Showing 69001 words to 72000 words out of 133697 words

Chapter 24 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8516

cewa fatimar bata jin daɗi ba ya dai roƙi ta bar su su dawo yau amma tace a'a, ganin bazata haƙura bane ya sa shi yi mata sallama, mai da akalar kiran yayi ga malam bugu ɗaya malam ya ɗaga yana faɗin "likita bokan turai ka shige abuja ba a ko jin ɗuriyar ka "
"ai insha Allah ina nan dawowa yau "
"Allah ya nuna mana "da ameen ya amsa yana faɗin "na kira ammy na faɗa mata yau zamu dawo ta ƙi amincewa wai sai dai ni na dawo ni kaɗai "
"To ai ba wani abu bane dan ka baro su can, sai su dawo da kan su "
"ba wai barin su bane matsala malam, su gwaggo Uwani suna kuma kasan halin ta da ya ranta shiyyasa bana son su zauna musamman fatima, dan ko jiya ban san mi ya haɗa suba har sai da su ka yi sana din tashin ciwan ta"
"Subahanalilahi, yanzu ya jikin nata "
"taji sauƙi, ina tsoron abun da zai biyo baya ne yasa nake son mh dawo tare "
"E gaskiya ya kamata ku dawo tare, ku shirya ku tahu zanyi magana da Aishar "
"To shikenan malam mun gode, sai mun dawo " Allah yasa malam ya faɗi sallama suka yi, kiran noraiz yayi awaya yace ya same shi a ɗaki, ko da yazo ce mashi yayi ya haɗa kayan shi yau zasu koma lagos, da fara ko uziri noraiz yafa kawo mashi akan ya bari sai gobe ko monday, ganin babu wasa a fuskar shazim ne yasa shi kama bakin shi yayi shiru.


Cikin parlorn su ka shigo hannun su ɗauke da basket, dinning area suka nufa, feenah ce ta fito da flaks ɗin abinci tana jerawa kan dinning
Jin motsin mutum ne yasa fatima fitowa parlorn, ganin su feenah yasa ta tsayawa a bakin ƙofar ɗakin ta, Ilham ce tace" ke zo nan " banza tayi da ita " ke bada ke nake magana ba " banza fatima ta sake yi da ita ganin bazata zo bane yasa Ilham tashi ta nufe ta " ke har ni zan kira ki kiyi banza da ni " da buɗar bakin fatima sai cewa tayi " eh nayi banza da ke ɗin sai aka yi mi " da sauri feenah ta ƙara so tana faɗin "lallai wuyan ki ya isa yanka " hannu Ilham tasa zata ɗauke fatima da mari bata kai da kai mata marin ba taji saukar lafiyyen mari a fuskarta har sau biyu, ɗago da fuskar ta tayi tana kallon shazim da ke tsaye gaban su, feenah zata buɗe baki tayi magana kenan ya ɗauke ta itama da wani a zabeben mari har saida ta dafe ƙarfen bene dan ba ƙaramin maruwa suka yi ba" ya shazim mi mukayi ka ma... " bata ƙarasa ba yasake ɗauke da mari ganin haka ne yasa Ilham watsawa da gudu ta nemi hanyar fita , magana ya fara cikin kakkausar murya "wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da wata banza a cikin ku zata sake ɗaga hannu ta daki fatima" yana gama faɗa ya wuce ta nan tsaye dafe da kumatu tana kuka, fatima ɗakin ta ta shige ta turo ƙofa, Ilham ce ta dawo ganin shazim ya fita ta kama hannun feenah suka bar part ɗin........
