Showing 90001 words to 92879 words out of 92879 words
maganar ba sai kawai tahau bawa Naj din hakuri tana tausarta Akan karta taho gidan,
Katsewa wayar tayi batareda kowa yace komaiba ta kalli hajjo cikin tausasa al'amarin tace"
Bawani abun damuwa bane ai zasu daidaitane Daman Dole za'a ringa fada irin Haka.
Qala dai hajjo bataceba saima wayar dad alfa data lalubo ta saka Kira Yana dauka ta sanar dashi tanason ganinsa da matarsa.
Anty Amina dai sake Dan tausar hajjon tayi sbd ko Batai magana taga alamar Kamar yadauka zafi ranta ya baci,
Ta Jima gidan sai maraice tana ganin shigowar Dad Alfa da mum Malika tasan Magana zasuyi da hajjo ta miqe itada Hanifa suka nufi dakin Hanifa ta dauko gyalenta ta fice bayan ta gaidasu cikin biyayya.
Zama sukai bayan sun gaida hajjon wadda Bata tsaya batawa kanta lokaciba ta kallesu Kai tsaye tace"
Nace Hannah tabar gidan JALAL Bata bariba gashi matsalar tashin hankali tafara shigowa tsakaninsu yarinya da tsohon ciki za'a sakata damuwa matsala tabiyo baya,
Dan Haka ke Malika tunda kekika turata da manufar cusa kanta akansa bayan anfada Miki shi me auren yace baya ra'ayi yanzu duk da bamu San me gaba ta tanadarba sanin gaibu sai Allah Amma kisani wlh karki bini bashin rantsuwa duk aka samu babbar matsala akan Hannah har Najma tabaro gidanta tadawo to wlh ko sati bazata cikeba da dawowa zansa naki mijin yaqara aure sai kema kisamu lokacin fuskantar matsalar gabanki Dan Naga hadda rashin zafin hakan yasa kikeson mijin wata koreta yaqara aure.
Mum Malika dataji saukar zancen kamar saukar Aradu a girgice take kallon hajjon tana son gane ko rikicin tsufa ne murya na Dan rawa da mamaki tace"
Hajjo meya kawo maganar qarin aure ga mutumin daya manyanta?
Maganar Marshal da matarsa Kuma ai tsakaninsu ne Ni menene nawa daza'a mun qarin kishiya akan sabanin dasuka samu.....
Hajjo dai Bata bi takan zancen mum Malikan ba ta kalli Dad Alfa tace"
Kaji abinda nafada Kai ko?
Inshallah hajjo za'ai yanda kikace.
Ja matarka kuje banson maimaicin zancen yanzu.
Suna fita mum Malika taso haukace Masa sbd maganar auren sai yanzu tasake tabbatarwa dataga ya amsawa hajjon a ladabce ma musantawa,
Qafafunta na rawar disco ta Isa dakinta tashige ta lalubo wayarta tashin farko Hannah takira murya na rawa cikin ihu tace"
Hannah ki tattara kayanki yanzu yanzu kibar gidan nan....
Cikin mamaki ta kalli wayarta Jin yanda mum din ke maganar hankali tashe tace"
Mum Kamar Yaya nabar gidan bayan yanzunema nakejin dadin gidan da masu gidan ke fada,Babu inda zani mum Malika gskia.
Kutumar uba,Ina cewa kibar gidan yanzu shine kike fadamun Babu inda zakiΒΏTo saurara kiji maganar aurenki da Marshal ba kubarta yanzu babuta Dan kuwa hajjo tamun barazana da kishiya duk Kika kawo matsala ga aurensu......
Cikin zallar mamakin mum din Hannah tace"
Mum menene Dan anmiki kishiya idan har zansamu shiga gidan Marshal?Naga ai kin Gama manyanta Babu wani abinda yarage Dan anmiki kishiya akan farin cikina,nidai Babu inda zani yanzu danake ganin haske kiyi hkr kawai mum.
Zagi da fada Kamar mum zata tashi sama ta ringa jehowa Hannah din Amma Hanna ta kashe wayarta tana cewa"
Lallai mum tafara batan lissafi.
Mum dakejin Kamar ta Ari hauka akan al'amarin idan ba barin gidan Hannah tayiba batada nutsuwa Dan Haka Kai tsaye Marshal takira Yana ganin kiranta yaqi dauka sbd bayason wata damuwar akan wadda yake ciki da matarsa tsawon kwanakin ko dakin kwanciya sun Raba sbd tadaina kwana dakinsa.
