Showing 45001 words to 48000 words out of 133697 words
Chapter 16 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt
nayi magana da c.p dake chan yace suna nan suna bin ciken idan suka shige da sun samu zasu sanar da ni "
"da dai yafi, dan bazan yi asarar million dollars ba a bazan, in ma ban da shashan ci irin na yaran yanzu ina ake samun matsala irin haka ai tun chan ya kamata ka duba bawai sai kun zo nan ba "
"sorry dady insha Allah zasu dawo "
"Allah ya sa, ina so yanzu daka fita kasake kiran c.p ɗin kaji a wane mataki suke "
"to" fitowa saurayin yayi da wani kallon yabi su shazim dake zaune kan sofa sannan ya kama hanyar fita daga parlorn, mansoor ne ya daka mashi tsawa yana faɗin "kayi hauka ne luqman, sa'annin wasan ka ne mu daza kallemu ka wuce kafi ƙarfin ka gaishe da mune "
wanda aka kira da luqman ne yace "sorry yaya ban lura da kai bane "
"idan baka lura dani ba, baka ga shazim bane ko kafi ƙarfin ka gaishe da shi ne "
"a'a"
"oya koma ka gaishe shi kafin ranka ya ɓaci " juyawa luqman yayi ya koma cikin parlorn, sai da yaje har gaban shazim sannan ya ce "ina wuni ya hanya " idan har bango na magana to shazim ya amsa mashi gaisuwar, dan yi yayi kamar ma bai san da wata hallita ba wai luqman a parlorn, duk abun da ke faruwa uncle Ibrahim na tsaye bakin ƙofar badroom ɗin shi yana kallon su, sake gaishe da shi luqman yayi still bai amsa ba,gyaran murya uncle Ibrahim yayi, hakan yasa gaba ɗaya suka mai da hankali su kan shi ƙara sowa yayi cikin parlorn yana faɗin "shazim baka ji ana gaishe da kai? " maimakon shazim ya bashi amsar tambayar da yayi mashi sai ma cewa yayi "uncle anwuni lafiya" ganin ya waske ne yasa uncle Ibrahim amsa mashi gaisuwar yanama luqman alama ya tafi da ido , ficewa luqman yayi daga parlorn ( luqman ɗan uncle Ibrahim ne, shine babban ɗan shi sai feenah daga feenah sai sa'ada da aliyu, uncle ahmad kuma mansoor ne babba sai faisal daga faisal sai mahmud sai kairiyya sai salma )
Episode 22_23
Kallon shazim uncle Ibrahim yayi yana cewa "shazim ya su ammyn ku da malam?"
"lafiya qalau suke "
"to masha Allah, ya gajiyar hanaya "
"alhmdllh "
"ka shiga wurin innah kuwa? "
"a'a, daga part ɗin uncle ahmad nake, amma daga nan chan zan tafi "
"haba shazim ai tun da kuka zo chan ya kamata kufara shiga, bawai sai yanzu ba "
"haka ne uncle, na ɗan gajine to shine sai na ɗan kwanta "
"ah to gaskiya tashi ku tafi,inya so sai ku dawo "da to suka amsa haɗi da miƙewa suka nufi ƙofa, suna fita uncle Ibrahim ya ciro wayar shi daga aljihu dake ringing, picking yayi yanufi bedroom ɗin shi.
