Showing 117001 words to 120000 words out of 133697 words

Chapter 40 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8515

ƙofar ɗakin shi ya zauna .


Ciki shazim ya shiga,ba kowa a main parlorn , sama ya nufa zuwa part ɗin shi, yana tura ƙofar ya shiga wani ƙamshi ne ya bigi hancin shi,ba irin wanda ya saba jiba a ɗakin , wani irin ƙamshi ne gashinan dai, bin ko ina na ɗakin ya shiga yi da kallo sai gani yayi kamar an canza mashi fasali , azuciyar shi yace
"wannan wane irin ƙamshi ne " ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi nan ma ƙamshin yaji irin na parlorn, mai da ƙofar ɗakin yayi ya rufe , gaba ɗaya ƙamshin ya addabe sa dressing mirror ɗin shi ya nufa inda yake ajiye room fresh ya jawo ƴar locker room fresh iri iri a cikin locker, daya daga cikin su ne ya ɗauka haɗi da maida locker ya rufe, fesa room fresh ɗin ya shiga yi sai da ya tabbatar ya canza ma ɗakin iskar shaƙa tukun ya maida turaren wurin zaman shi, kayan jikin shi ya shiga ragewa, toilet ya nufa sai kamar bayan minti biyar ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani a hannun shi yana goge kanshi, ajiye towel ɗin yayi daya gama guge kansa,zama yayi kan kijrar dake bakin dressing mirror ɗin nan ya shiga shafe shafen shi sai da ya ɗauki kusan minti biyar zaune yana abu guda daga baya ya nufi corridor da wardrobe ɗin sa take,ash ɗin jallabiya ya ɗauko ya sa, komawa yayi bakin dressing mirror ya feshe jikin shi da turare, yana shirin barin wurin yaji anturo ƙofar bedroom ta ciki mirror ya zuba ido dan ganin wanene wannan daya fi ƙarfin yi mashi nocking, a iya sanin shi dai ko Ammy bata shigar mashi ɗaki babu nocking, turo ƙofar tayi ta shigo hannunta ɗauke da tray data shirya mashi abinci, zuba mata ido yayi yana kallonta ta cikin mirror har ta gama shigowa ta nufi ɗan table ɗin dake tsakiyar ɗakin ta ajiye mashi juyowa tayi tace " dinner ne na kawo maka " banza yayi da ita kamar ma bai san da zamanta a ɗakin ba, matsowa tayi kusa da shi kamar zata shige jikin shi tana fa ɗin " ya shazim wai minene matsalar, ina sonka kuma kaima nasan kana sona to banga wani abu aciki ba da zaka rinƙa wulaƙanta ni " baƙaramin ɓaci ranshi yayi ba wai yau wannan yarinyar ce ta samu power har ta iya tsayawa a gabanshi tana faɗa mashi waɗannan magan ganun, bai gama fita daga mamaki ba yaji ta kai mashi runguma ta baya 😲.......


