Showing 3001 words to 6000 words out of 92879 words
kalli fuskarta zuwa kirjinta da kafadunta dake bayyane suna wani qyallin haske da samun lafiyar fata ta maida kallonta kan fuskarta datafi komai kyau da daukan ido atare da ita ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tareda sauke numfashi kadan kafin ta janyo lotion na jagggins tana shafawa kadan kadan Dan batason Mai da yawa Ta miqe bayan ta shafa turaren POSSES ajikinta tareda mist na Rednight ta zare band din kanta ta gyara daurin gashinta tayisa sako sako sbd Taji dadin kan nata ta nufi wardrobe ta Ciro doguwar riga Mara nauyi zata saka wayar Hanifa data bari kan mirror din nata takawo haske tana vibrating ahankali ba qara sbd Wanda Dabi'arsune rashin sakawa waya qarar ringing Dan kusan itace ta koyawa Hanifan hakan qarar waya na damunta shiyasa Sam wayarta Bata qara idan Ankira saidai vibrating shiyasa itama Hanifan ta koya sbd Naj din.
Ahankali ta waiwayo ta kalla wayar taga sunan dayake Kai _MARSHAL_
dauke Kai tayi tana cigaba da saka kayanta Dan tunda takeda Hanifa Bata taba daga wayar 'dan uwanta ba idan yakira Wanda shi kadaine kawai Bata daukan wayarta idan shine yakira idan har Bata kusa tun kuwa tasowarsu suna qananu haryanxu.
Sanin baya Kira biyu 'daya yakeyi yasa ta sake waiwayo wayar tana kallon sunan destination dinda caller ID ta rubuto _HAWAII US STATE_
Hanifa Babu wani Abu a duniya dayafi Mata qanin nata Wanda su biyu kacal mahaifiyarsu ta Haifa ta bar duniya Wanda tazarar shekara uku ce a tsakaninsu yanayin aikinsa da girman matsayinsa yasa baya tareda ita wayama sai yasamu lokaci suke iya Yi Dan Haka Babu abinda Hanifan Bata Wasa dashi irin waya da marshal din Dan Haka bazata so ta rasa kiranba takai hannu a natse ta dauka tareda nufar kofa ta bude ta fito ta kalli zainab dake kusa tace"
Miqawa Hanifa wayarta Ana Kiranta.
Karba zainab tayi ta nufi Hanifan da sauri ta miqa Mata cikin sa'a kuwa har lokacin Kiran Bai katseba tana ganin me Kiran ta dauka tana Kiran sunansa cikin tsananin kaunarsa da kowa ya shaida kaunace me girman gaske a tsananinsu.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022π₯_*
*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*ππ
Dβaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*πππ
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*ππ
09134848107
*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_
3
Komawa Naj din tayi Dan tayi sallah tana Shiga dakin tun kafin Hanifan ta qaraso dakin ta tayar da sallarta Dan tasan Babu ranar da zasuyi wayan Hanifan Bata hadasu ba suka gaisa Wanda daga ita harshi din basa buqatan gaisawar sbd shi dai Bai taba gaidata ba hakama itama batajin zata iya gaidashi din tun koba komai shine qani Amma gabaki daya matsayi dayake dashi da jin yazama billionaire yasa baya iya gaida mutane kokuma tace wasu mutanen tunda Yana gaida Hanifa da hajjo kakarsu,itadaima gabaki daya Bata wani buqatan shiga rayuwar kowa musamman irin tasa rayuwar wata iri kamar ta Mara kowa komai nasa yawanci kafin suji sunfara gani a labarai kullum koken hajjo da Hanifan rashin dawowarsa akai akai duk da dai taga kamar yafara sauyawa Dan yanzu Yana Dan yin kokari a shekara yazo so uku ko so biyu Haka.
Harta kammala sallar azahar data la'asar da aka gama idarwa lokacin Basu Gama wayarba wadda fiyeda Rabin harshen zancen turanci ne Hanifan keyi Dan Kamar yafi Kama bakinsa yanzu fiyeda hausarsa bugu da qari ma duk rayuwarsa yanzu idan Basu yakira bama baida Wanda zai Kira suyi yaren hausan sbd dad dinsu dai Yafi zama yanzu a Angola sbd tun wasu shekarun aiki da yayi acan bayan rasuwar mahaifiyarsu ya auri wata Yar can wadda gabaki dayama Bata wani Jin hausa Saida tahadu dashi ne ma tafara koya harta iya bayan auren danshi yasa ko dad din yakira sbd duk sun sama zama da yare yanzu Basu wani cika Yin hausar ba sai dai idan sun Kira su Hanifan da hajjon.
