Showing 15001 words to 18000 words out of 133697 words

Chapter 6 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8489

lokaci inzai dawo, wai kuma yanzu sai yamma tukun, Allah ka shirya mai babban suna kai dai, ameen Ammy ya fada hadi da tashi ya nufi dinning, warmer din dake kan dinning din ya shiga bu dewa yana duba abun da ke cikin su. cup ya dauka ya hada tea sannan ya zu ba arish, wurin Ammy ya dawo ya zauna suna fira shi da Ammy yayin da shi kuma yake cin abincin sunjima suna fira har aka fara kiran sallar zuhur sannan su ka tashi Ammy ta nufi dakinta shi kuma ya nufi part din sa domin yin alwala.....


✨ _HIDAYA_ ✨


Flat house ne me kyan gaske Masha Allah na masu rufin asiri kutsa kai nayi cikin parlorn gidan wanda komai na cikin sa brown color ne, hidaya naga ni zaune kan dinning ta lunch ita da mahaifiyar ta kamanin su ɗaya, tashi hidaya tayi mahaifiyar ta tace " mi ki ke nufi, naga kin tashi ? "
" na ƙoshi ne mama" wai ni kam hidaya mike da munki ne, a ce kwata kwata mutum baya son cin abinci, ko baki da lafiya ne,"
" lpy ta kalau mama, dan nayi breakfast a makare ne , amma lafiya ta qalau, to shikenan, bedroom din ta ta nufa, kayan jikin ta ta cire ta shiga toilet ta dan jima sannan ta fito jikinta daure da da towel, dressing mirror din dake dakin ta nufa simple make-up tayi sannan ta nufi wardrobe din dake kusa da dressing mirror din, gwon ta dauko ta atamfa da mayafi, shiryawa tayi cikin kayan Masha Allah dan bakaramin kyau kayan sukai ma fatar taba, da yake hidaya chocolate ce ita ba faraba sannan ita ba baka ba, wayarta dake kan bed ta dauka da jaka wurin da takalmanta suke ta nufa ɗan flat shoe ta dauko tasa , fice wa tayi daga dakin bedroom din ta nufi na mamar ta zaune ta same ta kan gado sallama tayi hadi da cewa" mama zan tafi gidan su maryam" mama tace " to shikenan sai kin dawo ina gaishe da hajiya lubabatu, sannan karfa kiyi yamma kinsan dai Baban ku yana gari, insha Allah mama bazan jima ba zan dawo, to saikin dawo fita tayi daga bedroom din hadi da ficewa , a bakin gate ta tsaya tana neman abun hawa bata jima ba ta samu napep shiga tayi sannan ta yima mai napep din kwatancen anguwar da zai kaita, tafiya sukayi mai dan nisa balaifi sannan suka iso wata anguwa bakin gate din wani gida yayi parking me napep din fita tayi hadi da bashi kudinsa ya wuci ita kuma ta nufi gidan, mai gadi ta samu zaune akan ɗan benchi, gaishe da shi tayi, ya amsa mata yana faɗin "yasu mama ku, suna lafiya da alama ya santa shiga tayi cikin gidan, part biyu ne gidan daya daga ciki part din ta nufa shiga tayi tai parlor gidan yake kamar ba kowa wani dan corridor ta nufa ɗakuna ne kusan guda hudu ƙofofin su na kallon juna wanda, ke farko ta shiga bedroom ne mai kyau , bed ne sai wardrobe da toilet da dressing mirror, ba kowa dakin sai karar ruwa daga cikin bathroom alamar a kwai mutum a ciki wuri tasamu gefen bed din ta zauna batajima da zama ba sai ga maryam ta fito daga bathroom daure da towel " a she dai zaki zo maryam din ta fada , wlh kuwa , zan zo mana, ykk ya gida ya su mama, lpy qlu suke maryam ta fada hidaya tace " bakowa ne gidan sai ke kadai? "
