Showing 114001 words to 117000 words out of 133697 words
Chapter 39 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt
shi an rubuta am sorry dear da baƙin fenti, kwashewa maryam tayi da dariya tana faɗin
" soyayya ruwan zuma, lallai dr " ta fa ɗa haɗi da sake buɗe kwalin ta fito da sauran kayan da ke ciki, sweet ne da uban chocolate masu ɗauke da sorry a jikin ledojin su, ba maryam ba har ita kanta hidayar sai da ta dara...........
_Episode 58_59_
............. "Amma fa dr na matuƙar son ki hidaya " maryam ta faɗa yayin da take buɗe wani chocolate ta kai baki, taɓe baki hidaya tayi
"ke ki kaga haka "
"wai ke haryanzu kina a kan bakanki na baki son shi "
Kwanciya tayi haɗi da juya mata baya batare da tace komai ba, binta da ido maryam tayi tana faɗin
"karki fasa zaki sha mamakin abun da zanyi maki kuwa "
"ke maryam kin daɗe ko mi za kiyi ana so dole ne "
"haka ki kace? "
"eh haka nace "
tashi maryam tayi zata fice, da sauri hidaya ta riƙota
"wai ke ƴanzu ko kunya bakiji sai kije ki faɗama ummah "
"sakar ni" maryam ɗin ta faɗa taba fisgewa daga riƙon da hidayar tayi mata ta nufi ƙofa, a sukwane hidayar ta rigata isa bakin ƙofar, abun ma dariya ya so ba maryam amma sai ta ɗaure fuska bata yi ba tace " ki matsa man a gabana "
"wallahi bazan matsaba tun da ke baki san wasa ba "
"wasa ko zakiga wasa " maryam ɗin ta faɗa tana ƙoƙarin janye hidaya
"dan Allah maryam kiyi haƙuri wasa fa nake "
"Ina ruwana da wasanki ni bani hanya na wuce " haka su kai ta jayayya har ummah tayi nocking ta hidaya sai roƙon maryam take akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, gajiya ummah tayi ta sake wani nocking ɗin tana faɗin
"wai lafiya kuke da baza ku buɗe man ba " da sauri hidaya tasa hannu ta buɗe tana yima maryam alama da da ido akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, ummah na shigowa kallon su tayi tana faɗin "ku lafiya naga duk kunyi wani tsaye cirko cirko " hidaya ce tayi carb tace
" ba komai ummah magana muke"
"maganar ce har sai kunzo bakin ƙofa? "
maryam tace " tafiya zanyi ne daman"
"tun yanzu zaki tafi maryam?, ga abinci can a dinning, ki bari sai kinci sai ki wuce gida "
" naci abinci ummah kafin na fito daga gida daman saboda naga ta dawo ne da wuri kuma ina kiranta bata ɗauka ba yasa nayi tunanin ko lafiya "
"to shikenan, ki gaishe da mamar ku "
"za taji insha Allah " jinjina kai ummah tayi haɗi da ficewa ta ba ɗakin
"shine zaki wani ce zaki tafi "
"idan ban tafi ba mizan yi maki ne, ko so kike na zauna ki cigaba da ɓata man rai "
"haba dan Allah wane irin ɓacin rai kuma "
"koma dai minene ni tafiya zanyi yi "
"Amma ai kin tsaya na baki wancan kayan "
"bana so" shine kawai abun da maryam ta faɗa ƙofar ta nufa ta buɗe bin bayan ta hidaya tayi tana bata haƙuri amma taƙi sauraronta,ba yanda ta iya haka maryam ta tafi ba tare da ta amshi chocolate ɗin ba ko ban kwannan arziƙi ba su yi ba, juyawa tayi ta koma ciki dinning ta nufa wurin ummah .