A bakin part ɗin innah suka tsaya shazim na faɗin " muna shiga da masifa zata tare ni nasani " murmushi mansoor yayi yana cewa "lamarin ka kai da innah ai sai Allah "
"ai big bro innar ce ta cika matsala "
"kai kuma baka ganin zarau sai ka tsinka "
"innar ce ai sai da irin haka "
"haka dai kace, wuce mu shiga karka ƙara bata lokaci tace da ka bari sai gobe " dariya suka kwashe da ita yayin da suke shiga part ɗin bakin su ɗauke da Sallama, feenah suka samu kan sofa tana charting a wayarta, tashi tayi zaune tana amsa masu sallamar da sukayi, zama su kayi kana sofa, sai kallon shazim take, shi kuwa tun da suka shigo ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, mansoor ne yace" ina innah take? "
"yanzu ta shiga ciki "
"ok ce mata gamu nan "
ta miƙe kenan sukaji muryar innah tana faɗin "dama kunyi tafiyar ku dan bana da lokacin ku yanzu nima"murmushi shazim yayi a zuciyar shi yana faɗin "sarki,baki taɓa shanye raɗa" kamar daga sama yaji muryar innah na faɗin
"kayi murmushi mana tun daga mahaukaciya sabon kamu na magana"
kallonta shazim yayi batare da yace komai ba, hakan dayayi ne ya harzuƙa ta daman a harzuƙe take
"kai ni daina kallona da waɗannan idanun ka, karka cinye ni "
da buɗar bakin shazim sai cewa yayi "dagama kin samu ina maki kallon love "riƙe haɓa innah tayi tana faɗin
" riƙe kayan ka bana buƙata "
"ke dai da kin karɓa " tsaki innah ta ja tana faɗin "sai yanzu kayi lokacin zuwa ka gaishe ni kenan, koko sai yanzu uwar taka tace kazo ka gaishe ni? "
"kusan haka, yan zunma sa'a kika ci har kika ganni "
"ba shakka mara mutunci, to koh ita uwar taka in tazo bata isa ba tace sai lokacin da ta gadama zata gaishe dani ba, bare kai "
"kuma fa hakane, dole ta gaishe da ke kamar yanda ke ma kike gaishe da magabata so ina ganin bawani abun tashin hankali bane"mamaki ne ya kashe innah takasa cewa komi, mi shazim yake nufi,ta shi shazim yayi yana faɗin "big bro ta shi muje bacci nake ji" sannan ya kalli innah yace "asuba ta gari tsohuwa mai ran ƙarfe" sannan yayi gaba abun shi sallama mansoor yayi mata haɗi da bin bayan shazim da harara innah ta raka shi tana faɗin " bauɗaɗɗe kawai maramunci " feenah ce tace innah "wai miyasa ya shazim yake maki haka ne?"
"mi yasa fa,ai ba komi bane face abun da uwar shi ta koya mashi, ai zanyi maganin su daga shi har ita dani suke magana"
suna fita part ɗin uncle ahmad suka wuce zuwa bedroom ɗin mansoor, zama shazim yayi bakin bed mansoor na tsaye yana waya shazim ne yace " nizan tafi na kwanta naga ka kama waya"
"ok sai da safe " ficewa shazim yayi ya nufi part ɗin su, yana shiga ya nufi bedroom ɗin shi kayan jikin shi ya rage ya shiga toilet, bayan minti biyar ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, clothes set ɗin shi ya nuf, pajamas ya ciro riga da wando masu taushi ya saka sannan ya nufi wayar shi dake haske alamar kira zama yayi bakin bed haɗi da ɗaukar wayar dan yaga mai kiran shi,majeed ne picking yayi
bakin shi ɗauke da sallama " on the other hand majeed yace "mutanen abuja, ya gajiyar hanya "
"alhmdllh majeed, ya aiki?"
"aiki alhmdllh, ina ka ajiye wayar kane ina ta kiran wayar ka bakayi picking ba "
" wlh kuwa majeed, time ɗin da kakira ina bacci ne dana tashi kuma naje part ɗin uncles ɗina ne,yan zu na dawo, ya ake ciki"
"dama maganar kayan da mukayi order ne sun iso "
"masha Allah, ka duba duk abun da mukayi order sun sako mana shi "
"eh na duba, sai dai akwai matsala"
"matsala, tami fah? "
"ina jin sunyi mistake ne, dan gaskiya kayan da mukayi order basu suka kawo mana ba amma ina tuna nin mistake ne suka samu, amma kakira kaji"
"ok to shikenan, amma abun da mamaki "
"wlh kuwa nima nayi mamaki sosai, musamman kayan dana gani a matsayi namu "
"wane irin kaya ne?"