Kwashe dadduman tayi ta nade tareda zare milk hijab din datai sallan ta ajesu cikin wardrobe ta juya ta nufa water dispenser dake dakin nata Dan Shan ruwan dumi kawai ta matso ruwan dumi cikin cup tadawo ta zauna kan kujera tareda bude laptop dinta tana Sha tana duba saqon datace Sarah taturo Mata ta email.
Tana cikin aikin wayarta takawo haske tana vibrating ta dan kalla wayar ahankali da idanuwanta dake bayyanarda Bata buqatan Kiran kowa a lokacin taga sunan Dr sa'id ajikin wayar take ta saki ajiyar zuciya siririya sbd bazata iya sharesa ba kokuma nuna qosawarta dashi din sbd tsananin mutuncinsa datake gani dakuma yanda shima yake matuqar mutunta dakuma kulawa da ita.
Kallon Hanifa dake waya har lokacin tayi kafin ta dauki wayar tana amsa Kiran cikin taushin muryarta me zallar daukan hankalinsu sbd nutsuwa wadda sukafi daukanta da Jan aji tace"
Barka Dr sa'id.
Murmushi yasaki me Dan qaramin sauti daga nasa bangaren sbd yasan iya gaisuwarta kenan akoda yaushen
Ita bame hayaniyar surutu bace Dan Haka cikin taushin murya shima yace"
Kinbar office kokuwa na biyo na kaiki gida?
Ajiye cup din hannunta tayi bayan ta qarasa shanye ruwan tana kallon screen din laptop din gabanta tace"
Nadawo tun kafin time din tashina yayi sbd Ina fama da Dan ciwon Kai
Thank you.
Ajiyar zuciya ya sauke boyayya kafin yace"
Sorry,
Ki huta to idan natashi Zan biyo na dubaki.....
Cikin nutsuwa ta katsesa da cewa"
No kadaka wahalan da kanka gurin zuwa ba stress ne kawai na Dan meeting din danayi Amma yanzu yariga ya wuce.
Ko Naj Bata fadaba yasan damuwan fitanar Abaas ce bataso Dan ya tabbatarda fitarsu jiyan saita kusa zautarda Abaas din Wanda shi tuni ma yake Masa kallon Mara lafiyar qwaqwalwa Dan wasu abubuwan dayakeyi sunfita daga dabiun lafiyayyun mutane,
Kishinsa na hauka ne bana mutanen dasukasan kansu bane,
Fitinarsa ta marasa ilimi da wayewa ne kamar wanda baida ilimin da wayewar,
Shi gabaki dayama ya rasa ta Yaya Macen datake da tsananin aji da sanin darajar Kai tareda wayewa irin Naj ta yadda da auren namiji kaman Abaas lamido,
Ta Yaya Allah yabashi irin wannan sa'ar me girma ta samun Naj amatsayin Mata.,
Shi Yana tsananin son Naj tareda sanin qimarta Dan Haka bazai taba cire Rai ga samunta ba matuqar ba aurenta aka daura din ba da Abaas shiyasa ma duk haukan Abaas din Bata damunsa Dan bayama gabansa shi Naj din ce kawai a gabansa Dan kuwa irin son dayake Mata idan ya aureta zai maidata sarauniyar rayuwarsa Dan kuwa zai tattaleta tamkar ita kadai yakeda ita a duniya.
Kashe wayar tayi tana ajewa daidai itama Hanifa na aje tata wayar ta dawo gurin Naj din ta zauna tana janye laptop din gefe tareda rufewa tana cewa"
Naj zamuyi mgana akan Abaas.
Fararen idanuwanta ta zubawa Hanifan tana cewa"
Wai Ni rayuwata shikenan kullum akan maganar rashin aure yake?
Ahankali Hanifa ta girgiza Mata Kai tana riqo hannayenta duka biyu cikin kulawa da tsananin qaunarta tace"
My beautiful Naj tasan cewa bantaba damuwa da rashin aurenta ba sbd nasan aure lokacine dashi Kamar mutuwa ta yanda idan lokaci yayi Babu mai hanawa ko tarewa,
A zuciyata dakuma adduata kullum shine Allah yasa wannan jingikirin yazamo babban alkhairi agareki,
Wlh banajin dadin yanda su dattijo da su Dadah suka sakomin ke gaba akan rashin auren Nan gashinan umma itama tabisu tana tsangwamanki da rashin aure.