_*✨KATSINA✨*_
Abie ne da uncle Ahmad da uncle mustafa zaune a parlorn suna magana
Uncle mustafa ne yace
" yaya yanzu yaushe zaka tafi kenan"
Amsa Abie ya bashi da
"da wannan week ɗin nace amma yanzu ina jin sai wani week ɗin saboda safwan da za su zo gobe "
"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen abie ya amsa,
uncle Ahmad ne yace
" wai yaya idan sun zo su safwan ɗin anan za su zauna?"
"eh mana Ahmad idan ba nan ba ina zasu zauna "
"a gaskiya yaya da zaka ji shawara ta da ba su zauna anan ba "
"saboda mi? "
"yaya bawan Allah nan yana cikin tashin hankali, rayuwar cikin barazana take, sai nake ganin zaman shi a nan kamar akwai gangance "
"Ahmad bawani gangance nasan da lilin da yasa nace ya zauna nan "
"to shikenan yaya,bawani abu Allah ya bashi lafiya "
"Ameen shi ne kawai, yaushe zaka koma Abuja ne " abie ya tambaya
"tuna ni nake ranar friday zan tafi "
"ok Allah ya kaimu, wai addimisson ɗin su Aaimah shiru "
Uncle Ahmad yace
"Inajin fa basu fara ba dawa ba kuma kaga late aka nemar masu addimisson ɗin Amma na san bazai wuce wannan week ɗin ba tun da makarantar next month su ke fara lectures "
"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen su ka amsa su duka, dadi ce ta fito ta zo wurin su ta zauna kan sofa gaishe da ita su kayi, amsa wa tayi da kulawa a fuskar sannan tace
" mi ake tattaunawa ne tun ɗazu? "
uncle Ahmad ne yace " magana muke ta yanda zamu nemo maki yaron ki "
"mai makon naji kunce kun nemo shi sai kuce magana kuke ta yanda zaku nemo shi, na lura so kuke mu sa ƙafar wando ɗaya da ku kafin ku nemo shi "
Abie ne yace
"ba sai an kai ga haka ba"
"to yauahe zaku kawo man shi gidannan? "
Amsa Abie ya bata da
"insha Allahu nan bada jimawaba, da wannan satin zan tafi kadunar to amma saboda zuwan su safwan yasa na fasa sai wani satin"
"Allah sarki gobe ne kenan zasu zo, to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen " su ka amsa su duka, fira suka shiga yi cikin nisha ɗin har sai da lokacin sallar zuhur yayi sannan suka nufi masallaci dadi kuma ta nufi ɗakin ta.
_*✨SHAZIM✨*_
Lokacin da hidaya ta fita daga office ɗin shi bai wani jima ba shima ya nufi Abnoor
Aiki yayi sosai sai daga baya yanufi office ɗin majeed,bai same shi a ciki ba hakan yasa yayi tunanin ko yana duba patient ne zama yayi kan sofa yana jiran ya dawo, wayar shi dake ringing ya jawo duba mai kiran yayi, Mansoor ne, picking kiran yayi sallama yayi, amsawa mansoor ɗin yayi yana faɗin
"kai dai babu ruwanka yanzu da neman mutane, idan mutum bai nemeka ba shikenan kai ba ruwan ka da shi "
ɗan yatsine fuska yayi yace
"kai ai na lura neman mutanen kae yi "
"gashi kuwa na neme ka "
"to naji, yaushe ne ma kace zaka zo "
"ok ka ma manta yaushe nace zan zo, nalura kamar baka son zuwana saboda zan zo na ɗauke maka habibtyn ka "
"wait mansoor idan ba so kake nayi maka rashin mutunci ba to ka daina haɗa ni da wannan sakaryar yarinyar"
"lallaima shazim sakaryar kace?"
