Showing 27001 words to 30000 words out of 92879 words
bayan fitarta ta rufe dakin tashiga wanka.
Sai dare Su Hanifa suka dawo Hannah kuwa da alama acan zata kwana
Koda suka dawo tuni ta kwanta saidai sukai Saida safe a waya sbd ciwon Mara dake damunta yanda Hanifa taji muryarta yasata zuwa dakin ta dubata saidai ta Dan daure ta nuna Mata ba wani Abu kawai Dan ciwon marane hakanan Hanifa ta tafi tabarta saidai ta tafi da room card din dakin sbd zuwa dubata idan taji shiru da yawa ta fice ta tafi bayan ta rufo Mata dakin,tun yamma yafara yimata ahankali yanzu yafara yimata tsanani Dan kuwa sosai take jinsa gashi tasan lokacin period dinta baiyiba da sauran lokaci.
Daqyar tasake lallabawa tayi wanka da ruwan zafi sosai ta 'dan gasa Marar ta fito ko miqewa tsaye Bata iyayi sosai ta daddafa daqyar ta Isa gadon ko kayan bacci Bata iya sakawaba ta fada gadon ta dunqunqune cikin duvet cover tana rufe idanuwanta dasukai ciki ciki sbd azaba.
Qarfe goma Sha biyu jirginsa ya sauka Bai tsaya jiran Azo daukansa ba yadauka taxi ya qaraso Lodge din tun daga reception aka sanar dashi katin dakinsa Mr Isma'eel Khamis ya karba Baice komaiba ya wuce ma'aikatan gurin na biyedashi da luggage dinsa.
Bangaren dasuke Yana daya daga cikin kebantaccen bangare da ba'a aje mutane da yawa yawanci ma sai couples sbd rashin hayaniya da tsaruwarsa Kai tsaye wayarsa ya fidda yayiwa Isma'eel text cewan gashinan hanyar dakinsu ya miqo Masa katin dakinsa.
Cikin sa'a katin na hannun Hanifa Dan Haka Kai tsaye ya karba ya fito suka hade a Hanya ya miqa Masa Yana Masa barka da isowa suka rabu ya wuce dakin duk da baya tareda gajiya sbd Babu wani nisa sosai daga can din zuwa Nan.
Kai tsaye bude dakin yayi da katin ya shige tareda karban luggage dinsa ya qarasa shigewa dashi ya rufe kofar Yana nufar Yana kunna wuta Mara haske ya aje wayarsa Yana Dan motsa fuskarsa sbd qamshin dayake gauraye da dakin na turarent possess dakuma humrah me sanyin qamshi.
Yamutsa fuska yayi Yana nufar fridge ya bude yaga har drinks dinsa ansaka a fridge din ya dauka daya ya bude ya shanye ya juya yabar gurin ya nufa toilet yashige tareda tubewa ya sakarwa kansa ruwan zafi yayi wanka da brush ya fito duk lokacin Bai lurada fararen panties din dake shanye a hanger na toilet din ba yafito daure da towel ya shirya cikin fararen _Fred Segal pyjamas_ ya kashe wayarsa gabaki daya ya nufi gadon ya Haye Yana yaye bargon zai shiga Yana ayyanawa aransa tabbas Hanifa tashigo dakinsa shiyasa yake ganin komai ba daidaiba da safe zasu sauya Masa kusan komai na dakin qamshin Nan na matane Yana Masa yawa.
Jin jikinsa yayi ya hadu Dana mutum da sauri ya tashi zaune Yana Dan yaye duvet din yakai hannu kan side lamp ya kunna Yana waiwayowa idanuwansa suka sauka Kan fararen cinyoyinta dasuke bayyane towel din jikinta ya zame saura kadan yabar jikinta
Ya dauke idanuwansa Yana maidawa kan fuskarta dake fayau tana baccin wahala Wanda ya takeyi tana farkawa sbd tsananin azaba.
Saukowa yayi gadon Yana Dan rintse idanuwansa cikeda mamaki da takaici ya dauki wayarsa ya kunna Kai tsaye no Hanifa yayiwa text cewan waye a dakinsa.
Karanta massage din tayi yafi so biyar tana maimaitawa cikeda mamakin tambayar Wai waye a dakin nasa bayan yaga ko waye dinne.
Kai tsaye da takaicin tambayarsa ta rubuta masa "itadin daice wadda kagani ko kanada wata matarne bayan ita?"
Kashe wayar yayi ganin abindata rubuto Yana sake boyayyan tsaki ya shafa sumar kansa sbd baya iya kwanciya da wani a gado daya baimasan ta Yaya zai kwanta da ita a gadon.
