Showing 42001 words to 45000 words out of 133697 words

Chapter 15 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8506

tayi fuuu kamar zata tashi sama, fatima ce tace "aunty feenah abun ba magana "juyowa tayi ta kalli fatima sama da ƙasa fuska a haɗe tace "sannu" ta juya tayi gaba, da idanu kwai fatima ta bita, taɓe baki noraiz yayi, fuskar sa'ada da ɗan damuwa ta kama hannun fatima tana faɗin "sorry sister " ɗan yaƙe fatima tayi tana faɗin "bakomai" tsaki kairiyya ta ja a zuciyar ta tana faɗin "ko yaushe feenah zata dai wannan banzar ɗabi'ar "
parking lot ɗin airport ɗin suka ƙara so time ɗin har shazim ya shiga bayan mota ya zauna, aminu na saka kayan su cikin booth, amsar trolly ɗin dake hannun sa'ada kamal yayi ya saka a booth, buɗe ma su baya yayi, noraiz ya shiga sa'ada ta ce " kamal mu zamu tafi a motar aunty kairiyya "
"to shikenan hajiya " kama hannun fatima tayi suka nufi inda motar kairiyya ta ke, tsaye suka same ta bakin mota,
sa'ada tace
"lafiya dai aunty kairiyya"
"babu komi, ku nake jira ne "
sa'ada tace "aunty feenah tafiya tayi?" eh kawai kairiyya tace haɗi da buɗe motar ta shi, suma shiga sukayi fatima na gaba kusa da kairiyya sa'ada na baya, key tai ma mortar haɗi da yin reverse tabi bayan motocin da su shazim ke ciki, suna tafiya kamal na tambayar noraiz ya lagos da ammy, da alhmdllh noraiz ya amsa mashi sosai suke fira da shi har suka kawo wata danƙareriyar anguwa ta ji da faɗa, gidajen dake anguwar ka ɗai sun isa su sa ka fahimci cewa anguwa ce ta manyan mutane, gidaje ne naji da faɗa, road road ne gasunan kala kala kowane road kalar tsarin ginin gidajen ta da ban, karya kwana animu yayi ya shiga wani road bin bayan shi su kamal suka yi shi da kairiyya , masha Allah wani haɗeɗen estate ne naji da faɗa, aƙalla gidajen dake cikin estate ɗin zasu kai 20 duk da akwai wainɗan da anyi foundation ba'afara gina su ba, tsarin gidajen dake cikin estate ɗin yafi na sauran gidajen dake sauran road ɗin haɗuwa da tsari,komai na gidajen iri ɗaya ne, tafiya suka yi mai ɗan tsayi, sannan suka kawo bakin main gate ɗin estate ɗin ,securitys ne zaune kan bench a bakin gate ɗin estate ɗin, ɗaya daga cikin su ne ya taso ya nufo motar, sauke glass ɗin motar aminu yayi, gaisawa yayi da security ɗin, tambayar shi securityn yayi daga ina, amsa aminu ya bashi "daga airport muke, yallabai shazim ne ya zo " liƙawa security yayi yana cema shazim "ranka ya daɗe barka da zuwa, ya hanya "da alhmdllh shazim ya amsa masu, sauran security ɗin ma ta sowa su kayi suna gaishe da shazim sannan suka nufi motar dasu noraiz ke ciki suna gaishe su, cikin sakin fuska suka amsa masu, buɗe masu gate security yayi ,ciki aminu ya danna kan hancin motar kamal na biye da shi, sai da suka ɗanyi nisa da tafi sannan suka iso bakin wasu gidaje biyar dake jere duk da akwai yar tazara tsaka nin su , huɗu girman su ɗaya, ɗayan kuma yafi su girma sosai, mai girman dake tsakiyar su aminu ya nufa , parking aminu yayi bakin wannan ƙaton gidan wanda yafi sauran gidajen girma da haɗuwa parking lot ɗin gidan ya nufa yayi parking, motoci ne da a ƙalla zasu kai biyar an rufe su, fitowa aminu yayi ya buɗe ma shazim ƙofa amma sai shazim yace kawai ya ɗauki kayan ya wuce, hakan yasa shi nufar booth ɗin motar ya fito da trollys ɗinsu, ya nufi entrance ɗin shiga gidan ya tsaya, kamal ma ya nufo nan yayi parking a parking lot fitowa noraiz yayi, su fatima kuma wani part kairiyya ta nufa da su tayi parking, fitowa sa'ada da fatima suka yi, sa'ada ta buɗe booth ta fito ma fatima da trolly ɗin ta, fatima leƙa ta window tana faɗin "aunty kairiyya sai mun shigo " da to kairiyya ta amsa, reverse tayi ta nufi wani part tayi parking, ficewa tayi ta nufi cikin part ɗin.
