Showing 6001 words to 9000 words out of 92879 words

Chapter 3 - DEEN MARSHALL COMPLETE DOCUMENT .txt

27 Nov 2024

5667

yasa mazan ke ganin tafi karfinsu Ana samun matsalar fasa aurenta Kashi Kashi Kuma Sam Bata nuna damuwar hakan shiyasama ta tabbata dai itace Bata tashi aurenba inji su Dadah da Dattijo.


Cikin kulawa ta taimakawa Hanifa da wuyan ya riqe Mata sosai kamar ba lafiya ta kwanta ba tasamu ta danyi breakfast sai alokacin takira Dr said Wanda shine likitan Hanifan ta sanar dashi.
Dayake yanason ganin Naj din sai yace zaizo yakawowa Hanifan magani kafin ya wuce aiki.


Kafin Dr said din yazo taje dakin hajjo ta gaidata tareda Hado Mata ruwan dumi da Zuma Wanda itace hajjon ta koyawa Naj din Sha kasancewan itama abincin masu nauyi Basu cika Bata lafiyaba.


Bayan ta dan sha ta dago ta kalli Naj din tace"


Zaki tafi office ne?


Da fararen idanuwanta ta Dan kalli hajjon ta maida kallonta kan agogon dake daure a hannunta tana cewa"


Eh Amma ba yanzu ba Ina jiran Dr sa'id ne zai kawo maganin Hanifa wuyanta ya riqe Bata iya motsawa.


Dan numfashi hajjon ta sauke tana Dan jinjina Kai irin na manya tace"


Yau Kuma da riqewan jijiya ta tashi
Allah yabata lafiya.


Amin Naj din tace tana miqewa sbd ganin Kiran Dr sa'id akan wayarta.


Kamar dai yanda yasaba da gidan da dukkanin iyalan gidan tareda farin sani da securities na gidan sukai Masa amatsayin likitan Hanifan yasa Yana zuwa Kai tsaye aka bude Masa qaton gate din gidan yashigo har ciki da motarsa Amma iyakacinsa gate din farko baqi basa shigowa da motocinsu gate na biyun Dan Haka Yana parking ya fito yasake gaisawa dasu Mike ya wuce ciki Kai tsaye.


A babban palon farko na gidan ya tsaya Wanda yake matsayin na baqi ya zauna bayan su ruqayya sun kawo Masa ruwan black tea suna tiriri sun ajiye Masa kenan saiga Naj din ta fito ta qaraso tareda zama kujeran dake kallon tasa Tai Masa kallo daya ta Dan dauke Kai tana cewa"


Barka da safiya Daddyn Naufal.


Wani irin kyakkyawan murmushi ya sauke sbd a duk lokacinda takirasa da dadyn Naufal zancen na tsumasa sbd hakan na nuni ne da kusanci a tsakaninsu har wani lokacin Jin yake inama ace itace mahaifiyar Naufal din.


Kwarjininta yasa duk yanda mutum yaso baya iya Mata kallon qurulla Wanda shima wani lokacin hakan nasashi Jin fargaban zai iya mallakar Naj din kuwa Dan dai gskian magana bakowane namiji ne zai iya cika idon Naj din ba haryayi Mata irin kallon tsaf kona qurullaba saidai kuwa idan shima nasa kwarjinin ya take nata ne hakan zai iya yiyuwa.


Dan numfashi ya sauke Yana janyo qwazonsa na namijin daya ciki ya sake kallonta yace"


Barka da fitowa Naj.
Ya hajjo ta tashi lfy?
Yasu umma ma?


Alhmdlh" tafada a taqaice tareda sake kallonsa tace"


Maganin Hanifan.¿


Miqa Mata qaramar ledan maganin hannunsa yayi Yana cewa"


Kada a shafa Mata komi agurin Tasha maganin kawai saita gasa jikinta da ruwan dumi shikenan zai sake.


Ok bari nabata maganin yanzu coz tana buqatansa yanzu Nan.


Ta dauka lokaci sosai kusan awa daya kafin tafito cikin shirinta tsaf na zuwa office ta fito daga gidan gabaki daya tashiga gidansu cikin sa'arta Dattijo baya Nan bare maganar fadan jiya na Dadah ya tashi Dan Haka Kai tsaye sassansu ta nufa
Ummanta na daki tana ayyikanta taje ta gaidata umman ta Gama yimata Gore goren da tariga tasaba dasu ta fito suka hada ido da anty Amina dake zaune tsakar gidan tana waya Ta taso tana kashe wayar suka shiga dakin Naj din tana sake bayyanar Mata da kada kalaman umman su daga Mata hankali tacigaba da rayuwarta cikin salama sbd Haka Allah ya tsaro Mata ba komai bane rashin auren da wuri tunda su ganshinan sunyi sun fito din.


