa ganin tana son kama hannun shi ne yasa shi sauri kama nata hannun yana ƙara mata sannu, da ƙyar ta buɗe bakinta tana tamabayar ina abun da ta haifa, da sauri bilkisu ta miƙa mata jaririn da ke hannunta, amsa tayi ta zuba jaririn ido tana kallon shi hawaye na bin idanun ta, gaba ɗaya duk tabi ta karya masu zuciya da kukan da take, ta ɗauki tsawan lokaci tana kallon jaririn daga bisa ni ta miƙa ma nuraddeen shi,amsa yayi yana kallon ta, murmushi ta sakar mashi, da ƙyar magana take fita daga bakinta tace "ina so kasa mashi sunan mahaifina dan Allah, sannan kayi man alƙawarin baza ka taɓa bari yayi maraici ba, ji nake kamar bazan tashi ba "
"dan Allah ki dai na cewa haka cuta ai ba mutuwa bace insha Allah zaki samu lafiya "
Bilkisu hawaye ne kawai ke zuba daga idanunta duk ta karaya
"ina so dai ka ɗaukar man alƙawari "
"Insha Allah zanyi maki yan da kike so fatana Allah ya baki lafiya " nuraddeen ya faɗa,"na gode, ina so kowannan ku ya yafe man duk wani abun da nayi mashi, duk wani wanda kuka san na taɓa mu'amula da shi ina son ku roƙar man shi yaya feman "
sai haƙuri su ke bata ciwo ba mutuwaba ne, sai dai tayi murmushi idan su ka faɗa mata haka, nurse ce ta shigo ta sanar da nuraddeen likita na son ganin shi, tashi yayi ya bi bayan ta har office ɗin dr , wurin zama dr ya nuna mashi, zama yayi yana zuba dr ido yana sauraron mi zaice, magana dr ya fara " da man ba wani abu bane yasa na kira ka, game da jaririn ya kamata a nemo mashi madara saboda lafiyar shi zuwa wani ɗan lokaci sai mahaifiyar ta shi ta cigaba da shayar da shi,sannan ita ma akwai wasu magunguna da ya kamata ita mahaifiyar tashi ta riƙa sha " dr nagama faɗa ya rubuta mashi sunan magungunan da madarar da ya kamata a riƙa ba yaron kafin mahaifiyar shi ta cigaba da shayar da shi, yana gama rubutawa ya miƙa mashi, amsa yayi haɗi da yima dr godiya ya fice zuwa ɗakin da ruma take kwance,yana buɗe ƙofa ya samu bilkisu ta kifa kai da bango sai shashekar kuka take ruma kuma jikinta rufe yake da farin ƙyalle,wani irin faɗuwa da gaban shi yayi jikake dam dam, dafe saitin zuciyar shi yayi yana nufar gadon da take kwance hannun shi na rawa ya yaye farin ƙyale da aka rufe ta da shi, fuskarta ta bayyana idanuwan ta a rufe suke fuskarta da alamun murmushi, suma tsaye nuraddeen yayi lokacin guda ya tsinci kanshi ciki wani yanayi mara daɗi, hawaye ne suka shiga sakkowa daga idanun shi,zubewa yayi ƙasa kan gwiwowin shi yana faɗin "yanzu shikenan na rasa ruma har abada,kai hakan bazai yiwuba " sai sambatu yake kamar wanda ya zare, jin maganganun da yake ne ya ƙara karya zuciyar bilkisu ta ƙara sautin kukan da take.


_*ALLAH SARKI RUMA UBANGIJI ALLAH YA JIƘANKI DA RAHAMA ABUN DA KIKA BARI ALLAH YA RAYA SHI*_


A wannan yana yin faɗa maku tashi hankalin da nuraddeen, bilkisu, iyah, mahaifiyar ruma suka shiga ɓata lokaci ne suna shiga tashin hankali mara misltowa.
bilkisu ta ciga da kula da jaririn har aka yi adu'ar uku, sannan nuraddeen yayi ma yaron huɗu ba da suna Abubakar sadiq,ya ciki alƙawarin da ya ɗaukar ma ruma, har akayi arba'in da rasuwar ruma sadiq na hannun bilkisu, da ta tashi komawa katsina da sadiq ta tafi har aka yaye shi, san da aka yaye shi mijin bilkisu ya nemi da abashi sadiq,amma sai nuraddeen yace a'a shima yana son yaron shi ya taso a gaban shi,bilkisu ta so ace nuraddeen zai bar mata sadiq a hannun ta amma bata da yan da zata yi haka ta dawo da sadiq hannun mahaifin shi,lokacin da mijinta aka tura shi ƙasar china jakadancin nigeria, har kurfi ta zo ta sake roƙon nuraddeen daya bata sadiq ɗin ta tafi da shi, amma yace a'a idan dai sun zo nigeria zai riƙa zuwa masu hutu, taji haushin ƙin bata sadiq da nuraddeen yayi amma bata da yan da zata yi tun da ɗan shi ne dan dole ta haƙura ta tafi da kewar yaron.


