Showing 21001 words to 24000 words out of 133697 words

Chapter 8 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt

27 Nov 2024

8492

ana picking call din yace kasa meni a office dina yana gama fada yayi rejecting kiran bayan 30 seconds sai gashi anturo kofar, wani security ne ya shigo gaishe da shazim yayi hadi da cewa dr gani " wai hayaniyar mi nake ji ne" afuwan dr bari naje na duba " ok kawai yace masa, fita security yayi inda su Victoria suke ya nufa nan ya same su har lokacin basu dai na fadan da suke, hidaya sai kuka take saboda a rayuwarta ta tsani fitina, su maryam ne ke maida ma Victoria martanin, ɗaya daga cikin nurses ɗin mata security ya tambaya mike faruwa amsa ta bashi " zuwana kenan na same su suna hayaniya sai dai ban san miye maƙasudun faɗan na su ba "
" to shikenan " shine kawai abun da security ya faɗa ya komawa office ɗin shazim ya sanar dashi cewa " sir su nurse Victoria ne ke hayaniya, ina jin dai wani abun ne ya ha dasu "
"Mutsww"shazim yaja tsaki a ranshi yace "nonsense kawai dasu, zasu wani tada ma mutane hankali , sakarkaru banza "


achan kuwa waje dr kabir ne ya fito daga office ɗinsa ya nufi inda su Victoria suke shima hayaniyar su ce ta dame shi, yana isowa wurin dukan su su kayi shiru tsaki yaja hadi da cewa" wlh kunbani mamaki matuƙa , ashe bakuda hankali " ya fada hadi danuna hidaya ya nace wa " wacece nan , mi kuma akayi mata take kuka" da yake duƙe take shiyyasa bai gane ko wacece ba, maryam tace "dr hidaya ce" matsowa yayi kusa da ita yana fadi "mike da munta ne " amsa maryam ta bashi da cewa " Victoria ce ke ci mata mutunci ita kuma bata iya ramawa shine take kuka, mukuma " hannu ya daga ma maryam hadi da cewa "ya isa haka, oya tashi " yace ma hidaya, mikewa tayi fuskar nan duk tayi sharkaf da hawaye "wuce muje" yace, binsa tayi a baya har office ɗinsa , toilet ya nuna mata " shiga ki wanke fuskar ki " shiga tayi ta wanke fuskarta sannan ta fito
wuri ya nuna mata kan sofa da ke cikin office din
zama tayi tana sauke ajiyar zuciya
ita bakomai yafi bata haushi ba wai a ce daga taimako Victoria zatayi mata haka, gyaran murya dr kabir yayi haɗi da zama kan sofar yana fuskantar hidaya yace " hidaya nasan wannan ba halinki bane miyasa kike biye ma mutane irin waɗanna, ke da ita bafa ɗaya bane al'adar ku ba ɗaya ba kwata kwata ita batasan kunya ba saboda ba'a koya mata ba amma ke duk wanda ya ganki zai yimaki kallon wacce bata san mutuncin kanta ba, pls hidaya karki sake"
" insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba nagode "
" bakomai karki damu tashi ki tafi kicigaba da abun da kike yi "
" ok" ta faɗa hadi da mikewa ta fice, wurin patient ta koma ta cigaba da turama dr su.