"abun da mamaki, amma bari na turo maka kagani da idonka"ok kawai shazim yace haɗi dayin rejecting, ba'afi one minute ba sai ga saƙo ya shigo wayar, shiga cikin saƙon yayi,yana buɗe saƙon ya ci karo da kayan maye su cocaine, India he ga alcohol iri iri masu matuƙar tsada da haɗari ga lafiya ɗan zaro idanu yayi yana faɗin "ya Allah, miye kuma wannan , daga ina, na waye? " ɗan dafe kanshi yayi, sai kuma chan yayi dialing number majeed tana fara ringing yayi picking
"kanaji majeed, kasan mi za'ayi "
"a'a saika faɗa "
"kawai kusa su a store, ba sai an maida masu ba, ina son na san ko na waye "
"to shikenan, amma ya za'ayi da magungunan da suka kusa ƙarewa "
"karka damu zan sake ordern wasu, amma waɗannan ku bar maganar su kawai har sai na dawo sannan "
"ok to shikenan, sai da safe"
"ok mu tashi lafiya" yace sannan yayi rejecting ɗin kiran,tashi yayi yashiga toilet ya ɗaura alawala 2 minute ya fito ya nufi carpet ya shimfiɗa ya kabbara sallah, yana gama mawa ya ɗauki quran, ya shiga karantawa ƙarar shigowar message yaji awayar shi sharewa yayi sai ga wani message ɗin ya sake shigowa
bai koma takan wayar ba har sai da ya kammala karatun sannan ya ɗauki wayar ya nufi switch ɗin ɗakin ya kashe light nan take bedside lamps suka kawo,hawa yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe iya waist ɗin shi, sai sannan ya jawo wayar, message ya gani da baƙuwar number buɗa message ɗin yayi,yana gama karan tawa ya danna power yayi switching ɗin ta, adu'a yayi ya shafa sannan ya kashe bedside lamps, ƙara jan blanket yayi zuwa chaist ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi........
Washe gari
bayan ya dawo daga masallaci sallar asuba komawa yayi ya kwanta, sai wurin 8:30 ya tashi yayi breakfast bayan ya gama ya nufi part ɗin uncles ɗin shi domin gaishe da su,daya je part ɗin uncle Ibrahim, bayan sun gaisa yake tambayar shi yaje ya gaishe da innah kuwa, ce mashi yayi eh bayan bai je ɗin ba yace eh ne dan ya san cewa zai yi yaje, shikuma bai shirya ma tujararta ba tun da safe, yana fita daga part ɗin bedroom ɗin mansoor ya nufa, yana shiga ya same shi yana shirin tafiya office, gaisawa sukayi, sannan mansoor yace mi zai hana ya bishi su tafi office ɗin tare, bai yi gardama ba, dan shi kwata kwata baya son zaman gida kamar mace, shiyyasa a kullum yake ma noraiz faɗa saboda zaman gida, shiryawa yayi suka tafi tare,sai da yamma liƙis sannan suka dawo, a bakin ƙaramin gate ɗin estate ɗin mansoor ya hango feenah ta fito daga motar wani sauray, riga da wando ne a jikinta tayi rolling da ɗan ƙaramin gyale, sai waige waige take kamar tana tsoron wani ya ganta, kwata kwata bata lura da motar su ba tana sauri ta shiga , kallon ta mansoor kawai yayi har ta shige ciki sannan yace" narasa gane mike damun ya rinyar nan, amma zanyi maganin ta " shazim ne yace
"lafiya dai ko bro,kai da wa??"