" A'a suna nan , kawai dai suna ɗaki ne, ok, naji shiru ne da na shigo , A'a suna nan bari dai nasa kaya dai" maryam ta fada haɗi da nufar wardrobe, kaya ta dauko riga da skirt na martial , shaf shaf ta shirya sannan ta dawo wurin hidaya ta zauna tana fadin " wai ni kam sister ya kuka kare da Victoria kinsan tun ranar da ku kayi fada da ita, bamu sake wata magana ba, ya kuka kare naga dr ya mai da ki wurin ta, kin kuwa san dadin da naji, domin nasan insha Allah burinki ya kusa cika" hidaya tace " bakomi , bamu sake wata magana da ita ba da sunan sa in sa ba, dan har roƙuna su kayi ita da destiny akan na taya ta bama dr hakuri ya maida ta wurin ta, to ke saikika ce mata mi? Maryam ta fada ta na tsare ta da idanu , hidaya tace " mazan ce kuwa maryam, tun da ta roƙe ni mi zai hana, amma wallahi hidaya baki da hankali sai kawai kije kice ma dr dan Allah yayi ma Victoria hakuri koh, uhmmm ko dai yanzu kin haƙura da shi ne baki son sa yanzu? Maryam ta jefa mata tambaya hidaya tace " wlh maryam bazan boye maki ba ina son dr har zuciyata, to amma shine zaki taya ta kuma kinsan cewa son shi take, dama kawai take jira ta raba shi da kowa , to ya zanyi maryam, komi tayi dan kanta tun da har ta roƙeni zan taya ta mana,maryam tace " uhmm sannu uwar masu tausayi tun da ta rokeki ai sai ki bashi haƙurin, wlh ke ba kisan wacece Victoria da destiny ba, su kan su muna funtar junan su suke yi inma baki sani ba to kisani ita kanta destiny din son dr take muna funtar Victoria kawai take, shiyyasa kike fadan haka ni da na daɗe dasu ni zan baki labarin ko su su waye garama tun wuri ki mai da hankalin ki a kan dr ki kyale wata Victoria da destiny chan , amma fa inkinji shawarata, dan wallahi kika tai make su, sai kinyi dana sannin haka, amma fa inkinji, shikenan ngd sosai da shawarar ki , amma sister sai nake ganin kamar dr bazai soni ba, kina ganin in ya shigo hospital duk matan dake hospital din bamu isheshi kallo ba, amma zan ciga ba da rokwan Allah in har shi alkairi ne a rayuwa ta Allah ya tabbatar man, to ameen, amma ya ka mata kisanar dashi cewa kina son sa, ko ba komai zai san ke masoyiyar sa ce, koya kike gani, zanyi kokarin haka insha Allah, amma gaskiya ina tsoron abun da zai biyo baya karma ya zo ya da katar dani kamar yan da yayi ma Victoria , abun da bazan soba kenan
Maryam c tace " to idan baki fada masa ba taya zai gane kina son shi , ki fada masa kawai insha Allah ba abun da zai biyo baya sai Alkairi kuma insha Allah zan taya ki da adu'a, smeen sister nagode sosai Allah ya barmu tare, ameen karki damu maryam ta fada chanza firar su kayi zuwa wata suna nan zaune har a kayi sallar asr , sallah suka tashi su kayi sannan suka fita daga dakin suka nufi parlorn gidan


