Showing 27001 words to 30000 words out of 133697 words

Chapter 10 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8494

na ko"
"eh naji" rejecting uncle ahmad yayi batare da ya saurari mi shazim ɗin zai sake cewa ba,
"sai ku shirya kai da su"
"haba ammy, ni bazan je ba "
"to wallahi bari kaji bazaka dinga ja man zagi ba wurin su kaji na faɗa maka, gara ma tun wuri ka shirya ku tafi"
"to, amma sai next week "
"Allah ya nu na mana"ammy ta ce haɗi da ficewa ta bar part ɗin ..... 🖊




Episode


13

✨Noraiz-Fatima✨


zaune suke parlorn Ammy, fatima na duba wani novel yanzu ba school sai Islamiyya, shikuma yana aiki a laptop ɗin sa, aje novel din tayi tana cewa
"ya noor ka kuwa tuntubar man big bro maganar school ɗin dan Allah " ture laptop ɗin yayi yana cewa "kima bar wannan maganar , dan wlh yace kusa da Ammy za kiyi karatu , ki tambayi Ammy ma a ga banta yace haka, har sa baki tayi amma yace a'a"
"hai wai shi ya Shazim miyasa yake haka dan Allah , to yaya ita Ammy mi zai hana tace sai nayi "
"kawai kiyi haƙuri kiyi karatun ki anan a kwai makarantu masu kyau kamar na can zaki samu duk abun da kike so, kuma na san zai sama maki mai kyau da tsada"
"ya noor ya zanyi dole na hakura, Allah ka ɗai yasan da lilin sa na hana ni"
"nasan bazai wuce saboda innah ba ya hanaki "
"anya dai, Allah yasa haka alkairi ne"
"ameen "Noraiz ya faɗa
(Suna da saurin fahimtar dan uwansu saboda sun ɗauke shi tamkar mahaifin su da suka rasa tun basu san kansuba, saba nin wasu yan uwan idan akace mahaifin su baya da rai, zaka samu insuna son abu dan uwan su yanu na masu illar abun maimakon su fahimce shi, sai kasamu suna kullatar shi a rai wasu harsu kai da faɗin dan yaga mahaifin su baya da rai shiyyasa yake masu abun da duk yaga dama,zasu dunga ɗaukar shi a matsayin mai tauye masu haƙƙi
abu buwa dai iri iri, Allah kasa mana ƙaunar ƴan uwan mu da fahimtar su ka bamu ikwan rufa ma junan mu asiri ameen 🙏 )


Ammy ce ta fito daga bedroom dinta tana cewa "yaya da kanwa mi ake shiryawa ne, aketa ƙusƙus"
"sirri Ammy ki zauna ayi dake"
Noraiz ya fada yana nuna mata kan sofa, zama tayi tana faɗin " ina sauraro kuwa, wane sirrin ne ake shiryawa"fatima tace "ammy maganar makaranta ce"
"mi ya faru "
"bakomi, ya noor ya sanar dani yan da ku kayi da ya shazim"
"hakane sai dai kiyi haƙuri "
"dama ya zanyi ammy dole na haƙura, amma ban san mi yasa ya shazim bai son zama na abuja ba "
"nima kaina ban san dalili ba nasan dai bai wuce innah"
sun jima suna tattaunawa kan maganar, sai ga shazim ya shigo da alama daga abnoor yake saboda yau friday dama bai cika jima wa ba saboda zuwa masallaci, wurin su ya nufo ya na faɗin " Ammy ina wuni, mi a ke shiryawa ne nagan ku zazzune a parlor"
"lafiya lau ya aiki, sirri ne kaima zoka zaune" murmushi yayi yana neman wuri kusa da Ammy ya zauna, gaishe da shi su fatima sukayi noraiz nace wa " ashe dama na bika naga ka dawo da wuri"
"ai kafi son zaman gida ne saikace wata mace, zan ga yan da zaka ƙare idan kafara business "
"ai koh lallai " Ammy ta fada hadi da mangare ma shazim kai, sosa wurin yayi yana fadin "Ammy haka ne fa, in ba mace ba miya haɗa namiji da zaman gida" dariya fatima da Noraiz suka yi ganin yan da shazim ke bata fuska , maka masu harara yayi, shiru suka yi suna ƙumshe dariya, basu wani jimaba suna fira suka tashi domin shirin zuwa masallaci ammy kuma da fatima suka tafi daki domin yin sallah suma....


