Showing 87001 words to 90000 words out of 92879 words

Chapter 30 - DEEN MARSHALL COMPLETE DOCUMENT .txt

27 Nov 2024

5683

saitaji kadaici da kewa Kuma takasa cin abincin Daren ma sbd wata vegetable rice da egg aciki brian yayi ita Kuma taji batasonta Dan Haka cake da milk kawai Tasha tayi wanka tasaka rigar baccinta qarama tana idar da sallar ishai Yana dawowa dayake tayi locking kofar daga ciki bayan tafiyan Brian Yana Danna doorbell ta taso tafito bayan ta aje hijab dinta.
Tana budewa ya kalleta Yana yaba kayan jikinta yashigo ta tura kofar ta rufe Yana rungumota ta baya kafin yayi magana ahankali ta furta"


Sannu da dawowa.


Lumshe fararen idanuwansa yayi hannunsa kan cikinta ya amsa da murya can qasa kafin yace"


Kinci abinci?


Girgiza Masa Kai tana cewa"


Banason abincin daya dafa idan naji zanyi Amai.


Juyo da ita yayi Yana kallon cikinta yace"


Yanzu kina nufin bakici komaiba?


No,I ate cake.


Ajiyar zuciya ya Dan sauke Yana Kama hannunta suka nufa bedroom Yana cewa"


Bari nai wanka muje nakaiki kici abinci.


Wanka yayi ya shirya cikin black _H&M_ riga da wando ya tayata ta shirya itama cikin riga da skirt peach and white sai qaramin scarf da shine ma dakansa ya daura Mata akai suka fito hannunsa riqeda Nata yabude Mata gaban motar tashiga ya zagaya yashiga ya tada motar security ya bude Masa suka fice.


Wani babban five star Eatery suka Isa inda suka nufi can sama VIPs anan yayi Mata ordern abinci kala kala dasu snacks aikuwa kusan duk abinda aka kawo ta Dan ci
Takoshi sosai suka fito bayan yabiya shima yaci abincin yakoshi suka kamo hanyar gida.


Suna dawowa wanka taso Yi Amma tun amota ganin irin kallon dayake Mata da yanda yake kissing hannunta akai akai Dama tasan zaiyi wuya wani abun Bai biyo baya ba Dan kuwa tun a Palo suna shigowa ya janyota jikinsa yana sake shinshinan qamshinta dayafi komai yamutsashi ya sakar Mata wani sanyayyan kiss a wuya ta lumshe ido Yana waiwayowa ta kallesa ya rankwafo Yana Kama bakinta da nasa Wanda tun tanacin abinci acan yake bin bakin da qananun kiss yanzu kuwa na gasken yake buqata.


Dauketa yayi gabaki daya bakinta na cikin nasa ya nufi daki dasu ahaka ya kwantar da ita Kan gado bayan yasamu zare kayan dake jikin,
Saura kadan ya rasa numfashinsa lokacinda yaji tana kissing din bakinsa da kanta take ta qarasa kwance notikan kansa Dan kuwa yau ta ballowa kanta aiki Dan martanin datake maida Masa shiyafi komai haukatarda nutsuwarsa.


Saida suka kammala wanka ta saka kayan bacci ta kwanta bacci take ya dauketa sbd kasala da gajiya Dan kuwa duk lokacinda yayi kwanciya da ita wannan gajiyar saitazo Mata sbd ba qaramar dauriya takeba da yanayinsa na zama cikakken lafiyayyen namiji mai Jin karfi.


Washe gari ma agurin aiki ya wuni sai yamma sosai ya dawo lokacinma Brian yatafi Kuma yau dinma fita sukai suka ciyo abincinsu wani gurin daban kafin suka dawo.
Washe gari dazai fita Kai tsaye ya sanarda Brian ya daina abincin dare kuma kafin yayi aikin Komai na abinci yaringa tambayar Mrs dinsa
Brian yace to.


Da farko idan yatambaya tana fada Masa abinda zai dafa din Amma ko taci Bata wanijinsa yanda takeso Dan Haka dasukai waya da Hanifa tabata shawaran ta karba girkin tanayi kafin cikinta ya tsufa.
Hakan kuwa tayi ta karba girkin gidan daga hannun Brian Amma na yamma kawai sbd na safe MARSHAL din baya Bari tunda Yana Nan na Rana kuma yawanci cereals takesha tunda ita kadaice Saida yamma tayi na Daren idan yadawo suci tare.