Sai alokacin tasaki wani kyakkyawan murmushi tana kallon kyakkyawar fuskar Hanifan tace"
Bana damuwa da dukkanin zancensu na rashin auren
Koba komai Baga Abaas Nan ba tunda sun saka auren 4month masu zuwa ai zancen ya mutu yanxu Ina Dan samun sauqinsu.
Bata fuska Hanifa tayi tana cewa"
Abaas lamido bazai taba auren Naj Dina ba matuqar bazai sauya hali ba.
Murmushi me sauti Naj din tayi tana riqota da murmushi akan fuskarta tace"
Kuma Kinga as long as Hanifan Naj bata Aminta dashiba Naj bazata taba aurensa ba.
Dariya suka saki lokaci daya sbd yanda haryanxu suke irin wannan wasar wa junansu
Hanifa tace"
Alqawarine ai kidainma Wasa da zancen,
Inshallah nice Zan tayaki zaban mijin danasan zai darajanta min ke tunda idonsu umma ya rufe Akan kowa Kika samu ki aura nikuma bazan yadda ba taqarasa tana 'yar dariya,
Kinga dama shima Marshal nafada Masa Ni Zan tayasa tantance Matar dazai aura sbd shima shine ya tsaya akan nayi aure da wuri sbd yanayin qarancin lafiyana kema kece Kika tsayawa Isma'eel sbd lokacin amininsa arfat yakawo kudin aurenki Kika ci amanata Kika bi bayansu Saida ya aureni da yanzu lukuman ne mijina ko?
Dariya suka kwashe da ita su biyun suna tunano lokacin musamman yanda Hanifan Bata wani so auren Isma'eel din ba Amma da hajjo da Naj din suka hade Mata Kai gurin Dad dinsu akai auren sbd dama ya dade Yana Sonta tun suna secondary school sbd 'dan yayar dad din nasu ne
Shima Marshal Isma'eel din yafi kwanta Masa sbd yasanshi sosai Yasan halayensa ba laifi Kuma shi Dama Wanda zai iya kulada Hanifan da lalurarta yake muradin ta aura din shiyasa.
Dan qaramin mayafi Naj din ta Dora akanta suka fito daga dakin har lokacin Fuskokinsu dauke suke da yanayi na dariyar tuna baya dasuka samu kansu
Anty Amina ta kallesu tana cewa"
Hanifa ki fadawa hajjo yau ba hirar dare saidai gobe kayan umma dazata aika sako abekuta zamu hada.
Anty Amina wannan fira taku keda hajjo ai yau kuwa zatayita mitan rashin firar Daren nan dakuke.
Fita sukai umma dai da guntuwar harara tabisu da ita Dan sun kasa gane abinda yake cin ranta,
Tsakani da Allah 'yarta Kamar Naj wadda kaf gidan tafisu ilimin Boko da wayewa tareda abun duniyama ace anyi sadakarta ga duk me rabo idan Batai aureba wlh zata mugun cutatuwa Dan kuwa ciwon zuciyama kamata zaiyi Amma hanifar datakeson ta karkato Mata Naj din tamafi naj din kasa fahimtarta tana ganin Kamar sun takurawa Naj din.
Dakin Dadah suka nufa tun Basu qarasa ba ta tsuke fuska Dan tana zaune kofar dakin kan kujerar roba da qaton farin glass dinta.
Dariya Hanifa tasake tana qarasawa gabanta da cewa"
Dadah my love.
Uwar harara dadar ta sakar Mata tana hararar gefen Naj tace"
Yaudarata za'a kenan?
Da sabuwar dariya Hanifa tace"
Mezaisa na yaudari Dadah me ran qarfeΒΏ
Kawai dai dama......
Cikin hanzari dakuma zallar Kokonto Dadah ta katse Hanifan da cewa"
Wlh idan har kikacemun matsala yarinyar Nan tasamu da Abbas to wlh yau daga ita har uwarta kwanan bacin Rai zasuyi mummuna kuwa
Kuma wlh gobe zuwa jibi suga 'danyan hukuncin dazansa Dattijo ya yanke Inga qarshen Boko da wayewa...