_TASHIN SENS FEENAH WALLAHI BA RUWANA_




_Episode _60_61


...........................Please duk ka ajiye wani fushi a gefe da kake yi dani,abun da ya wuce ai ya riga da wuce " ta faɗa tana wani ƙara manne mashi ajiki haɗi da zagayo da hannunta tana shafa ƙirjinsa, ranshi ne yayi wani mumunnan ɓaci har bai san lokacin da yayi wurigi da ita ba bata faɗa kan komai ba sai kan table ɗin dake tsakiyar ɗakin gaba ɗaya ta faɗa kanshi tray ɗin da tashigo da shi ya kafa abincin da ta kawo mashi ya zube ajikinta, azabar zafin abincin da taji ne yasa ta fasa wata uwa ƙara gashi hannunta ya bugu sosai, bata gama dawowa hayyacin ta ba ya ɗago da ita wanke ta yayi da lafiyayyun maruka har sau huɗu tangal tangal ta shiga yi juwa ta kwashe ta sai ƙasa jikake tim ta faɗi ba ƙaramin buguwa ƙugunta yayi ba, fashewa tayi da wani matsannancin kuka tana faɗin " wayyo Allah nah momy zai kashe ni, na bani innah kizo ki taimake ni ya ɓallaman ƙugu "
tsawa ya daka mata yana faɗin " tashi ki fita ki bani wuri kafin ranki ya ɓaci" wani kukan ta sake fashewa da shi dan bazata iya tashi ba dan ba ƙaramin azaba take ji a ƙugunta ba gashi idanuwan ta bata wani gani sosai saboda marukan da yayi mata har jini ya kwanta gefan indanta na hagu,ganin bata da niyyar tashine yasa shi jan hannunta data bugu ƙiyyy ya jata har bakin ƙofa yana zuwa yayi wurgi da ita wani ihu ta kwala zaiyi wuya ace su Ammy basu ji ta ba dan kware baki tayi sai ihu take tana tabani ta lalace hannunta ƙugunta,maida ƙofar bedroom ɗinshi yayi ya rufe nan ya barta sai kuka take tana kiran su Kairiyya su zo su kawo mata ɗauki.


Noraiz ne ya shigo a sukwane jin ihun mutum, bai ɗauki murya ba ya dai ji ihu da kuke kuke sunyi yawa kuma a part ɗin yayan shi hakan ne yasa shi shigowa a guje,a nan durƙushe ya sameta sai kuka take
"wai wacece ke wannan ihun lafiya?, miya sameki?" bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma sake fashewa da wani kukan da tayi, su fatima ne suka banko ƙofar ɗakin har rigen rigen shigowa suke Ammy na bayan su, noraiz sai magana yake ma. ta amma taƙi shiru gashi bai gane ko wacece a cikin su ba bare ma ya san minene ke damun ta, sai da ya ga shigowar su kairiyya sannan ya fahimci cewa ita ce , tsaki yaja haɗi da cewa
" yo wai ashe ke ce ki ka wani addabi mutane da ihu, ai ba wani ya aiko ki part ɗin nasa ba koma mi yayi maki wallahi Allah ya ƙara " abun da yasa ya faɗi haka yasan dole ita da shazim ne wani abun tayi mashi har yayi mata
"wane irin sakarci ne wannan noraiz, bakaga halin da take ciki ba kake mata Allah ya ƙara kenan ma kasan abun da ya sameta?" Ammy ta faɗa yayin da take matsawa wurin feenah da kairiyya ke ta ƙoƙarin ɗagawa amma ta kasa saboda da ta ɗago feenahr take komawa saboda bata iya tashi
"yana wuce wani abu tayi ma ya shazim, tun da daman ya hanata shigo mashi part amma da yake ba jin magana take ba ai gata nan ta shigo "


noraiz ya faɗa yayin da yake ƙoƙarin juyawa ya nufi ƙofa, da katar da shi Ammy tayi ta hanyar cewa


"na ga kana shirin fita ina zaka ko bakaga halin da take ciki bane kuma yaushe shazim ɗin ya shigo gidan "


"na gani Ammy mi zan yi mata?"


"lallai noraiz tambayata ma kake yi ko"


"A'a Ammy mi zan yi mata to"


"kira man shi yayan naka da yayi mata haka, ai sai ya zo ya san yanda zaiyi da ita idan ma hospital zai kaita"
"
to noraiz yace haɗi da nufar ƙofar bedroom ɗin shazim ɗin yayi nocking shiru ba'a bashi izinin shigaba ba kuma a buɗe ƙofar ba,Ammy tace


"lafiya?"


"da alama dai bai ciki, dan ban ji motsin shi ba "


kallon feenah Ammy tayi tana faɗin " wai ma mi ya sameki da nayi tunanin ko ke da shazim ne?"