Wannan kenan..........


✨ _Ammy_ ✨


Zaune take kan sallaya a bedroom dinta bata jima da gama yin sallah ba wayar ta da ke kan dressing mirror ce tayi ringing hannu tasa ta dauko wayar murmushi tayi hadi dacewa "Allah sarki mai babban suna ina jin ya kara so, daga wayar tayi hadi da Kara wayar a kunne sallama tayi da murmushi a fuskar ta, on the other hand na cikin wayar yace wa'alaikumus salam my Ammy ya gida, lafiya lau mai babban suna ya hanya, alhmdllh ammy mun kusa sauka insha Allah , nan da Karfe 5:30 shiyyasa na kira ki fada ma ilya yazo ya dauke ni na kira Yaya bai dauka, may be baya kusane Ammy ta fada" to Ammy ki fada ma ilyan, yanzu kuwa Allah dai ya kawo ku lpy, ameen Ammy wlh harna ƙosa na ganni kusa da ke, Allah dai ya dawo da kai lafiya, ameen ya fada, kashe wayar tayi , mike wa tayi daga kan sallayar parlor ta fita kan sofa ta zauna , number ilya ta shiga nema cikin wayar ta sai ga fatima ta dawo daga Islamiyya wurin Ammyn ta nufo hadi da cewa " barka da gida Ammy, mikike yi zaune ke kadai s parlor? , ta fada yayin da take samun wuri kusa da Ammy ta zauna, amsa Ammy ta bata da "number ilya nake nema saboda zai dauko mai babban suna , ya noor ya dawo ne ta fada hadi da mikewa harzata nufi upstair Ammy tace " dawo uwar zumuɗi cewa nayi zai dauko shi bawai ya dawo ba" da wowa tayi tana turo baki gaba hadi da cewa "to Ammy ƙarfe nawa zai dawo , Ammy tace" ƙarfe 5:00 insha Allah jirgin su zai sauka, shiyyasa yace a kira mashi ilya yaje ya dauko sa;; Ammy dan Allah zanbi ilya inzai tafi, cewa Ammy tayi" to shikenan maza kije " bata ma tsaya sauraron mi Ammy zata ce ba ta nufi dakin ta da sauri, wanka ta fara shiga bata jima ba ta fito sanye da bathrobe shaf shaf tashirya cikin doguwar riga abaya tayi rolling da gyelen a kanta, wayar ta kawai da jaka ta dauka ta fice daga dakin inda tabar Ammy nan ta sa meta, ƙara sowa fatima tayi wurin ta tana fadi" yawwa Ammy na shirya kinyi ma ilyan magana " A'a bari nayi sai kin shirya tukunnan , ai a kwai sauran lokaci, duka yanzu ƙarfe 4:00 kuma kinga cewa yayi sai 5:30 jirgin zai sauka
Ammy ai da kinyi mashi magana, kinsan fa a kwai nisa Airport din zamu yi kusan 20 to 30 minutes bamu kai ba fah kuma ga go slow" Ammy tace "haka ne nasha'afa ne shiyyasa amma bari na kira ilyan ya fitar da mota sai ku tafi ta fada yayin da take kiran ilya a waya yana picking tace " ilya ka fitar da mota zakuje Airport kai da fatima domin dauko mai babban suna yana hanya, to Ammy insha Allah yanzu kuwa zan fito da ita ilya ya fada da yake shima Ammy yake cewa, to shikenan ga fatimar nan fito wa Ammy ta fada hadi da rejecting din kiran, mike wa Fatima tayi hadi da cema Ammy sai sun dawo a dawo lafiya Ammy tayi mata sannan ta tashi ta nufi , kitchen innah Asabe ta samu a kitchen din tana gyarashi domin fara shirye shiryen dinner , Innah asabe na ganin ammy tace " barka da fitowa hajiya, da yawwa Ammy ta amsa mata" kina bukatar wani abune ? Innah asabe ta fada saboda ganin Ammyn datayi a kitchen a wannan lokaci " eh kinsan mai babban suna na hanya to shine nake son a daura dinner tun yanzu , kuma shima shazim bai ci komai ba ya fita ga fatima ita ma kuma, kinga in aka gama da wuri zai fi ai, innah asabe tace"ah yaufa muna da babban bako,shiyyasa naga fatima ta wuce da gudu dan bata ma lura da niba Ammy tace" kinsan halin Fatima da zumuɗin, ai ina ce mata yana hanya duk tabi ta rude tana chan tabi ilya Airport, dariya Innah Asabe tayi hadi dacewa" Allah dai ya kawo shi lafiya, ameen Ammy tace shirye shiryen daura dinner suka shiga yi..


✨ _SHAZIM_ ✨


shigowa yayi main parlor bakinsa dauke da sallama, da alama daga waje yake baya cikin gidan, su Ammy dake kitchen suka amsa mashi sallamar, fitowa Ammy tayi daga kitchen din tana cewa" kai ashe baka gidan, ka kuwa yi waya da ƙanin ka? ya ce man ya kira wayarka baka dauka ba "
" Eh na ɗan fita ne tun dazu har bedroom din ki nazo na same ki kina bacci, wayar na silent ne sai daga baya naga kiran sa, yace man ai kunyi waya akan kitura mashi ilya ya dauko shi, eh Ammy ta fada hadi da Komawa kitchen din shikuma part dinsa ya nufa, bedroom dinsa ya wuce kayan jikin sa ya rage ya nufi toilet bayan kamar 15 minutes sai gashi ya fito sanye da bathrobe dressing mirror dinsa ya nufa hadi da zama kan stool din dake gaban mirror din, ya jima yana yan shafe shafensa sannan ya nufi wardrobe , shiryawa yayi cikin kana nun kaya riga da wando, wandon baki iyakar sa gwiwarsa sai rigar fara mara nauyi mai gajeran hannu, wurin dressing mirror ya koma feshe jikin sa yayi da turare sannan ya fita daga bedroom din ya nufi down stairs parlorn Ammy, dinning ya nufa yaga bakomi, fita yayi daga parlorn ya nufi kitchen wurin su Ammy yana shiga yace " Ammy akwai abinci, yunwa nake ji, gashi nan ana girkawa saura ka dan mukarsa Ammy tafada, gaskiya Ammy bazan iya jiraba sosai nake jin yunwar babu wani abu koda mara nauyi ne? Ya tambaya, Ammy ta ce" bari na yanka maka fruit ta fada hadi da bude fridge ta dauko fruit ta wanke yanka mashi tayi ƙanana ta zuba mashi a ɗan bowl ta mika mashi amsa yayi hadi da cewa " nagode sosai Ammy sannan ya fice daga kitchen din, main parlor ya koma TV ya kunna hadi da daukar remote yana chanza channel zuwa TVC news, zaman shi yayi kan sofa yana shan fruit tana kallo
Wannan kenan............