Hawa yayi gadon ya kwanta gefe daya tareda rufeta sbd jikinta dake bayyane ga towel din ta saman kirjinma yakusa zamewa Yana rufeta ya kashe wutar dakin ya kwanta Yana rufe ido dandai shi bazai iya kwanciya a sofa ba yabar Mata gadon.
Cikin bacci yaji mutum cikin jikinsa gabansu daya tana fidda wani irin numfashi me zafi da 'duminsa yake sauka cikin wuyansa yanasashi Jin wani iri ya bude idanuwansa ahankali ya zubawa fuskarta dake cikin wuyansa tana Nishi ya daga hannunsa ahankali yakai jikinta zai janyeta hannuwan ya sauka Kan shafaffen cikinta dake Mata ciwon zuwa mararta take tasaki wani irin numfashi da ajiyar zuciya wadda tasashi janye hannun Yana rufe ido sbd dumin numfashinta Yana Masa wani iri.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022π₯_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*ππ
Dβaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*πππ
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*ππ
09134848107
*_DM 19_*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINKππΎ_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINKππΎ_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINKππΎ_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINKππΎ_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*********************
Juyowa yayi Yakuma kallonta da idanuwansa da bacci yagama sakinsu yafara karantar yanayinta ahankali sai ya lura da kaman tanada matsalane Dan kuwa ko ayanda yasanta sama sama yasan bazata shiga jikinsa a hayyacinta ba,
Qaramin numfashi da yasaki Yana waiwayawa ya duba agogo yaga Daren yaraba sosai Babu ta yanda zai iya Kiran Hanifa yanzu ya lumshe idanuwansa Yana Kuma kallonta kafin Kai tsaye ya saka hannuwansa biyu ya juyota daidai Yana kallon fuskarta dake Dan tsatsafo zufa duk da sanyin aircon daya Kama dakin.
Baisan ya zaiyiba tunda ba Saba irin wainnan abubuwan yayiba aikine kawai su Hanifa suka hadosa dashi kawo Masa ita dakinsa gabaki daya.
Shafa fuskarta yayi tareda bude bakinsa ahankali cikin nutsuwa akaro na farko daya Kira sunanta.
Bata motsaba sbd wani irin rawa da jikinta keyi zufa na keto Mata
Ganin irin zufan yasa ya yaye musu bargon gabaki daya Yana dauke idanuwansa akan jikinta dake bayyane yakai hannu Yana janyota jikinsa Yana sake Kiran sunanta wannan karon da 'dan sauti saidai har lokacin Babu wani alamar tasan wayema yake tareda ita bare kiransa.
Dayaga baisan meyake faruwaba Kuma gadai zafi tanaji tunda tana zufa shikuma bazai iya kallonta ahaka ba Kaya jikintaba sai towel Wanda shida Babu duk daya sai kawai ya kwanta ya rufe jikinta da nasa ta hanyar sanyata cikin jikinsa ahankali yaji dumin jikinta na shigewa jikinsa.
Qamshintane yafi komai takura Masa sbd qamshine daya riga yagama kame jikinta tun Yana Dan rufe ido Yana budewa yanajin wani irin rashin sukuni ahakan Kuma baccin dole me daukeda ciwon Kai me qarfi ya daukesa Dan kuwa a rayuwarsa kaf baya iya tuna ranar dayayi baccin takura irin wannan Mai cikeda rashin sukuni na komaima.
Qarfe bakwai da arbain ta bude idanuwanta dasukai Mata mugun nauyi da kanta ma dayake Sara Mata sosai ta lumshe idanuwanta dasuka Dan kumbura tasake budewa tareda juyawa gefen gadon Dan lalubo wayarta taga karfe nawa gabaki daya batada qarfin jikin daqyar ta daga hannun tana lalubowa ko Ina taji bataji wayarba saita sauke numfashi Mara karfi tana tashi zaune ahankali ta zauna dakyau tsakiyar gadon tana bude idanuwanta da kyau suka sauka kan mutum zaune akan sofa Yana aiki da laptop a gabansa jikinsa sanyeda kayan geaming daya dawo jikinsa dake daukan ido duk kusan a bayyane sbd rigar jikinsa batada hannu hakama wandon jikinsa three quarter ne sai slippers din Gucci masu taushi a qafarsa gabaki daya hankalinsa nakan abinda yakeyi duk da yaji tashin nata Amma Bai dagoba abindake gabansa kawai yakeyi.