kallon motar feenah dake parking lot ɗin sa'ada tayi, aranta tace kenan gida aunty feenah ta dawo , trolly ɗin fatima ta ja suka nufi entrance ɗin gidan ,kamal na parking noraiz ya fito ya nufi aminu dake tsaye yana jiran fitowar shazim ya kai masu trolly ɗin cikin gidan amma bai fito ba noraiz na isowa ya tambayi aminu lafiya, amsa aminu ya bashi da shazim ya ke jira ya fito noraiz ya ce " ok muje kawai" da to aminu ya amsa yana gaba noraiz na baya, buɗe ƙofar aminu yayi suka shiga har time ɗin shazim bai fito ba yana zaune cikin mota, haɗeɗen parlor ne mai kyan gaske dan inka shiga sai kayi tuna nin ba acikin estate ɗin kake ba, babu motsin kowa aciki sai ƙarar ac dake aiki ita kaɗai,kota ina ƙamshi ne ke tashi cikin parlorn, up stairs aminu ya nufa , ɗakuna ne saman sosai, wata yar hanya aminu ya bi nanma wani parlorn ne wanda yafi na ƙasa haɗuwa da tsari, wani stairs ɗin suka ƙara nufa nanma parlor ne shima ya haɗu ga tsari mai kyau,sannan suka nufi wani ɗan corridor , bedrooms ne kusan guda huɗu anan aminu ya tsaya yana ajiye trollys ɗin yayi ma noraiz sai anjima, godiya noraiz yayi mashi sannan ya ja trolly ɗin shazim ya shiga ƙofar dake kusa da shi, ɗan ƙaramin parlor ne mai kyan gaske kusan tsarin shi ɗaya da parlorn shazim dake lagos, nan kamshi yake mai daɗin gaske ga sanyin ac, bedroom ya nufa nan ma ya haɗu shima kamar na lagos ne sai dai yafi na lagos girma da wasu abubuwan, har cikin wardrobe noraiz ya saka ma shazim trollys ɗin shi sannan ya fice daga ɗakin yanufi nashi, shima nashi ya haɗu sosai banbancin shi dana shazim bawain mai yawa bane bedroom ya nufa ya rage kayan jikin shi ya nufi toilet domin ya watsa ruwa ..