" ni da feenah mana kana nufin baka ganta ba "girgiza kai yayi alamar a'a, sarai ya ganta amma sai ya fake a bai ganta ba, dan shi gani yake kwata kwata babu abun da ya shafe shi da lamarin feenah, tun da iyayen ta suna sane da abunda take, kuma tushen lalacewar ta daga kakarta ne tun da ita ke goya mata baya akan duk abunda take so, so mizai hana tayi abun da taga dama tun da ta samu ɗaurin gindin kakarta da kuma mahaifin ta.ta babban gate suka shiga, sai masifa mansoor yake, shazim na jinshi bai ce komi ba
suna shiga ciki part ɗin innah mansoor ya nufa, yana parking yace ma shazim ya fito su shiga su gaishe da innah, shazim yace "gaskiya ni nagaji zan wuce ciki, anjima na zo na gaishe ta kawai "
"miyasa bazaka shiga ba, duk fa yau bamu gaishe da ita ba yaka mata ace kazo mun shiga bafa wani jimawa zamuyi ba, dan nasan bawani anjimar da zaka zo, kawai ka fito mu shiga "
"nagaji ne bro, ka bari sai anjima "
"pls bawani jimawa zamuyi ba "ok kawai shazim yace ba dan yaso,ya so mansoor ɗin ya bari sai anjimar fitowa yayi haɗi da bin bayan shi suka shiga ciki,innah suka samu zaune a parlor mai aikin ta na mammatsa mata kafa,sallama su kayi haɗi da ne man wurin zama,gaishe da su mai aikin tayi, amsa mata sukayi mansoor na faɗin "barka da yamma innah, ya gida "
"lafiya lau, ya aiki"
"alhmdllh"
"shi wannan fanɗararen yafi ƙarfin ya gaishe ni ne "
"a'a innah, kin tari numfashin shi ne "
"bana ra'ayi ne yau "acewar shazim, hararar shi innah tayi tana faɗin
"riƙe kayar ka, bawai ina jiran taka ba"
taɓe baki yayi,yana faɗin"dama ance abun da baka samu haɗa shi da baka so " tsaki innah taja ba tare da ta sake cewa komi ba
sallamar feenah suka ji,yanzu sanye take da doguwar riga ta material maima kon riga da wando da suka ganta da su ɗazu a bakin gate , amsa mata sallamar sukayi,harara mansoor na watsa mata harara, gaban ta ne ya ɗan faɗin ganin hararar da ya ke jifanta da shi dan ita a sanin ta batayi mashi komi ba, wuri ta samu kusa da innah sannan ta kalli shazim tana faɗin "ina wuni Ya shazim "yi yayi kamar ma bai san da shi take ba,innah ce ta ja tsaki tana faɗin "Allah dai wadar mai wulaƙanta ɗan adam"banza yayi da ita duk da yasan da shi take, sosai sharetan da yayi ya sosa mata zuciya dan har idanunta sun tara kwalla, tana matuƙar son shazim amma sai wulaƙanta ta yake yana share ta kamar bai san daga inda ta fito ba, mai da idanun ta tayi kan mansoor tana faɗin "ina wuni ya mansoor "bai amsa mata gaisuwar ba sai ma hararar ta da yayi,innah ce tace "tofa yau ina ganin ikwan Allah, daga me shareta sai mai harara, kenan kai ma kakoyi baƙin hali irin nasu o'o "tsuke fuska shazim yayi dan ya san ba da kowa take ba face shi, kallon yan da ya tsuke fuska tayi tana faɗin "aikin banza aikin wofi,wai duk dan kar a raina shi" yanzu ɗauke kai shazim yayi kamar bai san dawa take ba, feenah da duk ta sha jinin jikinta, tace ma mansoor "Yaya mi nayi kake hararata "
"zaki sani ne"innah ce tace
"kai wai lafiya mansoor mi tayi ne"
"wlh sai na bata ɗan banzan kashi a gidannan "da buɗar bakin innah sai cewa tayi "ai sai ingani tun da kakoma zalunci"
"wai miyasa innah kike haka ne, duk ke ke ɗaure mata gindi take duk abun da ta gadama "
