Showing 30001 words to 33000 words out of 133697 words

Chapter 11 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8490

ba, sai fa munje gidan Aunty Safiya mutafi da Najma "
"duk da haka dai kujira kuyi breakfast sannan"mom ta faɗa, da to suka amsa mata, dole suka tsaya sai da suka yi breakfast ɗin sannan mudi ya kaisu gidan ya dawo, basu wani jima ba saboda ko da suka je Najma harta shirya su kawai take jira, basu wani bata time ba mus'af ya kaisu shagon saloon ɗin da zasuje, wurin ya haɗu babu wani nau in gyaran jiki da basa yi, kama daga wankin kai har izuwa kunshi da gyaran ƙafa......


Wannan Kenan


✨Ammy_Fatima _Noraiz ✨


Zaune suke kan dinning suna breakfast, shazim ya shigo jikin sa sanye da jogging suit white color,sai p_cap black color , wurin su Ammy ya nufo yana faɗin"ina kwana Ammy"
da lafiya lau Ammy ta amsa mashi "Ammy ai da kun bari na dawo sai muyi breakfast ɗin tare"
"kai da shigowar ka ba yanzu ba, waye zai tsaya jiranka"
"amma Ammy ba gashi nashigo da wuri ba"
"yau koh" Ammy ta faɗa
Noraiz ne ya ce "yaya da ƙarfe nawa zaka je abnoor yau"
"yau bazan jeba"
"amma yaya saboda mi"
"haka nan, zamu je wani wuri ne shiyyasa, idan kun kammala breakfast ɗin, Ammy ku shirya" Fatima tace "wannan wane bazata ne haka yaya "
Ammy ma cewa tayi "ina zaka kaimu" murmushi yayi haɗi da cewa "surprise ne, ku dai kawai ku shirya"
daɗi suka ji saboda sun san wani abun mamakin ne yake son yi masu bazata dashi, saboda shi idan ya so fa akwai wasa da dariya, in kuwa baiso ba tofa zaka same shi kadaran kada ham, duk da da man akwai kyakyawar alaƙa tsakanin sa da ahlinsa, wani lokacin in yana tare da su zaka same shi kamar bashi ba, cigaba su kayi da breakfast, shi kuma part ɗinsa ya nufa domin watsa ruwa sannan ya dawo yayi breakfast , san da ya kammala nasa breakfast din dukan su sun shirya shima ko mawa yayi part dinsa ya shirya cikin wani haɗaɗen yadi wanda yasha ɗinkin zama ni" wurin su ya dawo, Ammy ce tace "kai Masha Allah ba ƙaramin kyua kayi ba"
"nagode sosai ammy" gaba yayi yana faɗin "to ku taso mu tafi" tashi su kayi su ka bi bayan shi zuwa compound din gdn, anan suka samu motar da zasu fita da ita ilya ya gama gyara ta ya fito da ita compound , nufar motar suka yi, shi ya shiga ma zaunin driver ya yin da Noraiz ke kusa da shi Ammy da fatima kuwa baya suka shiga, reverse yayi ya nufi gate, a dawo lafiya su ilya suka shiga yi masu, driving yake , su Ammy sun zuba ido ne suga shin ina kuma zasu, wani katafaren shopping mall na ji da faɗa ya nufa dasu,sabon mall ne daga gani ba'a jima da fara aiki a cikin sa ba, parking yayi a parking lot ɗin wuri sannan yace "Ammy ku fito, mushiga ciki " to kawai Ammy tace sannan suka fito,sai da suka fito su duka sannan yace "kowa ya kalli sama " kamar yan da yace haka suka ɗaga kansu suna kallon saman shopping mall, in da aka rubuta (WHITE HOUSE SHOPPING MALL) da man yan baƙi ammy sauke kanta tayi tana kallon shazim cike da alamar tambaya, ganin kallon da ammy keyi masa yasa shi murmushi yana faɗin "surprise " cike da mamaki ammy tace "wai ni kam ina zaka kai son kuɗi ne shazim"matsowa yayi kusa da ita haɗi da dafa kafaɗar ta yace"ammy ina da ku idan ban nemi kuɗi ba mizan yi"
"haba shazim business nawa kake "
"Ammy koma nawa nake, wannan ba wani abu bane, ki sa mashi albarka "
"to Allah yasa albarka ya ba da sa'a "da ameen suka amsa su duka, shazim yace "Mu shiga ciki" ciki suka shiga ya na gaba suna binshi a baya,wani matashin saurayi ne a ƙalla zai yi kimanin shekara 27 ya nufo su, gaishe da ammy yayi da shazim,gaishe da shi noraiz da fatima su kayi, da fara'a a fuskar shi ya amsa masu, shazim yace"ya aikin hameed "
"alhmdllh, komai na tafiya dai dai"
"masha Allah,muje ina son nu na ma su ammy ko wane part "