Murmushi kawai Naj tayi tana cewa"


Anty Amina Ni wlh kinmafi bani tausayi sbd fadan umma akan fitowan Nan Taki.


Kiji yarinya ke bakiga tausayin kankiba
Duk rigimarsu gwarani nayi harna tara yara nafito
Gwara dai kiji tausayin kanki kisamu kiyi shine rufin asirin.


Wani murmushin kawai tasaki tareda daukan abubuwan dazata dauka ta fito ta fice
Tana fitowa ga mamakinta Dr sa'id na Nan waje Yana jiran fitowarta ya ajeta office Dan batason doguwar hayaniya yasa kawai tashiga suka wuce Amma cikin ranta tana Dan fatan kada su tadda Abaas a ALFA'S din sbd bazata iya daukan hayaniyarsa da fitinarsaba ciwon Kai kawai zai sakar Mata na Wunin gaba daya.
#MAMUH#








*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*


*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107








*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_




5
Duk yanda Dr sa'id yaso suyi mgn Bata yiyuba sbd ganin motar Abaas lamido na cikin gurin hakan ke tabbatarda Yana Nan Kuma ko ayanzu Haka yasan Yana iya ganinsu daga sama ta office dinshi
Shi kansa baya buqatan iya zallan wulaqancin Abaas din a bainar jama'a bakuma Dan komai ba sai Dan Naj dayasan tana iya kokarinta gurin tolerating din Abaas din Wanda gabaki daya Bai cancancetaba Kota Ina Sam sam Allah ne kawai ya bashi babbar sa'ar samunta idanma shine ya aurentan kenan Dan shima Bai cire raiba yanama Dan ji a jiki jikinsa Kamar shine ma me sa'ar aureta din kowama ya huta.


Fitowa yayi ya zagayo zai bude Mata ta bude da kanta ta fito da Dan guntun murmushi akan fuskarta tace"


Thanks Dr.


Jinjina Kai yayi Yana kallonta yace"


Atashi lafiya.
Ya juya ya koma cikin motarsa ya tada yabar gurin bayan tuni ta shige alfas din Sarah dake jiran isowarta ko Dama Bata hayeba tana qasa tana Nan reception tana jiranta sbd bazata fara isaba it's kadai Dan shakkar Abaas zai iya Mata komai kafin Naj din taqaraso bazata iya ba gskia Dan yanda ya qware agurin cin zarafin mutum ta yanda duk hakurinka da dannewarka sai ranka yayi mummunan baci zata iya kasa hkr ta maida Masa mgna saidai ya koreta aikin Amma sbd Naj yasa itama take kokari tana hadiyewa tareda jinjinawa jarumta da qarfin zuciya irin na Naj datake hadiye maganganunsa.


Ma'aikatan dake gurin na qasa da Naj din gaidata suka hau yi suna Mata barka da isowa ta amsa musu tana wucewa kaman yanda ta Saba suka wuce Sarah na gefenta tana fada Mata Abaas yariga ya iso yau tunda safe ya iso office din.


Suna Isa cikin office dinta ta ajiye handbag dinta tareda waiwayo ta kalli Sarah dakyau kafin ta bude Baki tace"


Sarah daga yau banason maganar Abaas a office please
Zuwansa da rashin zuwansa duk bana buqatan sani okay??


Yes ma'am.


Juyawa tayi tana Shirin zaunawa aka turo kofar aka shigo
Sarah ce kawai ta juya tana ganin Waye ta Dan matsa gefe tana cewa"


Good morning chairman.


Ko kallonta baiyiba ya qaraso ya zauna kan sofa dake office din tana ganin Haka ta sulale ta fice bayan ta ajewa Naj laptop dinta.


Har lokacin Naj dake tsaye Bata juyoba tana hankalinta nakan wasu takardu dake hannunta ta sai qamshinta me sanyi da Dadi dayaketa sake gauraye office din Hadi da sanyin AC Wanda suke qara qona zuciyar Abaas din.