✨noraiz✨


Parlorn ammy ya shigo jikinsa sanye da kananu kaya farar riga da bakin wando, yana shigowa Ammy na fitowa daga bedroom dinta sanye take da hijab har kasa, Noraiz yace " yawwa Ammy harkin shirya kenan " "eh" Ammy ta fada, ficewa su kayi, parking lot suka nufa wurin wata bakar mota rang rover suka nufa Noraiz ne ya bude mata kofa sannan ya zagaya driver seat ya zauna hadi da yima motar key ya nufi main gate, megadi ne ya tashi ya bude masu gate gaishe da Ammy mai gadin yayi amsa mashi tayi cikin kulawa sannan Noraiz yayima motar key suka fice
tafiya su kayi sosai sannan suka sha kwanar wani road mikewa suyi sosai sannan suka tsaya abakin wani gida horn Noraiz yayi abakin gate din gidan.
ƙofar dake jikin gate din gidan aka bude wani mutum ne ya leko yana ganin motar Noraiz ya koma da sauri
gate din gidan aka bude ciki Noraiz ya danna hancin motar ciki, parking lot din dake gidan Noraiz ya nufa hadi da yin parking, fitowa su kayi shi da Ammy suka wuce cikin gidan
part biyu ne gidan , ɗaya daga cikin part ɗin suka nufa da sallama abakin su suka shiga cikin parlorn
parlorn ne mai girman gaske wani dattijone zaune kan carpet sai wata yar tsohuwa dake kusa da shi tana mika masa magani da ruwa
wurin su suka ƙarasa wannan yar tsohuwar ce ta dago tana amsa ma su sallamar da su kayi, haɗi da cewa "oyoyo ango saukar yaushe" noraiz na murmushi yace "jiya "yayin da suke wuri zama kan carpet, ammy tace "ina kwana ummy, ya jikin baba "
ummy tace "lafiya lau, jiki alhmdllh" masha Allah Ammy tace , sannan ta kalli baba tana faɗin "ina kwana baba, ya ƙarfin jiki" " jiki alhmdllh da sauki
wa nake gani kamar NURADDEEN? " Baba ya tambaya
Noraiz yace " shine mlm ya ƙarfin jiki? "
" jiki alhmdllh nuraddeen saukar yaushe"
" jiya" Noraiz ya bashi amsa
" masha Allah ya karatu?"
"Alhmdllh mlm"
masha Allah malam ya faɗa
nan suka shiga fira har baba yana tambayar noraiz ina wannan ƙaton gwawron yyn nashi,mai gudun aure, murmushi kawai Noraiz yayi yana bashi amsa da yana hospital
" Masha Allah, Allah ya taimaka " ya fada, sunjima suna fira har kusan 12 sannan Noraiz yace " mlm zanje wurin yaya "
" to a dawo lafiya "
"Allah yasa " Noraiz ya fada hadi da nufar kofar parlorn ya fice, daga gidan, kallon ammy malam yayi yana faɗin" jiya ahmad ya kirani kan maganar shazim, sun ji shi shiru, kuma suna ta kiran shi basu samu, har mansoor sai da ya kirani shima bai samun shi "
"eh haka yace man nima da ya kirani "
"kin faɗa ma shazim ɗin?"
"eh na faɗa mashi, amma har yanzu ce man yayi bashi da wacce yake so " ɗan nisawa malam yayi sannan "na lura so yake mu cire hannun mu daga maganar, mu ƙyale shi da su ahmad ɗin su yanke mashi duk hukuncin da suka ga dama "
" haka nace mashi, zamu cire hannun mu a lamarin suyi duk abun da suka ga dama"
ummy tace "ba haka za'ayi ba malam, ina ga a ƙara mashi lokaci ko da ba mai tsayi ba"
malam yace "lokaci na nawa za'a bashi zainab, tun yaushe ake bashi lokaci "
"duk da haka dai, a ƙara mashi ko da wata ɗaya ne "malam yace "to shikenan"


Noraiz yana shiga cikin eko parking yayi a parking lot, fitowa yayi s ya nufi cikin hospital, da yake office din shazim chansama yake hakan yasa shi hawan lifter
yana fitowa daga lifter office din Shazim ya nufa nocking yayi daga ciki aka bashi iznin shiga
ƙofar ya tura ya shiga, shazim ya samu zaune yana aiki cikin laptop
sallamar da yayi shazim ya amsa mashi wuri ya samu cikin daya daga kujerun office din ya zauna
" ya aiki yaya? "
"Alhmdllh " kawai shazim yace yana yana tambayar jikin malam
" alhmdllh yaya , yaji sauki" dr kabir ne ya shigo office din yana ganin Noraiz yace
" saukar yaushe Noraiz "
" jiya Yaya, ya Aiki " Noraiz ya fada
"Alhmdllh Noraiz, ya school "
"school alhmdllh "
"masha Allah" fira suka shiga yi ta yaushe gamo shida dr kabir shazim na sauraron su yana aikin gaban sa, kiran sallar zuhur ne ya katse masu firar suka fice zuwa masallaci domin yin sallah
daga cana abnoor shazim da Noraiz suka wuce.........


✨ Aairah ✨


dawowar su kenan daga school dan ko uniform basu cire ba suka haye bed saboda ba ƙaramin gajiya su kayi ba ' dan Aairah da wani irin zazzabi ta dawo


