Showing 9001 words to 12000 words out of 92879 words

Chapter 4 - DEEN MARSHALL COMPLETE DOCUMENT .txt

27 Nov 2024

5663

auranba tunda auren akeso ido rufe.


Anty Amina ce tashigo dakin ranta Babu Dadi itama sbd tsakani da Allah suna Jin zafi da 'dacin dukkanin wani fadan cin zarafi da akewa mahaifiyarsu saidai Kuma Babu yanda zasuyi tunda mijine agareta hakama Dadah uwace to Amma Kuma meye laifinka Kai idan anqi aurenkaΒΏ


Cikin nutsuwa anty Amina ta zauna kan kujeran madubin dakin ta kalli Naj din a natse tace"


Najma hakuri Zakiyi ki daure ki Kuma qara daurewa da halayen Abbas ayi auren Nan ki huta da wannan fitinar umma ma ta huta da wannan fitinar muma masu gani zuciyoyinmu na daci mu huta,
Idan Kuma kina ganin bazaki iya auren Abbas din ba ki dakatar dashi Kai tsaye saiki bawa Dr sa'id damar fitowa sbd yamafi Abbas din cancanta da mutunci tareda nutsuwar aura tako Ina,
Auren Abbas tabbas idan ba wani rahaman ubangiji babu ta inda zaku samu nutsuwa tako Ina Dan zafinsa yayi yawa kekuma miskilancinki yayi yawa zaku wahala ku duka.


Kallon anty Amina ta dago tayi da fararen idanuwanta dasuka Dan sauya Wanda iya Nan kake iya ganin damuwarta sai Kuma ahankali ta saki Dan guntun murmushi tareda bude Baki tace"


Nagode anty Amina.

Shiru sukayi tsawon mintuna biyar kowa kowa da abinda take tunani cikin ransa kafin ta miqe ta fice daga dakin Kai tsaye ta nufi dakin ummansu dake zaune kan kujera shiru da alama damuwace take cinta bakuma yanda zatayi tunda itama tayi iya yinta bazata jawo mijiba ta daurawa Naj din aureba duk abinda sukeji Dole Haka zasuyita daurewa suna hadiyewa har Allah yakawo ranar auren.


Qarasowa tayi gaban umman wadda sai alokacin ta dago a sanyaye ta kalla Naj din ta dauke Kai tana cigaba da tunaninta.


Zama Naj tayi gaban umman tareda riqo hannayenta tana kallon fuskarta ta bude Baki ahankali tace"


Umma kiyi hakuri kadaki saka damuwa aranki,kinada ilimin addini umma kinsan cewa aure lokacine da ubangiji ya dibar maka wlh idan lokacin Nan baiyiba bazakayiba meyasa kike damun kanki da abinda su Dadah ke fada bayan kinsan kinamun addua Kuma insha Allah zanyi auren kila Wanda Allah ya zabarmun ne a mijin Bai bayyana ba kokuma kila lokacin ne haryanxu baiyiba da saura idan Kuma auren ne Allah baice nayiba harna bar duniya Yaya zakuyi da hukuncinsa?
Umma addua kawai Zakiyi Allah yasa hakan shine mafi alkhairi gareni dakuma iyayena.


Kallonta umman tayi idanuwanta na kadawa jajir sbd tabbas su yayanta basusan irin mugun zama da cusgunawa tareda tozarci da hantarar datake samu daga dattijon har Dadah akan wannan al'amarin,
Ta dauka,ta hadiye,ta danne,ta shanye,ta boye duk wani mugun wulaqanci da tozarcin dasuke Mata akan al'amarin Wanda matsi da fitinarsu yasa taji Kota Yaya sotake Naj din tayi auren kowama ya huta kishiyoyi masu Mata dariya su daina Yan gidan masu zundenta su daina,yan matan gidan masu cewa ilimin Boko da aikin office yasa Naj taqi auruwa duk kowa ya daina a zauna lafiya,
Da wanne zataji gata da tsohuwar bazawara a Naj din.


Sake kallon Naj tayi da idanuwanta dake jajir har lokacin ta bude Baki Kai tsaye da sanyin murya tace"


Najma nasan aure lokacine Amma Kuma Allah yakawo Miki mijin meyasa bazaki lallabashiba har ayi auren tunda dai haryanason auren nakiΒΏ
Abbas dinnan duk halinsa dakike gani idan anyi auren lallabashi Zakiyi zai sauya shikenan kowa ya zauna lafiya.