Duk da kadaici da rashin zamansa sosai sai yamma bai Hana shaquwa me qarfiba Shiga tsakanin rayuwar auren nasu sbd baya fita aiki sai goma na safe ta wuce hakama karfe hudu zuwa biyar yadawo daganan Kuma shikenan bata wani motsi sai acikin jikinsa musamman da cikinta ya fito sosai Dan yanzu Yana wata shida haryana shiga na bakwai,
Tunda cikinya yafara tsufa kamar ansake jona musu juna sbd shi gabaki daya hannunsa koyaushe Yana cikin rigarta Kan cikin kokuma saman cikin duk yabi ya zare Mata cikin gidan bazaka taba cewama yasan yanda ake kame fuska ba duk da idan yanata tareda wasu kokuma suka fita kamewan dawowa take har itama Yana cika idonta.


Naj Bata samu kantaba Saida ya tabbatarda Babu wani sauran kunya a idanuwanta gurinsa musamman yanda ya mugun lalatata da saka 'yan iskan kayanda dasu gwara Babu Wanda harta Saba Dan idan tasaka Masa wasu kayan kasa zuwa office yake Haka zai lalace acikin gidan suna zuba soyayyarda duk motsi daya idan tayi saiya furta Mata kalmar I love you.


Sayayya kayan baby kuwa harta gaji da kaiwa dakin da akaiwa jeren komai na baby,
Asibiti Kuma dama duk bayan 10 days suke zuwa Ana dubata.


Cikinta baizo Mata da matsalar komaiba shiyasa tananan ayanda take saidai haske data qara sosai na samun lafiyayyar rayuwar hutu da Jin Dadi ko kumburi bataiba saidai tsini da cikin kawai yakeyi Wanda koyaushe yake cikin daukanta hoto.


Lokacinda su Hanifa suka dawo US tareda Isma'eel a _Ala Moana_ sunkai musu ziyara inda suka sauka a wani babban hotel Amma a gidansu Hanifan suka wuni duk da Hanifan zata koma taqarasa shiryowa tadawo gabaki daya.
Kwanansu biyar a garin kafin suka tafi saidai ba Honolulu suka komaba New York suka tafi taron wani aikin sojoji da akai acanma Saida sukai kwanaba goma kafin suka nufo hanyar dawowa gida.


Da daddare sosai suka iso Dan Haka suna isowa wanka kawai tayi ta kwanta sbd Yar gajiyan zama jirgi duk da Babu wani nisa sosai.
##MAMUH#




*****************************
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902






*_DM 52_*


*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
******************************


*_52_*
Washe gari Bata Farkaba sai qarfe goma na safe shima sbd ya tada itane da dumin numfashinsa dayake sauke Mata a cikin wuyanta Yana yawo da hannuwansa cikin fingalalliyar rigar baccinta wadda Koda cikin daya tsufa Bata daina saka Masa ire irensuba.


Wani irin numfashi ta sauke tana ware idanuwanta masu sauran bacci akan fuskarsa Dake daf da tata Yana Mata wani kallon da ita kadaice tasan ma'anarsa.
Ta dan lumshe idanu ahankali tana sake numfashin kiss din daya sakar Mata a bayan kunne tareda sake cusa kansa cikin kirjinta duk da girman cikinta na hanasa manne Mata yanda yasaba ta bude idanuwanta tareda zura hannuwanta ta saqalo wuyansa tana nufar bakinsa da nata kafin ta Isa ya qarasa zuro kansa ya hade bakinsu sukahau kissing juna cikin nutsuwa da soyayyar dasukeji me qarfin gaske akan junansu daga nan lalabo rigar jikinta yayi yaqarasa zareta ya jefar Yana mannuwa da jikinta sunan cigaba da kissing juna.


Wanka tafito ta shirya tareda sakan gown Mara nauyi me Fadi sosai guntuwa wadda take ta masu ciki ce, ta daure gashinta da ko kafin barowarsu New York taje beauty parlor angyara matashi tafito tana qamshin Tom Ford dinsa da wani lokacin shi take shafawa wayarta Kan kunnenta tana waya da Hanifa dake sanar da ita komawarta Nigeria cikin satin Inshallah.


Hanifa Nima inason zuwa sbd na haihu acan din amma nasan bazai yadda ba.


Hanifa tace"


Tabbas bazai yardaba sbd Nima munyi mgna dashi din na tambayesa yaushe Zaki koma ki haihu agida yace Babu inda Zaki anan Zaki haihu kafin kuje gidan daga baya.


Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa"


Dama nasan bazai yardaba yanzu ke yaushene ranar tafi........kasa qarasawa tayi sbd cak muryarta ta dauke da abinda idanuwanta suka ganar Mata ahankali ta furta sunan Hannah tana kallon dining din da hannahn ke zaune sanyeda Jean and blouse na Burberry kanta da wula qarama Wanda ke nuni da kamar a gidan takwana,tasake maimaita sunan Hannah din tana qin yarda da itadince.


Hanifa dataji Naj takira sunan Hannah itama Saida gabanta ya Fadi cikin mamaki tace"


Wace Hannah Kuma?
Ba karatu takeba a qasar?yakamata ace tadawo tunda duka duka program din na 1year ne suna gabanin kammalawa me tazo Nan bayan ta tsaya tayi abinda yakaita qasar.


Cikin rashin sanin abin fada Naj tace"


Bari idan naji abinda tazo Yi zankiraki.


Kashe wayar tayi ta nufi dining din Kai tsaye
Hannah dataji tahowar qamshin Marshal ta waiwayo da sauri tana Kiran sunansa,ganin Wadda ke tsaye akanta yasata hadiye wani mugun abu daya taso Mata tana qurawa cikin Naj din data tsufa ido shedan na saka Mata fata da adduar Allah ya barar da cikin.
Daure fuska tayi Kamar yanda Naj ta Dan kame fuska ta dauke Kai Yana maida hankali kan abincin datake kokarin fara zubawa taci"


Kai tsaye Naj tabude Baki tace"


Zaki dakata sai maigidan yafito kafin kici komai,sbd koni danake Matar gidan banacin abinci saiyazo..


Isowarsa dining din Yana zuba qamshi yasa Naj sake Dan kame fuska ya Dan ranqwafa yayi kissing din gefen fuskarta kafin ya zauna Yana kamo hannunta daga tsayen datake ya zaunar a cinyarsa Yana kallon cikinta kafin ya kalleta cikin kulawa yace"


All ok??


Kallonsa tayi tana kasa hadiye zancen Dake ranta ahankali a natse tace"


Kasan da zuwantane??
Yaushe tazo??


Hannunta daya riqe yai kissing kafin yace"


Yes nasan dazuwanta,
Tazo jiyane,
Munacan takirani jiya akan ta kawo Mana ziyara bama Nan,inda taxo da nisa bazata iya komawaba a jiyan shiyasa nace Brian yaje ya daukota da mota ya kawo tunda muma a jiyan muka dawo.


Daga hakan baiqaraba ya kalleta Yana cewa"


Zauna kici abinci kinajin yunwa.


Gyada Kai kawai tayi batareda tace komaiba ko sake kallon Hannah din ta zauna a kujeran kusadashi tana fara cin abincin.


Har suka Gama bakin Hannah ne kawai ke tashi agurin Wanda duk da Marshal din take maganar Naj dai bayan kunnuwanta Dake saurare ko idanuwanta taqi Basu musamman dataga yanda yakeyi Yana kallonta akaikai.
Tana gamawa ta miqe tabar gurin Takoma bedroom ta zauna kan kujera tana sauraron yanda zuciyarta ke bugawa da zafi take idanuwanta suka cikoda hawayen baqin cikin barin Hannah ta zuwar musu harma da kwana gashi bataga alamar Hannah din zata tafiba ayau.


Saidata lallashi zuciyarta ta nutsu kafin ta miqe tasake fitowa lokacin tuni sukabaro dining Yana zaune Palo Yana waya Hannah din na zaune ta kafesa da idanuwa Kamar mayya tana kallon izzarsa da kamewarsa tareda ainihin sirrin kyau da kwarjini da Allah yayi Masa.


Qarasowa tayi fuskarta akansa tana sauya yanayinta zuwa bayyanarda nauyin da cikinta yayi Mata
Yana wayar ya dago yana kallonta tana tahowar ya miqa Mata hannunsa daya ta Kama ya zaunar da ita Kan qafafunsa da Yana kallon fuskarta da alamar lafiya dai ko?


Gyada Masa Kai tayi kafin ta Dan kalli Hannah data bala'in hade fuskar takaicin Naj da baqin cikinta Yana bayyane Kan fuskarta.
Cikin nutsuwa da muryarta me sanyi da Bata canjaba tace"


Hannah Yaya aiki zance ko karatu?


