Showing 18001 words to 21000 words out of 92879 words

Chapter 7 - DEEN MARSHALL COMPLETE DOCUMENT .txt

27 Nov 2024

5665

sai daga baya ta saka kayan ta zauna bakin gado sbd zuciyarta data fara harbawa da sauri da sauri Kamar zata Fado ta Dan dafe kirjinta tana sauraron bugun zuciyarta daya sanyata lumshe fararen idanuwanta ta rufe tanajin kamarma hadda faduwar gaba.


Miqewa tayi ahankali takoma Palo inda hayaniyar baqin gidan take Anata fira
Tana fitowa dukkanin idanuwansu suka sake dawowa Kanta suna Yana baiwar kyawu da Allah yayiwa Naj din qamshin wani irin fitinannan turaren da ummanta ke Mata gyara dashi daya Gama Kama jikinta Dana kayanta tareda kayanta da aka turara ya gauraya palon cikin nutsuwa da farin ciki a fili hajjo tace"


Masha Allah, Allah na gode maka da ganin wannan Rana Allah kasawa aurensu albarka da farin ciki me dorewa.


Amin Hanifa ta amsa idanuwanta akan Naj da ko itama dasuka taso tun yarinta tare sukai rayuwa tare koyaushe tana yabawa.


Qarasowa tayi gefen Hanifan ta zauna tana duba wayarta hankali kwance ba damuwar komai su Kuma suka cigaba da sha'anin gabansu.


*****
An daura Auren JALALUDDEEN MARSHAL ALFA da NAJMA ABDULLAHI BELA akan sadaki naira dubu dari cif Wanda duban jama'a suka shaidar cikin mamakin sauyi da aka samu ciki harda jama'ar su Abbas da yawa sun halarta sbd basusan cewan an fasaba duk da hakan dai kowa tanata fatan Allah yasanya alkhairi Wanda aketa bawa Marshal hannu Ana tayasa murna shidai bin kowa yake da mayun idanuwansa sai hannu dayake bawa manyan mutanen dasuke miqa Masa hannu Dan tayasa murnar aurenda Saida ya iso gurin yasan nasane.
Isowarsa gurin yasa mahaifinsa daketa dakon jiran isowarsa ya qaraso gabansa Yana kallonsa Kai tsaye yace"


Za'a daura auren Najma dakaine Ina roqon alfarman ka amince da hakan sbd wancan ya fasa adaidai lokacinda Babu wani mafita shiyasa a matsayinsa na mahaifinka Kuma itama Ina matsayin uba gareta na hadaku ta hanyar nema maka aurenta Ina fatan zakamin biyayya.


Fararen mayun idanuwansa ya zubawa Dad din kafin ya Dan sauke Kai cikin miskilar murya yace"


Ok Dad.


Hakan dayace yasa Dad din Jin wani irin sanyi da nutsuwa sbd yanata nazarin yanda zai fahimtar da jalal din hukuncin dasuka yanke Kai tsaye akansa batareda Jin shawararsa ko raayinsaba tunda ba yaro bane yanada iko da yancin zabarwa rayuwarsa abokiyar rayuwarsa da kansa duk da yasan karba Masa Marshal din yayi sbd yariga yazo gurin bazai iya komawaba yasa Dad din kunya Amma yanayinsa kawai ko Bai fadaba Dad yasan anyi Masa shigar sauri Dan kuwa Babu tsarin aure agabansa yanxu musamman da wannan din da za'a daura da ita Dan kuwa a yanda suke dinnan ba lallaiba ta kwantar Masa da Kai shikuma bayasa ran macen dake qarqashin ikonsa zatana Masa kallon qani ko wani Abu Dan kuwa shi mijin macen dazata bisa ne Amma tunda su dad din suka zaba auren dama agurinsu zata zauna so ba damuwarsa bane sosai aciki tunda shi bataredasu zai zaunaba a taqaice ma yaji bazai iya dogon zamaba komawa zaiyi.


Dan Haka Ana gama daurin aure akai gagarumin reception da akai liyafar alfarma shidai ko ruwa Bai Sha ba aka fara watsewa ya zame yayo gida kansa na 'dan sarawa Dan Haka Koda ya iso gida Kai tsaye flat dinsa ya wuce ya zare babbar rigar jikinsa da hula da komaima ya cire ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi ta shower Yana sauke ajiyar zuciya.


Sai dayayi wanka yafito yaji ya Dan samu nutsuwa da saukin ciwon kan ya saka guntayen qananun Kaya yaje fridge yasha ruwa kadan yadawo yashige daki ya kwanta Yana kashe wayarsa cikin nutsuwa bacci ya daukesa.


