Showing 66001 words to 69000 words out of 133697 words
Chapter 23 - Doctor Shazim season two by Kainaat complete by Khadija M. Abdulwahab .txt
koro to" acewar Asma'u,
Amina tace "wai baza ki yi magana bane"
Sai a lokacin ta samu damar cewa "ya shazim ne ya koro ni ya mansoor yace ba inda zani, ganin yace ba idan za ni ne yasa nayi zama na, wallahi ina faɗa maku kaɗan ya hana bai make ni ba "
Asma'u tace "dama nasan za'a rina, ni narasa miyasa ya shazim yake wannan isa da mallakar, samun ya mansoor ɗin yayi " Amina tace
"Wallahi kuwa rainin wayaun shi yawa gare shi, sai kace wani ɗakin shi da zai wani koro ta "
Asma'u tace " samun ya mansoor ɗin yayi da har zai nuna mashi wannan isa da mallakar " farida ce tace "wallahi babu ruwana kun ga tafiya ta, dan zai iya fitowa a kowane lokaci kuma kun san mi zai biyo baya idan ya kama ku kuna gulmar sa "
tsaki Asma'u taja tana faɗin "matsoraciyar banza da wofi kawai, yo to sai mi dan ya kama mu "
"Wallahi kun san mi zai biyo "
"duk abun da zai biyo baya bawai muna tsoron shi bane "
"ok haka kuka ce Allah ya fito da shi inga ta tsiyar cika baki " tana gama faɗa ta shige war ta ɗakin kairiyya
*✨SHAZIM✨*
A can bedroom ɗin mansoor, bayan fitar Fiddausi da gudu, kallon shazim mansoor yayi yana faɗin "wallahi kaji kunya, sai kace kai ka kawo ta da zaka wani kore ta, idan kai baka soyayya an gaya maka kowa irin ka ne wanda bai san in da ke mashi ciwo ba"
"Wannan kuma ki ake ji, ko yanzu nasa ke ganin wata acikin su sai na ɓata mata rai yanda baka tunanin, inga abun da zaka iya "
"Zan kira ta sai inga abun da za kayi, mara mutuncin kawai "
"Oho dai koma mi zaka ce ka daɗe baka ce ba, na mamajo kawai "
"Naji ni na mamajo ne, wanda bai san inda ke mashi ciwo ba fa "
"Kai ake ji idan ma ka fita kasa kairiyya ta kawo man tea " ya faɗa haɗi da neman wurin zama kan sofa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya
"Wannan ne kuma baka isa ba "tsaki shazim yaja ba tare da ya bashi amsar maganar shi ba, ficewa mansoor yayi daga bedroom ɗin zuwa parlor, kamar yanda Farida ta bar su Asma'u na gulmar shazim haka mansoor yazo ya same su,bakin benan ya tsaya yana sauraron duk abun da suke faɗa, kairiyya ce da ke kwance ta hange sa ta witsiyar ido, gyaran murya tayi masu amma hakan bai sa sunyi shiru ba sai sake ba da ƙaimi da su kayi wurin yin maganar "da alama sara kuke baku duba bakin gatarin ku " jin haka ne yasa fahimtar akwai abun da take son su fahimta, ɗagowar da Amina zatayi karab idanunta kan mansoor daya harɗe hannuwan shi kan ƙirji yana kallon su, duƙar da kai su ka yi ƙasa , ƙara sowa mansoor yayi cikin parlorn"sannun ku da ƙoƙari ko " ya faɗa yana binsu da idanuwa,ba wacce ta ce ƙala a cikin su saima tashi da su kayi sumi sumi su ka bar parlorn , tashi Fiddausi tayi zata bi bayan su , muryar mansoor taji yana faɗin "koma ki zauna " dawo wa tayi ta nemi wuri kan