Showing 24001 words to 27000 words out of 92879 words
Banda gabaki daya Bata lura dasuba Dan batasanda suna dakinba Dan hakan taqarasa fitowa Kai tsaye ta rufo toilet ta nufi closet tana cewa"
Hanifa ruqayyat takawo wankin kayan da aka dauka jiya??
Tsit dakin yayi musamman Hannah data waiwayo da sauri ta kalli marshal din taga idanuwansa basa kan Naj suna kan wayarsane ta kalla Hanifa da ita Kuma Jalal din take kallo Dan kuwa akan idonsa sak Naj ta fito Kuma ta tabbatarda ya qarewa Naj din kallo sak kafin ya basar ya dauke Kai.
Da sauri Hannah ta miqe tana cewa"
Umm Naj Ashe kina ciki bamu saniba sorry Bari mukoma Palo zamu jira ki Gama shiryawa tukuna.
Wuta Naj ta dauke tareda waiwayowa cikin tsananin mamaki da takaici ga sabon baqin cikinta ba Hannah ce kawaiba akansa idonta ya sauka daidai ya dago zai miqe ya fice idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke idonta suna sauyawa kin wani irin baqin ciki da kunya da takaici lokaci daya suna taso mata ta juya Kai tsaye Takoma toilet din daukeda kayan barcin data fitar zata saka a hannu.
Kodata Gama shiryawa ta fito basa dakin sun tafi har Hanifa Bata dakin tana dakin hajjo taredashi da hajjon suna magana sbd gobe zai koma duk yanda taso kasa Masa maganar Naj din kasawa tayi ta kalli fuskarsa dake fresh Kamar wani Dan baby hankalinsa nakan hajjo Yana sauraron bayanin datake Masa akan dawowarsa yanzu akan lokaci sbd akwai nauyin iyali akansa.
Marshal bazakai magana da itaba kafin ka wuce?
Kaji koda akwai wani abun datake buqata?
Shiru sukai suna jiran Jin amsarsa saisukaga ya miqe Yana kallon agogon hannunsa yace"
Zanje na kwanta gobe zantashi da wuri.
Kofa ya nufa hajjo tace"
Goben ka tabbatarda kayi mgn da ita kafin ka wuce.
Da umarni tayi maganar ba wani Wasa acikinta shiyasashi Dan dakatawa batareda ya juyoba kafin ya taka yafice Hanifa na bayansa tana sake Dan saka Baki a maganar.
Sam ba irin wannan auren yasoba Wanda kowa zai ringa shiga tsakanin mu'amalarsa da matarsa sbd yanason yayi nutsatsiyar rayuwar aure Mara hayaniya da soyayyarda baya buqatan shigan wani zancen,
Ya lura zata ringa hada Masa tarin mutane acikin rayuwar auren Wanda baya buqatan hakan Amma zaiga tsarin dazai dauka.
Koda ya Isa sashensa Saida yakuma wanka da ruwan dumi kafin yayi Shirin bacci ya kwanta.
Bacci me qarfi da dadi itama yau tayi shiyasama tayi lattin tashi sallar asuba Dan sai guraren qarfe bakwai ta bude idanuwanta dake tareda sauran bacci ahankali tana Dan motsawa ta lumshe ido sbd Jin sabon qamshin daya Shiga hancinta ta tashi zaune tana 'yar miqa botiran gaban rigarta uku na sama suna budewa sbd miqar datai ta zuro qafafunta qasa tareda miqewa tsaye idanuwanta suka sauka Kan mutum a tsaye cikin dakin Yana kallonta jikinsa sanye da _Prada-gabardine straight leg trouser _ brown sai White spread collar long sleeves gabaki daya dakin ya gauraya da qamshinsa fararen idanuwansa ya zuba Mata akaro suna yawa ajikinta sbd tunda aka daura Masa aure da ita ake maimaita kalmar girmansa datai Wanda haryau yakasa ganin wani Abu dayake tunanin ya girme Masa
A taqaicema kallon dayake Mata yasa yake qara ganin zamtowarta qasanshi.
