Showing 18001 words to 21000 words out of 133697 words

Chapter 7 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8493

dariya " koke fah " ya fada hadi da cire facemask din da yasa MASHA ALLAH nafada daganin wannan kyakyawar fuskar ta Noraiz kamannin sa daya da fatima , dan dai shi namijine ita kuma mace.
ilya ne yakaraso inda suke yana washe baki Noraiz yace " kice tare kike da ilya Ammy " ya fada yana mikama ilya hannu domin suyi musabaha.
ilya yace " ina wuni, ya hanya, ya aka baro mutane turai " dariya fatima da Noraiz sukayi jin ilya yace wai ya aka baro mutanen turai, amsa mashi Noraiz yayi da " alhmdllh ilya ya gida " amsawa ilya yayi da " lafiya qlu " ilya yace hadi da daukar trolley din Noraiz suka bar wurin, parking lot suka nufa booth ilya ya bude ya saka trolley da jakar Noraiz, shiga sukayi cikin motar Noraiz da ilya naga ita kuma fatima na baya, key ilya yayi ma motar suka bar airport din, hanyar gida suka nufa suna tafe suna fira Noraiz ne yace " wai ina ya shazim fatima " amsa ta bashi da "may be yana gida , danni banjima da dawowa daga Islamiyya ba na biyo ilya" "ok " kawai Noraiz yace yayin da suka iso anguwar su horn ilya yayi time dinda suka iso bakin gate din gidan, megadi ne ya bude masu gate din, ilya ya danna kan hancin motar ciki, parking lot ya nu fa parking yayi, fitowa su kayi daga motar suka nufi cikin gidan, ilya na biye da su a baya hannun sa dauke da trolley da bag din Noraiz.
Shiga sukayi cikin gidan bakin su dauke da sallama
Da sauri Noraiz ya nufi shazim dake zaune kan sofa, hugging din sa yayi hadi da cewa nayi missing din ka yy sosai
shafa kansa shazim yayi kamar wani karamin yaro yana cewa " to ai yanzu komai ya wuce tun da gaka nan ka dawo"
" haka ne kuwa yaya " Noraiz ya fada
Ammy ce ta fito daga kitchen ita da Innah Asabe wurin su suka nufa Ammy nace wa" oyoyo mai babban suna " tashi Noraiz yayi ya nufi Ammy hugging dinta yayi yana cewa " nayi kewar ki sosai Ammynah " nima nayi kewar ka mai babban suna " Ammy ta fada, Innah Asabe ce ta matso tana cewa " marhabun lale mai babban mutum, ya hanya, ya kuma karatu " Amsa ya bata da " alhmdllh " nan suka shiga firar yau she gamo, ilya haurawa yayi upstairs domin kaima Noraiz kayan sa part din sa, baijima ba ya sauko yana cema kayan na part dinka nakaima maka.
godiya Noraiz yayi mashi, ficewa ilya yayi ya koma bakin gate wurin mai gadi dama nan take zama.


Noraiz ne yatashi yana cewa " zanshiga na watsa ruwa na fito naga time din sallah magrib yakusa" ya fada yayi da yake haurawa upstairs.
Ammy c tace " shazim abincin fa koba yanzu ba "
"A'a Ammy sai an jima in mun dawo sallar magrib sannan" to shikenan " Ammy ta fada , tashi yayi ya nufi upstairs shima
Ammy ma da Innah Asabe nasu bedroom din suka nufa aka bar fatima ta gyara kitchen da jera abinchi kan dinning ( sbd bata sallah ) tana gama wa itama ta nufi nata bedroom din wanka tashiga ( dama tana yin wanka kusan sau hudu arana intana period )


✨ _NORAIZ_ ✨


Fitowa yayi daga bathroom sanye da bathrobe ( part din sa shima ya hadu sai dai bai kai na shazim girma ba, amma dai masha Allah yayi kyau ) dressing mirror yanufa mai kawai yashafa ma jikin sa yanufi clothes set dinsa jallabiya ya dauko black color yasa wurin kayan sa da ilya ya kawo masa ya nufa, turare ya dauko cikin jakar sa ya fesa gadi da mai dashi
Ficewa yayi daga part din dama yayi alwala tun a toilet , part din shazim ya nufa dake kusa da nashi
yana shiga shazim din na fitowa daga bedroom din shima sanye ya keda jallabiya
Ficewa kawai sukayi suka nufi masallachin dake chan main gate din gdn basune suka dawo cikin gidan ba sai da su kayi har isha tukun suka dawo cikin gdn
parlorn Ammy suka yada zango fatima kadai suka samu zaune a parlorn suna zama sai ga Ammy ta fito wuri ta samu ta zauna tana cewa " to a tashi ga abinci chana najira " to suka cemata hadi da nufar dinning din Fatima ce tayi serving din su.......