"ok to shikenan "ciki su ka wuce, wura re ya shiga nuna masu shi da hameed , sai da ya kaisu ko ina a cikin mall ɗin sannan suka ya da zango a office ɗin shi, hameed kuma ya koma wurin ma'aikata ,office ɗin ya haɗu sosai kamar ba office ba, ammy na kan sofa su fatima na ƙasa kan carpet, shi kuma yana zaune kan swivel chair,ammy ta ce"shazim wuri yayi kyau Allah ya taimaka "
"ameen Ammy"
ammy tace "yanzu wa zai kula da nan? "
"a kwai wani ƙanin hameed shi zai kula da nan, hameed kuma noraiz sai su cigaba da kula da wan can business ɗin " "to shikenan, hakan yayi kyau"
sun jima a office ɗin sai da rana tayi sanyi suka fito,yace su shiga ciki kowa ya zabi abun da yake so,
da sauri fatima ta jawo masu cart, suka shiga jidar abun da ransu yayi masu musamman Fatima da Noraiz, Ammy kuwa shazim ke tura mata nata cart din tana daukar abun da take so, sai da kowa ya dauki abun da yake so, ma'aikanta wurin suka kwashe kayan suka zuba masu a booth, sallama suka yi ma su ammy,har parking lot hameed ya raka su,( bayan aikin asibiti shazim yana business sosai tun kafin ya fara aiki da buɗe abnoor yake business, yana sai da motoci wanda hameed ke kula da shi yana da boutique da gidan gona sai white house da ya buɗe yanzu, amma ba shi ke kula da su ba kula mashi ake da su ) mai makon ya kaisu gida wata hanyar ya kuma sake ɗauka , in da ake sai da laptop's ya nufa dasu yana parking suka fito shi da noraiz , su ka shiga ciki, noraiz ya zaɓar ma fatima laptop mai kyan gaske shima,kuɗi ya biya suka fito zuwa mota, daga nan wuren bu ɗe ido yai ta kaisu, Ammy ba ƙaramin dadi tajiba saboda rabon ta da ta shiga gari da sunan miƙe ƙafa har ta manta, sai da yamma likis sannan suka koma gida, godiya su duka suka shiga yi mashi, shi kuma yana cewa "dan Allah su bari mana,wannan ai wajibi ne a gare sa daya yi masu fiye ma da haka"
Ammy tace "duk da haka shazim, bakaji mi hausawa suka ce ba?, yaba kyauta tukwici, tunda bamu da tukwicin dazamu baka shine muke godiya"
"to shikenan " kawai ya iya cewa , ilya ne da mai bama flowers ruwa suka shigo da kayan da suka zo dasu, su kuma kowa daki ya nufa domin watsa ruwa ,Fatima na shiga ɗaki wayanta dake cikin bag ta ciro daketa ringing, ya dr ne ke kira, katsewa kiran yayi zata kira sai kuma wani kiran ya sake shigowa,picking tayi haɗi da sallama amsa mata sallamar yayi hadi da cewa"yar ƙanwata ya kike ya gida ya su Ammy? "
"lafiya lau Yaya"
"masha Allah, ina gaishe da su sosai"
"zasuji Insha Allah "
"miye labari "
"ai ni yaya fushi nake da kai, "
"to fah, kaina bisa wuya ni kuwa mi na ai kata"
"wai ace in gama secondary school, Amma yaya ko irin text dinnan na congratulations ban samu daga gareka ba kai da ya mansoor "
"Allah sarki fatima, kiyi hakuri kinji, so naima ace nazo har Lagos din, amma kuma wasu yan abu bu wa ne suka sha kaina, amma kiyi haƙuri kinji"
"shikenan yaya bakomi, dama yanzu baka wani ji dani,"
"kai , ya za ki ce haka "
"haka ne mana, yau she rabonka da zuwa Lagos, tun kuna mutunci da ya shazim sosai "
murmushi yayi mai sauti yana cewa"waya ce maki bama mutunci sosai yanzu"
"to baga shi nan ba yanzu baka son zuwa Lagos "
Fatima kenan, ya fada a zuciyar shi , a zahiri kuwa cewa yayi"fatima yana yin aiki ne kawai ba wani abu ba, amma Insha Allah ina nan zuwa Lagos very soon "
"to Allah ya kaimu ya nuna mana lokacin" da ameen ya amsa fira suka shiga yi da bisani suka yi sallama, ya mansoor ta kira shima tayi mashi ciwan baki ra shin kiranta, haƙuri ya shiga bata, sun jima suna waya,
a chan parlor kuwa Ammy ce ta fito daga ɗakin ta, Innah asabe ta samu a kitchen tana jera kayan da suka siyo, gaishe da Ammy tayi, amsa mata Ammy tayi cikin kulawa, Inna asabe tace "mi za'a dafa yau da daddare "
"A'a ba sai an dafa komai ba munyi takeaway da muka fita"
"to shikenan "kawai Inna Asabe tace, gyara kitchen din kawai suka yi.....


