Showing 3001 words to 6000 words out of 133697 words

Chapter 2 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8486

ya faɗa tare da cewa "bari naje nayi breakfast ɗin sai na dubasu"
"ok muma ga mu nan sakkowa"tashi yayi ya fice ya nufi dining, tunkafin ya isa yake jin hayaniyar Aaimah da Aairah sunata zagaye dining Aairah ta ɓatama Aaimah baby jiba da tea itakuma Aaimar nacewa saita rama shine fa suke ta zagaye dining baaba larai sai cewa take su bari amma ina kamar ƙara zugasu take.


Tsawa abdallah ya daka masu tare da cewa "ashe ku shasha shune ban sani ba, zaku dawo ku zauna ko sai ranku ya baci sakarkarun banza da wofi, wallahi kushiga hankalin ku kullum girma kuke amma ɗabi'un ku sak na yara. bashiri kowace cikin su ta nemi wurin zama, baaba larai ce ta matso zatayi serving ɗin ya abdallah tana faɗin " abdallah an tashi lafiya"
"lafiya lau baaba, ina kwana," Alhmdllh tace "mizan zuba maka"
"a'a kibarshi kawai baaba Aairah ta zuba man,"
"to shikenan ni bari nawuce kitchen"
Aairah yace ma tayi serving ɗin sa ita kuma Aaimah tayi sauri ta chanzo hijab ɗin ta tunda sungama breakfast ɗin su , to tace haɗi da tashi ta nufi bedroom ɗin su.


Abie ne ke saukowa shi da mom hannun ta riƙe da jakar kayan sa , "abie kafito " ya abdallah ya faɗa ayayin da yake kar ɓar jakar kayan a hannun mom,yana faɗin "abie muje koh" yayin da yake fita daga parlorn , bayansa suka bi har da Aaimah wacce sakowarta kenan daga bedroom ɗin su dataje chanzo hijab,"adawo lafiya, alhaji Allah ya kiyaye hanya yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" "ameen ya rabbi baaba larai" abie ya bata amsa, fita sukayi compound ɗin gidan wurin motar abie suka wuce wacce baka driver ya daɗe da fito da ita dan har ya abdallah ya saka ma abie kayan shi a booth ɗin motar bankwana suka shigayi su Aairah har da hawaye abie sai lallashin su yake.


abdallah ne yace" dan Allah abie ka kyale yarannan sai sun sa kayi late", "kuyi hakuri bazan jimaba zan dawo may be na dawo nan da 2 days kunji" "to abie Allah yatsare hanya"
ameen abie yace
abdallah ne yace "to kuwuce ciki ku ɗauko school bag ɗin ku na ajiye ku a school, abie Allah ya tsare" ya faɗa haɗi da tasa keyar su Aaimah zuwa ciki, mom ce ta matso kusa da abie tana cewa "wallahi barrister kamar kar ka tafi nake ji"
" tofah yara shagwaɓa uwa shagwaɓa toni wazan kama" ya faɗa yana dariya "uhmm kaima kasan wanda zaka Kama" ta faɗa tana ɓata rai, "yau naji shiyyasa kenan kika ƙi magana sai da yaran ki suka shige ciki zakiyi man adawo lafiya , ashe shagwaɓa za'ayiman ban sani ba ", mom tace "ok hakama zakace "ta faɗa haɗi da juyawa zata nufi ciki , hannun ta abie ya riƙo yana faɗin "Sorry kubrah, kema kinsan wasa nake , karki damu bazan jima ba zan dawo insha Allah"


"to shikenan Allah ya dawo man da kai lafiya" ameen abie ya faɗa yayin da yake shiga cikin mota sit ɗin baya ya zauna bala driver na gaba key yayima motar, hanu mom ke ɗaga ma abie shima yana ɗaga mata,suka nufi gate,buɗe masu gate baba mai gadi yayi yana faɗin a dawo lafiya " mom na nan tsaye har sai da motar tafita daga gidan sannan ta juya tashiga ciki , dasu Aairah tacikaro suma sun fito a dawo lafiya tayi masu tawuce ciki abdallah ne ya sauko daga upstairs part din sa
Yana ce masu ku wuce mu Tafi.