Zubawa Dadah fararen idanuwanta Naj tayi tana sauraron kalaman bacin Rai na fada na fitowa daga bakin dadar take tahau fada me tsanani Wanda yasa umma yin tsit daga aikin datakeyi Dan tana jiyo fadan Wanda aketa zubawa har ita ba'a ragawa ba qarshe ma korarsu tayi daga gabanta tana tabbatar musu da cewan aure da Abaas anyi angama idan Kuma shiyace yafasa da kanshi wlh auren sadaka zasuyi Mata can ta qarata da kyawun idanma shine take korar maza akansa.
Jiki a mace suka bar gurin suka fice gabaki daya Kai tsaye suka shige gidansu Hanifan Wanda gabaki daya Anguwar Babu kamarsa ga girma da kyau dakuma wani irin tsaro na musamman na sojoji Dan cikin gidan ma gate biyu kafin ka Isa ainihin cikin harabar gidan Wanda ke daukeda motoci na alfarma wainda ake sauyawa akai akai kusan guda shida a ajiye,
Uku na Marshal ne sai guda daya ta Dad dinsu sai daya ta Hanifan ce dayar Kuma ta hajjo ce wadda Bata cika hawa ba sbd Bata fita Sam Sam sai Dole Kuma driver ne yake tuqa ta,
Hanifa ma Sam Bata Jan mota sai Dole sbd yanayinta Wanda yasa dad dinta dashi marshal din suka qarfafa dokan rashin tuqin itama driver ne da ita sai Kuma idan zasu fita da Naj sai Naj din tayi driving.
Suna Shiga qaton palon su ruqayyat da Khadija dake palon suna gyaran yamma Wanda yake kamar Dole koba komai qaida sai sunyi gyaran safe Dana yamma suka Dan durqusa suna musu sannu da shigowo.
Kai tsaye palon dazai isar dasu dakin hajjo suka nufa suna shiga tana zaune makeken palonta me ado na qyallin arzikin duniya da Allah yabasu sanyin ac Dana qamshin turarukan wutan umman Naj daya Gama Kama koina na palon kujeru da curtains duk qamshin sukeyi me Dadi da sanyi
'yar dattijuwar na zaune fara tas da ita me zubin hasken larabawa tana sanye da doguwar jallabiyar mutanen Kuwait me Fadi tana dagowa ta kallesu tasaki wani irin nutsatsen murmushi tana kallon kyakkyawar fuskar Naj da ako yaushe take sanyata murmushi Dan Kamar yanda take tsananin so da kaunar Jokokinta biyu rak Haka take tsananin so da kaunar Naj din musamman daya zama Naj din tazama tamkar jinin gidan itama danma Naj din taqi dawowa gurinta gabaki daya saidai yau ta kwana gidan jibi Kuma tace gidansu zata kwana danma Allah yasa Hanifa ko bayan datai aure Bata barsuba tana nan gidan saidai idan Isma'eel yazo gari ya dauketa su koma gidansu Yana komawa ta dawo Nan gida sbd duk da akwai Yan aikinta Hanifan hankalinsa Bai kwantaba daya barta ita kadai da masu aiki Dan yanayinta.
Zama gefen hajjo Naj tayi tareda kwantawa ta kwantar da kanta kan cinyar hajjon ta lumshe fararen idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya ahankali tace"
Hajjona yau akan shimfidarki zanyi bacci.
Shafa kanta hajjo tayi cikin kulawa tace"
Kiyi hkr NAJMA kinji komai lokacine dashi rashin aure ba wata mummunar kaddara bace idan su dadan sun gaji da zamanki a gidan Ni subani inaso.
Murmushi kawai Naj din tayi tana cewa"
Hajjo idan aka baki Ni kema Zaki gaji da zamana ba aure wataran.
Murmushi kawai hajjon tayi tana kallon Hanifa da duk yanayinta bayada Dadi har lokacin akan fadan Dada Wanda akwai cin zarafi masu 'daci da yawa aciki.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022π₯_*
*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*ππ
Dβaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*πππ
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*ππ
09134848107
*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_
4
Anan gurin hajjo tayi niyar kwana Dan Haka Babu wata damuwa Kamar yanda tasaba rayuwarta na rashin riqe damuwan Abu ta sakewarta musamman dayake tanada daki daki me zamanta agidan a cikin babban palon hajjon wanda dakin Babu abin daya rasa najin Dadi da tsari musamman irin na rashin hayaniya da akasan Naj din batada ita Wanda hanifa ma anan dakin take yanzu idan tana gidan sbd tabaro part dinsu Dad dinsu tunda Babu kowa a part din.