✨Shazim✨


wayar shi dake cikin aljihu ya fiddo, number ammy yayi dialing saida ta kusa tsinkewa sannan ammy tayi picking bakin ta ɗauke da Sallama, amsa sallamar shazim yayi yana faɗin ammy ya gida, da lafiya lau ta amsa tana tambayar shi ya gajiyar hanya da kuma mutanen abuja "gajiyar tafiya akwaita ammy alhmdllh" murmushi ammy tayi mai ɗan sauti tana cewa "gajiya sai kace wanda yaje a mota ko a ƙafa" kwantar da kanshi yayi jikin saet ɗin motar yana shafa kanshi ya ɗan lumshe ido yana faɗin "da gaske nake ammy " ammy tace
"to yayi, ya mutanen gidan? "
"wallahi ban saniba dan ban shiga ba"
"to saboda mi, ina fatima da mai babban suna? "
"fatima na part ɗin uncle Ibrahim, noraiz kuma na part ɗin mu "
"to kai kana ina? "
"ina cikin mota, yanzu muka iso ne ammy, na tsaya in kira ki ne "
"ok miyasa ku baza ku sauka part ɗin ibrahim ba kona yaya ahmad "
"bakomai ammy, shi da kanshi uncle Ibrahim ɗin yasa aka gyara mana nan"
"duk da haka shazim da kuna zauna part ɗin shi, nasan shima dan ya san halinka ne ba zaka zauna part ɗin shi ba yasa aka gyara maku nan "
"ammy ba haka bane"
"to yaya ne in ba haka ba? "
"kawai ya san zamufi sakewa ne apart ɗin mu shine kawai"
"shikenan shazim, amma da mun gama wayar nan ku shiga part ɗin innah ku gaishe ta dan Allah "
"to" kawai yace dan wallahi kwata kwata bai son ganin tsohuwar,
"to sai anjima, in ka shiga kace ina gaishe dasu dan Allah "
"to insha Allah zasuji "daga haka yayi rejecting ɗin kiran,number malam ya lalubo bugu ɗaya malam ya ɗauka da Sallama, gaishe da shi noraiz yayi, cikin kulawa malam ya amsa da tambayar shi hanya da su fatima, sunjima sosai suna waya da malam sannan suka yi Sallama, cikin aljihu wando ya maida wayar, sannan ya buɗe motar ya fice, ya nufi part ɗin su ko da ya shiga bedroom ɗin shi ya nufa yayi wanka ya kwanta kan bed, nocking ya ji anayi daga parlor, shiru yayi kamar yana bacci dan ya san bazai wuce noraiz bane, kuma ya san ya zo ne dan su tafi parts ɗin uncles ɗin su, shiyyasa yayi shiru dan bai shirya zuwa wurin kowa ba yanzu, jin shiru yasa noraiz tuna nin koh yayan nashi barci ya ke, barin bakin ƙofar yi ya fice daga gidan, gidan dake kusa da wanda kamal ya aje fatima da sa'ada noraiz ya shiga da Sallama, parlo ne mai girma ya ji furnitures masu kyan gaske, tsit yake ba kowa a ciki, wani ɗan corridor ya nufa ya shiga wata yar ƙofa,nan ma wani ɗan ƙara min parlor ne, shiga ciki yayi da sallama, kyakyawar tsohuwa ce zaune kan carpet jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani sai feenah da ke kan sofa kusa da ita fuskar ta duk hawaye jin sallamar norai ne ya sa feenah goge hawayen da ke fuskar ta,zuba ma noraiz ido tsohuwar tayi har ya ƙara so cikin parlorn ya neman wuri ya zauna kan sofa yana faɗin "inawuni innah " amsa mashi tayi da "lafiya, ai nayi tuna nin kaima kafi ƙarfin kazo ka gaishe da ni kamar ɗan uwan ka mara kunya, dan nasan idan ba Ibrahim ya kira shi ba bazai ta ɓa shigowa nan ba saboda aisha ta riga da tasa ya gama raina ni baya ganin mutunci na "
"kiyi haƙuri innah yana nan shigowa bacci ya kwanta saboda jiya bai samu yayi bacci sosai ba "
"kai da Allah yi man shiru, wane haline kuma na abdulƙadir wanda ban sani ba, itama fatima tafi ƙarfin tazo ta gaishe ni koh"
"A'a innah tana tare da sa'ada nasan zasu shigo ne "ta ɓe baki innah tayi tana faɗin "Allah sa"
da ammen noraiz ya amsa haɗi da miƙewa yana faɗin" innah zanje part ɗin uncle Ibrahim"
bai jira mai zata ce ba ya fice abun shi, da harara feenah ta bishi yana fita tace "kingani koh innah shima noraiz wulaƙanta ni ya ke, dan tunda suka zo ko kallon banza bai yi min ba, da ya shazim ya dizgani a airport dariya yayi shida fatima "
"rabu da yan banza, zanyi maganin su ne daga su har uwar ta su, kuma shi wannan mara mutuncin nasan miye maganin sa, bari dai kawunnan nashi su dawo"
"yawwa innah shiyyasa nake sonki wallahi "
"ai karkiji komai,su dai dawo, zai san dani yake magana, sai dai kuma abun da nake so a wurin ki shine ki kama kanki ki daina son taɓa jikin shi dan nasan halinki da ɗabi'ar banza "
"Insha Allah innah na bari bazan sake ba "
"Allah ya sa " da ameen feenah ta amsa, suna nan zaune suna fera sa'ada suka shigo ita da fatima ko da fatima ta gaishe da innah cewa tayi" sai yanzu kika ga damar zuwa, ai da kinyi zaman ki baki shigo ba "haƙuri kawai fatima ta bata, ko kallonta bata yiba suka cigaba da fira ita da feenah, ganin haka ne yasa fatima cema sa'ada ta tashi suje part ɗin su aunty kairiyya, tashi sa'ada tayi suka fice zuwa part ɗin uncle ahmad, anan suka samu noraiz shida mahmud,gaishe da mahmud fatima tayi, sannan suka shiga bedroom ɗin mama ( asiya mahaifiyar su mansoor ) suka gaisa tana tambayar fatima ya su ammy, sun ɗan jima suna fira da ita sannan suka tashi suka nufi bedroom ɗin kairiyya.