Dagowa yayi ya kalleta tareda zubawa fuskarta dakeda wani irin sanyin kyawu da nutsuwa tareda wani irin fizgar mutum ido kafin ya taso ahankali ya dawo gabanta ya tsaya Kai tsaye yace"


Meyasa Dr sa'id ne kawai zai kawo office?


Dan dagowa tayi ahankali ta kallesa tareda rufe takardun hannunta din ta ajiye ta koma ta zauna a natse tareda fiddo wayarta daga jaka cikin muryarta me kamewa tace"


Yaje duba Hanifa ne ya wuto Dani.


Rintse idanu yayi cikin qoqarin controlling zuciyarsa yace"


Kullum bashida aikine saina zuwa dubata kokuwa itace kullum batada aiki saina kwantawa ciwon dashine zaije Yana dubata ta yanda ke Kuma zai ringa kasancewa dake kokuwa nine da akewa kallon Mara hankali akeson shashantarwa da wannan zancen kullum"" ya qarasa fada Yana Dan daga murya sbd maqura da bacin ran nasa yake qara kaiwa.


Wannan karon kallon mintuna biyu cif tayi Masa tanason fahimtan idan Abaas din Yana lafiya kokuwa sbd kalamansa sun Sosa ranta Dan kuwa kamar Yana cin zarafinsu ne daga ita har Hanifan.


Kamar bazata tankasa ba saita dauke kallonta daga kanshi tace"


Zaifi idan ka tsaya da rashin fahimtanka a iya inda ka Saba kawai.


Cikin fushi yace"


Alaqarki da likitan Nan ta wuce dukkanin hakurina sbd Naga kin sabarwa kanki iya zama cikin motarsa Dan Haka tunda kin yanke zama taxi motar kowa saiki zaba tsakanin Ni ko shi waye Dan bansan ya alqarku zata cigaba da kasancewa ba bayan munyi auren....


Jajir idanuwanta sukai saidai har lokacin Bata dago ta tankasaba saima hakan yaqara qunan zuciyarsa yaci gaba da fada cikin maganganu masu dacin sauraro Amma taqi sake ko dagowa ta kallesa hakan yaqara lalata duk wani sauran hakurinsa ya fice ransa amatuqar bace.


Harya Gama ya fice tana zaune a inda take da wayarta a hannunta tana dubawa,
No Hanifa takira Bata daukaba Dan Haka takira no hajjo taji Yaya Hanifan take hajjon ta sanar da ita cewan wuyan dai Bai sakiba har lokacin.


Sama sama tasamu tayi wasu ayyukan ta tattara tabar office din Takoma gida sbd hankalinta gabaki daya yakoma kan Hanifa sbd tasan yanayin ciwukanta yanzu a Haka saita share kwanaki wuyan a riqe.


Tana Isa Kai tsaye gidansu Hanifan ta sauka Koda ta iso jikin yadan qara tsanantawa Hanifan Dan Haka kamar dai koyaushe itace tareda ita,itace tasan ciwonta da damuwarta da kulawa da ita bayan hajjo wadda itakuma tsufa yazo Mata bazata iya wani abun ba.,
Tun suna secondary Naj tasaba da kulawa da Hanifa sbd duk gata da tarin dibbin dukiyardasu Hanifan suke dashi basa tareda kulawa ta wani Dan uwa,
Masu aiki sune komai nasu sai hajjo wadda itama dai komai masu aikin ne keyi idan har Hanifa na buqatan kulawa da soyayya irin ta uwa to agurin umman Naj ne take samunta sbd umman da mahaifiyarsu aminai ne Suma tun yarinta shiyasa ma Suma suka taso Kamar umman ce uwarsu,
Umma na tsananin qaunar Hanifa Wanda yasama Hanifan kejin qarancin rashin uwa fiyeda DEEN Wanda shi asalima ko uwar tasa Bai saniba sbd gurin haihuwarsa ta rasu shiyasa ta taso a wani irin miskilallan mutum na qarshe sbd bai taso cikin hayaniyar taron mutane ba tun fara high school dinsa yabar qasar Yana Hawaii acan yayi karatunsa acan yake rayuwarsa ta matsayin babban Navy marshal Wanda zallan iliminsa da yakaisa acikin shekarunsa da basuyi yawa ba hakan Kuma yasa da yawa manyan mutanen Nigeria dake can harma Dana wasu qasar suna kawo sha'awan son hada zuria dashi saidai haryanzu kaman Shirin aure baya gabansa Dan baitaba sha'awan aure yanzu ba duk da hajjo da Hanifa sun fara nuna damuwarsu akan hakan Amma Yana dakatar dasu baya buqatan su takurawa junansu shiyasa ma basa matsa Masa sosai da maganar Dan sanin bayason yawan nanata zance.