✨Victoria✨


"destiny wai kina ganin abun da gurutu ya bamu yana aiki kuwa, kusan fa wata daya kenan bawani chanji"
Destiny tace"karki damu na yarda da Gurutu, mukara lokaci kawai, idan ma muka ji shiru mu sake Komawa kawai"
"gaskiya abun da za'ayi kenan gara kawai mu koma"
destiny tace "to shikenan amma mu ƙara lokaci mugani "

✨Hidaya✨


Zaune take bakin gado wayar ta dake gefan ta ce ta fara ringing picking tayi hadi da manna wayar a kunne tana fadin "hello maryam ykk ya gida"on the other hand maryam tace"lafiya lau hidaya"
hidaya tace "Masha Allah"
"mi kike yine haka naji kamar muryar ki tayi ƙasa? " maryam ta tambaya, amsa hidaya ta bata da "lpy qlu, kawai dai ina kwance ne"
Maryam tace"ok to yayi, ya labari doctor kinsan kwana biyu ban shigo hospital ba, ina dai fatan kin fada masa abun da ke ranki"
sauke ajiyar zuciya hidaya tayi, sannan tace"ina fa maryam, wlh da na gansa rasa duk wani kwarin gwiwata nake, sai kawai naji na kasa fada masa"
Maryam tace"gaskiya hidaya kina da aiki, yanzu nan fada masa dinne kika kasa yi "
"uhmm maryam kenan dan dai kawai bake bace a matsayi na ba ne shiyyasa"
"ba haka bane hidaya, daurewa kawai zakiyi ki fada masa"
"to shikenan maryam zanyi kokari naga na fada masa nagode sosai"
"bakomi idan ma kin kasa sai mu nemi number shi, kota waya ne sai ki fada masa, fata na kawai shine ya amince dake amatsayin abokiyr rayuwa, in ga ta tsiyar su destiny da Victoria "
"to Allah yasa ya soni koda bai kai wanda nake masa ba" hidaya ta fada
"to ameen sister, ki cigaba da adu'a Insha Allah dr naki ne ke kadai"
"to Allah yasa"
da ameen maryam ta amsa mata sun dan jima suna wayar daga bisani suka yi sallama......