Kallon dayake Mata yasata dakatawa daga wucewar datasoyi ta shige toilet saita nufi kofar ficewa daga dakin zata fice bacin ran dake ranta Yana bayyanuwa kan fuskarta akaro na farko da mace ta wucesa tabarshi tsaye
Kai tsaye ya damqi hannunta tareda dawowa da ita baya ya tsayar da ita gabansa fuskarsa a hade tsaf ya kalli hannunta datake kokarin fuzgewa a fusace batareda tace komaiba Dan bazata iya bude Baki Tai Masa mgna ba Sam,
Ba wani riqo yayi Mata ba Amma gabaki daya takasa qwacewa ta dago a fusace ta kalli fuskarsa idonsa cikin nata ta janye idonta Kai tsaye tace"
Meye hakan?
Kabar hannuna.
Wannan auren ba wani aureneba kamar kowanne dazai baka Daman tabani so can u get your hands off me.
Sabon kallo yayi Mata Jin abindata fada daya basa mamaki Dan baiyi tunanin zata iya magana Haka ba.
Fizgota yayi ta Fado jikinsa ya dago shanyayun idanuwansa ya zuba Mata Yana kafin ya kalla kirjinsu daya manne Dana juna tana ganin hakan ta qwace da qarfi cikin tsananin bacin rai tareda turesa da iya qarfinta yayi baya ya zube kan gadon dakin kafin ta juya ya janyota tafado jikinsa daidai turo kofar Hanifa data shigo dakin Hannah na bayanta Jin shiru sbd dama itace ta fito din tace yashiga Naj din na ciki Dan wucewa zaiyi.
Da sauri a firgice Naj ta waiwayo kofar tana kokarin tashi daga jikinsa idanuwanta na cikowa da hawayen baqin ciki da bacin Rai
Hanifa kuwa juyawa tayi da sauri tana cewa"
Sorry sorry.
Hannah kuwa da sauri ta qaraso gurin tana Kama Naj dakeson tashi tana cewa"
Bari na taimaka Miki.
Sakinta yayi yana tashi daga kan gadon Kai tsaye ya fice daga dakin Yana duba agogon hannunsa sbd lokaci dayaso shige Masa Bai luraba.
Hajjo Kamar koyaushe idan zai tafi har mota take rakasa itada Hanifan Haka suka fito Hannah na gefensa tana fada Masa irin yanda zatai missing dinsa a can harabar gidan ya tararda Dad Alfa dazasu fita tare tareda mum Malika daketa zuba nata iyayin na zatai kewarsa matsayinta na uwa.
Gidansu Naj yashiga tareda Hanifa yaje yayiwa umma bankwana tareda bar Mata abindaya Saba Bata duk yazo idan zai koma hakama Dadah wannan karon kyautar dataso firgitata yayi Mata kafin yafito tareda Dattijo suna maganar Yana sanar dashi abar Naj din taci gaba da aikinta idan tanada ra'ayin.
Motarsa data sojojinsa lokaci daya suka tashi sukabar kofar gidan wasu na 'yar murnar zasu samu 'yancin unguwa zakai iskancinsa cikin anguwa yanda kaga dama ka tada hayaniya da rigima son ranka tunda sojojin Marshal sun tafi sojojin dake tsoron gidan basuda muguwar fitina da ikon wahala Kamar na Marshal din matuqar Yana gari ko Rigima da fada andaina a layin Dana bayansa sai Kuma suntafi Dan Haka yau kowa yayi yanda yaga dama.
Toilet tashige saidatai kukan baqin ciki Mai isarta kafin ta iya alwala ta fito baqin ciki da kunyar kanta na kamata tayi sallah tana idarwa tun kafin Hanifa tadawo dakin Takoma tayi kwanciyarta ta rufa tana rufe ido Dan komawa bacci saidai tasan halinda zuciyarta take ciki bazata iyaba.
Hanifa data dawo dakin Bata wani jawo zancen komaiba itama Takoma ta kwanta tana murmushin abinda itace kawai tasan metakeji aranta.
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
*_DM 17_*
Koda tagaji da kwanciya da kame fuska taga hakan zai sake cutatar da itane sai kawai ta watsar da al'amarin ta sakewarta taci gaba da abun dayake gabanta tayi wanka ta shirya cikin riga da wando na Shan iska tafito ta nufa kicin ta hado abin datake buqatan ci tadawo dining ta zauna tanaci Hanifa ta fito itama a shirye cikin atampa doguwar riga tayo gurinta tana cewa"
Zanci Nima yunwa nakeji.
Qarasowa tayi ta zauna tana kwada Kiran ruqayyat tace"
Ki kawomin abinci Nima inajin yunwa sosai.
Sunacin abincin tanata jawo fira da zantuka kala kala Wanda dama tasaba itace me janyo Hira a tsakaninsu itace me zancen itace me Hira.