"ƙwarai kuwa ba sakayar bace, ni da zaka taimaka wallahi da zuwa kayi yau ka tattarata ka mai da ma iyayen yanta ita dan nagaji da zama da muke yi a gida ɗaya "
"Amma nayi mamaki shazim ko da ace yau baka san taba ai baka faɗi haka ba bare ma tana ƴar uwar ka "
"ni dai da zaka taimaka da kazo gobe ka tafi da ita "
"bazan zo ba ɗan rainin wayau, idan da gaske ne ka gaji da zama da ita ja dawo da ita da kanan "
"bana da wannan lokacin kuma "
"to nima bana da shi "
"Alright haka kace "
"Kwarai ma kuwa " yana faɗar haka yayi rejecting kiran, murmushi gefan baki yayi haɗi da cire wayar daga kunnan shi, kwanciya yayi kan sofar latsar wayar shi ya shiga yi, anan majeed ya shigo ya same shi, zama yayi yana faɗin
" yaushe ka shigo?"
hannu ya miƙa mashi su kayi musabaha
" tun ɗan ɗazu na shigo "
"Ok naje duba patient ne, lafiya dai ko"
" lafiya, maganar waɗan nan kayance nake so muyi "
" ok , wanda ke hannun mu ko wanda kace a tura "
" eh wanda nace ku aika "
"anyi kamar yanda kace"
"yawwa nagode sosai "
"Amma shazim baka gani gara mu miƙa kayan nan hannun ƙungiyar drugs "
"a'a majeed, idan mu kayi haka kamar mun ba masu kayan kayan su ne, kasan yanda cin hanci yayi yawa a ƙasar nan muna bada kayan nan masu su za su fito ne su ba cin hanci su amshi kayan su "
"haka ne, amma to idan mun bar su nan mi za muyi da su"
"ba abun da za muyi da su, kawai ina son yin amfani da au ne wajen gane mai kayan daga nan sai na ɗauki matakin da ya dace akan shi "
"to shikenan, amma a canza masu wurin zama daga store "
"ka jika da wata magana, idan ba nan ba ina zamu kai su, a nan zamu bar su har Allah ya toni asirin masu "
"shikenan " majeed ya faɗa canza firar su kayi zuwa wata, ana kiran sallar asr su ka fita su ka nufi masallaci, da suka gama sallah majeed office ɗin shi ya koma shazim kuma yace mashi briefcase ɗin shi kawai zai ɗauka gida yake son ya koma saboda fatima, sallama su kayi majeed na faɗin yana gaishe da fatimar.
Yana shiga office ɗin kamar yanda yace briefcase ɗin kawai ya ɗauka ya rufe office ɗin, motar shi da yayi parking a parking lot ya nufa, shiga yayi yayi mata key haɗin da yin reverse ya nufi gate , mai gadi na ganin shi da sauri ya tashi ya buɗe mashi gate ɗin , yana ɗaga mashi hannu har ya bar hopital ɗin.
yana fita wata ɓakar jeep ta fito daga bayan Abnoor, ta mirror ya hange ta abun yaso ya bashi mamaki saboda ya san bawani titi ko wani gida da za'a mota zata iya fitowa daga wurin, tuƙi yake yana kallon motar da farko yayi tunanin hanya ce ta biyo da ita may be ko matsala ta samu ne yasa ta tsaya a bayan Abnoor ɗin, sai da yaga ya bar titin abnoor ɗin ya hau wanda zai kai shi gida yaga motar tana nan tana binshi, tafiya ya fariyi a slowly abun mamaki sai kawai yaga mai motar yayi parking,murmushi ne ya so kufce mashi dan abun yayi matuƙar bashi mamaki, key yayi ma motar ya cigaba da tafiya, shima mai jeep ɗin key yayi mata ganin haka ne yasa shi yin kwana ya sauka daga titin da zai kaishi gida, shima mao motar canza hanya yayi zuwa wacce shazim ɗin ya bi, yanke shawara kawai shazim yayi daya tsaya ya ga ko waye kd binsa a baya, gangarawa yayi bakin hanya yayi parking kashe motar yayi ta zare key ɗin motar ya fito, mai motar na ganin ya fito da sauri yayi reverse ya a wani irin masifan gudu ya shiga wata kwana, jinjina kai yayi yana faɗin " ƙaramin ɗan iska ai da ka tsaya sai naji dalilin bin nawa da kake " komawa yayi cikin motar ya kama hanyar gidan malam, yana isowa horn yayi mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga , parking yayi sannan ya fito ya shiga ciki, parlorn ummy ya fara zuwa zaune ya sameta ita da mai aikinta tana ɗan daddana mata ƙafu saboda fama takeyi da su kwana biyu, ƙara sawa yayi ciki bakin shi ɗauke da sallama