✨KATSINA✨


Abie ne da abdallah ke sauko wa daga up stairs zasu tafi masallaci, da Mom suka ci karo a parlor ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da food flask" Masha Allah irin wannan kyau haka barrister, gaskiya kar ka sa matan mutane suyi ta kalle man miji" dariya abie yayi abdallah kuwa duƙar da kai yayi yana murmushi a zuciyar shi yana fadin " Mom duk da an tsufa amma ana kishi, Allah ya bani mace irin Mom" nace ameen dr
"da har ina cewa zan ƙara maki a bokiyar zama, amma kike faɗin haka"
"tab wallahi kaima kasan wasa kake, ai auren mu inkaji ana auren zobe, ba saki ba yaji ba kishiya"
dariya abie ya sake kwashewa da ita yana faɗin "za kuwa kisan ba wasa nake ba, dan daga nan zance zan wuce" in ban da dariya ba abun da abdallah ke ma iyayen nasa, yana kallon su cikin birgewa
"ka dai faɗa , nawa jine kawai"
"ai kuwa zaki san bawasa nake ba, kaga abdallah wuce mu tafi kar mu makara" ficewa su kayi suna jin Mom na masu a dawo lafiya
bedroom ɗin su Aairah ta wuce bude ƙofar tayi ta shiga
shiri ta same su suna yi "yawwa kun shirya kenan"
"eh"suka bata amsa
"yawwa kuyi sauri ku ƙarasa , ga abinci can kitchen mungama, ku jera kan dinning sannan su mudi ma ku tabbatar kun kai masu nasu nizan shiga nayi wanka ne kunji"
Aairah tace
"ok Insha Allah za muyi yan da kika ce, amma Mom wai ya maganar walimar mune, munga ba'a fara shirin komai ba, kuma fa jibi ne"
Mom tace" tana nan mana ba jibi bane, jira nake anjima yayan ku ya kaimu shopping ko kuma abie dinku, saimu siyo duk abun da ya dace"
Aaimah tace"to shikenan Mom Allah ya kaimu an jimar" ameen Mom tace hadi da fi cewa daga dakin tana sake tuna masu aikin da ta sa su, suna gama shirin suka fita domin yin abun da Mom tasa su, suna kammalawa nan main parlor suka tsaya suna kallo
su abie ne da ya abdallah suka shigo, sannu da dawowa su kayi masu hadi da gaisawa, amsa masu su kayi abie ya samu kan sofa kusa dasu ya zauna ya yin da shikuma ya abdallah ya haye up stairs, fira su qka shiga yi da abie akan walimar da za'a yi masu , sun jima suna fira har Mom ta sauko tana cewa "shiyyasa naga barrister bai shigo ba, ashe kuna nan kun tasa shi gaba da abun da kuka saba watan surutu "
Aairah tace"kai Mom bafa surutu muke masa ba, maganar walimar mu fa mu keyi" dinning Mom ta nufa tana faɗin
"to yayi, sai ku taso ga abinci na jiran ku" ta sowa suka yi har da abie suka nufo dinning din, abie nace ma
"Aaimah jeki ki kira yayan ku, kinji"
"to sbie" ta fada hadi da nufar up stairs ta nufi part din abdallah , samun shi tayi yana waya jira tayi sai da ya gama sannan tace yaya kazo mu ci abinci, da to kawai ya amsa mata, ya yin da ita kuma ta fice tabar ɗakin ko mawa dinning din tayi wurin zaman ta na ɗazu ta koma ta zauna plate taja wanda Mom tayi serving ɗin kowa, shiru kowa yayi anata bama ciki hakkin sa, sai da suka kusa kammalawa sannan abdallah ya sauko ya nufo dinning ɗin, Mom tace "lafiya baka fito ba tun time din da aka kira ka"
"Ina wani ɗan aiki ne shiyyasa" ya fada hadi da neman wurin zama ya zauna plate ɗin abinci Mom ta miko masa, thanks ya faɗa hadi da dau kar spoon ya fara cin abincin, suna gama wa su Aaimah suka gyara wurin yayin da su Mom suka koma kan sofa, suma suna gamawa wurin su Mom ɗin suka dawo, firar walimar da za'ayi masu suka shiga yi, basu tashi ba sai da lokacin sallar asr yayi sannan su abie suka wuce masallaci, suma daki suka shiga domin gabatar da tasu..