🌹~ _KAINAAT_ ~ 🌹


_MURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL AIRPORT


Mutane ne iri iri wasu najiran time din da zasu hau jirgi, wasu kuma sun zo daukar yan uwan sune, wasu na cikin mota wasu na zaune akan chairs din da aka ta nada domin masu zama.
Motar su fatima ce ta kara so cikin airport din parking lot din dake wurin ilya ya nufa parking yayi, fatima ce tabfara fitowa sannan shima ya fito, cikin airport din suka nufa inda mutane ke zaune fatima ta nufa, wuri ta samu ta zauna , wayar ta da ke cikin bag ce ta fara ringing fito da ita tayi "YA DR" shine sunnan daya bayyana akan screen din wayar, picking call din tayi hadi da sallama, on the other hand nacikin wayar ya amsa mata sallamar " ina wuni ya dr , ya gida ya kwana biyu, lafiya lau Alhmdllh Bintalo, turo baki Fatima tayi cikin shagwaba tace" haba Yaya nace fa bana son sunnan amma baka dai na ceman ba, ta fada tana dan bubuga kafafu, dariya na cikin wayar yayi, ai kuwa nan tashiga yi mashi kukan shagwaba tana cewa " dariya ma na baka koh"
"sorry fatimaaaaaa" ya fada hadi da jan sunan,
Uhmmm kawai tace,
sake mgn nacikin wayar yayi "bana ce kiyi hakuri ba, ai duk laifin kine kinsan fa nace kibar ceman ya dr nan da kika kware wurin kirana dashi, shiyyasa nima nace maki haka kinga nima na rama kenan, amma kiyi hakuri bazan sake ba kinji" "shikenan Yaya ya wuce"
"Yawwah koke fa, yasu Ammy kina ina ne haka naji hayaniyar mutane?
amsa ta bashi da " Ina airport , munzo daukar ya noor ne "
" ok yau zai dawo kenan, kice ina gaishe dashi ina mashi ya gajiyar tafiya "
" to zai ji Insha Allah yaya "
" ok take care of your self for me pls, bye" ya fada, itama " bye" tace masa hadi da rejecting call din, game ta shiga bugawa a wayar tana nan zaune aka fara sanar war iso war jirgin 5:30 tashi tayi ta koma inda mutane ke tsai tsaye domin tarbar yan uwan su passengers ne suka fara biyo wata kofa da aka rubuta EXIST da manya harafi wacce domin su aka tana de ta fatima dai na nan tsaye, mutane kuwa wanda suga yan uwan su nata rugawa da gudu suna tarbarsu, ita dai sai zare idanu take sokawai take taga ta ina ya noor din ta zai bullo. Wani matashin saurayi ne ya bullo jikin sa sanye da ƙananun kaya jeans and T -shirt na company gucci, jaka rataye a kafadar sa baka jikinta an rubuta ADIDAS da farin paint da manyan haruffa, hannun sa rike da trolley yana ja P-cap ce a kansa sai face mask akallah zai yi kimanin shekara 25 a duniya.
Fatima ce ta rugo da gudu tana fadin ya NOORRR tana nufar wannan saurayin, sakin trolley din dake hannun sa yayi fa dawa tayi jikinsa tana dariya hadi dacewa " shine kawani boye face dan nasha wahala wurin gane ka koh " janye ta yayi daga jikinsa yana cewa " Autar Ammy kedai haryau Allah baisa kinsan cewa kingirma ba koh, fatima tace " haba ya Noor haka ma za kace koh, shikenan tunda baka yi farin ciki da ganina ba " ta fada hadi da juyawa zata bar wurin, hannun ta ya riko yana cewa " sorry my yar qanwerh, wasa fa nake maki, kema kinsan nayi farin ciki da ganin ki autar mu " ya fada hadi da jan kumatunta tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login