Saida 'yan daurin aure suka dawo kowa yaji da Wanda aka daura auren zallan mamakin al'amarin yasake yayata gidansu Naj da hayaniya saidai Kuma tunda dai ansamu andaura Mata auren ba'a fasaba gabaki dayaba a watse a banza yasa aketa sabuwar murna Allah yayi lokaci yayi tayi aure duk da wasu da yawa sun manta da banbancin shekarun sbd matsayinsa da yanayinsa yasama har wainda suka kusan haihuwarsa suna basa tsananin girma sbd matsayi da kamewa shiyasama ake mantawa da wani banbancin shekaru sai murna sukewa umma Allah yabasu Wanda yafi abundama suke buri tako Ina.


Dadah kuwa Banda sadaka da godiyar Allah tana washe bakin babu abinda takeyi yau Jin takeyi wani irin sakat daga ita har Dattijo da sai baza babbar riga yakeyi Yana gaisawa da manyan mutanenda yasan Albarkacin auren Naj da jalal ne yakeci Dan kuwa ganinsu Koda appointment ne shi bazai samuba Dan Haka sai farin ciki yakeyi Yana baje babbar rigarsa ta tsadaddiyar shaddar da Alhaji Alfan ne yake dinka Masa daman.


Yana dawowa gidan yakira Naj a waya yace maza tadawo gida yanzu.


Da mamaki ta fito zuciyarta ba Dadi sbd dai ga dukkan alamun data gani agun mutane andaura auren kenan
Ta hadiye wani Abu me daci da nauyi daga maqogoranta Dan kuwa auren Abbas shine mafi mumman al'amari daya sameta a wannan rayuwar.


Ko data shiga gidansu sama sama takejin Ana mata adduar Allah yawa aure albarka Saikuma tafarajin Ana Kiran sunan Jalal da cewan mijinta
Kanta ne taji ya dauka ciwo sbd komaima ita yanzu a duhu yake Mata Kai tsaye dakin Dadah ta Isa sbd tasan Dattijo daya aika kiranta Yana can tana Isa tashiga da siriryar sallama ta nufi gefen Dadah daketa washe Baki cikin farin ciki ta zauna ahankali tareda bude Baki cikin taushin muryarta tace"


Barka da jumaa Dattijo.


Gaida Dadah tayi itama duk da dazun sun gaisa data shigo.


Kallonta Dattijo yayi dakyau yana Dan kame fuska yace"


To Najma Kamar dai yanda Kika sani yau ne ranar daurin aurenki da Abbas
Amma sbd rubutowa ta ubangiji Allah baiyi shine mijin ba Dan kuwa a jiya suka sanarda sun janye sbd abindaya faru a jiyan da safe.


'dan shiru yayi kafin yacigaba da cewa"
Sakamakon hakan yasa Babanki Alhaji Alfa da hajjo suka bayyanarda buqatarsu tason nemawa JALAL aurenki muka amince atake sbd Babu wani zabin kokuma mafita Daman cigaban dayafi hakan Dan Haka dai a taqaice andaura Miki aure da JALAL yanzu ke matarsace halak malak saidai Hajjo ta nema alfarmar kada a takuraki da maganar tarewa gurinsa kokuma wani abun yanzu duba da yanda akai auren Dan Haka Zaki zauna gurinta kafin daga baya idan an natsa Kya koma sashen mijinki kokuma ki bisa can qasar dayake.


Akaro na farko a rayuwarta data kafe Dattijon da ido idanuwan nayi jajir ko qyaftawa batayi zuciyarta ta tsananta dokawa har batasan lokacinda ta bude bakiba tace"


JALAL qanin Hanifa?
An daura auren kokuwa dai za'a daurane yanzu??


Gano inda ta dosa da Aniyar bijirewa auren yasa ya tsuke fuska cikin bori yace"


Andaura Kuma wallahi kibar maganar Nan dakikeson fada acikinki Dan kuwa kisani kikaje Kika dagawa bayin Allahn Nan hankali akan banzan tunaninki na girman Kai suka raba auren Nan dake da mahaifiyarki zaku bar gidan Nan Dan kuwa Banga amfanin rashin godiyar Allah ba,
Dukkanin masu fasa aurenki Babu Wanda yakaisa bare yafisa ba'a ma hadawa ga qauna da mutunci da mahaifinsa da kakarsa dama 'yar uwarsa dasuke Miki har kin Isa kice bakyason auren,
To kiji da kyau Dadah kizama shaida wlh taqi auren Nan bani ba ita Kuma Tak banyarda tasake cewaba.