_Episode 36_37_


........ Ilham ce ta dawo ganin shazim ya fita, ta kama hannun feenah suka bar part ɗin zuwa part ɗin Innah, feenah sai kuka take kamar wata ƙaramar yarinya, gwaggo Halima su ka samu akan sofa a parlor da cup a hannun ta tana shan kunun gyaɗa, da sauri ta juyo tana kallon feenah da ke ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya "ku kuma lafiya daga ina haka?"
basu bata amsar tambayar da tayi masu ba, sai ma neman wurin zama da su kayi kan sofa, feenah har wani ƙara ɗaga murya take duk dan innah da gwaggo uwani su ji su fito
"wai ku ba da ku nake magana ba,ke kuma ko ki man shiru ko wallahi na make maki baki, sakar yar banza kawai" Ilham tace " mama ya shazim ne fa ya same mu yayi ta marin mu baji ba gani "
"wani iskancin kuka yi mashi ko "
"ba abun da muka yi mashi, abinci kawai muka je kai mashi shine ya haumu da mari "
"ke Ilham ƙarya kike shazim ba zai mare ku ba haka nan dole da abun da kuka yi mashi, kuma ma ko ba abun da kuka yi mashi ya mare ku yayi man dadai dan kun cancanci fiye da haka " jin abun da gwaggo Halima tace ne yasa feenah ƙara sautin muryar kukan da take, sai Aunty maryam ta faɗo parlorn kamar an jehu ta "mi nake ji, ba dai wannan mara mutuncin ba ne ya mare ku"
tsawa gwaggo Halima taa daka mata " ke maryam ki shiga cikin hankalin ki na ƙara jin kin faɗi wani abu a nan ranki zaiyi mumunnan ɓaci shashasha kawai kema"
turo baki maryam tayi tana faɗin
"haba Aunty mi yasa zaki ce haka, du ba fa kiga fuskar feenah duk sahun hannun shi, in ban da zalinci mi suka yi mashi har haka "
gwaggo Uwani ta fito tana faɗin "wallahi bai mari banza ba "
gwaggo Halima tace "yaya sai dai fa ki ga laifin shazim, amma ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba su ke da laifi "
"dama haka zaki ce tunda da man ba son ganin laifin shi kike ba "
"Wai miyasa a kullum kike cewa, ina goyan bayan shi ne, ni ba goyan bayan shi nake ba kawai ina goyan bayan gaskiya"
" to ai sai ki ta goyan bayan gaskiyar, amma wallahi bai mari banza ba sai ya gane kuskuren shi "
"to shikenan in dai shazim ne ga kai ga fata "
"Wallahi Aunty laifin su " sa'ada ta faɗa wacce shigowar ta part ɗin keknan,juyawa su kayi su duka suna binta da idanu, gwaggo Uwani ce tace" munafuka ubanwa yasa bakin ki daga shigowar ki " turo baki sa'ada tayi " wallahi ba ƙarya nake ba,Aunty Ilham ce ta mari fatima kawai dan tayi magana bata jita ba, ita kuma Aunty Feenah tasa ɗan kwalinta ta shaƙe mata wuya bayan tasan tana da matsalar numfashi "
tafa hannu gwaggo Halima ta shiga yi tana salallami " yanzu da kashe ta ku ka so yi kenan, dan uban ku ku sau nawa mutum ke maku magana kunayin banza da shi bayan kuna jinshi , wallahi da ni na riƙa ku da sai kun yaba ma aya zaƙinta mutanen banza kawai "
gwaggo Uwani tace "ke yanzu kenan harkin yarda da maganar wannan shashasha yarinyar "
"dole na yarda da ita dan na san sa'ada bazata yi masu ƙarya ba"
Feenah tsagai tawa tayi da kukan da take ta kalli sa'ada tana faɗin "wallahi kika bari na kama ki sai kin gane baki da wayau " duka gwaggo Halima ta kaima feenah "dan ubnki idan kin kama ta kiyi mata bungun da zata kasa tashi mar mutunci, kuma wallahi daga ke har Ilham ɗin sai nasa Usman yayi maganin ku "