Zubawa umma ido tayi akaro na farko tana Jin dacin hukuncin ummanta ahankali ta bude Baki tace"


Umma halayen Abaas ba masu lallabuwa bane.....


Ta Yaya Zaki yanke hukuncin ba masu lallabuwa bane tunda Baki auresan kin gani ba saidai idan shima kinada Shirin sakawa ya fasa auren Dan shima kina ganin bekai bane kaman yanda mutane suke fada.


Da mamaki ta sake zubawa umman ido tace"


Umma idan Kuna tunanin naqi aurene Dan akwai abinda nakeso agurin namijin dazan aura Kuna kuskuren fahimatar halayena da kuka sannu dasu duk da karatun danayi da da wasu cigaban Dana samu hakan Sam bayada alaqa da rashin aurena...


To ki amince da Abbas kawai ayi auren Nan idan ba hakan bane Najma sbd idan dukiya da rayuwa ne Abbas din yanadasu Kuma Yana tsananin sonki idan harkin daukeni mahaifiyarki.....


"Umma kadaki Bari fushi yasa ki lalata rayuwar Naj mana." Anty Amina ce ta fada hakan tana isowa gaban umman Wanda idanuwanta suka rufe gabaki daya.


Naj kasa cewa komai tayi sai idanuwanta dake kan umman sunyi jajir ahankali ta dauke idonta ta bude Baki tace"


Zan aura Abbas idan har hakan Kika zabarmun.
Juyawa tayi ta fice daga dakin gabaki daya tana shiga dakinta wayarta kawai ta dauka ta fito ta fice.


Dadah dake zaune tsakar gidan tana Jin duk hayaniyar tasu farin ciki yacika ranta tunda tasan yanzu Kam Naj din bazata bada matsalaba tunda Zuciyarta ta karye da abinda umman tayi Dan Haka ta tashi Takoma dakinta a Daren zata fadawa Dattijo ya sanarda Abbas ya sanarwa iyayensa za'a matso da bikin Nanda sati uku ko biyu ayi ayi kowa ya huta Dan kaf zuriar gidan Naj din ce kawai ta riqe a gabansu batai aureba da wuri.
#MAMUH#








*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107










*_DM 7_*




*_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NANπŸ‘‡πŸΎ_*


https://youtube.com/c/sudaiskura


_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._


_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy._


_PLEASE SUBSCRIBE_






**********
Kodata dawo Hanifa tasamu komawa bacci Dan Haka Kai tsaye toilet ta Shiga tayo alwala tafito ta tayarda sallah.
Tana idarwa Shirin kwanciya tayi Dan batajin tanajin yunwa har zata kwanta ta fito ta nufi dakin hajjo
Tana Shiga kallo daya hajjon tayi Mata ta karanto yanayinta cikin kulawa dakuma tsananin qaunar data kewa Naj din tayi Mata hannu datazo ta kwanta kan cinyarta
Naj din ta qarasa ta kwanta qasa tareda Dora kanta kan qafafun hajjon ta rufe ido ahankali tanajin zuciyarta na samun nutsuwar data kasa samu daga gurin iyayenta.


Saidata fara bacci ahaka kafin hajjon takira sunanta ahankali tace taje ta kwanta a godonta
Ta bude idanuwanta tareda tashi zaune ahankali ta miqe tana cewa"


No hajjo zanje na kwanta da Hanifa sbd jikinta.


Shikenan kije Saida safe kiyi bacci karki saka damuwan komai aranki Allah ya tashemu lfy.


Amin"tace tana ficewa dakin.


Washe alhmdlh daga ita har Hanifa lafiya kalau suka tashi Hanifa wuyanta ya sake Takoma garau dinta dama Haka take yanzu lafiya yanzu ciwo,kokuma yanzu ciwo yanzu lafiya.
Itama sakayau ta tashi ba wani yanayi na damuwa kokuma dake nuna tana cikin wani hali sbd ta riga ta yarda ta yanke shawaran auran Abbas Dan Haka ta kauda bayyana damuwa a fuska da yanayinta sbd hajjo da Hanifa dasuka samu saqon an saka ranar auren an maida sati uku masu zuwa Wanda dad din Hanifan ne yakira hajjon ya sanar Mata sbd Dattijo ya kirasa ya sanar dashi Dan komai na harkan auren Naj da dad din akeyi sbd suna basa girmansa da matsayi na uba agareta sbd baitaba banbantataba da yarsa Hanifan tun daga karatun primary kuwa har zuwa yanzun.