Mom ta shigo ɗakin su tana cewa " lpy kuke, ko uniform baku cireba kun lama bacci "
"wallahi mom mun gajine sosai shiyyasa, kuma ma Aairah bata jin daɗi , zazzabi ne a jikin ta "
"wani aiki ku kayi ne a makarantar" mom ta fada yayin da take ƙarasawa kan bed, hannun ta ta ɗaura saman wuyan Aairah "ya salam " mom ta fada saboda jin zafin dake fita daga jikin Aairah " mi ke damun ki?"
" zazzabi ne da ciwan kai"
" ok yaka mata kitashi ki cire uniform ki watsa ruwa, bari naje na dauko maki magani kafin yayan ku ya dawo" tashi tayi zaune mom tace ma Aaimah ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka, to tace hadi da nufar toilet, ficewa mom tayi daga daki
Uniform ɗin jikinta ta cire ta daura towel, Aaimah ta fito tana cewa sister kishiga ga ruwan chan " to nagode sister " ta fada toilet ta nufa
kayan jikinta ita ma ta cire Aairah na fitowa ta shiga
kan gado Aairah tahau hadi da jan blanket saboda data yi wankan wani sanyi take ji
Mom ce ta shigo hannun ta ɗauke da tere wanda ta hadoma Aairah abinci
" wai kwanciyar kika sake " wurin ta mom ta nufo, table ɗin dake ɗakin ta jawo ta daura teren da ta shigo dashi, hawa tayi kan gadon tana fadin " tashi kici abinci ga maga ni nan "
tashi tayi zaune " baki sa kaya ba kenan? " mom ta fada hadi da nufar wardrobe dinsu, riga mara nauyi mom ta dauko mata
" tashi kisa,, mom tafada yayin da take mika mata rigar
amsa tayi hadi da tashi ta sanya rigar sannan ta dawo kan gadon ta zauna abincin da ta haɗa mata tamika mata
tana gama ci mom ta bata magani tasha sannan ta koma ta kwanta blanket Mom taja mata
ta haɗa tiren da Aairah taci abinci ta fice da shi yayin da take cema Aaimah inta gama shiri ta fito taci abinci ita ma
shaf shaf Aaimah ta shirya sannan ta dawo kusa da Aairah
"sister ya jikin naki"
"da sauki " Aairah ta fada
"ok Allah ya kara sauki, bari naje naci abinci na dawo "
gyada mata kai Aairah tayi alamar sai kin dawo
ficewa Aaimah tayi daga bedroom din , parlor ta nufa Mom ta samu kan dinning ita da abie
ƙarasawa tayi wurin su tana cewa " ina wuni abie "
" lafiya lau , yanzu Mom din ku ke fada man Aairah bata jin dadi, ya jikin nata? "
" da sauki abie "
" to Allah ya bata lafiya, Idan abdallah ya dawo sai ya duba ta, inma taka ma ayi mata allura, koh mi kenan dai " abie ya fada, Aaimah a jiye spoon din dake hannun tayi tana dariya hadi da fadin " kace yau akwai buduri , Aairah za a yima allura tashin hankali kenan "
" ka jita sai kace ba jirgi daya ya kwasu ku ba, kema son allurar kike ne " Mom tafa da hadi da mangare ma Aaimah kai, sosa inda Mom ta mangare ta tayi tana turo baki da fadin " Allah gara ni da Aairah Mom"
"Bawani nan " Mom ta fada,suna gama cin abincin abee ya mike yana cewa " bari naje na duba jikin ta " ya fada yayin da yake nufar dakin su, samunta yayi kwance kan gado kamar yanda Aaimah ta fita tabar ta duk ta rufe jikinta da blanket har fuska, ƙarasawa gaban gadon abie yayi yana fadin " Aairah "
"na'am abie " ta amsa mashi hadi da danjan blanket din ta fito da fuskarta
" ya jikin naki "
" da sauki abie "
" to Allah ya ƙara sauki, Idan abdallah ya dawo sai ya duba ki kin ji" zanbur ta tashi daga kwance tana fadin
" amma dan Allah abei idan ya dawo dan Allah karka bari yayi man allura, yaba ni mgni kawai " ta fada hadi da maida fuskarta kalar tausayi " to shikenan kwantar da hankalin ki magani kawai zai baki, kinji koma ki kwanta "
" to abie "
" Allah ya baki lafiya " abie ya fada hadi da nufar kofa ya fice....


✨SHAZIM ✨


Sai bayan da akayi sallar magrib suka bar abnoor shi da Noraiz , direct gdn malam suka nufa domin ammy na chan har da fatima wacce daga school chan ta wuce
Suna shiga gidan parking su kayi sannan kowanen su ya fito daga motarshi saboda Noraiz da motar shi yaje eko wurin shazim
part din malam suka nufa
zaune suka same shi a parlorn shi yana duba wani littafin addini
sallama su kayi hadi da shiga cikin suka nemi wuri suka zauna


Amsa masu sallamar yayi yayin da yake cire medical glass din dake fuskar
gaishe dashi shazim yayi yana tambayar shi ya jiki
" alhmdllh ya aiki "
'' alhmdllh malam''
"to Allah ya taima ka"
" ameen malam"
fira suka shiga yi sai da aka kira sallar isha sannan suka tashi
masallachi suka nufa harda malam ana gamawa suka dawo ciki,za su nufi part ɗin ummy malam yace noraiz ya tafi, shi kuma yana son magana da shi, wuce wa noraiz yayi, su kuma shi da malam suka shiga part ɗin malam, part ɗin ummy noraiz ya nufa, ammy da ummy ya samu a parlor fatima da yarinye kuma na kitchen
Zama yayi kan sopa kusa da ummy yana mata shagwaɓa akan yunwa yake ji
"ga abinci can su fatima na girkawa"
"gaskiya ni bazan iya jiran su gama ba "ammy tace "to sai dai karka jira ɗin"ummy tace "a'a baza ayi haka ba, bari naje kitchen ɗin baza a rasa abun da zai ci ba kafin su gama "ta faɗa haɗi da tashi ta nufi kitchen ɗin , ammy tace "da kin ƙyale shi ummy, sai kace ba namiji ba "
"A'a ke dai, wasa da ciki ai bai da amfani sai ulcer ta kama mutum"
"wallahi kuwa ummy" jifan shi ammy tayi da pillow.