" a kan mi zaki haɗa su da shi, duk wannan marin da wannan mara mutuncin yayi masu bai isa ba "
"ai mai sauƙi yayi masu, gara nasa usman yayi masu dukan da ko wani su kaga zai dake ta sa hana, bari ma kiga yanzu zan kira shi "
"a'a sadiya kar ki kira shi a bar zancen kawai ya mutu "
"idan har kinga zancen ya mutu to sai idan ita fatimar ce tace ta yafe masu "
"wallahi baza ki ja masu raini a wurin yarinya ba, tun da dai zancen ya wuce a barshi kawai "
" idan fa ba ita tace zancen ya wuce ba to fa bazai wuce ba, sa'ada kira man fatimar " da to sa'ada ta amsa haɗi da fita,ko da taje part ɗin shazim ta samu a parlor, gaishe da shi tayi, harta miƙe zata nufi ɗakin fatima yace mata bacci take saboda maganin da ya bata, koma wa tayi part ɗin Innah , ganin ta dawo ita kaɗai ne yasa gwaggo halima tace " ina fatimar take "
"ya shazim na samu a parlor yace bata jin daɗi ya bata magani bacci take"
"to yaya kin dai ji ko, har sun kaita ga kwanciya, wallahi ko suje har part ɗin su bata haƙuri ko yanzu nasa Usman yayi maganin su "
"dan Allah dai ki ƙyale su,tun da harya bata magani zata ji sauƙi ne "
"sai fa sunje sun bata haƙuri, idan ba haka ba kuma tam"
"ba inda zasu, wai ke sadiya mi ke damun ki, to kisa usman ɗin ya dake su " innah ta faɗa wacce shigowar ta kenan daga part ɗin uncle Ahmad
"mama dukan fatima fa su kayi bayan sun san tana da matsala "
"koma mi su kayi mata baza su bata haƙuri ba "
"shikenan mama, amma bana jin daɗin abun da kuke yi "
"dallah ni yiman shiru tun da baki san ciwan ƴaƴan ki ba "
"Allah ya huci zuciyar ki " kawai gwaggo halima ta faɗa haɗi da tashi ta shiga kitchen, zama innah tayi kan sofa hannu ta miƙa ma feenah " zo nan ƴar albarka dai na kuka zai gane bai da wayau, yi shiru kinji " matsowa tayi kusa da innah ta ɗaura kanta saman kafaɗar ta "kar ki damu sai yayi dana sanin marin da yayi maki har ita munafukar fatimar, Allah dai ya kaimu anjima" lallashin feenah innah tai tayi har sai da taga ta shiru.


✨SHAZIM✨


duk wani shiri da zai masu na tafiya yau ya kammala , shi ka ɗai yake kiɗan sa yake rawar sa, bayan mansoor ba wanda yasan da shirin shi na tafiya yau jira kawai yake su uncle su yi taron su da yamma su kuma su wuce, fatima ce ta fito daga ɗakin ta parlor ta nufo har kan sofar da take kwance, gaishe da shi tayi sannan tace mashi za ta je part ɗin uncle Ibrahim ta ɗauko kayanta,da to ya amsa mata haɗi da ce mata kar ta saki ta daɗe, to tace ta fice zuwa part ko da ta shiga ba kowa a parlor ɗakin sa'ada ta shiga samunta tayi zaune gaban dressing mirror tana shafa powder zama fatimar tayi kan gado tana kallon sa'ada da ke kallonta ta cikin mirrorn
"Wai lafiya sister kike kallo na kamar baki sanni ba "
"Fatima ai dole na kalle ki, wai daga bari ki ɗauko magani shikenan ko "
" wai dama dalilin da yasa kike man wannan kallon ne "
"Ok tambaya ta ma kike "
ganin kamar ran sa'ada ya ɓaci ne yasa fatima cewa"sorry, ya shazim ne yace na kwana can "
"Ok ya jikin na ki "
"da sauƙi "
"Allah ya ƙara sauki, yau ɗin zaku tafi?"