Ranar bataje aiki bama Koda hajjo ta zaunar da ita akan maganar auren ta tambayeta akan tafada Mata gaskia idan batada ra'ayin auren Abbas din tasa dad yayi mgn dasu Dattijo a fasa
Tacewa hajjon ta amince da auren Abbas da raayinta ba Dole su dattijon sukai Mata ba.
Hanifa ma tayi tayi akan suyi maganar Amma tace Mata subar maganar ayi auren ahuta.
Dole suka haqura sunaji suna gani aka hau fara shirye shiryen auren gadan gadan.


Tunda aka fara wannan maganar Bataga ko shigowar saqon Abaas dinba a wayarta bare kiransa Wanda Bai wani dameta ba sbd tasan dama za'ai hakan Dan Haka ta tattara dukkanin alamarinsa ta cire akai ko a office Basu hadu ba sbd dama gabaki daya Bata zuwa office dinsa shine me zuwa nata to tunda yaga tagama shigowa hannunsa tunda zata zama matarsa saiyayi watsi da ita shima saima wani basarwa yakeyi a yanda Sarah take fada Mata yasa dokar shigar maza office dinta matuqar ba'a zo anfara tambayarsaba Koda kuwa aikine.
Hakan ya Bata mamaki sbd kaman rashin tunani yashigo al'amarin nashi Dan hakama Ana saura sati biyu bikin tafara hutun bikin auren dazatayi ta daina zuwa office.


Gidansu kuwa sosai da sosai aka hau shirin wani irin gagarumin hidima sbd bikinta kowa yasaka Masa burin holewa tunda sunsan za'a kashe dukiya sbd alaqarta da gidan tsohon marshal Alfa shiyasa suka hau shiri da anko anko na biki kala kala Wanda ita amaryar ma gabaki daya komai baya gabanta mamakinta daya har lokacin Abaas Bai taba kirantaba.


Dadah kuwa farin cikinta da murnarta a bayyane suke ba wani shamaki sai ji takeyi da Naj din tana lallabata hakama Dattijo manyan kudi tako Ina sai shigosa sukeyi sbd Alfa ya sakar Masa kudin hidamar auren fiyeda tsammani ga hajjo ma data tanadarwa Naj dukiyar aure ta musamman shiyasa kowa sai qara rikicewa yakeyi da harkan bikin.


Ummarta tuni tahau aikin gyaran 'yarta sbd dama gyaran amare aikintane Dan Haka yanzu da Abu yake nasu ba kissa ko kadan gyaran Naj din takeyi ta ciki ta waje abinka da kyakkyawar farar mace tuni tafara sauyawa sosai Dan kuwa har wani daukan ido takeyi.


A duniya qawayenta biyu ne daga hanifanta sai Sarah Dan Haka kullum Sarah na gidan sunata shirye shirye Wanda Hanifan ce ke komai itadai nata ido da Kuma Dan murmushin yaqe Wanda babushi ko kadan cikin zuciyarta.


Saida akai saka lallenta kafin aka kawo kayan lefe mota biyu Wanda yasa gidansu yasake daukan bidiri suna sake yadda da Naj dama me kudin ta tsaya jira duk da hakan dai sudai sunyi murna musamman ummanta data ringa sadaka tana ciyar da mabarata sbd Allah yasa wannan karon 'yarta tayi aure.


Ba gidansu Naj din kawaiba ya cika da baqin nesa Dana kusa ba hatta gidan Alfa yasamu saukar isowar Dad Alfa din tareda matarsa da sabbin masu aikinta datazo dasu har guda biyu sai babba 'yar yayarta datake riqo tun tuni wato _HANNA_ Wanda take wata irin wayayyiya datake ji da kanta da Kuma kyau da Allah yayi Mata itama wadda asalin irin son datakewa Marshal Deen ne yasa tadawo hannun mum Malika saidai hakan be wani taimaka ba sbd takanyi shekara Bata ganshi ba duk da kuwa iyayen nasu sunsan da maganar so a tsakaninta da marshal din Dan Yana kulata ba laifi shiyasa akeda maganar da yiyuwar aurensu gashi Kuma yanzu sun dawo gida gabaki daya da zama tasan yana zuwa Nan akai akai fiyeda can gurinsu sbd Hanifa da hajjo Dan Haka Suma gidan yanzu zai rayu tunda su dad din sun dawo.


Sai yamma sosai Naj tasamu damar fitowa gidansu ta tafi yiwa dad Alfa sannu da zuwa kodata fita mutanen dake waje sai binta da kallo sukeyi sbd yanda tasake wani irin washewa
Tsakani da Allah dai kowa ya kalleta saiyace Abbas yayi dace da kyakkyawar sa'a.