mom ce ta fito daga bedroom ɗinta jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani da mayafi sai jaka a hannun ta, ɗakin su Aaimah ta nufa samun su tayi duk sun sha abaya black color sunyi rolling da gyelenta sai side bag da ko waccen su ta rataya sai glass irin na gayu ɗinnan, shirin fita suke daga ɗakin sai ga Mom ta shigo "yawwa kun shirya kenan to ku fito mu wuce abie dinku da yayan ku na waje mu ka dai suke jira" Aaimah tace
"Mom ba kice munyi kyau ba" yan yatsu kawai Mom ta haɗa al'amar komai yayi, ficewa su kayi zuwa compound din gidan inda anan suka samu abie da ya abdallah, shiga su kayi cikin motar ya abdallah ke driving yayin da abie ke kusa da shi, sukuma suna baya su da Mom, a dawo lafiya su mudi su kayi masu yayin da abdallah ya fice da motar suka hau kan titi, wani ƙaton shopping mall ya nufa dasu, parking su kayi a parking lot dake wurin wanda aka tana da domin masu siyayya, sai da ya gama dai dai ta parking din motar, fitowa suka yi, cikin mall din suka nufa, barka da zuwa waiters su kayi masu,inda ake ajiye cart suka nufa, guda biyu suka ɗauka, Aaimah na tura daya tana biye da abie da ya abdallah , yayin da Aairah ke tura daya tana biye da Mom,siyayya suka yi sosai, sun jima a shopping mall sai da suka tabbatar sun tanadi abun da suka san zasu buƙata sannan suka nufi wurin biyan kudi, abdallah ya biya duk abun da suka siya ma'aikatan wurin suka ɗaukar masu kayan zuwa booth,
wurin da ake sai da snacks suka wuce pizza da shawarma da ice cream ya abdallah ya sai masu daga nan suka wuce gidan dadi, suna isa bakin gate din gidan ya abdallah yayi horn, mai gadin ne ya leƙo, ganin motar abdallah yasa shi komawa ciki da sauri hadi da bude masu gate, ciki ya shiga da motar parking lot dake compound din gidan ya nufa hadi da yin parking, sannan suka fito,booth abdallah ya buɗe, snacks ɗin da suka siya ya ɗauko haɗi da miƙama su Aairah , cikin gidan suka nufa, parlor ne dan dai dai matsakaici yasha royal sofas masu kyan gaske , wata yar tsohuwa ce (dadi kenan) zaune ita da wata mata aƙalla zatayi kima nin shekara 38 zuwa 40 ( Aunty Rabi kenan, ƙanwar abie ce, zaune take da dadi tun lokacin da Allah yayi ma mijinta rasuwa, kuma gashi Allah bai bata haihuwa ba shiyyasa ta dawo kusa da mahaifiyar ta tana kula da ita) sallama su kayi, aunty rabi ce ta amsa masu sallamar hadi da cewa "wannan shi ake kira tafi da gidan ka, wannan ziyarar bazata haka yaya"
dariya abie yayi hadi da cewa "ke dai bari kawai rabi, munje siyayya ne saboda walimar su Aairah, shine muka biyu ta nan" nan suka shiga gaisawa, wurin dadi suka matsa itama suna gaishe da ita amsa masu tayi cikin kulawa hadi da taya su Aairah murnar kammala makaranta da hadda nan suka shiga fira "Muhammad yaushe ne walimar su yan biyu" dadi ta tambaya, amsa abie ya bata da" jibi ne Insha Allah"
"to Allah ya kaimu" da ameen suka amsa , miƙama aunty rabi snakcs ɗin dake hannun su suka yi, amsa tayi tana ma abie godiya, Aairah tace "amma dai dadi zaki zo koh"
"Insha Allahu kuwa, ai audu zai zo ya ɗauke ni da kansa, koh audu" tafada tana shafa kan abdallah dake kusa da ita, ɓata rai yayi yana cewa, "wai dan Allah dadi bazaki daina ce man audunnan ba, nifa suna na abdallah , ba audu ba" dariya su ka kwashe da ita su duka ban da abdallah dake zabga ma su Aairah harara saboda dariyar da suke mashi "ai inba kishiya kayi man ba, bazan daina cemaka haka ba, shima abun da zaisa na daina kawai dan kar ta raina min ango ne, amma da bazan bari ba"
"to shikenan ashe baki ba cin kaza kuwa, tunda haka ki kace" dariya suka sake kwashewa da ita, dama duk abdallah da dadi suka haɗu wuri daya tofa zaka sha dariya , mai aikin dadi ce ta fito daga kitchen wurin su ta nufo tana gaishe da su abie,mom tace "uwani ashe kina nan, ya kwana biyu"