✨Aairah_Aaimah✨


Ana kammala masu saloon din da kunshi mus'af yazo ɗaukar su, mus'af ne yake cema Aairah " kai masha Allah sweetie irin wannan kyau haka kin kuwa ga yanda kunshi nnan yayi matukar yi maki kyau"
"nagode sosai" Aairah ta fada
Aaimah ce tace
"da yake ya mus'af Aairah ka dai ka sani shiyyasa kace nata yayi kyau mu ko ka kalli namu, abun yar wariyar launin fata ce"
"No Aaimah ba haka bane, na qalbie ne ya ɗauke man hankali, amma kuma naku yayi kyau sosai"cewa Aaimah tayi
"shikenan ya mus'af bakomi"
"mu tafi koh"mus'af ya faɗa nufar motar suka yi, Aairah ta shiga gaba, sai Aaimah da najma a baya,
gidan su Aairah ya nufa dasu, parking yayi a compound , su Aairah suka fita , masu decoration suka samu a compound din suna decorating, main entrance din gidan suka nufa, koda suka shiga ciki baaba larai da Mom da Aunty rabi suka samu a parlorn, suna aikin zuba souvenirs cikin jakunkuna masu dauke da sunan Aairah da Aaimah, shiga suka yi parlorn bakin su ɗauke da sallama, amsa masu sallamar su Mom suka yi, da gudu su Aairah suka nufi Aunty rabi, suna fadin "oyoyo Aunty, ashe kin zo"
Aunty rabi tace "na zo Mom ɗinku ke faɗa man kuna wurin salloon, buɗe mugani " ta faɗa tana cire ɗan kwalin Aairah
" kai masha Allah, gaskiya yayi kyau"
"na gode sosai Aunty" Aairah ta fada, Aaimah cewa tayi" to ni bari na tashi, tun da na lura Aunty baki tani ta Aairah kike"
Aunty rabi tace "sorry Aaimah, ke ma ina ta ke, mu ga naki kema" mom ce tace " to tunda abun ƴar wariyar launin fata ce ,matso kinji ƴata naga naki harda ƙunshin" ta faɗa tana miƙama najmah hannun, da sauri najmah ta ƙarasa wurin Mom, nan tashiga nuna mata
Ina wuni, suka ji mus'af yace,
Mom ce tace "wai dama mus'af tare kuke"
"eh" yaba Mom amsa, gai sawa su kayi har da su Aunty Rabi da baaba larai , mus'af bai wani jima ba yayi masu sallama ya wuce gida, shi ka ɗai ya tafi, a nan Najma zata kwana.
zama su kayi nan parlor suna taya su mom aikin da suke, har suka kammala sannan suka wuce daki, wanka ko wace cikin su tayi da sallah magrib wacce ake kira, basu fita daga daki ba sai da suka yi harda sallar isha sannan suka fice daga dakin suka nufi parlor , yanzu ma mom da Aunty Rabi suka samu a parlorn, zama suka yi sai ga abie da ya abdallah sun shigo, nan suka zauna suna fira,