🌹~KAINAAT~🌹


Fita sukayi wajen mota suka shiga abdallah ya jasu gate suka nufa wanda tun fitar abie baba megadi yabar masu shi buɗe gaishe dashi suka yi ya amsa yana masu adawo lafiya da ameen abdallah ya amsa yayin da suke fita daga gidan,
abdallah ne yace" dama ana duka school ɗin ku wallahi dasai nasa yau anmaku dukan tsiya. "
"dan Allah ya abdallah kayi hakuri bazamu ƙara ba"
"kundai ci sa'a kawai ba'a duka da kungane kuranku yau da daga yau bazaku sake baccin safe ba, ace wai kuna bacci har school bus tatafi kuga yan hutu koh"


Kayi hakuri dan Allah wallahi baza mu ƙara ba"
, "ni da'allah kuyi man shiru sai bada hakuri sai kace masu tuban gagaskiya bayan nasan ƙarawa zakuyi" ya faɗa yayin da yake hawa kan titin ring road in da nan ne school ɗin su take bakin gate ɗin school ɗin yayi parking tare da cewa "kufito kuwuce ciki, fita sukayi suna yi mashi adawo lafiya Allah yasa yace motar yayi ma key yabar wajen tare da Kama hanyar hospital ɗin da ya


Episode 3_4



.


LITTLE ANGELS PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL. shine sunan school ɗin
Kamar yanda school uniform ɗin suka kasance pink and white color haka paint ɗin school ɗin shima pink and white color ne.
Cikin school ɗin suka shiga Masha Allah school ce mekyan gaske ta yayan masu arziki Upstairs ce makarantar wanda ya kasan ce down na yara up kuma na manya ne, up stairs suka nufa domin an daɗe da gama ASSEMBLY shiyyasa suka nufa class, S. S. 3 shine class ɗin su , shiga sukayi ciki for master ɗin su suka samu yana ma shirin fita domin ya gama abunda ya kaishi.


"Aairah And Aaimah Muhammad hashim , why are you coming late" for mastern ya faɗa, Sorry sir we have wake up too late that the reason why we came to school late and it will never Happen again Aaimah ta faɗa yayin da Aairah ke ta bata fuska irin tafi ƙarfin ta bashi amma sa.


this should be the last, get sitet for mastern ya faɗa hadi da fita daga class ɗin .


Kallan juna sukayi haɗi da kwashewa da dariya, Aairah tace Why are you coming late tana kwai kwa yona maganar for master ɗin , dariya suka sake kwashe wa da Ita,
Aaimah tace this should be the last. wannan karan duka yan class ɗin ke dariya.


Sit ɗin su suka zauna suna cigaba da dariya,
Allah ya shirya ku twins domin yanzu abun naku sai adu'a mu samma make Aairah da uncle Hamza na magana sai wani harar sa kike," bazaki gane bane "Aeesha" Aairah ta faɗa wacce akakira da Aeesha tace to ganar dani.


"Ke wallahi haushi uncle hamza ke bani dafa Ina masa kallon mutumin arziki ashe dan banza ne, baki ji munce ya dai na zuwa gida yi mana lesson ba, Ai korar sa ya abdallah yay, saboda abun da ke kai shi bashi yake yiba, Ko kunya baijiba yace wai yana son Aaimah sai kuma yana lesson kiga yana kokarin taɓa ma mutun hannun ai kuwa rannan ashe duk abun da yake faɗa a kunnan ya abdallah, shine fa ya kore shi yace karya Kara ganin sa, to Wallahi inta kaice maki komu dukan da mukasha wurin ya abdallah sai kin tausaya mana dan Wallahi buguwa mukayi kamar gangar church kuma mom tace ba ruwan ta gashi abie baya gari, shiyyasa innagan shi Nake jin kamar na shaƙe sa"Aairah ta faɗa tana hura hanci, Allah ya shirya sa to Aeesha ta faɗa , Ameen dai.
be silent biology teachern su ne yace haka wanda shigowar sa kenan yasame su sunata surutu, natsuwa suka yi suna sauraron lesson ɗin dayake masu.


_F. M. C MEDICAL CENTER_


zaune a office ɗin shi da ke Amenity, waya ce a kunnan sa da alama waya yake.
"haba dude ai dole nace haka tsawan shekarar mu nawa muna tare ace baka taba ziyarta taba su mom ma a suna ka ɗai suka sanka sai waya, ai tare bata ce haka ba amma nasan maganin ka zan haɗa ka kawai da ammy ne nasan ita zata saka kazo ba dan kashirya ba konasa mom takiraka may be kazo ya abdallah ne ya faɗi haka,, On the other hand nacikin wayar yace,, sorry my man ba haka bane nima ina san zuwa to ayyuka ne suka min yawa shiyyasa amma insha Allah ina nan zuwa very soon,, ai nima ina da tarin ayyuka amma Nake ajiye su na ziyarceka,, inkuma Sai zanyi aure zaka zo inji to, duk da in zanyi sai tare da kai don ina samun mata zan haɗa ka da ammy kaima ka fito da taka ko aba da kai sadaka" abdallah ya faɗa yana dariya.
"haba kaima kasan wa za'a ba da sadaka Indai aure zakayi bisimillah ban hanaka ba amma ni ba yanzu ba.
"shikenan tun da kai bazaka chanza ba kullum ace mutum amsar sa ɗaya, ina gaishe da su ammy "ya abdallah ya faɗa .
"zasuji insha Allah nima ka gaishe man dasu mom kace mata ina nan zuwa very soon "
"Allah yasa domin kuwa na san halinka,"
Karka damu dude zan zo insha Allah, to shikenan sai anjima , abdallah ya faɗa , ok nagode sai anjima kashe wayar yayi shiri yayi haɗi da fita daga office ɗin dakin tiyatar yanu fa.
10:00 am
LAGOS.