✨ _KATSINA_ ✨


Zaune suke kan dinning suna dinner su duka gidan baka jin komai sai karar plate da spoon
Suna gamawa abie da abdallah da Mom suka koma kan sofa yayin da su Aairah ke gyara dinning din, suna gamawa wurin su abie suka dawo suka zauna fira suka shiga yi abie na tambayar su yaushe zasu fara exam din SSCE " saura 3 weeks abie " suka bashi amsa " to Allah ya bada sa'a, da Ameen suka amsa " abie wace school zaka kaimu in mungama " Aaimah ta tambaye shi" ban gane inda zan kai kuba , kuda kuke da school a cikin grinku, a i ba sai kunje wani gari ba " abie ya fada yana tsare su da idanu " A'a gaskiya abie Muyi primary school da secondary school a nan sannan kuma ace munyi high school a nan gaskiya abie s chanza mana " to sai dai kunga ma exam din tukunnan, to shikenan abei " chanza firar sukayi zuwa wata, sai kusan 9:30 sannan su Aairah suka nufi dakinsu sbd sun fara karatun exam gakuma zuwa school gobe
Suna shiga bedroom din su wanka sukayi hadi da sanya pajamas dinsu sannan suka dauki books dinsu suna dubawa sai wurin 12:00 sannan sukayi bacci.......
Episode 9_10


Sanye suke da uniform din su na school, ko wacce rataye da school bag din ta, ficewa su kayi daga bedroom din suka nufi main parlor su Mom suka samu kan dinning suma basu jima da zuwa dinning area ba, gaishe dasu su kayi hadi da samun wuri kan dinning din suka zauna, abie ne yace " yau yan biyu an shirya dawuri kenan " amsa suka bashi da " eh abie "
"to Allah ya taimaka ya ba da sa'a"
da ameen suka amsa, mom ta miko masu tea da ta hada masu " thanks Mom" suka fada hadi da sa hannu suka Karba, basu fi minti 10 ba suka tashi suna goge bakin su da tissue paper suna fadin sai mun dawo , a dawo lpy su mom suka yi masu fice wa su kayi suna fadin Allah yasa.


Suna fita daga gidan sai ga school bus dinsu ta shigo anguwar, sai da ta kawo dai dai inda suke tayi parking, kofar bus dince ta bude shiga su kayi daga ciki suka nemi wuri suka zauna kusa da wannan friend din ta su Aeesha
Aeesha tace "twin friends yau wace rana kun fito da wuri kun hau bus first round " ta fada da murmushi a fuskar ta " kedai bari kawai Aeesha sa'a ce kawi yau " Aairah tafada yayin da Aaimah ke cewa " sai kace kema kullum da wuri kike zuwa Aeesha " dariya Aeeshar tayi hadi da cewa " ai wlh duk da haka gara ni dai "
"bawani nan, wlh kema muguwar let comer ce " Aaimah tafa da yayin da bus din keshiga cikin School
bus stop, bus din tanu fa parking tayi aka bude kofar student nata fita suna nufar assembly ground
Inda ss 3 ke tsayawa nan su Aairah suka nufa annan suka samu sauran yan class din su wanda suka zo dawuri, gaisawa suka shiga yi.
bayan 30 minutes aka gama assembly kowa ya nufi class din su