wani matashin saurayi ne ya shigo parlorn da sallama hannun shi riƙe da briefcase, da sauri noraiz ya nufe matashin yana cewa "oyoyo ya mansoor,nayi kewar ka sosai"rungume shi mansoor yayi yana cewa " lil bro saukar yaushe? "
" tun ɗazu, ina ta zuba idon ganin ka, ya aiki" shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "alhmdllh,ya su ammy da auta? " muryar fatima sukaji fitowar ta kenan daga ɗakin kairiyya tana cewa "gani anan yaya "juyawa mansoor yayi yana cewa "autar ammy, yan graduation kice tafiyar harda ke"ɓata fuska fatima tayi tana faɗin "ai ni fushi nake da ku kai da ya dr, ko ɗan text message na happy graduation" matsowa kusa da ita mansoor yayi yana faɗin "sorry lvly sis bahaka bane munso muzo har lagos ɗin Allah ne dai bai nufa ba, amma kiyi haƙuri gift ɗinki na nan na ajiye maki"washe baki fatima tayi tana faɗin "tnxs big bro"
"to shikenan autar ammy ni zan shiga ciki na watsa ruwa " mansoor ya faɗa haɗi da nufar up stairs,"to sai ka fito "fatima ta faɗa, tashi noraiz da mahmud su kayi suka fice su fatima kuma suka zauna kan sofa suna fira ita da sa'ada.


shazim daga wannan kwanciyar bacci yayi awan gaba da shi ba shi bane ya tashi ba sai gab da magrib, yana tashi ya nufi toilet yayi wanka haɗi da alwala,sannan ya shirya ya fito daga bedroom ɗin ya nufi dinning, abinci yaci kafin ya fice daga part ɗin,ya nufi masallacin dake cikin estate ɗin ,ana gama sallah ya fito ya nufi part ɗin uncle ahmad,kairiyya da su fatima ya samu a parlor , gai she dashi kairiyya ta sake yi tana cewa" ya gajiyar tafiya ya shazim " amsa mata yayi da Alhmdllh sannan yace" uncle fah? " yana sama ta bashi amsa, tashi yayi ya nufi up stairs ya shiga wani ɗan ƙaramin parlor, zaune uncle ahmad yake kan carpet, mama na kusa da shi,sallama yayi ya shiga ciki, amsa mashi sallamar sukayi, wuri ya samu kan carpet ya zauna yana gaishe da su amsa mashi sukayi cikin kulawa uncle ahmad na tambayar su malam da ammy,"suna lafiya" uncle ahmad ya ce "masha Allah, kaje wurin Ibrahim?" shazim yace" a'a yanzu dai zan tafi " uncle ahmad yace
"to shikenan, bari sai ka ci dinner tukunnan sai ka tafi "
"bana jin yunwa uncle yan zu na ci abinci" uncle ahmad yace "to shikenan tashi kaje wurin Ibrahim ɗin "
da to shazim ya amsa haɗi da miƙewa ya fice,yana fita bedroom ɗin mansoor ya nufa, zaune ya same shi yana waya, harara ya watsa ma shazim, murmushi yayi haɗi da samun wuri kusa da shi ya zauna yana faɗin"my lover bro wannan hararar ta mi cece" katse wayar mansoor yayi yana faɗin"amma wallahi ka rainani shazim ni nema lover ɗin koh "
"eh mana, yaya "
"ni nama manta nayi maka magana fushi nake da kai "
"kaina bisa wuya minayi kuma lover bro "duka mansoor ya kai mashi ya kyauce "Allah zanyi maganin ka idan har baka daina ce man lover bro ɗinnan ba"