"to na ɗaure mata gindi sai aka yi yaya"kallon feenah mansoor yayi yana faɗin "wlh kinji na faɗa maki duk ranar da kika bari na kama ki jikin ki sai ya faɗa maki shashasha kawai"turo baki tayi tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri yaya ni ban san minayi maka ba "
"uban waye na ganki da shi yanzu a bakin gate, kinyi shiga kamar ba musluma ba "
gaban ta ne ya faɗin, dan bata yi tunanin wani ya ganta ba ,duk dan kar a ganta ne yasa tabiyo ta ƙaramin gate, kenan tanan shima ya biyo kuma hakan na nufin shazim ya ganta,ya salam, ƙatse mata tunani yayi ta hanyar cewa "tambayar ki nake? "
kame kame ta fara"am.... imm dama wani class mate ɗina ne "wanka mata mari mansoor yayi, ai ba shiri tayi bayan innah tana kuka, mansoor ne ya ɗaura da cewa "ni zakiyi ma ƙarya,saboda kin rainani, ban hanaki bin wannan ɗan iskan yaron ba,saboda ban isa in faɗa maki kiji ba shine kuka koma haɗuwa waje yana ajiye ki a baya dan kar wani ya ganki ko"fashewa ta sake yi da kuka tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri, wlh ba shi bane " hannu mansoor ya kai zai jawota daga bayan innah, kakkare ta innah tayi tana faɗin "wai miye haka mansoor so kake kaji mata ciwo ne, to wai ma miye a ciki dan ta kula shi kai waya san adadin matan da kake kulawa"duk wannan budiri da ake shazim na zaune yana daddana wayar shi hankali kwance kamar baya ɗaki,mansoor ne yace
"wlh ko mi feenah tayi laifin ki ne innah, tun da ke ke goya mata baya "
"eh na goya mata bayan sai aka yi yaya, da Allah ni ku tashi ku bani wuri"
"haka zaki ce innah? "
"Eh haka na ce, sai akayi yaya"
"to shikenan "shine kawai abun da mansoor ya ce yaja hannun shazim suka fice, da harara innah ta rakasu har suka fice , suna fita ta rufe feenah da faɗa ta inda taje shiga bata nan take fita ba, haƙuri take ba innah akan bazata sake ba insha Allah
"wannan kuma ke kika sani, kar Allah ma yasa ki daina, dan ni ba ruwana tun da duk abu da nake faɗa maki bawai yana shiga kunnen ki bane, abun da kikaga dama shi kawai kike yi"
"dan Allah kiyi haƙuri innah wallahi bazan sake ba, yan zun ma ban san zasu ganni bane "
"karma ki daina, kina ji kina gani zakiyi ma kanki tsiya da kanki, kuma wallahi muddun baki shiga cikin hankalin ki ba, shi wan da kike son kinaji kina gani zaki rasa shi, a banza"
"insha Allah na daina "
"da dai ya fiye maki ".
Shazim suna fita daga part ɗin innah part ɗin su ya wuce shi da mansoor
a parlorn shi suka ya da zango, mansoor ranshi duk a ɓace saboda feenah yasha hanata mu'amula da wannan saurayin amma ta ƙi daina wa saboda yasan halin yaron ɗan isaka ne amma bata ji,ga shigar banza iri iri ta iya, ta kasa gane abun da yake nuna mata,shazim ne ya fito daga bedroom ɗin shi ya cire kayan da yasa daga shi sai boxer da vest, dafa kafaɗar mansoor yayi yana faɗin "lafiya, tuna nin mi kake"ajiyar zuciya mansoor ya sauke yana faɗin "wallahi banajin daɗin abun da feenah take, ita kuma innah sai goya mata baya take "
"haba bro miyasa zaka damu kanka, duk fa wani abu da take laifin innah ne kuma uncle na gani"
"hakane shazim, amma da ban haushi kwata kwata innah bata kyautawa, ace yarinya na aikata ba dai dai ba amma ta hana a tsawatar mata "
"gaskiya kam bata kyautawa, amma da Allah ka share da komi ka je ka watsa ruwa "
"ok to shikenan "ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin "sai na dawo