Ganin ta dage da Kiran yasashi dauka sai kawai ta fashe masa da kuka tana fada Masa batasan me Naj din tasake fadawa hajjo ba Amma hajjo ranta yayi matuqar baci ta tursasa dad dinsa qarin aure baiyi niyyaba itadai yanzu yaje Hannah tabar gidansa.
Innalillahi yafada acikin ransa Yana rintse idanuwa gabaki daya baisan meyake damun kowaba musamman Naj gashinan ta gana musu azabar rashin juna dagashi har ita.
Koda yadawo gida Ashe mum takira Naj tai Mata tas akan hukuncin hajjon ta Dora da fadin idan ma Bai aura Hannah bakisan wazai iya auraba gaba..
Kiran yasa Naj sake shiga yanayi na damuwa me tsanani Tasha kukan bazataso hajjo tasa Dad Alfa yayi auren rashin niyaba da girmansa Dan Haka sai kawai taji ta yanke shawaran komawa gida sbd komai ya lafa zuciyoyin kowa su sauka Dan idan tabar gidan ne kawai zai iya binta subarwa Hannah gidan idan bazata tafiba itama tana ganin sunbar gidan zata tattara Dole tabar gidan koba komai cikinta yashiga watan haihuwa gida takeson haihuwan.
Koda yadawo Bai nema Naj dinba sbd bayason su sake samun damuwa akan maganar Kai tsaye yakira Hannah a waya yace ta hada kayanta driver zai maidata gidanta sai kawai tasaka Masa kuka ya kashe wayarsa Yana jifa da wayar.
Booking ticket da komai tayi na tafiyarta batareda tafada Masa ba sai Ana gobe jirginta zaintashi tasamesa har dakinsa Yana zaune Yana aiki a laptop ta kallesa shima ita din ya Dan kalla Kai tsaye tace"
Nasiya ticket gobe Zan tafi Nigeria Inshallah.
Takaicin maganarta yasa Bai dagoba ya kalleta cikin zafin Zuciya yace"
A sauka lafiya.
Juyawa tayi tabar dakin tata zuciyar na tafasa da zafi na yanda yaqi hanata tafiyar Dan Haka tana zuwa daki tahau hada kayanta kafin ta kwanta Dan tafiyar safe zatai.
Washe gari ko data fito yafita office da mota bayan yasa andauki Hannah data Sha kukan maganar daya fada Mata na Babu wani so ko Abu makamancin hakan aransa gameda ita shi matarsa Naj kawai yakeso bayan ita baya ra'ayin wata,shiyasa Koda aka kaita masaukinta Jin tayi qasar gabaki daya ta fita ranta dama dama danshi ta jona karatun yanzu Kuma tunda harya fito yafada Mata hakan bazata iya cigaba da zama anan dinba itama ticket din tasiya na barin qasar Amma gidan qanwar namanta dake Ghana ta nufa taqi komawa gida.
Taxi tahau takaita airport kaita airport idanuwanta sai cikowa da hawaye suke tana maidawa sbd kewarsa datakeji tun batabar qasarba,
Jirginsu na tashi ta rintse ido tana sakin hawayenta dasuka kasa tsayuwa.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022π₯_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*ππ
Dβaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*πππ
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*ππ
09134848107
*_DEEN MARSHAL_*
*_Mamuhgee_*
*_53_*
Jirginsu na sauka taxi ta dauka ta nufo gida fuskarta a kumbure da zallan kukan datasha acikin jirgin gakuma gajiyar zaman jirgi da tsohon ciki dan hakama Koda suka sauka kamarma batajin Dadi sosai Haka ta lallaba tabi taxi ta iso gida.
Securities na ganinta jiki na rawa suka dauka akwatinta zuwa ciki har gate na biyu daganan Allah yasa ruqayyat tafito kawo musu abincin Daren su sai ganin Naj tayi cikin farin ciki da girmamawa ta qaraso ta karba akwatin da handbag dinta tana Mata sannu da zuwa suka nufi ciki.
Hajjo da Hanifa ne zaune a palon suna fira sai ganin ruqayyat janyeda akwati sukai Naj na bayanta tafe da tsohon ciki fuska a kumbure
Da sauri hanifa ta tashi tarbota tana zaunar da ita gefen hajjo Dake kallonta kamar zata miqe.
Rungume hajjo tayi hawayen idanuwanta na gangarowa tana qaqalo murmushi tace"
Nayi kewarki hajjo da fatan nasameku lafiya?
Dafa kanta hajjo tayi tana qaqalo nata murmushin cikin kulawa tace"
Sannu da hanya Najma ke kadai Kika taho ko??