" sorry na dai na"
"da dai ya fiye maka, kuma ka tashi ni ka bani wuri "
"afuwan ya mansoor " juya mashi baya mansoor yayi yana faɗin
"ka tashi nace ka bani wuri" hannu shazim ya sa ya riƙe kunnuwan shi alamar ban haƙuri yana cewa"haba ya mansoor dan Allah fa"kallon shi mansoor yayi yace
"Uhmm , ya hanya, ya su ammy da malam"
"suna nan lafiya "
"masha Allah"
dafa kafaɗar shazim mansoor yayi sannan ya ce "bro wai miya farune ake ta kiran ka amma baka ɗaga waya wani time ɗin ma akashe, kasan ka ɓata ma su abbah rai sosai " kallon mansoor shazim yayi "yaya su abbah sun ta kura dole sai nayi aure ni kuma yanzu bana da ra'ayin yi"
"ƙanina kasan mi? " girgiza mashi kai shazim yayi,alamar a'a, ɗan nisawa mansoor yayi sannan yace "miyasa baka son yi aure yanzu, duk wani rufin asiri na duniya Allah ya baka shi, to miyasa bazaka godema ni'imar da yayi maka ba " kwantar da kanshi yayi saman kafaɗar mansoor sannan yace " yaya bawai bana son auran bane kwata kwata' a'a nafiso su ƙara man lokaci har nasamu wacce take sona nake son ta, amma yaya kowa yaƙi fahimta ta "
shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "karka damu bro ni na fahimce ka insha Allah suma su abbah zasu fahimce ka "
"Allah yasa yaya"
"Ameen "( a kwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin shazim da mansoor, mansoor ya girmi shazim bawai sosai ba, tare suka taso har makaranta tare suka yi )
"tashi muje part ɗin uncle Ibrahim dan nasan ba inda kaje tun da kazo "
"nayi baccine shiyyasa "
"ok tashi muje "tashi sukayi suka fice direct part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, bakin su ɗauke da sallama suka shiga,momy suka samu zaune kan sofa ita da aliyu, da gudu aliyu ya taso yayi hugging ɗin shazim yana faɗin "oyoyo yaya "ɗaga shi sama shazim yayi yana faɗin "haidar ykk,ya school"
"lafiya qlu yaya" masha Allah shazim ya faɗa haɗi da sauke shi ƙasa yana faɗin "momy anwuni lafiya "
"lafiya lau alhmdllh, ya hanya, yasu ammy da malam "
"lafiya qlu Alhmdllh "mansoor yace "momy ina wuni "
"lafiya qlu Alhmdllh, ya aiki "
"alhmdllh momy, uncle na ciki "
"eh yana part ɗin shi"
"ok bari mushiga momy " to momy tace sukuma suka nufi corridor dake kallon parlorn ,wani ɗan ƙaramin parlor suka shiga, shiru parlorn yake bakowa sai ƙarar tv da ta ac, mansoor ne yace su zauna may be uncle ɗin na ciki, zama sukayi kan sofa, muryar uncle Ibrahim su kaji daga bedroom ɗinshi cikin faɗa yana cewa "wannan ai maganar banza ce maganar wofi, amma kabani mamaki, to bari kaji tun wuri kasan yan da za'ayi " muryar wani matashi sukaji daga bedroom ɗin yana ba shi haƙuri "dan Allah dady kayi haƙuri, wlh mistake aka samu amma insha za'a dawo dasu, ko yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login