"yanzu ma kaya na nace mashi zan ɗauko"
"ok naso ace ya shazim ya bari ko da zuwa gobe ne "
"nima naso amma ya zanyi" fira su ka shiga yi duk akan tafiyar da su fatima za su yi sa'ada kamar zata yi kuka, anan fatima tayi wanka , bayan sun shirya ita da sa'ada sallah su kayi batan sun gama ne su ka nufi ɗakin momy , da sallama su ka shiga momy na zaune kan carpet ta gama sallar, jiranta su kayi har ta kammala, fatima tace "ina wuni momy"
"lafiya lau fatima, ya jikin ki "
"naji sauƙi"
"to Allah ya ƙara sauki, kiyi haƙuri kinji"
"bakomi momy"
"momy wai ya shazim yace zasu tafi, dan Allah kice ya bar fatima nan shi ya tafi "
"A'a gara dai su tafi, kuma ma fatimar ba makaranta zata fara zuwa ba "
"eh momy amma ai da sauran lokaci "
"duk da haka dai "
"momy baki son su tsaya ne "
"kinci gidan ku " turo baki sa'ada tayi tana faɗin "dan Allah idan kina so su tsaya ki roƙi ya shazim ɗin pls"
" sai kuma kiyi"
" shikenan momy tun da baza ki ba shi haƙuri ba bari na faɗama dady shi sai ya bashi, dama dady bai san zasu tafi yau ba " ( da yake suna gida shi da uncle Ahmad ) ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi ƙofar fita
" kika saki ko ƙafar ki ta taka waje sai ranki ya ɓaci dan baki da hankali bai faɗama dadyn ku ba shine ke zakije ki faɗa mashi kin dawo kin zauna kafin ranki ya ɓaci "
da wowa tayi tana turo baki " momy to dan Allah ke ki bashi haƙuri ya barta "
"Kima daina yi man magiya,gara su tafi ko itama ta huta "
ba yanda sa'ada bata yi ba amma momy tace bazata ce ma shazim ya bar fatima ba, har part ɗin uncle Ahmad su kaje nan ma sai da sa'ada ta roƙi mama kan tasa baki shazim ya bar fatima amma ita ma tace ba ruwan ta, tama fiso su tafi dan sarai tasan halin su gwaggo Uwani a ka bar fatima wahalar su kawai zata sha kafin su tafi.


Kamar yanda su uncle Ahmad su kace zasu yi meeting a yau, basu fasa ba yanzu ma haka sun hallara a babban parlorn da su ke meeting, Innah ce kawai sai su gwaggo da su uncle ba yaran, tattaunawa su ka fara daga bisani uncle Ahmad yace ayima Zainab magana tattaro kan ƙannanta, a waya gwaggo Halima ta kira ta, zaman jiran shigowar yaran su kayi,Aunty zainab ce ta fara shigowa sai Aunty maryam da Amina da Asma'u,Farida sai Fiddausi, kairiyya da su fatima ta shigo sa'ada na ɗauke da salma ƙanwar kairiyya ce, feenah da Ilham suka shigo wuri guda matan su ka zauna sai mazan
ya usman tare ya shigo da su Anwar, Mahammad, mahmud, luqman, noraiz, faisal, mubarak, Umar, musa harda ƙananan Aliyu da Aminu duka mazan sun hallara mutum biyu ne babu shazim da mansoor, ganin babu su ne uncle Ahmad yace "usman ina sauran ƙannan naka"tun kafin yace wani abu gwaggo Uwani tayi carabtace " na san dai mansoor zai shigo wannan mara mutunci sai dai wani daga cikin ku yaje ya kira shi amma bazai zo ba " gwaggo Halima tace " yaya baki ganin zarau sai kin tsinka, yanzu idan ya shigo ɗin batare da wani ya kira shinba fah "