"Alhmdllh" wace aka kira da uwani tace, su Aairah ma gaishe da ita suka yi, amsa masu tayi da lafiya lau"an kammala girkin " uwani ta faɗa , aunty Rabi tace "to shikenan, Aairah ku ɗauki wannan snack's kuje da shi kitchen sai ku taya ta jera abincin kan dinning" da to suka amsa mata, tashi suka yi suka bi bayan ta , Aaimah tace "wai Aunty uwani ina Nuratu ne naga kwana biyu idan muka zo bama ganinta"( diyar Aunty uwani nin ce nuratu) Aunty uwani tace "Nuratu na kauye, an kusa bikinta ina fatan za kuzo "cike da mamaki su Aairah suka ce "aure fa kikace Aunty Uwani, yanzu nan nuratu harta isa aure"Aunty uwani tace
"eh mana, duk sa'annin ta dake chan duk anyi masu aure har ma wanda basu kai taba ana masu aure, dan dai kawai ku kuna birni ne shiyyasa kuke ganin kamar bata isa ba" Aairah tace " to Allah ya nuna mana lokacin, Insha Allah kuwa zamu je" haka suka ciga da fira Aunty Uwani na basu labarin ƙauye su kuma suna mamaki har suka kammala jera abincin kan dinning, sallar magrib da aka kira ne yasa su abie nufar masallaci shi da abdallah Mom ɗakin Aunty Rabi ta nufa domin gabatar da sallah , su Aairah kuwa ɗakin Dadi suka nufa domin yin tasu sallar, sun riga su mom dawo wa parlor su da Dadi,suna ta zuba mata surutu su abie suka shigo hara da uncle mustafa ( kannin abie wanda ke bi masa, su biyar ne ɗiyan dadi abie shine na farko sai uncle mustafa daga nan sai aunty Rabi sai uncle Ahmad sai Aunty Asma'u itace yar autar su, da Uncle mustafa ne ka ɗai ke katsina, kafin Abie ya dawo nan shikuma uncle Ahmad har yanzu yana abuja sai Aunty Asma'u dake aure kano, Aunty Rabi kafin Allah yayi ma mijinta rasuwa barno take Aure time din .) bakin su dauke da sallama suka shigo,amsa masu sallamar su kayi yayin da su Aaimah ke cewa "uncle ina wuni"
amsa masu yayi cikin kulawa yana cewa "ya school naji yaya yace kun kammala, to Allah ya tai maka yasa a samu saka mako mai kyau" da ameen suka amsa mashi,dadi tace "yawwa mustafa naji daɗin zuwan ka, kamar kasan ina son ganinka kai da Mahammad "
abie yace "to fa mama Allah yasa lafiya "
"lafiya lau,maganar dai da na saba ce, mu shiga daga ciki" da to suka amsa haɗi da miƙewa suka bi bayan dadi, bedroom ɗin ta suka shiga, wuri suka samu bakin gado suka zauna, kallon su dadi tayi sannan tace"a kullum bazan gaji da maku maganar ɗan ƴar uwata ba, ba shi da wani a duniyar nan da zai kalla a matsayin uwa a gare shi bayan ni , ban san wane hali yake ciki ba, ƴar uwata zata ce ban riƙe alƙawari ba " uncle mustafa yace
"kiyi haƙuri mama, insha Allah zamu nemo shi a duk idan yake a faɗin duniyar nan "
"mustafa kullum haka kuke cewa, amma har yau baku nemo man shi ba, kullum sai nayi mafarkin shi yana cikin damuwa, yana buƙatar tai mako na "abie yace "ki ƙara haƙuri mama, insha Allah za'a gan shi, zanje har garin ku, nasan baza'a rasa wanda yasan inda ya koma da zama ba"
"to shikenan Muhammad, zan zuba ido har lokacin da Allah zai bayyanar da shi"da ameen suka amsa, dadi tace "ku tashi ku koma parlor kuci abinci "to mama suka faɗa haɗi da miƙewa suka nufi parlor, a dinning suka samu su mom, wuri suka samu suma suka zauna,aunty rabi tayi sarving ɗin su , sai wurin karfe 9 da kusan minti 50 sannan suka bar gidan harda uncle mustafa suka nufi gida, suna isa gida, baaba larai ta fito tayi masu sannu da zuwa, kowa ɗakin sa ya nufa, snacks ɗin da suka zo dashi baaba larai ta kai kitchen ckin fridge bayan ta ɗauki wanda zataci, ɗakinta ta nufa ta kwanta ita ma 😴.....🖊


Episode
14_15


WASHE GARI


Tunda suka yi sallar asuba basu koma bacci ba saboda ɗokin zuwa wurin ƙunshi da gyaran kai da za suje, ko da gari yayi haske wanka kawai suka yi suka shirya sannan suka nufi ɗakin Mom, koda suka shiga basu sameta ba kitchen suka wuce anan suka same ta ita da baaba larai suna shirya breakfast gaishe dasu sukayi, Mom tace"wai ba dai har kunshirya ba"
"munshirya , tafiya ma zamuyi" suka bata amsa
Mom tace"to sai ku bari kuyi breakfast tukunnan"
Aairah tace "ba fa direct saloon din zamu wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login