Miqewa yayi Rai bace ya gyara rigarsa zai fice yace"


Kuma duk abinda kikeyi kiyisa ki hada kayanki anjima Zaki koma gurin hajjon da zama afadawa kowa ba yanzu zata tareba kowa ya watse daga gobe banason zaman tsegumi"
juyawa yayi ya fice daga dakin Rai bace Dan baiyi tunanin zata musanya din ba yanda yasanta da komai yace hakane sbd rashin iya ja'injarta Amma wannan karon zata iya turjewa shiyasa ya rufe idon yayi Mata me gabaki.


Jajir idanuwanta sukai zuciyarta ta dauki wani irin mummunan 'daci da nauyi dataji tana marmarin mutuwartama Dan kuwa a rayuwa ta Jima tana kunsar baqin cikin maza Dana fashin aure Dana tsangwamar iyaye da 'yan uwa Amma Bata taba Jin an Mata tozarci da baqin ciki irin wannan,
Aure tsakaninta da Wanda ta girma Wanda yake matsayin qanin Aminyarta ta Yaya ake tunanin tayi aure da rayuwar aure da JALAL Wanda bayan sannu ta gaisuwa Babu abindayake hadasu....


Najma karki damu godiya zakiwa Allah jira da zaman gida ya qare Allah yakawo lokaci kema kin aure,
Tsananin Rabon dake tsakaninkine da JALAL din yake Kore waincan aurarrakin naki da ake fasawa,Rabo ne me qarfi na haihuwa kesa irin wannan auren Dan shi Koda aure ko Babu sai ansamu Rabon Dan Haka muke qara godewa Allah da Akai hadin, Allah ya kawo......Wani irin kukan baqin ciki Mai qarfi ta saki sbd maganganun Dadahn dasuka fasa wani qoqon baqin ciki cikin zuciyarta ta miqe tashige kuryar dakin Dadahn tareda zamewa qasa ta zauna tana wani irin kukan da tunda take rayuwarta Bata taba yinsaba.


Tun abun na Wasa Dadah hankalinta ya tashi da halinda Naj din tashiga saitaji murnarta na Shirin komawa ciki Dan kuwa matuqar Najma taje gaban hajjo ko Alhaji Alfa tana wannan kukan na tashin hankali da zallan baqin ciki zasu iya warware auren sbd gudun damuwarta Dan Haka hankali tashe tasa akai Mata Kiran Dattijo da Umma ta fasa musu kuka tana cewa"


Matuqar Najma taqi wannan auren aka warwareshi to Nima barin gidan Nan zanyi bazan zaunaba dan zuciyata harbewa zatayi da kunyar Alhaji Alfa da hajjo Dan Haka gatanan ki fada Mata gwara ta dangana da wannan tashin hankalin ta rungumi auren.


Ko kallon Najman Dattijo baiyiba ya kalli ummanta yace"


Ki saka Mata hankali cikin kanta tadawo tunaninta Dan kema nasan bazaki so auren ya warwareba Dan idanma ya warware na fada Mata hukuncina bazaiyi Mata Dadi ba Dan bazamu zauna da qatuwar budurwaba kamarta muna rarrashinta akan aure bayanma tuntuni yakamata muyi Mata auren Dole mu huta.


Kallon Najman umma tayi tareda miqewa tsaye ta Isa inda take ta janyo hannunta tana cewa"


Inshallah zata fahimta aure Amma yariga ya dauru ma maganar warwarewa tunda ai Dan an Isa da itane akai Mata auren maganar taje gaban hajjo tana wannan kukan Ni kaina bani ba ita Dan Haka Najma ki nutsu kidawo hankalinki rayuwar aure zakiyi a gidan yanzu ba wadda Kika sababa, su din yanzu dangin mijinkine Kuma kinsan son da suke Miki bazasu taba cutatar dakeba hakama jalal ki yadda ko kiqi yadda mijinkine yanzu bashi girma yazama Dole.


Kinga Fatima jeki da ita can kuyi sauran abinda zakuyi na tsakaninku ganinan zuwa na maidata gurin hajjon da kaina shikenan.
##MAMUH#








*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107








*_DM 13_*
Zaunar da ita bakin gadon dakinta umma tayi tana kallon yanda fuskarta gabaki daya tayi jajir sbd kukan tashin hankali musamman dogon hancinta yafi yin ja ta zauna gefenta tana tausasa murya cikin kulawa da tausayi tareda kewar rabuwa da ita dazatayi duk da kusa suke tace"