A chan parlorn malam,
"shazim bana son mu cire hannun mu akan lamarin su yanke maka hukuncin da baka so ba, gara tun wuri ka nema ma kanka masalaha"
"insha Allah malam,zanyi ƙoƙari,ka basu haƙuri"
"haka kake cewa kullum, har hakan yasa suna tunanin ni ke goya maka baya, kuma miyasa idan sun kira ka, ba su samun ka, mansoor ma ya kirani yace yanata ne manka amma baya samu "
"bakomi, inajin network ne "
"to kayi ƙoƙari ka kira su"da to ya amsa,tashi yayi yace zaije wurin ummy su gaisa, da to kawai malam ya amsa, part ɗin ummy ya nufa, a parlor ya same ta noraiz na kusa da ita yana cin abinci, wuri ya samu ya zauna yana gaishe ta
amsa mashi tayi cikin kulawa hadi da tmbyr shi ya aiki
"aiki Alhmdllh ummy, ya malam da jiki "
ummy tace " jiki da sauki Alhmdllh "
"to masha Allah, Allah ya ƙara sauki "
" Ameen" fatima ce ta nufo idan suke, gaishe da shazim tayi tana cema ummy sun gama, ga abinci can kan dinning, da to ummy ta amsa, wurin dinning fatima ta koma tana cewa"ummy na malam fa, part ɗin sa za'a kai masa"
"A'a, zai shigo "bata rufe baki ba sai ga malam ɗin ya shigo, tashi sukayi dukan su suka nufi dining ɗin, bayan da suka gama,shazim ya sake duba jikin malam ya sake rubuta mashi magunguna
Sannan suka yi masu sallama,suka kama hanyar gida Ammy da shazim mota daya suka koma yayin da fatima da Noraiz suka shiga tasu suma
Suna shiga gida Innah Asabe ta fito tana masu sannu da zuwa da tmbyr ya jikin mlm nan Ammy ke fada mata jiki da sauki alhmdllh, sannan kowa yakama hanyar bedroom dinsa, ita ma Innah Asabe nata dakin ta nufa........
Episode 11_ 12


Har yanzu kwance take kan gado kamar yanda abie ya barta sallah ce kawai take tashi tayi, Aaimah na zaune kusa da ita tana duba book dinsu na school saboda exam dasuke facing, nocking suka ji anayi Aaimah ce tace "waye" daga chan wajen taji ance "zaki zo ki buɗe ko sai kingama tambayar waye sannan" bashiri ta sauko daga gadon hartana niyyar faduwa saboda jin muryar wanda ke nocking din bakowa bane face ya abdallah, buɗe kofar tayi tsaye yake jikinsa sanye da gajeran wando iya gwiwa sai riga mara nauyi mai gajeran hannu
Matsawa Aaimah tayi gefe shi kuma ya wuce ciki daidai bakin bed din ya tsaya yana cema Aairah ta tashi, tashi tayi zaune, shima zama yayi bakin gadon yana fadin "minene ke damun ki"
"kaina ke ciwo sai zazzabi, amma naji sauki dan yanzu bana jin zazzabi"
"ok" ya fada yana kallon ta domin yasan karya take allurace kawai bata so
kuma dole sai yayi mata ita , hannun shi ya daura saman wuyanta zafi yaji zau "ki kace ya sauka zazzabin bayan gashi nan jikin ki da zafi"
"to yaya dan Allah ka bani magani kawai, wlh bn son kayi man allura dan Allah"
"a haka zaki zama likita kina gudun allura, wa zai zauna kiyi mashi ita kenan bayan ke bakiso"
"dan Allah dai yaya" tafa da hadi da hada hannu wanta
wuri ɗaya alamar yayi hakuri.
"shikenan to" ya fada hadi da ficewa daga dakin
dawowa Aaimah tayi kusa da ita tana cewa "ai kuwa nasan allurar zai maki , tun da jikin ki har yanzu da zafi" mi Aairah zatayi inba kuka ba , kuka rurus kamar wata ƙaramar ya rinya Aaimah kuma sai ƙara bata tsoro take
tashi tayi daga gadon ta fice daga dakin bedroom din Mom ta nufa, Mom fitowar ta kenan daga bathroom Aairah ta shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login