"Ammy shi ne ya mare ni ya kuma haɗa ni da table ɗin bedroom ɗin shi ko nan shine ya jeho ni "
sai da tayi magana tukun Ammy ta lura da jinin daya kwanta a gefan idon ta ga sawun hannuwan shi nan a fuskar ta ra ɗau, mi noraiz zai in ba dariya ba jin tace wai ya jehota, sa'ada ma ɓoyewa tayi bayan fatima ta sha dariyar ta, daƙuwwa Ammy tayima noraiz tana faɗin
"ya jeho ki dai ?, sai kace wasu kayan wanki " wata dariyar noraiz ya sake kwashewa da ita yana faɗin " kayan wanki fa kika ce Ammy " wani ƙululun baƙin ciki ne ya tukare feenah ganin yan da noraiz ya dage sai kwasar dariya yake yana mata Allah ya ƙara
" Noraiz wallahi zanci mutuncin ka kai da sa'ada, ku wane irin mutanene wai, tana wani hali kuna mata dariya saboda rashin tausayi "
" Ammy kina ji fa tace a bedroom ɗin shi ya mareta, in ba tsabar iskanci ba irin nata mi ya haɗata da bedroom ɗin shi " noraiz ya faɗa
tsaki Ammy taja haɗi da nufar bakin ƙofar bedroom ɗin shazim, nocking ta shigayi tana kwala mashi kira amma babu alamun ma yana ɗakin,
kallon feenah tayi tace " ko fita yayi? " girgiza mata jai feenah tayi tana faɗin " yana nan ciki, daya jeho ni waje mai da ƙofar yayi ya rufe " dariyace ta kusa kufce ma noraiz jin ta ƙara cewa ya jeho ta, da sauri ya sa hannu ya tushe bakin sa haɗi da sadda kai ƙasa
" shazim kana jina shine kayi banza dani ko saboda tsabagen rainin wayau ko " Ammy ta faɗa yayin da take sake nocking ɗin ƙofar still shiru babu alamun zai zo ya buɗe mata, ganin dai da gaske ba zuwa zai yi ba ya buɗe mata ba ne yasa tace su Kairiyya su kama feenah, haka su ka talalla bata kamar kayan wanki da take faɗi su ka fice noraiz na bayan su yana dariya mara sauti dan gudun kar Ammy ta ji shi, haka su ka saukko da ita daga saman stairs un expected su ka hangi shazim kwance saman sofa three seater ya ɗaura hannun shi na dama saman kanshi yayin da hannun shi na hagu yake saman cikin sa da alama ma bacci yake jallabiyar da yasa ce ɗazo a jikin shi , abun har so yayi ya ba feenah tsoro tun da ita dai ta san lokacin da ya fito da ita bedroom ɗin shi ya koma abun mamaki kuma gashi a parlorn Ammy, Noraiz ne yayi surin cewa "to ga ya shazim a parlor kin gani kenan ƙarya take da tace shine ya mare ta Ammy " zuba shazim ido Ammy tayi baccin shi kawai yake kwasa abun shi hankali kwance,zama kusa da shi Ammy tayi tana kiran sunan shi haɗi da bubbuga hannun sofar, duk abun da ke faruwa idon shi biyu yana jin su, sai da Ammy ta dake kiran sunan shi tukun ya buɗe ido yana kallon ceiling sai da ya ɗau sakanni sannan ya mai da duban shi ga Ammy
"lafiya na ganka nan kwance?" Ammy ta jefa mashi tambayar, ɗan ya tsine fuska yayi haɗi da yun ƙurawa ya tashi zaune
"kai na ne keman ciwo shine na sha magani na kwanta "
"Amma shazim mi feenah tayi kayi mata haka?"
"wacece kuma feenah?" ji wani tambayar rainin wayao nan wurin shazim
"ok baka ma santa ba "
"Ammy naji kina wata magana ne bayan ni tun da na dawo ina nan kuma ni banga kowa ba, shiyyasa na tambaye ki " fashewa feenah tayi da kuka tana faɗin
" wallahi ya shazim mun haɗu ba dinner naje kai maka ba kuma ma ai tray ɗin yana bedroom ɗin ka " hannu Ammy ta ɗaga ma feenah tana faɗin " ya isa haka feenah, yanzu kai ai sai kaje da ita medical room ka du ba hannun ta "
tashi yayi yana faɗin " Ammy cewa fa nayi kai na keman ciwo, bazan iya duba kowa ba a yanayin da nakeji kai na noraiz ya kaita asibiti " yana gama faɗa ya kama hanyar tafiya part ɗin shi
"tafiya ma kake?, kayima yarinyar mugunta sannan kace baza ka duba ta ba "
wai gowa yayi yana faɗin " bana jin daɗi ne Ammy kuma ni ban ma san akan mi kike magana ba " yana gama faɗa ya haye sama, da kallo kawai Ammy ta bisa tasan ƙarya yake shine ya dake ta amma zai ce wai bai ma san akan mi take magana ba
"Kairiyya ku ka mata zuwa waje noraiz ya kaita asibiti, kai kuma maza ka ɗauko key ka kaita asibiti " ammy ta faɗa tana kallon noraiz da ke tsaye, turo baki yayi yana faɗin
"Ammy ni bacci nake ji " ko kallon shi Ammy bata yiba tace " ku fita da ita kunji, gani nan zuwa "
da to su ka amsa haɗi da nufar waje da ita, Ammy kuma bedroom ɗinta ta nufa , ganin shirin ɗauko key take ta kai feenah da kanta yasa noraiz bin bayan ta yana faɗin
"dan Allah kiyi haƙuri zan kaita da kai na " ko kallon shi bata yi ba ta shige bedroom ɗin , wardrobe ɗin ta ta nufa buɗewa tayi ta ɗauko hijab sannan ta koma wurin dressing mirror ɗinta locker dake ji ta jawo key ɗin motar ta dake ciki ta ɗauka,
"Pls Ammy wallahi zan kai ta " roƙonta yayi tayi sai da ƙyar ya samu ta bashi key ɗin , tana bashi ya fita a tsaye ya samu su fatima riƙe da feenahr sai ruri take tana kuka yan ƙara so wa wurin su yace
"Allah ko kiyi mana shiru ko wallahi na koma, ƴar rainin wayau kawai wani ya aike ki ɗakin shi da zaki ta wani cika ma mutane kunne " ya faɗa haɗi da nufar motar Ammy da ke parking lot, da harara feenah ta raka shi duk buguwar da tayi bai hanata rashin kunya ba, fito da motar yayi zuwa compound in da su ke tsaye sa'ada ce ta nufi motar ta buɗe ƙofar baya su Kairiyya su ka shigar da ita, kairiyya ce ta zauna a baya tare da feenah fatima kuma ta shiga gaba, sa'ada ta koma ciki dan ɗauko masu hijaban su saboda duk cikin su babu mai hijab sai fatima ita ma gama sallar ta kenan taji ihun feenah,bayan kamar 5 seconds sai sa'ada ta fito hannunta riƙe da hijab ɗin kairiyya da ta feenah,miƙa masu tayi su ka amsa sannan ta koma ɓangaren da feenah take ta shiga ya zama sun sata a tsakiya ita kairiyya, reverse noraiz yayi ya nufi gate da tun fitowar shi ya sa mai gadi ya buɗe masu, ficewa yayi daga gidan hanyar Abnoor ya ɗauka idan su ka zo in da za su sha kwana da mugunta yake shan kwanar dan duk ya sha kwana sai fennah ta saki ƙara, sa'ada dariya kawai take kwasa a zuciyar ta tana faɗin