Palo suka dawo suka zauna bayan sunyi sallar azahar da akai suka dasa Hira hajjo na daki yau batajin Hira karance karancen Islamic books dinta takeyi.
Da yamma sosai saiga Sarah takawo Mata wasu files da ake buqatan tayiwa signing Nan ta maida hankali kan takardun tana dubawa Sarah na qara koro Mata sauran bayanan ayyukan dasuke zaman jiranta a office din tanason ta sanar da ita Abbas yadawo aikin da kowa yayi tunanin zai ajiye Amma Kuma ganin Hanifa yasa takasa fadar maganar tunda yanzu Naj din surukarsu ce kawo Mata maganar wani ba daidai bane zata Bari sai Takoma office din zata sanar Mata.
Ganin hankalin Naj yakoma kan aiki gabaki daya dama ita abida yasa takeson aikinta sbd shi kadaine zata zauna tayi batareda wani surutu ko hayaniyaba shirun tana aiki Yana bada nutsuwa Dan Haka Hanifa tabarta Takoma kicin gurinsu ruqayyat suna aikin abincin dare dama ita tana aiki cikinsu lokuta da dama sbd tanada sha'awan girke girken.
Sai bayan magriba tagama duba ayyukan da Sarah din takawo Mata suka tashi sukai sallah kafin Sukaci abinci Sarah tayi shirin tafiya gida suka fito tare ta rakota har waje tareda miqa Mata 10k tace tadauka drp na taxi taje gida.
daidai ta juya zata shige ta hango Hannah tafe tun Bata qarasoba tayi wucewarta Dan bazata iya da sauraren maganganuntaba.
Tana Isa daki ta wuce saidatai sallar ishai kafin tayi wanka tayi Shirin bacci takwanta sbd tana jiyo hirarsu Hanifa har lokacin Hannah na sashen.
Washe gari Haka ta wuni tana aikin wasu takardun data saka Sarah kawo Mata tun tanayi sama sama kwanaki suka Dan fara ja kusan tadawo da aikin office dinta gida takeyi saidai Sarah Dake faman Shan yawo tsakanin office da zuwa gidan kullum.
Hajjo data lura da aikin na Sanya Naj din samun nutsuwa sai tafadawa Dad Alfa akan maganar komawar Naj din aiki duk da Bata wani so Naj din Takoma aikinba Amma Haka ta hakura tabari saidai tasan JALAL zaiyi wuya yabari tunda ita din yanzu matarsace.
Dad alfa dakansa yayiwa Marshal magana cikin nasa mamakin yaji Kai tsaye yace abarta taje
Shikuma kawai bayason arinqa nanata Masa maganar auren da nauyinta dake kansa Dan tunda ya dawoma yamanta da maganar auren yake aikinsa da rayuwarsa yanda ya Saba ko tunota sai Yana waya dasu hajjo yakeyi idan sun jeho Masa maganarta.
Ta bangarentama tunda aka Bata damar komawa aiki tafisa mantawa da auren musamman da Dad Alfa ya siya Mata lafiyayyar sabuwar motar datake hawa Dan Haka yanzu aiki takeyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,
Babu damuwa da tunanin fada da gorin dattijo, Dadah da ummanta akan rashin aure saima kulawa da qauna dasuke nuna Mata a yanzu din Wanda yake na lallabawa kada ta bijire auren ya kwabe lissafi yadawo musu sabo,
Ta bangaren office kuwa yanzu girman datake samu gurin ya zarta na kowa dake ALFAS din sbd yanzu tana amatsayin Matar me company dinne sbd sanin da kowa yayi Marshal shikeda 60% shares a company din.
Abbas duk wani Abu dazai hadasu bayan meetings batabi sbd har lokacin Yana sauran 'danyar haukarsa atare dashi Dan kuwa kallo yake Mata harna qurulla wani lokacin Kuma harda 'yan maganganu Amma Bata taba ko kallon inda yakeba Dan dama wannan tun suna tare yasan halinta dabi'artane rashin tankawa da kulawa.
Qarshe sbd nunawa da son nuna rashin gazawarsa da kausar yafara soyayya receptionist dinsu Kuma cikin gaggawa suka fara gabatarda komai lokaci qanqani saigashi Ana sanarwar aurensu Nanda wata biyu masu zuwa.