Wani irin mummunan faduwar gaba da firgicine ya shigeta lokaci daya tasake kallonsa da idanuwanta dake neman sauyawa da shakkar Shidin ne kuwa kokuwa?
A firgice cikin tsananin tashin hankali ta kalli jikinta da Babu komai har towel dinma Babu Yana cikin gadon
Mummunan faduwa gabanta yayi tashiga wani irin tashin hankali da baqin cikin dayake neman danne numfashinta jikinta ya dauki rawa ta janyo rigar baccinta dake kan kujeran mirror hannuwanta duka rawa sukeyi ta saka rigar tareda lalubo towel din ta daura ta sauko gadon ko cikakken qarfin jiki batada taqaraso gabansa murya a shaqe da tsananin baqin ciki da tashin hankali tace"
Menene yafaru anan?
Menene kakeyi anan?
Yaushe kashigo?ta Yaya kashigo Nan?
When?How? and why????"" Ta qarasa da fushi me tsanani acikin muryarta sbd dukkanin inda tsoro da tashin hankali yake tashiga so take taji menene yafaru,fatanta komai Bai faruba a tsakaninsu Dan kuwa Babu abindatake iya tunawa sbd drink din bayan qarfi da yayi Mata daya Bata reaction har fitarda ita hayyacinta yayi she just can't remember anything.
Dagowa yayi akaro na farko ya zuba Mata idanuwansa fuskarsa a matuqar hade ya qare Mata kallo saiyaga bazai iya tsayawa Mata mgna ba sbd yafara Mata kallon Bata hayyacinta ciwon Kai zata saka Masa kamar yanda ta sakawa kanta.
Ganin kallon rainin dayayi Mata ya dauke kansa baida niyyar tanka Mata hakan yasake Cinna Mata hauka Rai bace ta dauke laptop din dayake aikin ta dire gefe tana kallonsa da idanuwanta dasukai jajir Kai tsaye tace"
Banyi Kama da mahaukaciyaba inaga
Zan bude maka zance akan maganar aure dayake tsakaninmu Wanda haryanzu ban amince dashiba maganar Miji da Mata a tsakaninmu bakada wannan rights din akaina sbd bana maka kallon miji idan akwai abin dayake tsakaninmu shine Kai qanin Hanifa ne,
Bakada iko ko wani izini dazai baka Daman kusanci Dani can you leave this room now please tafada tana nuna Masa kofa idanuwanta na cikowa da hawaye sbd kukan datakeson fashewa dashi da tsoron ko wani abun yafaru.
Bai dago ya kalletaba ya miqe tsaye tareda damqar hannunta ya nufi kofa da ita tana fizgewa tana qwacewa ya tsaya jikin kofa da ita ya kalleta da fararen idanuwansa dake bayyanarda bacin Rai qarara acikinsu ya saki hannunta ya bude Baki yace"
Babu abin daya faru anan Kuma Babu abin dazai faru din ko ba'a yanzuba sbd Babu abindake jikinki dazaisa wani abun yafaru idanma akwai ajikin naki to Ni yamun kadan so kidaina tunanin wani abun yafaru sbd bana sha'awan macenda bata iya banbance tsakanin namiji da muna maza Dan kuwa idan har wani abun zai faru bakinki bazai tambayaba da ajikinki Zaki tabbatar, mganar karban aure ko tashin karbansa wannan nine Zan sanar Dan a hannuna yake get that to your dumb Head and get out of my room now.
Ballewa hawayen idanuwanta sukai takasa daga ko qafarta sbd tsananin qunci da baqin cikin daya rufe zuciyarta kukan dakeson subuce matane yasata nufar toilet tashige tana rufo kofar da qarfi hawayenta suka qarasa ballewa suna gudu kan fuskarta.
Meya sametane?
Wace irin rayuwace wannan?
A rayuwarta kila Bata taba magana da fushiba irin yau din,
Ta Yaya za'a gane damuwarta da wannan auren,
Tayaya zasu gane Bata so da qaunar wannan auren har cikin zuciyarta.
Kuka sosai tayi idanuwanta dasuke a Dan kumbure suka qarasa kumburewar daqyar ta danne tayo wanka tareda alwala ta fito sanyeda kayan data shiga dasu tana fitowa ta dauki Kaya Takoma toilet din ta sanyo ta fito ta tayarda sallah har lokacin Yana zaune Yana aiki a laptop Babu alamar zai nuna dayasan da akwai wata halittar a dakin aikin kawai yakeyi Amma gabaki daya ransa har lokacin a bace yake Dan kuwa baitaba saka bacin ran kowabama aransa Amma yau ta kunnasa ta yanda yakejin ko ganinta baya buqatan yi.