Kulawa sosai sadiq ke sa mu wurin mahaifin shi da kakar shi iyah, ganin yan da iyah da nuraddeen ke kula da sadiq ya sa maijidda ɗaura mashi karan tsana duk da yake ƙaramin yaro, ƴan uwan shi na son shi amma ta hana su ma'amula da shi, ko wasa suke ya zo wurin su sai ta sa su kore shi ko su da ke shi, tun basu ɗaukan abun da take sa su har hakan yayi ta siri da sadiq ya shiga cikin su zasu yi ta kyarar shi da hantarar shi, haka zai raɓe yana kuka ta kuma ja mashi kunne akan muddin ya faɗa ma nuraddeen sai tayi mashi bugun tsiya, bawan Allah haka zai shiru bai taɓa faɗa ma mahaifin shi ba, wani munafuncin na maijidda idan a gaban nuraddeen sai ta nuna tana tausayi sadiq tayi ta ririta shi amma idan nuraddeen baya gida wahala iriri babu wacce bata sa sadiq har aiki wan da ya fi ƙarfin shi sa shi take yi lokacin yana da shekara shidda amma sai ta sashi abun da ya fi ƙarfin shi,lokacin ta ƙara haihuwa yaron na da shekara ɗaya a duniya, sunan yaron Ibrahim kyankyawa ne dan yafi su magaji kyau shiyyasa ita ma tafi son shi a cikin su, haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq ya taso cikin ƙiyayyar yan uwan shi, kwata kwata baya jin daɗin zama da su, sauƙin shi ɗaya idan mahaifin shi na gida ko kuma yaje gidan iyah ko su magaji na makaranta daya ke ba makarantar su ɗaya ba ta nan kawai ya ke samun sauƙin wahalar da yake sha ta su magaji dan har tafi wacce yake sha wurin maijidda, wurin iyah ya koma da zama dalilin wani bugu da su magaji suka yi mashi har suka ji mashi ciwo, daya je gidan iya ya faɗa mata har gida tazo ta sami maijidda tayi mata zagin wulaƙanci akan ita ta sa su magaji su ka daki sadiq, haƙuri ta shiga bama iyah ta na cewa "kiyi haƙuri dan Allah iyah, wallahi sadiq ƙarya ya ke faɗuwa yayi amma ba dukan shi su magaji suka yi ba " ji suka yi an ce "wayyayi iyah cu yaya ne cuka buge ci" Ibrahim da ke tsaye bayan maijidda ne yayi maganar lokacin yana da shikara uku, maijidda kamar ta nutsi saboda baƙin cikin abun da Ibrahim ya ce yaro ne amma sai wayen tsiya,gashi kuma bala'in son sadiq yake dan wani lokacin idan maijidda ko ƴan uwan shi suka daki sadiq nan zai zauna yana kuka da kuma mahaifin su ya dawo zai sanar da shi, murmushi iyah tayi tana faɗin "kaga ɗan albarka, dama na san ƙarya kike, da ma chan na lura ba son sadiq kike ba saboda kinga mahaifin shi ya fi son shi, idan bai fi son shi ba ya ki ke so yayi yaron nan ana haihuwar shi mahaifiyar shi ta rasu to dan mi mahaifin shi bazai nuna mashi kulawa ba, amma kinbi kin tsani yaro kin ɗaura mashi karan tsana kin hanashi wasa da ƴan uwan shi kin sa sun tsane shi saboda tsabar zalunci, to bari kiji wallahi ki shiga hankalin ki in ba haka ba zakiyi mamakin abun da zanyi maki shashasha kawai" tana gama faɗa ta ja hannun sadiq suka koma gidan ta, haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq na hannun iya har ya kusa gama primary school, yan primary 5 lokacin magaji ya kammala secondary yana bin mahaifin su kasuwa , uwani na ss1 halimatu na jss 3 Ibrahim kuma na primary 2 Allah yayi ma iyah rasuwa sosai sadiq ya shiga tashin hankali mara misltowa ya ci kuka kamar ranshi zai fita ana bashi haƙuri, bayan an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login