sofar da ta tashi, ɗuƙar da kai tayi tana wasa da ƴan ya tsun hannunta, tashi kairiyya tayi zata bar wuri da katar da ita mansoor yayi ta hanyar cewa "ki kaima shazim tea " da to ta amsa haɗi da nufar kitchen,haƙuri mansoor ya ba Fiddausi akan abun da shazim yayi mata" bakomi ai yaya " fira suka cigaba da yi ciki shauƙin soyayya, zuwa kairiyya tayi ta wuce ta gaban su zuwa sama hannun ta ɗauke da trayn da ta haɗo ma shazim tea,zaune yake kamar yan da mansoor ya barshi,ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayar shi, ciki ta shiga da sallama a bakin ta, sallamar da tayi ya amsa, ƙara sawa tayi cikin parlorn kan table ɗin dake ɗakin ta ɗaura mashi trayn, tnxs yace, fice wa ta yi zuwa parlor ta wuce su mansoor zuwa ɗakin ta, shazim yana gama shan tea ɗin wayar sa ya saka cikin pocket ya nufi main parlor, kallo ɗaya yayi ma mansoor da Fiddausi dake parlorn, hararar shi mansoor yayi, ɗaga kafaɗa shazim yayi yana faɗin "aikin banza " haɗi da kama hanya ya fice daga part ɗin, yana fita a waje ya ci karo da uncle Ahmad zai shigo, gaishe da shi shazim yayi, amsa mashi yayi yana faɗin "wai ina kaje ne tun ɗazu bayan kasan yau su uwani zasu zo, ai ko ba komi da ka tsaya kun gaisa tukunnan " amsa shazim ya bashi da "naje wurin Abdallah ne saboda wani aiki da muke "
"Ok to kashiga part ɗin innah ku gaisa da su suna can " da to ya amsa haɗi da nufar part ɗin, ciki uncle ahmad ya shiga lokacin har mansoor ya koma part ɗin shi ita kuma Fiddausi tana ɗakin kairiyya a nan zata kwana, sama ya wuce zuwa nashi bedroom ɗin.
Shazim tsayawa yayi a bakin part ɗin Innah kamar zai shiga kamar bazai shiga ba daga bi sani dai ya shiga bakin shi da sallama ciki ciki, in ba ka kalli bakin shi ba baza ka taɓa cewa yayi sallama ba,gwaggo Halima ce da innah sai Aunty zainab da ke ba yaron ta abinci sai maryam a parlorn, amsa mashi sallamar da yayi Aunty zainab tayi, bawai dan taji sallamar da yayi ɗin ba sai dan sanin ba zai taɓa shiga wuri ba tare da yayi sallama ba, wuri ya samu kan sofa ya zauna, kallon gwaggo Halima yayi yace " ina wuni Aunty "da yake haka yake kiran ta
"lafiya lau shazim, ina ka shige tun ɗazu nake ta cigiyar ka "
"na je wani ɗan aiki ne "
"Agogo sarkin aiki, a nan ɗin ma baka huta ba" murmushi yayi ba tare da yace komi ba, Innah ce tace "da yake uwar ka kawai ka sani shiyyasa ka gaishe da ita "
"to idan ban fara gaishe da ita ba ke zan gaida "
"wah ni, ai ba jiran ta ka gaisuwar nake ba "
"Koma kina so ba wai zan gaishe da ke ɗin bane " harara maryam ta maka mashi jin yan da yake mai da ma innah magana yan da ran shi ya so
"bana ma so, gida cike yake da ƴaƴan albarka, kuma sun gaishe da ni, ba taka nake jira ba " har ya buɗe baki zai mai da mata martanin maganar da tayi, gwaggo Halima ta katse shi ta hanyar cewa " shazim ya su Ammyn ku da malam " tayi hakan ne dan ta hana shi ba innah amsar maganar da tayi dan tasan abun da zai fito daga bakin shi ba mai daɗi bane