Umman Naj itace ta raini Deen din tun bayan rasuwar mahaifiyarsu har Saida ya girma yakai shekaru biyar kafin yafara kwana gidansu ahaka ahaka harya koma gidansu gabaki daya sbd lokacin dad dinsu yayo aure shiyasa a duniyarsa bayan hajjo da Hanifa da dad dinsa umma itace uwa wadda tabashi so da qauna ta uwa duk da itama umman ta Saba sosai da halinsa na ko inkulan tun Yana yaronsa saidai duk yadawo Yana zuwa har cikin dakinta ya zauna tayita kulawa dashi danma yanzu sbd yawan gidan nasu yasa ya daina Shiga idan yazo saidai tayi girkin abincin dayafi so ta aika Masa daga baya taje har palon hajjo acan suke Yar firarsu ta uwa da 'da.




No din Dr sa'id Naj takira saidai Bai daga ba Dan Haka tayi tunanin Yana aikine kokuma yashiga CS Dan yawanci hakan kesashi barin waya office Dan Haka Bata Bata lokaciba tasake hada ruwan dumi ta gasawa Hanifan jikinta tareda sake Bata magani gashi duk yanda taso Hanifan taci abinci takasaci qrshe dai da kanta ta hado Mata ruwan dumi da Madara da Zuma tasamu ta iya Sha tayi bacci.


Saida Hanifan tayi baccin tasamu ta tube tafada toilet tayi wanka tayi sallah tafito palon hajjo ta nufi dining ta zubo spaghetti kadan da salad tadawo ta zauna gurin hajjo suna Yar firarsu akan rashin lafiyan Hanifan da tuni Dad dinta yafara Kira sbd hajjon data fada Masa
Shima Isma'eel mijinta tun Naj na office yake Kira sbd Hanifa Bata daukan wayan kowa.


Tana Gama cin abincin kicin kenan saiga ummanta tashigo tareda zainab Yar gaban goshinta ayanzu kenan 'yar anty Amina.


Zama umma tayi ita Kuma zainab Naj ta miqa Mata plate din hannunta tana cewa"


Ki Kai kitchen.


Sosai umma ke girmama hajjo tamkar mahaifiyarta Dan Haka firarsu suka Dora daga nan Naj na gefe tana aiki a laptop dinta saiga Kiran Abaas yashigo wayarta ta dauke ido daga kan wayar tana cigaba da aikinta yasake Kira Bata daukaba har so uku ko kallon wayar Bata sake yiba.


Sai yamma sosai bayan ma Hanifa ta farka su umma suka tafi Takoma gurin Hanifan wadda video call din marshal yashigo wayarta daidai shigowan Naj din.


Qarasowa tayi gurinta tana Kiran sunanta cikin taushin muryarta tana cewa"


Yaya wuyan?


Nuna tayi Mata da wayarta ahankali tana cewa"


Please ki amsa mun Kiran.


Kallon wayar Naj tayi taga sunansa baro baro ajiki takai hannunta ta dauka wayar tana dawowa gefen Hanifan ta zauna ahankali tareda daukan Kiran ahankali kyakkyawar fuskarsa ta bayyana akan wayar Yana zaune palon gidansa dake _Honolulu Hawaii US_ sanye cikin black three quarter da black armless shirt dasuka matuqar bayyanarda hasken fatarsa data Gama renuwa acikin hutu da lafiya sai daukan ido fatar jikinsa takeyi sbd yanayin kayan dake jikinsa dauke Kai Naj tayi tareda miqawa Hanifa wayar tana tashi daga gurin Dan gidansu takeson Shiga Dan Haka Kai tsaye ta fice.


Wayarta ce kawai a hannunta ta fito daga gidan ta nufi kofar gidansu ta shige ta nufi sashensu Kai tsaye saidai tana Shiga ta tadda Dattijo tsaye ga Dadah a zaune hakama ummanta dukkaninsu suka zubo Mata ido Banda ummanta da abun duniya ya taru yayi Mata yawa idanuwanta sun kada sunyi jajir da alama dai ba lafiya ba.


Qarasowa tayi cikin nutsuwa tace"


Dattijo Ina wuni,
Dadah barka da yamma.