Banza Hannah din Tai Mata Kamar Bata jitaba saidataga Marshal din na kokarin Gama wayar kafin ta Dan kalli Naj din a wulaqance tace"


Ko wanne kike nufi lafiya kalau musamman yanzu dazan zauna Nan cikin na gida karatun zaifi tafiya kalau.
Gama wayar yayi tareda kallon Naj dake jikinsa ya kamo fuskarta da hannunsa dayan yakama bakinta yayi kissing kafin ya miqe Yana riqeda hannunta suka nufa kofa yakuma kissing hannunta yace"


Saina dawo,ki kula da kanki da Bby okay?????


Murmushi tasakar masa tana gyada Kai kafin tace"


Take care too.


Bayan fitarsa komawa tayi palonta ta zauna tareda daukan remote ta kunna TV tana kallo tana karba waya akai akai Bata sake bi takan Hannah ba.


Kamar yanda tasaba zuwan Hannah Bai hanata komaiba,data Gama abincin yamma taje tayin wanka ta sauya ado duk da ko lokacin ba wasu kaya masu takura tasakaba sai qamshinta takeyi tana fitowa Palo Yana dawowa,
Yana shigowa da Hannah dake zaune tana chatting a waya yafara cin Karo taci adonta Sama sama yake amsa gaisuwarta sbd Mrs dinsa daya hango tana tahowa gabaki daya tauke hankalinsa,
Wani murmushinda Hannah Bata taba gani a fuskar Saba taga ya sakarwa Naj din Yana Dan bude Mata hannu daya ta qaraso ta shige tareda rungumesa tana cewa"


Barka da dawowa.


Da ido ya amsa Mata suna wucewa zuwa bedroom dinsa Dan yayi freshen up.


Zuwan Hannah gidan Bai qareta da komaiba bayan gagarumin baqin ciki da takaici Dan tunda tazo babu iskan datake shaqa a gidan bana baqin ciki da takaiciba.


Naj gabaki daya ta iskance a gidan tagama lalacewa Marshal Wanda shikuma dama hakan yafiso shiyasa gidan yafara gundurar Hannah Amma ta nace taqi tafi,
Ko ina,kowane lokaci Naj cikin jikinsa acikin gidan,
Kiss kuwa a gidan Kamar ruwan Sha suka daukesa ya koyar da ita hakan,
Dakansa yafara gundura da zaman Hannah a gidan sbd sunsaba koina harkokinsu sukeyi Amma yanzu kamai ya dauko saidai bedroom dinsu.


Itadai Naj Bata bi takan Hannah sbd yanzu batada wani fargaba akanta damuwanta dayane yanda tayi tayi dashi akan Hannah din Takoma inda tafito Amma yace tabarta ta zauna harta tafi Dan kanta sbd kamar sun samu Dan break ne program din datake.


Hannah Bata fara kawowa Naj matsala ba sai dataga Naj dai dagake tako Ina tagama cike Marshal da rayuwarsa Baya iya ganin kowace mace sai ita Dan Haka taqi yadda da amincewa hakan tafara yiwa Marshal din shishigin son nuna itama matarsa zata zama Nan gaba.


Gabaki daya shi baisan abinda yake faruwaba a gidan sbd rashin zamansa dakuma koya dawo yanzu Bai cika zama Nan palonba Yana dakinsa wannan sabon tsarin Naj ne wadda Hannah takaita iya maqurar hakurnta Dan kuwa yanzu dai da qarfi da yaji take Kai kanta garesa musamman idan Yana dakin geamin acan tafi samunsa sbd lokacin Naj na baccin safiya.


Al'amarin yafara isar Naj takira Hanifa cikin damuwa take fada Mata maganar sbd Yan kwanakin har fada sunyi akan tace sai Hannah ta tafi shikuma can mum Malika takirasa tasakasa Masa tattausan lafuzan roqan alfarman Hannah ta zauna gidan taqarasa 'yan kwanakin program na karatunta daya rage Mata.
Ya amince da hakan shiyasa yanzu zamanta gidan yakeda matsayi tunda ta tashi daga baquwar datace tazo weekend gashi yanzu kullum idan zai fita da safe kusan tare suke fita ya ajeta a Hanya taqarasa da taxi ko bus.


Numfashi Mai zafi Hanifa tasake cikin mamakin mum Malikan da Hannah dama takaicinsu tace"


Mezaisa qatuwar tsohuwar budurwa kamar Hannah tazo tazauna gidanku bayan ko haihuwar farko bakuiba,bayan hakan kowa yasan cewa son mijinki take batun yanzu ba.