Duk wannan sha'anin nasane yakeyi shi kadai Dan kuwa ko hankalin saurara Bata badawa idan Sarah na kawo Mata zancen abindayeke faruwa bare ta fahimci menene dinma yake faruwa.
Sosai yanzu takejin dadin rayuwarta Babu takura Babu wani damuwa Haka take gudanarwa,
Kullum zata tashi tayi Shirin office tafito tasa masu aiki suyi Mata abinda takeso taci taredasu hajjo da Hanifa, tafito taje gurin dad Alfa tai Masa gaisuwar safe kafin tafito ta wuce aiki,
Idan tadawo zatai wanka tayi sallah taci abincin tayi baccin yamma kafin tatashi tayi sallar magriba sai suyi firar dare dasu hajjo wani lokacin idan Batai baccin yammaba gidansu take zuwa acan take baccin dakin ummanta kokuma firarta dasu duk da ba itace me firarba Yi akeyi tana Dan amsawa da eh ko aa sai ido datafi sauraron hira dasu.
Ahaka lokaci Mai Dan tsayi yaja tasamu sauyi sosai na jiki da rayuwa Dan kuwa fatarta ayanzu tafi samun qarin hutu da lafiya tareda kyau.
Tayi fresh sosai sbd har wani irin haske take qarawa kullum musamman dayake itama Bata cika Shiga Rana ba Dan rayuwarta bazata iya yaushene zuwanta kasuwaba kokuma siyayya irin gurare masu Rana sosai haka yawanci siyayyarta online shopping takeyi akawo Mata har gida sai idan sunso su fita da Hanifa zuwa manyan malls Haka siyayyan Yan abubuwan amfaninsu kaman su turaruka dasu Mai sai undies da qananun Kaya Haka
Musamman ita Naj indies basa isarta kullum cikin siyansu take.
Gabaki daya rayuwarta ta manta da auren dake kanta sbd rayuwar data samu kanta aciki ta rashin takura shiyasa ta sake sosai tana gudanar da rayuwar yanda takeso.
Kamar dai yanda Dr said yasake hadawa Hanifa appointment da Dr Kenneth a Sweden yanzu lokacin zuwanta ya qaraso Dan Haka suke cikin damuwa musamman Hanifan Wanda tasaka ran samun haihuwa sosai a ranta.
A yanda suka bibiyi likitoci tun shekarun aurensu na farko an tabbatar musu da cewa Hanifa bazata iya daukan ciki da kanta ba ma'ana zaiyi wuya saidai ayi Mata dashensa Wanda ta daga hankalinta sosai tashiga damuwa Suma sumshiga damuwa sbd halindata shiga qarshe akai dashen cikin na wata biyu ya fita shima tashiga wani mawuyacin hali na tashin hankali da shiga qunci da addua da komai aka samu ta dangana tayi tawakkali tadawo daidai saidai sun dibar Mata lokacinda zata dawo asake Mata dashen Wanda shine lokacin yayi yanzu saidai Kuma damuwa da tsoron ko zata samu ko bazata samuba ya Hana zuciyarta sukuni duk yanda takeson danne damuwar kasawa takeyi Wanda yake sake sakawa hajjo tausayinta sbd tana cikin jarabawa ta lalurar lafiya yau gobe Babu ga wannan jarabawa ta rashin samun haihuwa Dan ma tanada tawakkaline soda dama Koda damuwar abin ta taso Mata tana dannewa da rokon sassauci gurin ubangiji gashi a zuriar gidan basuda iyali da yawa sune suke fatar su cika gidan da nasu yayan Amma batajin za'a samu daga gareta kila saidai 'dan uwanta JALAL.
Damuwar da Hanifa take ciki tasa gidan kusan kowa damuwar yakeji ita kanta Naj din tunda aka tsaida ranar tafiya Sweden din ta nema hutu office ta daina zuwa koyaushe tana tareda Hanifar wadda damuwa tasaka ciwon gefen ciki ya kamata cikin lokaci qanqani ya kwantar da ita Nan hankalinsu yakuma tashi ga tafiyar nata sake qarasowa Dan saura Kwana biyu su wuce wannan karon tareda Naj din zasu sbd zasu hade da Isma'eel acan sai Hannah data nace akan zataje itama sbd ta tabbatarda Marshal zaije can daga Hawaii.