Kasa amsawa Naj tayi tana kallon Hanifa dake Mata sannu cikin kulawa.
Hanifa kaita dakinki tayi wanka akawo Mata abinci taci takwanta tayi bacci ta huta.
Miqewa tayi suka nufa dakin Hanifa lokacin tuni ruqayyat tabude dakin Naj din tafara gyarawa.
Bacci tayi Sosai Wanda ta manta rabonta dashi tun fara rigimarsu da mijinta.
Sai yamma ta farka lokacin tuni anty Amina tashigo suna murnar zuwanta duk da kowa yaqi tada maganar da akasan akantane dawowar tata kamar yanda Bata fadaba Suma Basu tada zancenba musamman hajjo har aka kwana biyu da dawowar tata.
Ranarda ta biyar da dawowa ranar aka daura auren Dad Alfa da anty Amina auren daya girgiza kowa sbd Babu Wanda yasan meyake faruwa bayan hajjo data saka dad din neman auren anty Aminan gurin Dattijo Kuma ta roqa alfarman adaura kawai Babu wani janye janyen saka Rana da shela.
Mum Malika hannu ta Dora akai ta ringa tsinewa Naj da Hannah akan sukeda laifin wannan muguwar qaddarar data sameta musamman Hannah sai kiranta take tana zunduma Mata zagi da fada Dan tarasa inda zata sauke haushinta.
Naj ma bataji dadin wannan aurenba Sosai daga ita har anty Aminan da ummansu sbd gujewa fitina Amma tunda andaura Babu yanda zasu iya Haka suka runguma qaddara anty Amina ta tare sashen Dad Alfa na qasa shikuma Yana sama.
Saida aka gama rikici da hidimar auren anty Amina tata damuwar tadawo sabuwa ta kewar mijinta sbd har cikin ranta batason ta haihu mijinta baya tareda ita.
Kullum wayarta ahannunta take tana jiran Kira ko massage dinsa Amma shiru Babu tun tana daurewa dai harta kasa damuwarta ta bayyanar Mata danma koyaushe daga hajjo har Hanifa da Anty Amina suna kokarin kulawa da ita ga Dadah ma da kusan lokaci lokaci tana shigowa dubata tunda yanzu ji da ita akeyi.
Yau zaune take a Palon hajjo tana Shan furar dataji nono sosai Hanifa na gefenta tana waya da mijinta
Hajjo Kuma tana cin apple din da anty Amina ke yanka Mata cikin kulawa.
Qamshin turaren dataji yashiga hancinta ko a mafarki tajisa tasan meyake nufi Dan Haka ta dago kanta ahankali ta kalli kofar palon idanuwanta suka sauka akan Wanda yake shigowa palon sanye cikin qananun kayan _HermΓ©s_ navy blue yayi wani irin kyau da kwarjini fuskarsa a kame idanuwansa suka sauka cikin nata ya sauke wani boyayyan numfashi Yana dauke Kai daga kallonta sai alokacin dukkaninsu suka ankare da zuwansa cikin muran da farin ciki suka fara Masa sannu da zuwa.
Bai zaunaba bayan angama gaisawa sashensa da aka gama gyarawa ya nufa yasamu yayi wanka da sallah kafin yaci abinci kadan ya kwanta baccin nutsuwar ganintama kawai da yayi.
Acan bangarenta kuwa samun kanta tayi dashiga wani hali na nutsuwar zuciya da ganinsa,musamman da idanuwansu suka Shiga cikin na juna tana iya hango soyayyarta dake cinsa shima Dan Haka Koda dare yayi yanayinta ya nuna samun nutsuwar datai maimakon ita takai Masa abinci hajjo Hanifa tasaka takai Masa Dan yace bazai iya zuwaba Bai Gama hutawaba da gajiya.
Haka ta zuba ido tayi kwanan tunanin abinda yake yanzu har gari ya waye
Tunda safe tayi wankanta ta shirya cikin doguwar rigar Kuwait gown Mara nauyi sosai tana qamshinta Amma still baishigo breakfast ba kamar bazatai magana ba sai kawai ta daure ta tambaya Hanifa lafiyansa kalau kuwa?
Kije kiduba da kanki Mana Nima dai bansaniba iyakacina palonsa na dire Masa na dawowata.
Jin hakan yasa takasa samun nutsuwa Ana gama abincin Rana da kanta ta hada zata Kai Masa saigashi yashigo palon cikin guntayen kayan _Nike_ black dasuka fitarda haskensa sosai.