Najma Dan Allah ki daina daga hankalinki akan abindaya kamata kiyi farin ciki akansa,
Farin ciki mukeyi kowama shiyake Dan tayaki murnar aure da Allah yabaki ikon Yi Wanda kinsani auren rahamace tunda kin dau lokaci da gwagwarmaya kafin kisamu kiga hakan.,
A shawarance matsayina na mahaifiyarki Ina Baki shawaran karki watsawasu hajjo da Alhaji Alfa qasa a ido kodan tsananin qaunar dasuke Miki wadda itace ta Sanya hakan,
Hakama Yaya kike tunanin Zaki iya kallon Hanifa kice bakyason Dan uwanta datafi so fiyeda komai a duniya wannan tunanin baiyiba ki ajiyesa Anan gida ki barsa zaman qarqashin ikon mijinki zakije kiyi bakida wani majagorancinki bayansa Dan Haka biyayya da bin umarninsa dole ne....


Wannan kalmar tasa wasu hawayen baqin ciki da ciwo masu zafi suka gangaro Mata tana sake sheshekar kuka ahankali, umma taci gaba da cewa"


A umarni Kuma na matsayina na mahaifiyarki Ina Baki umarnin ki aje maganar Araba aure anan ki barta Dan duk ranarda kikaiwa wani acikin gidan Alfa maganar daga ranar zakisan asalin kalan fushi da bacin Raina Dan Haka Dan Allah Najma na rokeki daki dauka dangana kiyi biyayya kaman yanda Kika Saba yiwa qanin mahaifinki Dattijo daya dauki damuwar tsakani da Allah yasakawa kansa akan al'amarinki,
Qanin mahaifinki ne Kuma Miji gareni Ni mahaifiyarki Dan Haka ya cancanta kiyiwa hukunsa biyayya Koba Dadi sbd baitaba nuna banbanci ko gazawaba a tsakaninku da nasa 'yayan daya Haifa tun bayan rasuwar mahaifinku da wannan biyayyar kawai Zaki iya saka Masa kodan yanda yake Shiga tashin hankali da damuwa ba dare ba Rana aduk lokacinda neman aurenki yasamu matsala Dan Haka kiyi hkr ki dauki dangana Allah ya sanyawa rayuwar auren albarka.


Amin anty Amina tace tana qarawa da nata nasihar da rarrashi Dan kuwa duk Wanda yasan Naj baitaba ganinta a mummunar yanayiba irin yanxu Dan kukan datakeyi harya zama abin kayar da gaba.


Ganin idan aka biyeta sanyi jikin kowa zaiyi yasa aka qyaleta quryar dakin umman ta dunqule a gado cikin mummunan yanayi na qunci da baqin ciki hawaye Kuma sun kasa tsayuwa daga idanuwanta.


Hidimar Wunin biki akaci gaba dayi har dare masu tafiya gida suka tafi akabar baqin nesa kawai wainda Suma washe gari Dattijo yace kowa ya watse yakoma 'dakinsa.


Mummunan yanayin da Naj din take yasa Dadah tacewa Dattijo yaje ya sanarwa Alhaji Alfa abar Naj din ta kwana gida har gobe tadawo sbd sudai duwarsu da tashin hankalinsu kada hajjo ko Alhajin sugan Naj a wannan halin komai zai iya faruwa Ana fadawa Alhajin yace bakomai abarta ta nutsu tukuna tazo Koda fiyeda goben nema zai fadawa mijin nata,da wannan aka barta gidan ta kwana.


Har safe tana dakin umma Nan takwana ko ganinta batason mutane nayi sbd tsananin kunyar kanta da wannan aure ga idanuwanta dasuka kumbura tsabar kukan data kwana tayi a Daren.


Hanifa na sane taqi zuwa sbd tana gidanta tun jiya da daddare mijinta ya dauketa suka tafi takuma qi kira Dan taji labarin kukan da Naj din keta faman Yi a bakin Anty Amina,
Taji tausayinta matuqa hakama tana iya kwatanta jin yanayi na damuwa da Naj din take ciki na auren Kai tsaye da Wanda ko taqamaimai kalma biyar Bata taba shiga tsakaninsu ba duk suka hadu tsawon shekaru kuwa Dan Haka take tausayin Naj din ga sanin halin JALAL datai na tsagwaron kamewa da basarwa Dan kuwa kafin Naj taganewa komai sai anga wuya.


Koda qarfe goma Sha biyun Rana tayi baqi kowa ya hada jakarsa ya kama hanyar komawa gida Dan Haka gidan su anty Amina dasu Khadija da zainab din Anty Amina sai aikin gyaran gidan suke Dan Haka Koda la'asar tayi gidan koina yayi fes fes sai mutan gidan kawai Kamar ba'ai taron biki ba dan ma da Dattijo Bai tsaya akan kowa ya watse yau ba da akwai wainda sai sunqara sati kila kafin su koma.