_EKO HOSPITAL._


Patient ne zazaune wanda da alama sun zo ganin likita ne.
wata Nurse ce tafito daga Office aƙalla zatayi kimanin shekara 25 jikin ta sanye da fararen kaya riga da wando hulace kawai akan ta saɓanin wasu nurses ɗin da ke sanye da baby hijab, baka ce amma ba baki sosai ba wurin patient din tanufo, hadi dacewa DR. Is on the way, yayin da take amsar Katin patient ɗin wani dattijo ne zaune bai bada card ɗin shi ba da alama ma baiji mi nurse ɗin tace ba,"hey bring your card"
nurse ɗin ta faɗa ganin bai ba da nashi Katin ba," ƴata ni bana da Kati yau nafara zuwa".dattijon ya faɗa dakyar alamar ba karamin kamu ciwan yayi masa ba ,cikin harshen hausa tafara mgn duk da batayi Kama da hausawa ba kuma bawani iya hausar tayiba sosai " to ya kake so ayi Katin ka keso nabaka ne komi"
"a'a naji ance ana bada magani kyauta shiyyasa nazo" dattijon yafada, wani kallon rainin wayau take ma dattijon har ya gama magana, cikin karaji tace "hey hausa people nabani mamaki, to bari kiji nan ba charity hospital bane dan hk kitashi kiba mutane wurin, in ban da abunki ta ina wannan hospital ɗin tayi Kama da charity hospital koh ance maki irin hospital ɗiin kune na arewa" nurse din ta faɗa hadi da nuna masa hanyar fita. " haba Victoria kin man ta me doctor yace duk time ɗin da marasa ƙarfi suka zo ne " wata kyakyawar nurse ke faɗin haka chocolate color ce a ƙalla zatayi kima nin shekara 23 itama sanye take da fararen kaya rigada wando sai farar baby hijab, zuwan ta ke nan tasamu victoria nayima dattijo masifa Ita bahaushiya ce sabanin victoria, "ina ruwana ai yan zu ba ya nan sai dai inkece zaki faɗa masa
Kasa tashi dattijon yayi jikinsa sai rawa yake, tsawa ta dakama dattijo, haɗi dacewa "I said get out from this hospppppp, kasa karasawa tayi adalilin saukar wani mahaukacin mari dataji a kuncinta batai aune ba tasake jin wani marin a dayan kunchinta bashiri ta kife ƙasa, gaba ɗaya hankalin patient dana nurses ya dawo kan wanda yayi marin.


Tsaye yake jikinsa sanye da blue uniform ɗin sa na aiki, kafarsa na sanye da black din takalmi sai hannunsa dake riƙe da briefcase da lab coat ɗin sa, dogone yana da tsayi, farine sosai kyakyawan gaske ya nada dogon hanci sai eyes masu black ɗin eyeball, small mouth me ɗauke da red lips, sumar kan sa wacce tasha gyara koma take kan shan gyara black color ta sauko saman neak ɗin shi ya sha rawani irin na larabawa, dama da ka ganshi kai tsaye zaka ce balarabe ne kukuma half cast , akallah zai yi kima nin shekara 29 zuwa 30.