Ko kallonta dadan bataiba sbd wannan karon tsaf tagama shirya duk wani rashin arziki da Naj din Bata tunani akan wannan maganar.


Kallonta Dattijo yayi da kyau Yana gyara tsayuwa da gyaran murya yace"


Ki saurareni da kyau kiji abinda Zan fada Miki sbd nafadawa mahaifiyarki kalma bayan kalma Amma Naga kamar ke din kinason watsar da maganar Kamar yanda kike watsi da masu neman aurenki,
Nafada naqara fada wallahi tallahi wannan karon kika Kori abbas da halinki yace yafasa auren Nan wallahi duk Wanda nasamu aura Miki zanyi bazaki maida wata a gidan Nan ba,
Yafara gajiya da halinki yazo ya sameni dazu ransa amatuqar bace na bashi hakuri akan za'a matso da bikin Nanda wata daya ma ayi a huta Dan Haka acikin watan Nan daya Kikai Masa abin dayasa yafasa wannna auren keda mahaifiyarki ku shirya hukuncina dazai biyo baya.


Daga fadar Haka ya juya ya fice Bai qara da komaiba sbd bacin ran al'amarin auren Naj din dayake kaisa maqura.
#MAMUH#






*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*


*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_






*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107






*_DM 6_*
Shiru ummanta tayi zuciyarta na suya da bacin rai da damuwa hadda sirkin takaicin Naj din wadda take ganin duk itace take qara tsimar da duk wani bacin Rai dake faruwa tsakaninta da Dattijo da Dadah wadda ita kaf duniya Bata ganin laifin kowa akan rashin auren Naj face ita mahaifiyarta sbd ganin suke idan su Naj tana Shure maganarsu ta lalacewar da neman aurarrakinta keyi it's uwarta ta tsaya ta ganar da ita Amma Ina ganin suke itacema take qara daure Mata acewarsu hamshaqin dayayi mugun ci ya tada wuya suke jira Wanda Allan daya halicceta yafita sanin cewan wlh a duniya tafi kowa farin ciki da qaunar ace yau taga 'yarta Naj tayi aure kodan irin daukan ido da fizgar maza datake dashi Amma saigashi qaddara ta Allah tasa duk kyawu datafi Yan zuriar gidan kowa yayi aure yabarta hatta qannenta da dama wainda suke Yan uba dama na dangi sunyi aure sun barta.


Ahankali Naj din ta juyar ta nufi dakinta ta Murda kofar ta bude tashige a Karo na farko dataji zancen Dattijo akan rashin aurenta ya daketa badan komaiba sai Dan yanda ako yaushe ake Dora laifin akan ummanta wanda keda kalamai na cin zarafi.


Bakin gado ta zauna ahankali tareda sauke numfashi tana Dan dafe goshinta ta lumshe ido tana tunanin itafa duk yanda akaso tayi aure da yanda ake ganin kamar taqi auren bazata jawo namiji da aura ba da qarfi Amma meyasa su basa gane hakan?
Shin menene akewa maza su tsaya su aureka Wanda ita Bata saniba ko shine yasa ake fasa auren nata bayan dai tasan acikin wainda sukai neman aurenta suna fasawa kowanne tana Dan iya nata kokarin gurin kulasa da Yar sake fuska tana iya kokarinta gurin aje miskilancinta ta kulasu yanda ya kamata Amma duk da hakan suke fasa aurenta bayan kowannensu Saida ya Aiko magabatansu dayanma har fara bikin anyi aka fasa sakamakon Wai yagano gabaki daya taba sonsa Bata taba sonsaba kawai aurensa zatayi Dan Ana cewa Bata aure.
Wannan shine yafi konawa Dattijo Rai aduk cikin masu neman aurenta suna fasawa sbd har Gama komai anyi Amma zancen ya watse tun akan wannan al'amarinta yaqara baqanta ransa shiyasa yanzu ya dage ya tsayawa Abaas sbd kada shima ya fasan duk da kuwa yagama karantar halayen Abaas sunada matuqar wuyar zama sbd zafin ransa yasa wani lokacin harshi rufe ido yakeyi Yana fada Masa magana musamman daya Gama gano sun Kai maqurar matsuwa a son aurarda Naj dayasa suke lallabashi shiyasa yasamu damar yimata duk kalar abinda yaga dama sbd yasan kome zaiyi baza'a fasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login