✨SHAZIM✨


Saukowa suke daga upstairs shi da Noraiz parlor Ammy suka nufa, kan dinning suka same ta , gaishe da ita su kayi Noraiz yace " ammy ina fatima nagan ki ke kadai kan dinning? " amsa ta bashi da " Fatima ai ta wuce school"
" kai na manta fah, amma Ammy yau she take gama wa ne "
" tace man dai next month zasu fara exam, daga wannan week din ma ta gama zuwa school sai kuma exam "
" Allah ya taimaka ya bada sa'a, yaya " Noraiz ya kira Shazim dake zaune yana sauraron su, da na'am ya amsa mashi , Noraiz yace " amma dai yaya fatima a abuja zatayi university kamar yanda take bukata intagama secondary school "sai da yayi kusan 5 seconds sannan yace "A'a nan za tayi school din ta gata ga ammy, " ya fada fuskar sa babu a lamun wasa, hankan yasa dole Noraiz ya kama bakin sa yayi shiru amma baiji dadin shawarar da yayan nasu ya yanke ba, saboda fatima ta ƙwallafa rai akan zuwa abuja saboda sa'ada , " Allah ya taimaka " kawai yace yaci gaba da breakfast din sa, Ammy duk da ta fison fatimar tayi karatu kusa da ita.amma sai tace "wai shazim mi yasa kake haka ne, tun da kai ka janye jiki da abuja, mi yasa suma zaka sa dole sai sun janye jiki da abuja ne wai, miye ai bun dan tayi karatu a can, duk ni ma nafi son tayi kusa da ni" ɗan nisawa yayi sannan yace "ammy ni ba haka nake nufi ba, kwai naga zaki yi kaɗai ci ne, ke kaɗai a gida "katse shi ammy tayi da cewa "in dai dan ta nine karka hanata zuwa abuja, idan bata nan baga ku nan ba kai da noraiz "
"ammy mu ba zama muke ba, idan muka fita tun safe sai dare fa muke da wowa"
"to naji sai dare kuke da wowa, itama idan ta je makaranta ba sai da yamma zata riƙa dawowa ba? " ta ƙarasa faɗa da sigar tambaya tana tsare shi da idanu
"ammy dan Allah kiyi haƙuri tayi karatun ta nan, itama sai ta fi jin daɗi karatun, chan haya niyar innah kawai ta ishe ta " uhmm kawai ammay tace ba tare da ta sake cewa komi ba ,
Ba wanda ya sake magana cikin su har suka kammala breakfast din , shazim ne ya fara ajiye fork din da yake cin arish hannu ya mika ya yagi tissue din dake kan dinning ya goge bakinsa sannan ya dauki robar ruwa ya sha, ya mike ya nufi sofar da ya ajiye briefcase dinsa ya na fadin "Ammy nizan wuce" cup din tea din da ta kai baki ta janye tana fadin " a dawo lafiya , Allah ya ba da sa'a, an jima ka dan zanje gidan baba may be baza ka same ni sanda zaka dawo, dan zanjima kilama sai dare ma zan dawo "
" ameen, ina gaishe da malam, sai na dawo" ya fada yayin da yake shirin barin parlorn, Noraiz yace " a dawo lafiya Yaya, Idan na ajiye ammy gidan malam zan biyu ta wurin ka insha Allah "
" Allah ya kawo ka lafiya " kawai ya fada hadi da ficewa, parking lot ya nufa motarsa wacce yasa aka wanke masa ya nufa, bude kofar motar yayi briefcase din sa ya aje da lab coat, sannan ya zagaya driver seat ya zauna , key yayima motar ya nufi main gate , gaisawa yayi da ma'aikatan gidan sannan ya fice daman mai gadi yariga da ya bude masa gate,eko ya nufa yana tafiya yana sauraron karatun alqur'ani a motar....