" Allah ya ƙara maganin mai shishigi kenan, mutum yace baya so to ina dalilin maƙale mashi, in dai ya shazim yanzu kika fara gani "
haka tai ta ma feenah dariya da Allah ya ƙara har su ka iso Abnoor, horn noraiz yayi mai gadi ya buɗe mashi ya shiga da motar ciki,parking yayi yana gama daidaita parking yace su sa'ada su kama ta su shiga ciki, fitowa su kayi har da fatima su ka kamata sai ɗangesa ƙafa take har su ka shiga ciki yayin da shi kuma yake bayan su, sun shiga nurses ɗin dake night su ka amshe ta,noraiz ne yaje office ɗin majeed ya sanar da shi abun da ke faruwa da yake yau bai tashi da wuri ba,
"Ya salam " majeed ya furta haɗi da cewa " shazim baya gida ne?"
" yana nan baya jin daɗi ne shiyya sa bai duba ta ba"
" amma wane irin rashin jin daɗi ne wannan da har zai hana shi duba patient " abun da yasa majeed ke faɗin haka noraiz ce mashi yayi faɗowa tayi daga bene koma yana zargin ta karye shiyyasa duk hankalin majeed ya tashi.
"muje na ga jikin nata" majeed ya faɗa yayin da yake tashi daga kan kujerar da yake, fice wa yayi noraiz ya
biyo bayan shi har inda feenah take sai uban kuka take kamar yarinyar goye, nurses ɗin da ke wurin duk haushi ta ba su kawai abun da yasa su kayi shiru su ka ƙyaleta tana cika masu kunne saboda kawai sun ganta tare da masu asibiti amma da ta sha masifa