"Ammy na lafiya haka ma malam "
"masha Allah "
Aunty Zainab ce tace "shazim ya kwana biyu, ya lagos "
"lafiya lau alhmdllh, ya gajiyar tafiya "
" ba gajiya" jan shi da fira gwaggo Halima tai ta yi har su ka ɗan ɗauki lokaci, tashi yayi zai tafi, da katar da shi gwaggo tayi ta hanyar cewa " ka jira yaya ta fito ku gaisa " kallon maryam tayi "maraya je ki kira ta su gaisa " tashi tayi ba tare da ce ƙala ba ta nufi bedroom ɗin innah, "zauna shazim kafin ta fito"
da to ya amsa haɗi da komawa kan sofa ya zauna yana amsar yaron Aunty zainab, tun da ya shigo yaron ke miƙo mashi hannu alamar ya ɗauke shi,amsar shi yayi haɗi da tambayar ya sunan shi "gaskiya shazim mutuncin ka ra gage ne yanzu bama ka san sunan shi ba kenan "
gwaggo Halima ta ce " a'a kar ki ga laifin shi,yaron da ba'a nan kika haife shi ba, kuma ma duka yaushe kika dawo ƙasar ne "
Aunty Zainab tace " haka ne, sunan shi Aayan "
" Allah ya raya " yace da Ameen Aunty zainab ta amsa,
Maryam samun gwaggo Uwani tayi kwance kan gadon innah amma ba bacci take ba, zama maryam tayi bakin bed ɗin tana faɗin "mamy wai shazim ne ya shigo, Aunty halima tace kizo ku gaisa "
"ɗan rainin hankali sai yanzu yayi lokacin zuwa kenan" maryam tace " ko dai aka ce ya zo ba "
"haka ne kuma yanzu haka wani cikin su yaya ne yace yazo ya gaishe da mu"
" ba ma mamaki " tashi gwaggo Uwani tayi tana faɗin "bari naje na same shi" ta faɗa haɗi da kama hanya ta fice, bin bayan ta maryam tayi.
firar suke cikin kwanciyar hankali shazim dai na sauraron ya ƙagara ta fito dan ya samu ya koma part ɗin su bacci ne cike da idanun shi.
gwaggo Uwani ce ta fito marya na bayan ta, a bakin ƙofar ɗakin innah ta tsaya tana faɗin " isashe ai nayi tunanin kafi ƙarfin gaishe da mutane "banza yayi da ita yana yi ma Aayan wasa duk da ya san da shi take ba tare da ya kalli in da take tsaye ba
"Eh dole kayi banza da ni saboda ga mahaukaciya sabon kamu na magana "ko kallon in da take yanzu ma bai yi ba,tsaki yaja a ranshi yana faɗin "da ya san masifa zatayi mashi da bai tsaya ba " masifa take ta in da take shiga ba tannan take fita ba, da dai ya gaji da jin banbamin da take, ajiye Aayan yayi kan sofa haɗi da kallon gwaggo halima yace "sai da safe "
"Allah ya tashe mu lafiya " da ameen ya amsa haɗi da kallon Aunty zainab yace "sai da safe "
" to Allah ya kaimu " ficewa yayi yana jiyo muryar gwaggo Uwani tana zazzaga masifa kamar ta ari baki " zanyi maganin abun da yake damun ka mara mutunci "
gwaggo Halima tace "gaskiya yaya kina abun da bai da cewa, yaron nan fa har ya tashi zai tafi na tsayar da shi dan ku gaisa amma kin fito kin rufe shi da faɗa mara tushe bare asali "
"Ok ni zaki ce ma haka saboda wannan yaron, ai da kin sani da baki tsayar da shi ba da kin bar shi yayi tafiyar shi "