Kalmar sonsa da Hannah keyi da Hanifan tafada ita tasake kashe jikin Naj din ta rintse ido kanta na neman sarawa zuwan Hannah gabaki daya ya hanata sukuni yanzu duk da Bata taba Bari Hannah din tagano rashin kunin nataba dashima kansa sbd karya gano zafin kishinta me tsanani.


Hajjo Dake zaune gefen Hanifa tanajin duk abinda suka tattauna tana Kuma iya jiyo damuwar dake cikin muryar Naj din itama al'amarin ya matuqar bata mamakin halin Malika Dan kuwa batai tunanin rashin tunanin nasu yakai can ba Dan Haka sai ranta ya soma baci da al'amarin tasan idan takira Marshal Tai Masa maganar ko yayane zaiji rashin Jin dadin Naj sbd ganin Kamar qararsa takawo akan wannan abun dazasu iya magana a tsakaninsu Dan hakan Bata kirasaba Saida aka kwana daya da maganar takira Dad Alfa ta sanar dashi komai tareda dorawa da cewan yasaka mum Malika takira Hannah tabar gidan Takoma masaukinta kokuma akama Mata wani gidan idan batason zama can.


Dad Sam baiji dadin al'amarinba musamman ya zaunarda Malika yafada Mata Marshal din yafada Masa baida ra'ayin auren Mata biyu kowace mace ma ba Hannah kawai ba,
Yayi Mata bayanin hakan yakuma fahimtar da ita ta zaunar da Hannah tafada Mata tabawa masu Sonta dama kawai tabar maganar JALAL din Amma shine ta turata sbd kawo fitina tsakanin Marshal din da matarsa.


Rufe ido yayi yai Mata fada sosai tareda cewa takira Hannah tabar gidan zai tura Mata isasun kudi takama wani gidan ta zauna Kuma tana gamawa ko sati Bai yadda taqara a qasarba Bata dawo gidaba.


Duk inda Rai yakai maqurar baci ran mum Malika yabaci sai kawai takira Naj tayi Mata fada tatas Wanda bayan Gori Babu abin daya qunsa Wanda duk yanda taso riqe kanta kasawa tayi Saida kuka yazo Mata ta kashe wayar tanayi.
Bayan Gama wayarsu mum Malika Marshal din takira shima tafada Masa irin fadan da Dad dinsa da hajjo sukai tareda Bata laifi tafada Masa takira matarsa tabata hakuri sbd ita Bata dauka abun zaizama abinda har Naj zata kasa tsayawa ayi maganarba anan tsakaninsu harsaita Kira hajjo da Dad Alfa tafada musu.


Zancen Bai Masa dadiba ko kadan musamman daya Kira dad dinsa yasake Masa maganar tareda sake bayyanar Masa da umarninsa na Hannah tabar gidan,
Hajjo ma fada Tai Masa sosai hakan duk saiya sakar Masa pressure sbd abinda Bai taba faruwa bane yau din yafaru sai yabawa Naj laifin rashin hakurinta data kasa fuskantarsa akan zancen harta kirasu hajjo da Dad Dan Haka daya dawo gidan dama itama kukan datasha zuciyarta tagama daukan 'daci sai kawai shedan yashiga tsakaninsu suka samu sabani me girma Wanda yasata kukan da Bata taba yiba tun aurenta dashi.


Shima fita yayi gidan sbd kukanta Dake neman qarasa rusa zuciyarsa Dan har cikin ransa yake jinsa Amma Dolene yayi Mata fadan abinda tai din.
Yini guda tayi adaki tana kuka cikin tsananin damuwa,fuskarta ta kumbura tayi jajir ahaka saiga Kiran Anty Amina tana dauka sai kawai ta fashewa Anty Aminan da kuka tana kasa magana,gabaki daya hankalin anty Amina dake taredasu hajjo yatashi Suma hankalinsu yatashi musamman hajjo anty Amina cikin damuwa me girma tace"


Naj lafiya kike wannan kukan Haka?
Meyake faruwane??


Cikin kuka tafara fadawa anty Amina komai taqare maganar da cewa"


Anty Amina Dan Allah nidai Zan dawo gida zuciyata takasa dauka,
Da wanne zanji?
Da kishinta Dake cina kokuwa da wannan masifar dazsuyita haddasa tsakanina dashi,
Zan dawo gida kawai sbd idan ban Dan tafiba zasu cigaba da hada fitanarda zata kawo babban fada a tsakaninmu banaso...


Shiru Anty Amina tayi sbd zamansu hajjo da Hanifa dake gurin yasa bazata iya fadar wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login