Tare suke da Hanifa dan haka Kai tsaye sashensu dad da mum Malika din suka nufa.


Babban lafiyayyan palon farko suka yadda mum Malika zaune tana waya tana ganinsu ta saki murmushi tana sallama da Wanda take wayar ta miqa musu hannu tana cewa"


Oh our beautiful bride is here
Naj you're looking morethan beautiful.


Murmushi me qayatarwa tasaki tana cewa"


Thank you mum Malika kun iso lafiya?
Ya gajiyan hanya?


Alhmdlh alhmdlh hanya alhmdlh.


Kallon Hanifa tayi dayake ita tunda suka iso tazo tana tareda dad Alfa tace"


Hanifa I'm so happy for Naj
Allah yasa albarka a wannan auren.


Amin mum.


Congratulations Naj.


Thank you mum Malika.


Hannah ce ta fito sanye cikin doguwar riga Mara dogon hannu kanta daure da wani Dan qaramin scarf da tsadaddiyar wayarta a hannu tana dubawa tana ganinsu ta qaraso da murmushi akan fuskarta tana zama gefen Hanifa tace"


Sister in-law Hanifa barka da shigowa I've been looking for you tun dazu hajjo tace kuna gidansu Naj.


Murmushi Hanifa tayi tana kallonta tace"


Dazu nashigo kina ciki kina wanka
Ya hanya?


Lafiya kalau sis Hanifa.


Maida kallonta tayi kan Naj dake duba massage din Sarah akan Wai Abaas ya dakatar da ita daga aiki.


Fuskar Naj din ta zubawa ido tana kallon kyan fuska Dana jiki da Allah yabawa Naj din ta gangara da idonta kan hannayenta dake farare tas kamar Bata aikin komai dasu gashi Tasha gyara tako Ina fatarta sai glowing takeyi
Dama can Naj na tsananin burgeta sbd tanason Abu me kyau ita shiyasa take tsananin son Marshal dinta ga wani aji da Naj din takedashi kamar ba Yar masu rufin asiri ba Dan Haka ta saki qayataccen murmushi tana kallonta cikin tayata murna tace"


Naj mijinki dinnan yayi sa'a
Congratulations to you Allah yabaku zaman lafiya.


Murmushi Naj tasaki tana kallon Hannah din tace"


Amin nagode Hannah.


Palon dad Alfa suka nufa inda suka samesa zaune Yana waya Dan kusan jama'arsa da yawa zasuzo daurin auren Yana ganinsu yasaki murmushi Yana kallon Naj datake murmushin Dole sbd saqon Sarah yabata matuqar mamaki shiyasa ta yanke shawaran Kiran Abbas din zatayi tana fita taji dalilinsa na korar Mata Sarah.


Zaunawa sukai Banda ita Naj din data zauna a qasa cikin biyayya da farin cikin zuwansa tace"


Dad Alfa barka da zuwa,ya Hanya?


Alhmdlh Najma ya hidiman?
Babu dai matsalar komai ko?


Babu komai Inshallah.


To shikenan Allah yasawa auren albarka yasa agama taron lafiya.


Hanifa ce tace Amin kafin suka Dora da zancen tahowar da Marshal zaiyi Wanda tun kafin suyi nisa Naj ta miqe tana cewa"


Zan Dan karba waya" ta fice.


No Abaas din ta Nemo Kai tsaye tareda Danna Masa kira tahau ringing.
Harta katse Bai dagaba ta sake Danna Masa Kiran sai akaro na uku ya dauka da cewa"


Hello.


Kai tsaye da muryarta me taushi tace"


Maganar office ce zanyi dakai akan Sarah ko Zan iya sanin abindaya faru ka dakatar da ita?


Takaicin zancen nata yaji Dan dama Yana sane yayi hakan Dan kuwa idan ba hakan yayiba yasan wlh har abada Naj bazata taba kiransaba har ayi auren kuwa to Amma yanzun data Kiran sai abin yabasa takaici ko gaidashi bazata iyayiba sai magnar Sarah Dan Haka cikin baqin ciki Kai tsaye yace"


Bana wannan maganar sai a office"


Kashe wayarsa yayi Yana sakin numfashi me zafi tareda komawa jifa da wayar Yana Jin tafasar zuciya.
Jin bazai iya hakura ba yasa ya zari key din motarsa ya fice daga palon mahaifinsa Kota cikin gidansu Bai bi ya fice sbd gidan Suma cikeda jama'ar biki.
Itama akaro na farko dataji bazata dauka wannan wulaqancin nasa ba cikeda takaici ta fasa sake kiransa ta wuce gidansu ranta a Dan jagule.