✨Lagos✨


Ammy da Fatima ne zaune a parlor bayan sunyi sallar magrib da isha suka dawo parlor suna duba kayayya kin da suka yi shopping, fatima tace " wlh kayan nan sunyi kyau sosai Ammy "
Ammy ta ce"ai kuwa sunyi kyau sosai"
Fatima tace" amma Ammy yaushe yaya yace zamu tafi abuja , amma dai sai cikin wannan week ɗin ko "
"to sai dai Idan ya dawo in tambaye shi, dan gsky ni bai faɗa min yaushe zaku tafi ba, duk da munyi magana yace next week amma ban ga yana wani shiri na alamar tafiyar ba "
"ok to shikenan Ammy" nan suka shiga duba kayan suna yaba kyan su,
Noraiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, amsa mashi sallamar su kayi, Ammy na ce wa "ina ka baro Yayan naka"
Amsa Noraiz yaba ma Ammy da
"tare muke dashi, yana compound yana amsa waya"
Ko rufe baki noraiz bai yiba shazim ya shigo, shima wurin su Ammy ya nufo, gaishe da Ammy yayi , ya nemi wuri kusa da Ammy kan sofa ya zauna, Ammy ce tace "ga abinci, kan dinning"
"to " ya bata amsa, dinning din suka nufa, suna kammala dinner din, fatima ta gyara wurin , su kuma kan sofa suka koma, Ammy na tambayar shazim yaushe zasu tafi abuja
"gaskiya ina tunanin sai upper week,zanje jos wani hospital ne suke son ganina next week"
"amma shazim naso ku tafi next week, jiya sai da Ibrahim ya kirani shi da innah nace masu kuna nan tafe next week, yan zu idan suka kira nace kun fasa gani za su yi kamar ni ke hana ku kuzo"
shazim yace "to ammy suyi haƙuri na dawo mana kiran emergency ne, patient sun fisu buƙatar gani na " "shikenan Allah ya kaimu upper week ɗin" da ameen suka amsa su duka, fira suka dan taba sannan kowa ya nufi ɗakin sa domin bacci......


✨katsina ✨


Kwance suke kan bed
ko waccen su sanye take da pajamas ɗinta , Aaimah da najma color ɗaya white sai Aairah dake da pink color , labari kawai suke a kan yanda walimar zata ka sance
Aairah tace "wallahi harna ƙosa naga gobe tayi"
Aaimah tace "faɗi kike anaji, ni baki san yan da nake jiba, Allah dai ya nuna mana goben lpy"
da ameen suka amsa, sun jima suna tattaunawa a kan yanda walimar zata kasance , har bacci yayi awon gaba da su....


WASHE GARI


Tun da safe suka tashi, shirye shirye kawai suke na walima, har mai makeup Mom ta ɗaukko, wacce zata yi masu kwaliyya, zuwa anjima, Idan lokacin walima yayi , su Mom kuwa suma tun da suka yi sallar asuba suke cikin kitchen ita da Aunty Rabi da baaba larai, suna ida shirya abubuwan da basu gama shiryawa ba jiya.
a chan compound kuwa yasha decoration, mai kyan gaske.
wurin karfe biyu na rana gidan ya fara cika da mutane, saboda bayan la'asar za'a gabatar da walimar , har gida ya abdallah ya je ya dauko Dadi, sai Aunty safiyya wace mus'af ya kawo,yan uwan abie ba wanda baizo ba da ƴaƴen su , sai wasu daga cikin ƙawayen Mom , hakama ƙawayen su Aairah na islamiya da boko duk sun zo, sai abokan abie dake nan katsina ba laifi suma sun zo , gida dai ya ciki Alhmdllh.....

✨Ammy ✨
Zaune take kan sallaya tana adu'a,
wayar ta dake bedside drawer ce ta fara ringing, miƙa hannun ta tayi ta ɗauki wayar haɗi da yin picking bakin ta ɗauke da sallama on the other hand cikin wayar muryar wata dattijuwar mace tace wa'alaikumu salam, ammy ta ce"ina wuni innah " amsa ma ammy tayi da "lafiya " ammy tace "innah yasu alhaji ahmad da su hajiya turai" da katar da ammy matar yi da faɗin "dakata aisha bawai na kira ki bane dan kiyi taman tambayoyi, na kira ne kan maganar da muka yi da ke, naga yau kusan wata kenan amma bangan su sunzo ba" ammy ta ce "dan Allah innah kiyi haƙuri, ko jiya da daddare munyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login