_*kun san halin wasu nurses ɗin namu ko yawan kuka su ka ga mutum nayi yanzu zai sha masifa su ce bai da dauriya bayan suma fa ba ita gare su ba*_


majeed na ƙara sowa tambayar ta ya shiga yi mike damun ta ina da ina ne ta bugu , bata bashi amsa ba sai sake ɓare baki da tayu tana wani kukan , noraiz ne yace


" dallah malama an magana, idan kuma ba inda ke maki ciwo mu tashi mu kuma gida "


"da kata noraiz saboda mi zaka yima ihu bakaga sai kuka take ba dole akwai inda ke mata ciwo kuma ka ce faɗowa tayi daga bene ba "


"haka ne faɗowa tayi " ya faɗa fuska a ɗaure shi a dole gaskiya ya faɗa, jin abun da yace ma majeed ne yasa feenah buɗe baki tace


"wurgi ya shazim yayi da ni har na faɗa kan table hannun ya bugu da ƙuguna amma ba faɗuwa nayi ba "
norai a ranshi yace " shashasha ana so a rufa mata asiri amma da yake bata san ciwan kanta ba take tona ma kanta asiri sai kace wani abun arziƙi ne dan ta sanar da ya majeed ya shazim ne ya ji mata ciwan"


tsaki yaja sannan a zahiri yace " ka rabu da ita kawai ya majeed ka duba ta ka gani ko ta samu karaya a ƙugunta dare yayi " ihu feenah ta sa jin noraiz na faɗin ko ta samu karaya, abun ma har so yayi ta ba majeed dariya, in ba sharri irin na noraiz ba yaushe daga wannan faɗuwar zata karye kuma a ƙugu


"ya isa haka dan Allah noraiz " nurses ɗin dake wurin yasa su ka kamata zuwa emergency room,cikin ƙanƙanin lokaci majeed ya shiga du bata daya kama hannunta sai ta fashe da kuka,hakan yasa ya gane cewa ta samu targaɗe ne a hannun,wurin gayran targaɗen sai da ta so ta tara mashi mutane da dai ya gaji tsawa ya daka mata yana faɗin wallahi ko dai tayi shiru ko kuma ya ƙyaleta da ciwan, nurses ɗin da ke ciki suna taimaka mashi tsaki kawai su ka ja duk ta ba su haushi sai kace ba mace ba wata cewa tayi
" zanga ranar da kika zo haihuwa ƙila ranar mutuwa zaki dinga yi kina dawowa"
"ai kam dai" harara kawai feenah ta maka ma su
"yo ashe abun iskanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login