"gaskiya yaya ki chanza, dan ko ɗazu banji daɗin abun kika yima Fatima ba, ya rinya ƙarama mi tasani game da abun da kike nufi "
"Wai sadiya magana kike son faɗa man saboda waɗannan yaran ko mi kike nufi "
"ni ba magana nake son faɗa maki ba kawai dai ina son ki san abun da kike aikatawa bai dace ba kwata kwata "
" a'a maganar dai kike son faɗa man a kan yaran da ban sani miye haɗin ki da su ba "
"Amma nayi mamaki yaya da ilimin ki kike faɗin haka,bayan kin san jinin da ke yawo a jikin ki shike yawo ajikin su amma kike faɗin haka "
"jinin da dai ke yawo a jikin ki amma ba jiki na ba "
"Ai kuwa ko kin ƙi ko kin so jinin da ke gudana ajikin ki shi ne dai ajikin su"
"Wa ni Allah ya tsari gatari da saran suka, ni bani da wata alaƙa da su "
"Ke kuwa ke da alaƙa da su, saboda uban su da kika haɗa uba da shi "
"dan na haɗa uba da uban su ba ahi ke nuna cewa sun zama jinina ba"
"Wannan kuma kin faɗi san ranki ne "
"Wai sadiya miye ribar ki idan kin goyi bayan yarannan ne, wata riba gare ki "
"ni kuwa ke da riba, saboda zumunci Allah ne yace ayi shi kuma na riƙe shi da hannu bibiyu "
"wahalar banza kike, yau da ace uban nasu kafin ya bar duniya ya bar wani abun arziƙi to da nace kina yi ne dan ki samu wani abu a wurin su "
"ko mi nake inayi ne dan Allah, kuma maganar mahaifin su dake, ina tuna nin ko bai bar komi ba da zai rasu ina tananin sai da ya rufa maki asiri ke da ƴaƴan ki da ƴan uwanki kafin ya bar duniyar"
"Wai dakata sadiya, gori kike son yi man kan abun da sadiq yayi man "
"Ni ba gori nake maki ba saboda ba ni nayi maki ba, ina tuna maki ne da abun kika manta "
"gorin dai kike man sadiya kuma na gode "
"duk yan da kika ɗauka yaya, Allah dai yasan mi nake nufi " Innah tace "wallahi kin bani mamaki sadiya, ƴar uwar ki kike ma gori akan abun da wani yayi mata, miye dan gan takar ki da shi da har zaki ba ɗe baki kiyi ma ƴar uwar ki ta jini gori "
"mama sai dai ku ƙi fahimta ta amma ni ba gori nike mata ba, kuma innah ki dai na cewa ba ni da alaƙa da su, duk duniya basu da wasu da zasu nuna a matsayin dangin uban su bayan mu, muma haka kamar yan da zamu nuna su mansoor a matsayin ƴaƴan yan uwan mu haka suma dole mu nuna su a matsayin haka"
gwaggo Uwani tayi cab tace" ki dai nuna su amma ba dai ni ba, bari kiji sadiya na san ko mi yasa kike wannan faɗe faɗen "
Aunty Zainab ce tace " dan Allah mama Aunty kuyi haƙu ku dai na wannan gan ganun ba dan ni ba "
"taya zaki ce haka zainab, gara dai ta ƙarasa yi man gorin da ta fara "
"Ni dai ko mi ki kace naji, kamar yan da muke zuminci lokacin da yake raye yanzu ma bazan fasa ba "
maryam tace " haba mama dan Allah karku zama ƙana nan yara a gaban mu, mu ya kama ta ace munyi haka kunyi mana faɗa amma ba wai ku ba" ta shi gwaggo Halima tayi ta fice daga part ɗin zuwa na uncle ahmad, bedroom ɗin mama ta nufa, tsit ta same shi ba kowa mama na ɗakin abba, hasken ɗakin ta kashe haɗi da hawa kan bede ta kwanta zuciyar ta duk ba daɗi.