Kwana biyu Ana fama da jikin Hanifan ansamu ta 'dan ji sauki ta warware Haka suka lallaba suka tafi tareda Dr sa'id din Wanda yake likitanta.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
*_DM 18_*
Koda jirginsu ya sauka Ana ruwan sama Dan hakan Isma'eel ne yazo da mota ya daukesu Kai tsaye suka wuce _copperhill mountain Lodge_ inda marshal yake zama matuqar Yana Sweden din,Koda suka Isa room cards din dakunansu suka karba suka wuce
Dr sa'id gabaki daya ba'a Lodge din ya saukaba nasa masaukin ya nufa Wanda yasaba zama Dan shima Yana Dan zuwa qasar akai akai Dan Haka dakin Isma'eel da matarsa Yana farkon floor din saina Hannah agaba tukuna na Naj acan qarshe Wanda dakin Marshal ne Isma'eel yabata card din batareda yayi tunanin komaiba tunda dai yasan zasu iya zama daki daya.
Dama sai asuba suka sauka qasar Dan Haka Koda suka shiga dakunansu har qarfe Tara na safe ta kusa Dan Haka wanka ajiye luggage dinta tayi cikin wdrp ta tube kayan jikinta ta jefe laundry ta nufi toilet ta sakarwa kanta ruwan zafi tana lumshe ido sbd Jin dadin saukansu a jikinta ta gasa koina nata tafito daureda towel qarami tana goge jikinta sai alokacin take qarewa dakin kallo da irin tsarinsa daya burgeta Dan kuwa komai haduwarsa a tsarance da natse take musamman komai na dakin is white ta nufi wrdrp ta fiddo qaramar akwatinta ta fiddo kayan shafarta ta ajiye gaban mirror ta dauki wasu kayan bacci riga da wando ta dawo gaban mirror sama sama ta shafa body mist ta saka kayan baccin ta dauko wayarta ta duba alkiblan sallah ta Dora jallabiya kan kayanta tayi sallolin da ake Binsu Ana idarwa ta cire jallabiyar ta maida ta Haye gado tashige bargo sbd wani irin bacci da gajiya takeji gabaki daya jikinta ba qarfi,
Wani irin bacci me Dadi da nauyine ya dauketa cikin nutsuwa gashi har lokacin ruwan saman akeyi Bata farkaba sai qarfe biyu da mintuna shima knocking kofan da akeyine ya tada ita ta bude idanuwa ahankali tareda tashi zaune ahankali taji Ana cewa"
Ur Lunch is here Sir.
Saukowa gadon tayi ahankali ta zura slippers din dake dakin masu taushi ta nufi kofar tana Dan mamakin Jin Sir din data ambaya ta bude tana amsa gaisuwar waitress din data kalleta da mamakin ganin mace sbd qarqashin sunan Deen Marshal akai booking dakunan Kuma a iya saninta wannan dinne nasa shigowa tayi ta nufa dining ta jere mata abincin tareda ruwa da drinks masu qarfi ma'ana energy drink Wanda Marshal din Kesha dama sune ake kawo Masa aduk lokacinda za'a kawo Masa abinci indai Yana lodge din ta juya ta fice bayan tagama tunda Babu ruwanta da sanin waye Naj Kuma Ina me dakin.
Brush tayo tafito ta nema wayarta ta zare layinta ta saka layin qasar da tun kafin su iso Isma'eel ya siya Mata dama itace kawai batadashi Amma dukkaninsu suna dashi har Hannah wadda dama tasaba yawon qasashenta da qawayenta ita dinma ta Dan fita wasu qasashen Amma ba dayawaba gurin aikinta da yawon ganin likitocinda Hanifa keyi tun kafin tayi aure Dan Haka itama sosai take waye da harkan qasashen na waje musamman ma dayake tafisu zama a miskilancen dayake bayyanarda ajinta sai hakan yake fin yimata kyau da fitarda wayewarta.
Bayan ta saka layin yahau massage din Isma'eel yashigo Mata akan shida Hanifa sun fita zuwa wani gurin Hannah ma ta fita zuwa gurin friends dinta saisun dawo.
No hajjo tafara Kira suka Dan Jima Suna magana kafin takira ummanta suna Gama magna ta ajiye wayar ta nufa dining din ta zauna tana duba abincin
duka ba taste dinta bane Amma Haka ta Dan ci kadan Tasha drink dinda Bata tsaya dubawaba sosai tafin ta miqe tabar gurin tana duba chats a wayarta tsawon mintuna saiga room service suka sake gyare gurin aka fitarda kayan abincin sauran drinks din Kuma aka saka a fridge