Kallonsa tayi tana ajiye basket din hannunta kan dining ta nufosa tana kallonsa da rauni sbd takai maqura gurin gazawa tana ta kamo hannunsa zatai magana ya Dan janye Yana dauke idanuwansa daga kanta zai wuce tasake riqo hannunsa tareda Shan gabansa Bata tsaya komaiba ta Dan daga qafafunta takai fuskarta saitin tasa ta hade bakinta da nasa tayiwa bakinsa wata irin tsotsa kafin ta sake tana kallon fuskarsa ahankali ta furta"
I'm sorry husband.
Kasa cewa komai yayi sbd tariga tagama sanin baya iya fushi da ita tareda sanin hanyayin kamasa tako Ina ya janyota jikinsa ya rungume ta gefe Yana sake Kama bakinta Yana kissing sbd cikinta daya tokaresu ya hanasu mannuwa da juna.
Gyaran muryan Hanifa ne yasa Naj zamewa ta waiwayo da sauri tana kallonta cikin fargaba saitaga ita kadaice Banda hajjo Dan ta manta da inda suke tuni.
Cikin Dan Jin kunyar kanta tace"
Ina hajjo??
Kallonta Hanifa tayi kafin ta kalli wanda yagama kamewa akan bayason tada maganarsa da Naj yanzu saita haihu ta kalla hannunsa dake riqedana matarsa tace"
Hajjo tafara fitowa taga abinda yake faruwa a palonta shine Takoma ta turoni akan ku tattara kubar Bata Palo Dan Allah.
Zaro idanuwa Naj tayi cikin wata irin masifaffiyar kunya tace"
Dagaske kike?
Da gaske nake Dan Haka kafin ku makantar Mana da 'yar tsohuwa da wainnan hot romances din naku ku qara gaba.
Fuskewa yayi Yana mamakin yanda hanifa yanzu ta iya gulma da saka ido Yana matarsa Yana cewa suje dining zaici abinci.
Ba kunya suka taru suka fuske a sashen hajjo sai dare bayan sunci abincin dare suka ficewarsu Yana riqeda hannunta shine yayi musu Saida safe Naj kuwa sauran nauyin hajjo yaqi barinta iya mgn.
Saida suka biya sashen Dad Alfa gaisuwa kafin su wuce suka taddashi palon qasan zaune anty Amina na gefensa tana juya Masa tea din data dafo Masa Mai qamshi.
Sama sama suka gaida Dad din suka fito sbd ganin shima hutawarsa yake da amaryarsa.
Rufe kofar palonsu yayi Yana janyota jikinsa ya kalli bakinta Yana shafawa yace"
I love you wifey.
I love you too" tafurta Kai tsaye cikin siriryar muryar data sake yamutsashi suka kwasa sukai bedroom dinsa inda suka baje komai.
Asubar fari naquda me qarfi ta tadata hafara hawayen azaba Dana abun kunyar daketa binta kala kala tun aurenta yanzu Kuma daga zuwa kwana dakin mijin sai naquda kowa zaisan abinda ya tado Mata da naqudar karma Dadah taji shikenan.
Hajjo yakira Kai tsaye ya sanar Mata aikuwa hankali tashe tareda Hanifa suka fito lokacin har Anty Amina ma daya kira ta fito aka dauketa zuwa asibiti aka bar anty Amina tayi musu breakfast tazo daga baya.
Muguwar azabar datakeji yasa yau duk miskilancinta da sanyinta guduwa ta ringa Kiran sunayen Allah tana roqan gafarar mutuwa zatai
Aikuwa hankalinsa yayi mugun tashi yacewa Dr sa'id ayi Mata CS kawai tadaina Shan wannan wahalan dayake jinya acikin zuciyarsa na neman tarwatsewa.
Basa hakuri Dr sa'id yayi Yana cewa Kar ayi gaggawa zata haihu dakanta Inshallah.
Bata haihuwa sai gap da magriba lokacin tuni ta mugun galabaita Ana gama gyarata wani wahalallen bacci ya dauketa aka fitowa dasu hajjo da lafiyayyar jaririyar da Bata bar komai na Marshal ba sai bakin mamanta data dauko murna tasa iyalan gidan kasa barin asibitin Saida Naj ta farka daga dogon baccin gajiyar datai ta kalli fuskarsa Marshal din dake zaune dakin Kan kujera Yana rungume da 'yarsa dayakejin Babu abinda yakeso aduniya yanzu Sama da ita musamman idan ta Dan motsa har cikin ransa yakejinta.
Murmushi Naj din tasaki lokacinda take kallonsa shida babyn shima ya sakar Mata nasa murmushin Yana tasowa yazauna kusada ita ya Dora Mata bbyn batareda ya damu dasu anty Amina dake dakinba umma dai sulalewa tayi tabar dakin gwara su hajjo sunsaba gani.