Lokacin da ya bar part ɗin innah part ɗin su ya nufa, a main parlor ya zauna kan sofa, gaba ɗaya ji yake zaman abujar nan kamar yana kan ƙaya yanke shawara yayi gobe ko da da yamma ne sai ya bar abuja ya koma lagos, ya ɗan jima zaune sannan ya tashi zai nufi sama zuwa bedroom ɗin shi, karab idanun shi suka sauka kan mutum dake zaune kan dinning ya duƙar da kai kan table , tashin farko bai gane ko waye ba sai da ya matsa dinning area sannan yaga ashe macece kuma fatima, ƙara sa wa yayi haɗi da kiran sunan ta amma ko motsi bata yi ba, bubbuga table ɗin yayi still bata motsa ba abun ya ɗaure mashi kai wane irin bacci ne take yi haka har bata ji kiran da yayi mata ba, gaskiya ba lafiya, hannu yasa ya ɗago da kanta, ya salam ya furta ganin ko numfashi bata yi, ruwan da ke kan dinning ɗin ya ɗauka buɗe marfin jirkar yayi ya ɗan zuba a hannun shi shafa mata yayi a fuska amma bata motsa ba, sai da yayi haka kusan sau uku sannan ta ja wani dogon numfashi "mi ke damun ki? " ya jefa mata tambaya, biji biji take kallon shi saboda nauyin da idanun ta su ka yi mata, sake jefa mata tambayar yayi, ware idanun ta tayi a kan fuskar shi, "da ke nake magana, mike damun ki "
da ƙyar ta iya furta "babu komi yaya, nayi dinner ne shine bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba "
"ok da man a nan kike dinner "
"a'a yau ne nayi a nan "
"Zaki faɗa man mike damun ki ko sai na ɓata maki "
"da gaske nake yaya ba komi " tsawa ya daka mata yana faɗin "ina wasa da ke ne, zaki faɗa man ko sai na ci mutuncin ki " fashewa tayi da kuka " Aunty Ilham ce ta mare ni "
"ta mare ki da kika yi mata mi keken "
"Wai dan momy tace na kira su su zo su ciki abinci, to shine sai tayi magana ni kuma ban ji ta ba, dan kawai nace banji ta ba shine ta mare ni Aunty feenah ta shaƙe man wuya "
"Ok shine kika zo nan kina kuka har sai da numfashin ki ya ɗauke ko "
"ba kuka nayi ba, bacci ne ya ɗauke ne "
"ok yayi, kinsha magani "
"Eh sa'ada ta kawo man "
" to yayi, ina so gobe tun da safe ki haɗa duk wani kayn ki dake can part ɗin gobe zamu koma lagos ina fatan kin ji ni"
"Eh yaya naji "
"ta shi ki wuce kije ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ƙofa zata fita " ina za ki "
"zanje na kwanta ne "
"Ok shine kika kama hanyar fita "
"Zanje ɗakin sa'ada ne "
" ba can zaki ba, ɗakin ki zaki wuce " da to amsa haɗi da nufar sama ta shiga ɗakin ta bata taɓa kwana a cikin shi ba, tashi shima yayi ya nufi na shi bedroom ɗin,a jiye wayar shi yayi kan bed ya shiga toilet ta ɗauro alwala, carpet ya shimfiɗa ya shiga gaba tar da nafilfilo da yake yi duk dare, bayan ya gama light ɗin ɗakin ya kashe haɗi da hawa gadon shi ya kwanta, bacci ya ɗauke shi cikin ƙan ƙanin lokaci
*WASHE GARI *
Bayan ya dawo daga masallaci ɗakin fatima ya fara liƙawa dan ganin a wane hali take ciki, zaune ya same ta kan carpet ta gama sallar subhi, gaishe da shi tayi, amsa mata yayi yana faɗin "ya kike jin jikin ki yanzu "
"lafiya lau"
"to masha Allah, ki ƙara shan maganin ki " da to ta amsa mashi, ta shi yayi ya bar ɗakin ya nufi nashi, wayar shi ya ɗauka ya kira ammay ya sanar da ita yau zasu dawo, cewa tayi sai dai shi ya dawo yau amma ban da fatima,bai faɗa mata