Amsa sallamar da yayi ummy tayi tana faɗin " lale marhabun da bokan turai " wuri ya samu kan sofa kusa da ita ya zauna, mai akin ummy ce tace " ina wuni "
"lafiya lau "
ya amsa mata haɗin da kallon ummy yace
"ina wuni ummy, ya ƙafafun "
"da sauƙi ya aiki "
"Alhmdllh"
"o ya fatima da jiki "
"Alhmdllh taji sauƙi sosai "
"to masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi "
"Ameen " sun ɗan jima suna ɗan taɓa fira da ummy kafin daga bisani ya nufi part ɗin malam
Samun shi yayi a kan carpet yana duba wani littafi,sallama yayi mashi haɗi da ƙara sawa ciki ya samu wuri ya zauna kan carpet ɗin, amsa sallamar malam yayi sannan yace
"daga ina haka da yamma "
"daga Abnoor nake, shine nace bari nazo na duba ku kai da ummy "
"ai kuwa ka kyauta,ina nuraddeen da fatima "
"Fatima dai na gida, noraiz kuwa yana mall kasan yanzu su noraiz an daina zaman banza "
murmushi malam yayi yana faɗin " haka ne kam su aboki na an girma yanzu ba'a zaman banza, to Allah ya taimaka"
"Ameen "
"fatima jiki yayi sauƙi ko "
"ta samu sauƙi dan ba inda bata zuwa yanzu "
"to Allah ya ƙara sauƙi"
"Ameen "
"yau she zata fara zuwa makaranta? " malam ya tambaya
"insha Allah nan da wani watan zasu fara karatu, da yake makarantar basu jima da bata addimisson ba "
"Ah abu yayi kyau Allah ya kaimu nan da wani wata "
" Ameen malam"
"ya wajen su kawun ka sun sake kiranka kuwa "
"A'a ba wanda ya kira ni cikin su " ya faɗi hakan kawai saboda bai son malam na mashi maganar yayi haƙuri ya ƙyale su
"shazim kenan, ina so kasa haƙuri a zuciyar ka, ko jiya Ahmad ya kirani yace suna nemaka ba su samun ka, abun da ya faru shazim yariga da ya faru tun da yaron nan yayi nadamar abun da yayi kayi haƙuri mana, yanke alaƙa da su bai da amfani saboda su ɗin jinnin ka ne "
"amma ai malam su basu ganin haka"
"wayace maka basu gani sun sani kuma duk wani abu da kaga suna yi maka suna yi ne dan suna sonka a matsayin ka na ɗan ɗan uwan su "
"malam kai kaɗai kake fahimtar haka, amma su ba haka bane a ransu ba "
"idan zaka biye wannan tuna nin naka bazaka taɓa fahimtar abun da nake so ka fahimta ba"
" malam na fahimce ka kuma nasan mi kake nufi"
"da ka fahimta da baka ɗauki wannan fushin da kake yi da su ba, ko ka manta lokacin da kana yaro miye wanda uba ke yima ƴaƴanshi wanda Ibrahim bai yi maku ba"
"malam baka san waye uncle Ibrahim ba shiyyasa kake cewa haka, kawai yayi ne saboda wani dalilin shi "
"hmmm lallai shazim,duk da ban zauna da Ibrahim ba sosai amma ina tabbatar maka da cewa mahaifiyar shi da yayan shi kaɗai za su nuna man sanin Ibrahim,suma sai dai su nuna man wani amma Ibrahim na san shi sani bana wasa ba a halayen shi babu wanda ban sani wanda ko ƴan uwan nashi basu san shi da shi ba, tun da kaji nace kayi haƙuri ka maida komai ba komai ba kayi hakan kawai"
"shikenan malam, amma wane hali ne nashi wanda ka sani har kake cewa ƴan uwan shi basu san shi da shi ba?"