Good morning sir, nurses ɗin suka shiga gaishe da shi hannu kawai yake ɗaga masu yayin yake kiran security
ƙara sowa security ɗin sukayi suna gaishe da shi cikin girmamawa, amsa masu yayi yana nuna masu dattijon haɗi da cewa kushigar min dashi office yayin da yake ba daya daga cikin securityn key din office ɗin shi, kamashi sukayi suka ɗaurashi akan keken daukar marasa lpy wannan nurse ɗince wacce tayima victoria mgn ta matso kusa da shi hannu ta mika zata anshi briefcase ɗin dake hannun shi dakatar da Ita yayi, magana ya fara cikin harshen turanci nurse "hidaya me nace ne gameda masu zuwa neman tai mako? "
" kace duk wanda yazo neman tai mako ah EKO aturashi ABNOOR, kuma itama nurse Victoria tasani kuma sai da nasake faɗa mata da tana ma datijjon faɗa"
"shikenan koma dai miye Wannan yazama nakarshe ina ba haka ba dukkan ku sai ranku ya ɓaci "ya fada haɗi da nufar office ɗin shi
🌹~ KAINAAT ~ 🌹
Tasowa victoria tayi daga duƙewar datayi domin ta maru, haryanzu bata dawo dai dai ba, masifa tafara yima nurse Hidaya akan Ita ta haɗa ta da dr haryayi mata wannan marin, "to bari kiji Victoria garama tun wuri kifita daga harkata basai da na gar gaɗe kiba amma mikika ce ke kina ganin dr shazim bazai iya yimaki komai ba ke yar gaban goshi, kedai kawai za fin mari ne yasa zaki sauke a kaina mizai hana shi dr bazaki bishi office kiyi mashi masifar ba "hidaya ta faɗa tana dariya sauran nurses ɗin ma dariya suke saboda sun san magana ce hidaya ta faɗa ma victoria saboda ba ƙaramin so take ma DR. SHAZIM ba, mutsww victoria taja tsaki saboda haushin dariyar dasuke mata ta kuma gane miyasa su dariya wuce wa tayi office ɗin dr saboda itace ke tura mashi da patient,
Shiga tayi cikin office ɗin haɗi dacewa, good morning sir zaune yake yana rubutu ajikin file wanda da alama na wannan dattijon ne yayin da shikuma dattijon yake kwance bisa gadon marasa lafiya a office ɗin , ko kallon inda take bai yiba sake gaishe da shi tayi, call nurse hidaya for me abun da kawai ya ce mata kenan, hakuri ta shiga bashi dan bazata iya daina aiki dashi ba domin in har chanzata zaiyi da nurse hidaya to sai dai tabar hospital ɗin saboda bazata juri ganin shi tare da wata ba, tsawa yada kamata domin yaga bata da niyyar fita daga office ɗin yace " get out from my office" haɗi da nuna mata hanya, fita tayi daga office ɗin zuwa office ɗinsu na nurses fashe wa tayi da kuka, tana faɗin bazai yuwu ba wlh dr shazim nawa ne ni ka ɗai babu wacce ta isa ta raɓesa sai ni taƙara fashewa dawani kukan, wata nurse ce tashi go office ɗin wacce itama daga ganin ta ba muslma bace tana cewa , "ai yanzu kika fara kuka victoria, dama ba sai da na faɗa maki ba kitashi tsaye amma kika kiji to wallahi Idan bakiyi wasa ba kina nan sake dabaki hidaya zata kwace shi, sai dai kizama ƴar kallo"
"haba destiny yaza ki man wannan mumu nan maganar, kisan kuwa yanda nake son dr shazim kuwa da kinsan yanda nake son shi da baki ce haka ba"
" victoria kenan inaga bakisan halin hausa peoples bane zaki sha mamaki inkika tsaya wasa domin kuwa Ita hidaya yarensu ɗaya bayan nan religion ɗin suma ɗaya kina ganin zai kula ki ne yana ganin hidaya, kawai kitashi tsaye"
"to ya zanyi ki bani shawara pls"wani munafukin murmushi destiny tayi haɗi da cewa yanzu dai kifara kiramashi hidaya tukkun nan zuwa anjima sai muyi magana "
" haba destiny yazakice nakirata sai dai yaji haushi amma ni bazan kira taba wlh" "kaji sakarya in ban da kina sakarci in baki kira mashi ita ba taya zai gane kintuba kuma itama hidayan ki roketa akan ta tayaki bashi hakuri nasan zatayi," "uhmmm shi kenan ta faɗa haɗi da barin office ɗin domin kiran hidayar, dariya destiny ta kwashe da Ita haɗi da cewa "zaki gane baki da hankali Victoria zakisan cewa ni ba kanwar lasa bace yanda kika ki brother samuel to haka zaki rasa shazim shima sakarya kawai" .


wurin su hidaya Victoria tanufa,ta zuwa ta tsaya hannunta riƙe da ƙugu tace" kizo dr . nakira tana faɗa ta juya kai gefe, "wakenan acikin mu?" watace cikin nurses ɗin dake zaune ta faɗa , "tasan kanta ai acewar Victoria , sarai sungane hidaya take nufi sbd sun San tana yar tsama da Ita amma sai suka nuna basu gane ba "hidaya kinsanfa ke nake nufi amma kinyi kamar baki ganeba zanje na faɗa masa bazaki zoba"
" kejiman Victoria da karfin halin, kin faɗi sunan tane daza kice ta ƙizuwa"
"ah to gane mana hanya sister maryam" acewar wata daga cikin nurses ɗin "haba Victoria nina rasa me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login