Washe gari akai gagarumar taron walima kawai sbd gabaki daya Naj din batada raayi na biki sbd komaima yafita kanta har akai waliman aka gama Bata cikin wani dadin zuciya sbd batasan me Abaas din yafadawa Dattijo ba yakirata itada ummanta a Daren yayi musu wani irin fadan cin zarafi duk da ummanta na cikin farin ciki na hidimar bikin Saida tayi kwanan bacin Rai.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107






*_DM 8_*
Washe gari kodata tashi miscalls din Dr sa'id biyar tagani a wayarta da text na cewan zaizo yau din yanason Mata fatan Allah ya Sanya alkhairi batai replying nashi ba sbd ganin massage din tun safe yayi Dan Haka ta share akan sai ya zo din.


Yau Bata leqo gidansu ba tunda tatashi tana tareda Hanifa data tashi da ciwon qafafu Dan Haka sai yamma tasamu fitowa ta da dogon hijab har qasa ta mask a fuskarta ta nufi gidansu inda acan tayi wani wankan ta shirya cikin wani brown lace riga da skirt saiga kiran Dr sa'id ta yafa gyale ta fito fuskarta ba kwalliyan komai sai Kohl dake cikin fararen idanuwanta.


Ko data fito Kai tsaye gidansu Hanifa ta shiga sbd tasan Yana ciki baya tsayawa waje musamman irin yanzu da komai zai iya faruwa.
Sabbin qarin securities tagani a waje da cikin gate na farko na gidan tareda ganin sabuwar motar gidan dake rufe a fili da alamun anfita da ita hakan yasa ta fahimci cewan DM na iso kenan ta Dan waiwaya hanyar sashen dayake matsayin nasa acikin gidan kafin ta dauke Kai ta qarasa sashen hajjo daidai shigowar Kiran Abbas tana gani taji bazata daukaba Dan Haka ta kashe wayar gabaki daya tana Shiga palon Kai tsaye.


Hajjo ce zaune a palon sai Dr sa'id shima suna maganar qafafun Hanifan daya duba ta kallesa tana cewa"


Dr barka da zuwa.


Kallon quralla yaso yimata Amma sbd hajjo na gurin yasa ya taqaita kallonsa fuska a sake yace"


Barka Amarya,ya hidima?


Murmushi kawai tayi tana qarasa dakinsu Kai tsaye tashige tana kokarin sake kunna wayarta Bata tsaya koina ba sai bakin gado ta zauna tana Kiran sunan Hanifan batareda ta dagoba.


Dakatawa tayi da abinda takeyi Jin shiru tareda Kuma qamshin turaren _TOM FORD Tobacco Vannile_ daya Gama gauraye dakin sanyin qamshinsa ko Bata dago ba tabbas tasan kodai DM Yana dakin kokuma yashigo ya fita sbd tsadar turaren kawai yasa Babu Wanda zata canka bayan shi Dan Haka ta miqe ahankali tareda juyowa akaro na farko idanuwansu suka shiga cikin na juna a bazata Yana zaune kan sofa gefen Hanifa da farin cikinta yasa ta daina Jin ciwon gabaki daya daga ita har shi Naj din suka zubawa ido
Ta dauke nata idon tana Dan dauke Kai daga kallonsa ta bude Baki Kai tsaye cikin dan sake fuska tace"


Barka da zuwa JALAL.


Dauke idanuwansa yayi daga kanta cikin muryarsa me Kai tsaye yace"


Ya hidima? Allah ya Sanya alkhairi.


Amin" tace Kai tsaye tana juyawa ta fice tana cewa"


Hanifan zanyi magana da Dr sa'id kafin kigama okay.


Tana fitowa palon Dr sa'id ma yagama mgna da hajjo suka fito zuwa harabar gidan inda suka tsaya suna mgna tsawon mintuna suna Shirin fita saiga taga Dr sa'id na kallon bayanta ta waiwaya ahankali daidai qarasowarshi zai wuce zuwa sashensa lafiyayyar fatarsa tana haskawa hakama qaqqarfan jikinsa dayake geaming yagama budewa tako Ina ta yanda duk qwaqwarka bazaka gano shekarunsaba sbd mugun miskilancinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login