Tana idarwa ta miqe ta tattara kayanta ta maida cikin akwatinta duka ta janyo akawatin ta dauka wayarta da handbag ta nufi kofa ta bude ta fice.
Dakin Hannah ta nufa Kai tsaye tayi Knocking tana jiran abude har lokacin idanuwanta a Dan kumbure suke.
Jin shiru yasa ta fiddo wayarta takira Hannah din.
Hannah dake bacci taji ringing wayarta na tashi ahankali ta lalubo tareda bude ido tana dubawa taga sunan Naj tasaki wani tsokin takaicin Naj din kafin ta dauka cikin bacci tace"
Yes Naj menene?
Kintafi da room card dinkine ko Yana reception ko hannun Hanifa?
Tashi zaune Hannah tayi tana bude ido dakyau Dan kuwa idan har Naj na neman Mabudin dakinta kenan Marshal ya iso kaman yanda tasani they can't share a room.
Cikin farin cikinta da Bata boyeba tace"
The card is here with me Amma kiban 10min koma kiban 6min ganinan zuwa na bude Miki you are most welcome Naj.
Kashe wayar tayi tana dirowa gadon dakin gidansu Sofia dasuka kwana ta dauki Jakarta da kayanta a hannu tareda daukan key din motar Sofia ta fice da sauri sauri gudu gudu tana Isa inda motar take tafada tareda tadawa taja da qarfi ta fice.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022π₯_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*ππ
Dβaya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*πππ
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*ππ
09134848107
*_DM 20_*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINKππΎ_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINKππΎ_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINKππΎ_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINKππΎ_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Batason Kiran Hanifa sbd batason damunta tunda tana tareda Isma'eel shiyasa ta takura kanta tayi tsayuwar jiran Hannah bakin kofar dakin tanajin gabaki dayama gida takeson komawa Amma sbd bazata iya barin hanifar ba ayanzu datake buqatarta akusa da ita shine kawai zaisa ta tsaya Amma da baby abun dazai hanata barin qasar a ranar gabaki daya toshewar numfashi takeji a garin gabaki daya.
Da kayan bacci riga da wando sai jacket data doro a sama jikin Hannah Babu kunya ta iso lodge din tayi parking tareda fitowa taqarasa reception ta wuce da sauri sauri
Tana qarasowa tahau bude dakin tana cewa"
Sorry nabarki kina jira,shiga
Shigo ki aje kayanki Zaki iya zama daganan har mu bar Sweden zanyi farin cikin zama taredake.
Bata cewa Hannah din komaiba ta shiga ta aje kayanta tareda nufar toilet tashige sbd tasan zatai matuqar wahala zama da Hannah sbd banbancin halayensu da rashin Jin juna dasukeyi,
Sam Hannah batai mataba sbd yanayin rawar kanta da iyayi dama komaima ita gabaki dayama Hannah is suffocating her Amma yanxu Haka zata zauna da ita kamema takeji akanta.
Wanka tayo tafito ta saka doguwar riga Mara nauyi ta zauna kan sofa tana shan tea me zafi ahankali tanajin Hannah dake cikin farin ciki shigewa toilet wanka,tana gamawa ta Haye gado ta kwanta ta rufa tana rufe ido.
Qarfe biyu zasuje asibiti Dan Haka biyu saura ta tashi tayi alwala tayi sallah ta shirya cikin _Pal zileri drawstring_ straight skirt navy blue da milk long sleeves sai milk scarf data daura ta fito daga ita sai wayarta a hannunta daidai Hanifa na qarasowa dakin zatai knocking suka kalli juna tana mamakin ganinta dakin Hannah ta waiwaya ta kalli hanyar kofar dakin Marshal tasake dawo da kallonta kan Naj din Kai tsaye tace"
Me kikeyi Anan Naj?
Kallonta Naj tayi Kai tsaye kafin ta Dan dauke tana cewa"
Nan nadawo.