ta buɗe baki kenan zata mai da ma gwaggo Halima amsa, sai ga mansoor ya shigo da sallama a bakin shi shazim na bayan shi, jikin shi sanye da baƙin wando cargo sai t_shirt fara, kallon gwaggo Uwani gwaggo Halima tayi tana faɗin "to yanzu gashi nan ya shigo " tsaki gwaggo Halima tayi batare da tace komi ba, wuri su shazim su ka samu kusa da su usman su ka zauna,uncle Ibrahim ne yace Faisal ya buɗe masu taro da adu'a, tashi Faisal yayi yayi adu'a bayan ya gama ya koma mazunin shi ya zauna,sallama uncle Ahmad ya fara sannan ya ɗaura da nasiha , kowa ya baza kunne yana sauraron shi har ya gama nasihar da ya fara sannan yace " a taƙaice dai maƙasu dun wannan taro ba komi bane face a kan maganar ranar da muka tsaida ce ta auran wasu daga cikin ku, tun tuni munso ace an kammala komi ranar auran kawai muke jira, sai dai hakan bai samu ba dalilin wasu da basu shirya ba a cikin ku muka ɗaga masu ƙafa zuwa wani lokaci, wasu sun gabatar da waɗan da suke so wasun ku kuma har yanzu shiru, yanzu dai munyanke hukuncin tsaida rana ga duk kanku da wanda suka gabatar da wanda su ke so da wanda su kayi kunnan uwar shegu da maganar,dama ɗaya ce zan ba ma wanda basu gabatar da zaɓin su ba tuntuni shine yanzu su gabatar mana, idan ba haka ba zamu zaɓa masa duk wanda ko wacce ta dace "
ɗan nisawa uncle Ahmad yayi sannan ya ɗaura da cewa" shazim da mansoor sai faisal ina magan ne a kan ku,tun a wancan lokaci na yi maku magan akan ku gabatar man da zaɓin ku amma shiru, abun da nake so na sani shine baku da raɓine ko kuwa wani abun kuke nufi na da ban, to kun daiji mi nace yanzu idan kuna da magana muna sauraron ku kafin mu zartar da hukuncin da muka yanke, muna sauraron ku " tun da uncle Ahmad ya fara magana su ka sadda kai ƙasa, kowa dake parlorn zuba masu ido yayi domin yaji abun da zasu ce,faisal ne yace " ni ina da wacce nake so "
Uncle Ibrahim ne yace "to muna sauraron ka"
"uncle dama farida ce " shiru su kayi basu ce komi ba,fiddausi kamar tayi kuka jin mansoor ya ƙicewa komai, shi kuwa mansoor so yake shazim ya gabatar da wacce yake so duk da yasan da wahala , uncle Ibrahim ne yace " muna sauraron ku kunyi shiru,ko kawai mu cigaba da abun da ya tara mu " da sauri Mansoor yace"uncle ni ina da wacce nake so" ajiyar zuciya ta sauke jin yace yana da wacce yake so
Uncle Ibrahim yace " to masha Allah kana iya faɗa mana wacece "
"dama uncle ba kowa bace Fiddausi ce " murna kamar ta kashe Fiddausi jin mansoor ya ambace ta
" to masha Allah"
Uncle Ahmad ne yace " to saura kai shazim muna sauraron ka "
ɗagowa yayi ya kalli uncle ahmad sai kuma ya sake mai da kanshi ƙasa, tsit kowa yayi jiran abun da shazim zai ce kawai su ke, tsawan 4 minutes shazim baice komi ba
"to idan na fahimta har yanzu baka fitar da zaɓin naka ba kenan"
sai a sannan ya buɗe baki yace "a'a uncle "
"to muna sauraron ka "
"ina so a ƙara man lokaci,bayan na su mansoor sai ayi nawa "
"wannan ne baka isa ba shazim,da cewa mu ƙara maka lokaci yau kusan shekara kenan, sai yanzu kuma ka sake cewa mu ƙara maka wani lokacin abun da bazi yuwu ba kenan "
Uncle Ibrahim ne yace " to yanzu dai munji ra'ayin wasu daga cikin ku,mansoor ya gabatar da Fiddausi a matsayin zaɓin sa faisal farida, Muhammad dama tuntuni mun san ya gabatar mana da kairiyya a matsayin zaɓin sa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login