✨HIDAYA✨


Tsaye take gefen titin anguwar su tana jiran abun hawa, kusan 5 minutes tana nan bata samu abun hawa bata samu ba, wata bakar motace ta shigo anguwar tasu, tunda motar ta shigo anguwar tasu take ma motar kallon kamar tasan mamalakinta, motar na ƙarasowa kusa da ita tana rage gudu, kallon motar kawai take sai da ta kawo dab da ita sannan aranta tace" wannan ai kamar motar dr kabir " parking motar a kayi hadi da sauke glass din motar, kyakyawan saurayine fari amma ba sosai chan ba, akallah zai yi kima nin shekara 28 zuwa 30, sanye yake da blue din kaya complete riga da wando sannan fuskar sa sanye take da glass, hidaya tace" ina kwana dr" amsa mata yayi da " lafiya lau , mikike yi tsaye anan " hidaya tace " ina jiran abun hawa ne dr" ok yace sannan kuma ysake cewa " to shigo ciki mu wuce "
" A'a dr katafi kawai zan samu abun hawa insha Allah " hidaya ta fada, glass din dake fuskar shi ya cire hadi da cewa " to fah, hidaya ko dai kina tsoron na sayar dake ne iye " murmushi tayi hadi da cewa " A'a ba haka bane "
ajiyar zuciya ya sauke hadi da cewa " to inhar ba haka bane, to kishiga mu wuce " to kawai tace hadi da zagayawa ta shiga ciki, key yayima motar yana cewa " wlh kina bani mamaki hidaya, sai kace wata ƙara mar yarinya in ki ka yi wani abun " murmushi kawai tayi masa ba tare da tace komai ba, haka sukai ta tafiya yana janta da fira har suka iso eko , parking lot din asibitin ya nufa hadi dayin parking, har tasa hannu zata bude kofa ya da katar da ita yana cewa " wai hidaya tsorona ki keji ne, naga har wani sauri kike ki fita"
"A'a " kawai tace hadi da duƙar da kanta ƙasa, " shikenan bakomi kina iya tafiya "ya fada ficewa tayi daga motar shikuma ya tsaya tatara kayan sa dake back seat, tana fitowa motar shazim na parking, dr kabir ne ya fito hannun sa riƙe da tarkacen sa yana cema hidaya su tafi , tafiya suke sunkusa kawo inda motar shazim take sai gashi ya fito,miƙa masa hannu dr kabir yayi sukayi musabaha, hidaya ta gaishe da shi, da lpy kawai ya amsa mata , wuce wa tayi tabar su shi da dr kabir tayi cikin asibitin, office din su da nurses kezama ta nufa, ba kowa ciki sai friend ɗin ta maryam da alama wadan da suka zo duk sun fita.
" lafiya yau ki ka yi late ? " maryam ta tambaya , ƙarasowa inda take hidaya tayi tana cewa "ke dai bari, banyi bacci bane jiya dawuri shiyyasa nayi late" dafa kafadar ta maryam tayi tana cewa " kingama yanke shawara yan da zaki tunkari dr da maganar koh "
" a'a gaskiya, maryam ina jin tsoro ne, ban san ya dr zai dauki maganar tawa ba " hannun hidaya maryam taja suka zauna sannan tace " ki kwantar da hankalin ki hidaya Insha Allah alkairi ne zai biyo baya, kinji" ajiyar zuciya hidaya ta sauke tana cewa " to Allah yasa haka maryam " da ameen maryam ta amsa mata hadi da cewa " tashi mufita" ta fada tana jan hannun hidaya, fice wa su kayi suka nufi inda yan uwansu nurses suke, gaishe da junan su suka shigayi , office din dr Shazim hidaya ta nufa tana cema maryam " sister bari naje office din dr na dawo"
"ok sai kin dawo " maryam ta fada, office din hidaya ta nufa hadi da tura kufar ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
amsa mata sallamar yayi, sannan tace "dr asa patient a layi " amsa ya bata da" eh " har zata fice sai kuma ta dawo sai da tayi 2_3 seconds sannan dai ta daure tace" afuwan dr dama ina so ne Muyi wata mgn " ɗago kansa yayi daga aikin da yake ya tsare ta da idanu alamar ina sauraronki, magana ta fara " dama dr maganar Victoria ce " daga mata hannu yayi alamar ya isa haka " ya zama na ƙarshe da zaki ƙara man maganar ta a nan, in ba haka ba kema zaki bita , fatan kingane "
" ok sir insha bazan sake ba " ta fada hadi da ficewa daga office din , direct wurin patient ta wuce, ta shiga aikin ta , a haka Victoria da destiny suka same ta, wuri suka samu suka zauna kusa da ita , gaisawa su kayi sannan Victoria tace " hidaya ya maganar mu ne" ajiyar zuciya hidaya tayi sannan tace " gsky kiyi haƙuri Victoria, ko yanzu daga wurin dr nake nayi nayi ya haƙuri amma yaki, dan har cewa yayi kona daina masa magnar ki ko nima ya koreni " wani kallon banza Victoria tayi mata sannan ta ce " munafukar banza, wannan nasan duk shirin kine, to kisani kamar yanda kika rabani da dr nima sai na rabaki dashi " mikewa hidaya tayi tana cewa" kije kiyi duk abun da za kiyi Victoria, tun da ke baki da mutunci " fada sosai ya kaure tsakanin su har Victoria na neman kaima hidaya duka, destiny na jenye ta, su maryam ne suka zo wurin saboda hayaniyar Victoria data jawo hankalin su, nan suka shiga cewa gsky baki da mutunci Victoria, komawa Victoria tayi kansu tana ce masu munafukai tasan ai da hadin bakin su, ai kuwa abun yayi masu zafi nan suka shiga maida mata da martani,


Hayaniya ce ta damesa harta na neman haddasa masa ciwan kai hakan tasa shi dole ajiye abun da yake yi, telephone ️ din dake office din ya dauka, dialing numbers yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login