Kallon mamaki Hanifa tabita dashi kafin ta kalli Hannah dake shiryawa cikin Adonta na daukan hankali ta Kama hannun Naj din tajata suka fita gabaki daya zuwa gurin motocin da zasu fita dasu ta saketa suna fuskantar juna cikin fara gajiya da halin Naj din tace"
Naj banso shiga cikin zancenku ba sbd ku duka biyun Ina sonku Ina qaunarku banason dayanku yashiga takura ko damuwa shiyasa nake dakatar da kaina ga fada Miki gskia duba da yanda akai Miki ba daidaiba ta hanyar daura Miki aure da Wanda kike ganin kin girma Amma Naga kinason yiwa kanki illa Dan kuwa shekarunki sun tashi sunbi iska daga lokacinda aka shafa fatihar aurenki da Marshal Dan kuwa yanzu shine me ikonki,
Duk ba wannan ba meyesa Zaki ringa bawa Hannah damar dazata ringa qara samun kusanci da mijinki bayan kinsan zata iya Jan raayinsa tunda ita mace ce Kuma itama din kyakkyawace kina ganin Jin kan Nan naki bazai damekiba agaba idan Baki dakata wannan shirmenba koni da hajjo bazamu iya taimaka Miki ba agurin Wanda kike rainawar sbd namijine wani lokacin Kaine zaka sauke Kai kabisa Amma bazaki gane hakan yanzuba sbd Baki Gama sanin meye auren ba kokuma nace kinsani zuciya ta hanaki fahimta.
Da yanayi na rashin me zatace ta kalli Hanifan idanuwanta akanta da damuwar meyene abin tattaunawa anan ta bude Baki zatai magana idanuwanta suka sauka kanshi Yana tahowa sanye cikin _Escada jeans_ blue da farar _Saint Lauren_ long sleeves sai _Shiels Emerald_ sunglasses dake fuskarsa daya Gama fito da fuskarsa dake wani irin daukan hankali Hannah ce taredashi tana sanye da jeans da Lois chiffon shirt sai qamshi take fitarwa suna tafe tana Masa firar outing dinta da friends dinta gabaki daya ta cika Masa kunne Amma baiyi yunqurin dakatar da itaba.
'dauke idonta tayi akansu tana fasa maganar dazatai ta Dan dauke Kai,
Waiwayawa Hanifa tayi tagansu ta juyo ta kalli Naj din data dauke Kai cikin kawar da zancen dasuka fara tace"
Muje wainda ake Kira sun fito.
Isma'eel yafadawa su hadu a asibitin kawai ya nufa motar dayasa aka kawo Masa ya karba key yashiga Hannah tashige gaba ya tayar suka bar gurin batareda ko kallon inda suke yayiba har it's har Hanifan Bai nuna yasan dasu dinba ya wucewarsa.
A motar Isma'eel su suka wuce motar shiru Babu Wanda yake magana sbd kowa da abindayake ransa musamman ita datake qara Jin duk garin yafita kanta.
Hanifa duk yanda takejin damuwarsu tata damuwar tafi damunta sbd tana cikin hali na tsananin damuwane Dan kuwa wannan karon idan akai Mata dashen baiyiba shikenan tasan batada Rabon zamtowa uwa da samun 'dan kanta.
Koda suka Isa asibiti Dr sa'id na can already Dan Haka shine ya tarbesu suka wuce zuwa ganin Dr Kenneth din Wanda ke fifth floor.
A reception ta zauna jiransu sbd Hanifan ce kawai zata shiga sai Dr sa'id Isma'eel Yana kofar office din Yana jira.
Kusan awanni hudu suka shafe kafin suka fito suka sauko daidai isowar marshal dake waya cikin nutsuwa har lokacin Hannah na gefensa Kamar wasu sabbin aure.
Dauke kanta tayi daga kansu tana kallon Hanifa cikin kulawa ta riqo hannunta tana cewa"
Are you ok sweetie?
Kallonta Hanifa tayi da idanuwanta dasukai jajir sai kawai takasa magana ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciya sbd batason yin kuka tana neman qwarin gwiwane.
Kamo hannunta Isma'eel yayi Yana shafa kanta cikeda kulawa da bayyanarda tsananin Sonta dayake cikin zuciyarsa yace"
Hanifa Inshallah komai zaitafi lafiya
Zaki dauka cikin lafiya ki haihu lafiya
Duk gamunan muna taredake I am here,Marshal is here, Naj is here too and Dr sa'id ma Yana Nan inshallah Zaki samu lafiya da abin dakikeso.
Ahankali ta gyada Kai tana cewa"
Thank you Zawj.
Murmushi yayi Yana cewa"
Muje to kina buqatan hutawa.
Kallon Marshal yayi Yana cewa"
Gobe za'a fara processing aikin.
Lodge suka koma tun a hanya Naj din ke Dan sake kwantarwa da Hanifan hankali Koda suka Isa daki ta wuce ta fada kan gado tana sauke nannauyan numfashi kanta na Dan sarawa sai daga baya ta samu ta lallaba