Bayan sallar isha tayi wanka tareda Shirin bacci tasaka riga da wando masu tsantsi na baccin kalar maroon ta janyo wayarta datun jiya data shiga tashin hankali take kashe ta kunna tareda ajewa gefe batareda tabi takan wayarba ta Haye gadonta tana Shirin kwanciya ummanta tashigo daukeda wani ruwan turaren humra me shegen qarfin qamshi ta ajiye gaban madubi tana zubawa a hannunta tahau shafawa Naj din akoina ajikinta tana cewa"


Sauko Dadah na Kira kutafi gurin hajjo duk da wannan baza'a kirashi da tarewaba Amma dai tafiyar kenan kila sauko ki sauya Kaya Mana.


Bata dago ta kalli ummanba tayi kamar bazata saukoba tsawon mintuna kafin dai ta sauko tana zura slippers dinta dake bakin gadonta ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko wata sabuwar jallabiyarta me Fadi kalar coffee brown ta warware ahankali ta saka kan kayan baccin Dake jikinta kafin ta jawo qaramin Chantelle veil ta yafa akanta Dan Bata daura ko dankwanlin jallabiya
Umma kuwa binta tayi tayi tana watsa Mata turaren harya ushers Yana Mata yawa murya a shaqe tace"


Umma Dan Allah ya Isa
Yana min yawa cikin Kai.


Dainawa umma tayi tana murmushi cikin kulawa tace"


To shikenan ai na barshi Haka Amma bazaki sauya kayaba.....idon da Naj din ta zuba Mata yasa ta waske zancen da sakin murmushi tana cewa"


Ko hakan ba laifi muje ku tafi gobe Amina zata kawo Miki kayanki Dattijo ma na gurin Dadah suna jiranki.


A dakin Dadah abun takaici agareta sabuwar nasiha da lallashi suka Dora Mata da dadin Baki da komai itadai tana jinsu batace komaiba sai sauraro kawai sai Kuma zuciyarta dake Mata zafi da baqin ciki har lokacin Haka suka Gama ta ta fito itada Dadah da Dattijo Wanda ya fito da Kaya niqi niqi shida Anty Amina da Umma habiba kishiyar ummanta zasu maida gidansu Abbas acikin Daren.


Suna isowa bakin gate da wani irin sauri sojojin Marshal suka taso suka bude Mata kofa suna Mata gaisuwa cikin tsananin girmamawa dayasa Dadah sakin wata sabuwar hamdala cikin ranta abun na Mata Dadi sabanin Naj da "thank you" kawai ta iya bude Baki ahankali tace tana wucewarta kamar ba Amarya ba Kai tsaye gurin sashen hajjo suka nufa gidan tsit Suma duk baqi sun tafiyarsu.


Itace a gaba Dadah na bayanta da kallon ikon Allah da wannan Alamari saidai dayake lallabata sukeson Yi sai batace komaiba suka Isa babban palon gidan dazai isar da ita bangaren hajjo.


Kai tsaye ta shigo palon hajjo idonta dasuka kumbura suna kan kofar dakinta datakeda niyar shigewa ta rufe ta kwanta data shigo Dan Haka Bata lura da mutum dake zaune a palonba Yana cin abinci kan dining ta shige tabar Dadah dake shigowa da zama tana washe Baki ganin Jalal din zaune yanacin abinci tareda hajjo.


Cikin sakewa da farin cikin ganin Naj hajjo ta taso tana yiwa Dadahn barka da zuwa suka zauna suna sake gaisawa.
A 'dan taqaice ya taso yaxo suka gaisa da dadah yakoma dining din Dan baima faraba yanzune zai fara cin.


Hajjo na kallon kofar dakin da Naj tashige tasaki murmushi tana cewa"


Inshallah ahankali zata sake ai tamayi kokari da biyayya ko ahakan Dan Haka baza'a takirata ba zatai zamanta taredani har su daidaita da mijin.


Zare jallabiyar jikinta tayi tabar kayan baccinta har zata kwanta ta fasa ta fito Dan zuwa gurin hajjo Dan Bata Saba fushi da hajjon ba duk kuwa yanzu tanajin kaman antaru an Mata rashin kyautawa da adalci.


Tana fitowa dukkaninsu suka kalleta hajjo na murmushi tace"


Zo ki zauna Nan Najma Babu Mai takuraki akan auren Nan Inshallah,
Zaki zauna Dani har sai lokacinda kikaji da kanki kinason komawa gurin mijinki.... Da sauri Dadah tace"


Ba maganar saita buqata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login