Washe gari aka sallamosu suka dawo gida inda suka tararda komai anyi musu tanadinsa adakinta inda zatai jegon Yan gidansu kuwa sai zuwa barka sukeyi Hanifa takasa saka ranta koina sbd farin ciki,
Dadah Kai tsaye ta sakawa yarinyar sunan _Anqi Allah yaso_ Naj najin sunan tasan da ita Dadah take saigashi yarinyar taci sunan hajjo suna kiranta da _Noor_
Bayan sunan Noor da sati biyu su anty Amina suka bar qasar itada Dad Alfa sukai tafiya zuwa umrah dakuma Malaysia da dad din zaije wani taron tsofin Marshals hahifa ma bayan tafiyansu anty Amina da kwana goma Hanifa ta wuce aka barsu sukadai sai hajjo da sabuwar tsohuwar Mai aikin hajjo Dake kula dasu bayansu ruqayyat dasu nasu aikin gyara dasu girki ne,
Mum Malika shiryawa tayi ta tafi Ghana tana cewa idan bataiwa Hannah dukaba bazata dainajin abinda takejiba dan haka ta tafi tayo Mata dukan tsiya tana kuka Hannah din na kuka suka dawo gida suka koma Yan kallon ikon Allah Dole Hannah din tafara bawa masu nemanta Daman zuwa gurinta badan tasoba sai Dan shafawa Kai lafiya dason maso wani tunda gashinan Bai kaita koinaba kotayi dinma baqin cikin zata kwasa gwara tayi aure tabar gidanma ta huta.
Watan Noor uku sabon ciki ya bulla jikin Naj batareda sanin kowaba tace Masa su tattara su koma kafin asan da cikin batason surutun dadah Dan Allah,
Dama shi hakan yakeso sukai Shirin komawa sukaje yiwasu umma bankwana da shigarsu kallo daya Dadah tayi Mata tace"
'yar nan wani cikin Kika Kuma Yi da jaririyar 'ya??
Kallonsa Naj tayi ganin murmushin da maganar Dadah ta sakasa ta dauke Kai ta wuce tana qin tanka maganar Dadahn sbd duk su umma da Dattijo na gurin
Sama sama cikin kunya tayi bankwana da iyayen nata tafito bayan umma ta hadota da kayan *_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902_* washe gari sukabi jirgin asuba suka wuce tareda barin 'yan uwa da kewarsu.
Tunda suka koma wata sabuwar rayuwar Jin Dadi da kwanciyar hankali suka bude Mai tattareda tsananin so da qaunar juna gashi Kuma wannan cikinma baida laulayi Dan Haka soyayyarsu suke Sha Babu cikas ahaka tasamu cikin yakai wata bakwai lokacin Noor tayi 10month saita yayeta Hanifa tabiyo jirgi daga us tazo ta dauketa da dukkanin kayanta gabaki daya akan itace zatai riqonta.
Wannan karon Bata samu wahalar naquda ba ta haifo 'danta namiji lafiyayye shima sukai bikinsu dagasu saisu Hanifa dasukazo da 'yarta Noor sai anty Amina datazo tareda umma da hajjo Wanda Suma Dagan umrah zasu wuce da umman tayo kafin Hajj.
##MAMUH#
*_ALHAMDULILLAH YA ALLAH_*
*_DUKKANIN KURAKURAI DAKE CIKI ALLAH YA YAFEMANA GABAKI DAYA DANI DANA RUBUTA DAKU DAKUKA KARANTA,_*
*_DAN ALLAH KARKUCE BAI KAMATA YAQAREBA SBD BANSAN ABINDA ZA'A CIGABA DA RUBUTAWANBA IDAN BA'A TSAYA A GABARDA LABARI ZAI TAFIBA CIKIN MARMARI BATAREDA ANYITA JANSABA HARYA FITA RANMU MU DUKA, DAN HAKA KAWAI MUCE ALLAH YASA MU AMFANA GA ABINDA MUKA KARANTA,_*
*_IDAN AKWAI INDA NAYI MANTUWAR WANI ABU KU DAUKESA AMATSAYIN AJIZANCI NA DAN ADAM,_*
*_SAIMUN HADE AGABA,_*
*_ALLAH YABAR SO DA QAUNA NAGODE SOSAI._*
ZAFAFA BIYAR.
*_ZAFAFA BIYAR 2022π₯_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*ππ
Dβaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*πππ
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*ππ
09134848107