Tanada Yan wasu kayan sawa a gidan Dan Haka Kai tsaye bayan sun Gama cin abincin dare Bata tsaya doguwar Hira ba Shirin bacci tayi bayan tayi sallah ta kwanta sai lokacin tabi misscalls din Sarah da Kira cikin nutsuwa tagama sauraran bayananta na aikin data bar Mata kafin ta Dora da cewa"
Ummm Naj dazu bayan tafiyarki Abaas yasake dawowa yasa an fiddo Masa da dukkanin record dinmu na aiki tun na January ya soke wasu daga ciki tareda fidda Kura kuren dazasu Iya bamu matsala Kuma Yana maganar a sauyani daga gurinki.
Dan sanyi muryarta tayi cikin bayyanarda rashin Jin dadinta tace"
Naj kiyi magana dashi please abarni agurinki sbd Ina barin gurinki na tabbatarda korata aikin zaiyi gabaki daya.
Ajiyar zuciya Me sanyi Naj din ta sauke tana tareda bude Baki cikin muryarta me Dadi Kai tsaye tace"
Karki damu zanyi magana dashi gobe
Kawai dai ki ringa kiyaye Masa tunda Kinga yanayin kalar fushinsa baya tunani me kyau idan ransa ya baci.
thank you Naj.
Ok then see you tomorrow"Naj din tafada tana kashe wayar tareda ajewa gefe tana Dan zamewa daga jingine datake akan gadon ta kwanta tana lumshe fararen idanuwanta ta rufe tana Dan yin bacci.
Hanifa dake zaune tana kokarin Kiran wayar mijinta tana sauraron wayar da Naj din keyi ta Dan saki guntin tsokin baqin cikin Abaas din datakeson koyawa zuciyarta Aminta dashi amatsayin mijin 'yar uwar tata tun yanzu.
Kashe wayarta tayi tareda miqewa ta zagayo tahau gadon ta kwanta tunda takasa samun Isma'eel din ga Naj shegen miskilancinta wani lokacin baya barinsu yin wata doguwar fira.
Qarfe 8 na safe ta fito wanka daure da towel me kauri tanaji wayarta na ringing Taki ko kallon inda take ta nufi gaban madubi tafara shafa Mai Wanda dama kusan komai product daya suke amfani dashi itada Hanifan.
Shiryawa tayi cikin doguwar riga maroon ta daura qaramin gyale akanta ta fito tana qamshin turaren Vivian rosalle har lokacin Hanifa na kwance sbd ciwon wuya data tashi dashi Wanda dama kullum cikin ciwuka take sbd sikla ce lafiyarta qarantacciyace sun Saba da rauninta shiyasa qaninta marshal baida wani abinda yafi komai so a duniyarsa bayan ita sai kakarsa tukuna mahaifinsa.
Dakin hajjo tafara zuwa har lokacin hajjon Bata farka ba itama Dan Haka Kai tsaye ta wuce kitchen su ruqayyat na ganinta cikin girmamawa sukace"
Ina kwana Anty.
Lafiya kalau ruqayyat
Please ku hado breakfast din Hanifa akawo daki batajin dadi.
Fridge ta qarasa ta bude ta dauko madara ta zuba a cup tareda zuba ruwan zafi aciki tayi dumi ta zuba Zuma kadan aciki ta dauka ta shanye ahankali tareda aje cup din ta koma ta diba dabino uku taci ta fice daga kicin din su ruqayyat suka bita da kallo Kamar dai yanda suka Saba sbd mamakinta har kullum Baya sakinsu na yanda take komai nata cikin wani irin burgewa da qaidojinta da nata ita ta shardantawa kanta su sbd maintaining rayuwarta.
Kalar abincin datake duk da gidansu ba masu halineba ta qayyade abinda take ciwa cikinta Wanda yake kamar dieting ne takewa kanta sbd gabaki daya rayuwarta batason abinci me nauyi tun tana yarinya Haka take idan taci abinci me nauyi sosai Yana wahalar da ita shiyasa data girma ta San yancin kanta tanada abubuwan datake ci kawai da wainda bataci Wanda shima yake qara bayyanarda miskilancinta da burgewarta da wasu ke gani acikin gidansu kuwa suna daukan hakan amatsayin nuna wayewa da nuna kudi Wanda