"abun da ya wuce shazim ya riga da ya wuce sai dai kuma mu fuskanci gaba "
"Amma malam da ka sanar da ni "
"ka kwantar da hankalinka, idan akwai ƙaddarar ka sani zaka sani, amma karka sama ranka wani abu ba komai bane fatana kawai ka daina wannan fushin mara amfani da kake yi da su "
"shikenan malam insha Allah zan dai na"
"kaji ɗan albarka ko kai fa " malam ya faɗa yana shafa kan sa, canza firar suka yi zuwa wata, ya jima sosai a gidan dan sai bayan da yayi sallar magrib sannan yayima malam da ummy sallama ya kama hanyar gida,
yana shigowa layin su ya hangi wannan baƙar jeep ɗin tayi parking a ƙofar gidan su mai gadi na tsaye bakim motar da alama magana su ke da mai motar, ƙara sawa yayi bakin gate ɗin, mao gadin na ganin shi da sauri ya nufi gate ya buɗe mashi, ko kallon inda jeep ɗin nan take bai yiba ya shige ciki, yana shigewa mai gadi ya maida gate ɗin ya rufe, parking yayi a compound kashe motar kawai yayi ba tare da ya ɗauki kayan shi da cikiba ya fito ya nufi mai gadi dake ƙoƙarin ficewa zuwa wurin wannan mai jeep ɗin, da hannu ya dakatar da shi,alama yayi mashi da ya zo, da sauri mai gadin ya nufo shi,yana isowa yace " barka da dawowa ranaka ya daɗe "
ba tare da ya amsa mashi ba ya jifa mashi tambaya
"wanene a bakin gate da na ganku a tare? "
"wani mutumi ne"
"wani mutumi? kana nufin baka san shi ba"
"eh ranka ya daɗe "
"ok, maganar mi na hango ku kuna yi? "
"tambaya ta yake wai da yaushe zaka dawo gida, to shine sai gaka ka dawo "
"shine kawai abun da na hango ku kuna tattaunawa " da sauri mai gadin yace
"eh shine ranka ya daɗe"
"am wa kake da suna ina fatan kasan halina, ka faɗa man maganar da kuke tattaunawa da shi karka bari nayi bincike na gano gaskiya"
"yallaɓai dai Allah kayi haƙuri, wallahi ina tsoron matakin da zaka ɗauka a ka ina, amma maganar gaskiya ya tambaye ni ne akan wai kai ke da asibitin abnoor, nace mashi eh naka ne to shine yace wai mahaifiyar shi ce bata da lafiya wai yaji ance a asibitin ka kuna duba mara lafiya kyauta wai bai san ta yanda zaiyi magana da kai ba shine yake so wai dan Allah na bashi wani haske ta yanda zai samu ayi ma mahaifiyar shi aiki"
"wane kalar haske kenan"
"wai so yake na haɗa shi da Ammy, to dana ji yace haka ne sai nace yaje asibitin ya kai ta za'a du bata ba dole sai Ammy ta sa baki ba, shine yace wai zai bani dubu ɗari dan na haɗa shi da Ammy "
"sai kace mashi mi kenan"
"zan bashi amsa ne sai gaka ka dawo"
"ok shine kawai abun da kuka tattauna"
"shine kawai ranka ya daɗe"
"to amma mi yasa naga kana ƙoƙarin komawa wurin shi "
"zan koma nace mashi ne idan da gaske yake ya zo ya sameka kuyi magana, "
"zaka iya tafiya, amma ba sai ka koma wurin shi ba "
"to shikenan nagode" mai gadin ya faɗa haɗi da komawa bakin