Showing 63001 words to 66000 words out of 92879 words

Chapter 22 - DEEN MARSHALL COMPLETE DOCUMENT .txt

27 Nov 2024

6148

taja zancen yafita sbd rashin Jin ta.


Umma kallonta take zuciyarta na zafi ta tiriri Tama kasa cewa komai sbd zuciya data Gama cinta
Hanifa ta Kama hannun umman suka Isa bakin gadonta ta zauna tana bude Baki ahankali tace"


Umma Dan Allah kiyi hkr karkiyi irin wannan fushin addua zamu taru muyi Mata,tayi lafi babba Kam wannan karon Amma Dan Allah Kar ayi fushi da ita tashiga damuwa kuma wani ciwon yashigeta tunda har dai akwai cikin.


Fuzgarta anty Amina tayi Dr sa'id da Isma'eel yabita Yana cewa"


Kibita ahankali sbd yanayinta Mana.


Kala Bata samu cewa ko wannnensuba sbd zuciya data Gama cinyeta itama.


Sarah da duk tagama Shiga rikita rikita ita ta Isa motar Naj dasuka zo da ita da sauri,
Anty Amina ta bude baya ta tura Naj din da lokacin take kuka sosai na abun duniya daya rufto mata tonon asiri cikin dare guda.


A mota Babu abinda Anty Amina keyi sai tsokin baqin ciki akai akai
Tanajin badan cikin ba Kamar ta rufe Naj din da mugun duka da zagi.


Suna Isa gida Sarah na parking suka fito Naj tayi gaba tashige gidansu tanajin bazata iya Shiga gidaba ta hada ido da hajjo da maganar cikin.
Bayanta anty Amina tabi Sarah Kuma da motar ta nufi gidan Alfa tashige tayi parking tafito itama jiki duk a mace da yunwa da damuwar halinda Naj take ciki.


Sashen hajjo ta nufa Kai tsaye cikin sa'a hajjon na Palo tana jiran Alfa dazasu asibiti tare,Sarah ta qaraso tana gaidata cikin girmamawa kafin ta miqa Mata key din motar Naj din tace"


Hajjo ga key din motar Naj zantafi gida Saida safe.


A asibitin Kika barotane?bazata dawoba ta huta tun safe.?


Shiru Sarah tayi tana Dan Jin nauyin fadawa hajjon saidai gwara ta fada Mata sbd a yau idan wani baijeba Dattijo zai iya yiwa Naj dukan fulawar biredi,ta daure tace"


Aa tare muka dawo tana Nan gidansu akwai matsala ne,tun asibiti ummanta tafara....shiru tayi tana kasa fada.


Da zallar mamaki hajjo ke kallonta tana cewa"


Meya samu Najman?
Matsala Kuma wace iri?


Miqewa dai tayi ganin yanda Sarah ke qaf qaf da ido tana qin fadar abinda Najma tayi ta nufi kofa tana cewa ruqayyat tashiga gidansu Najma.
Sarah Bata bita ba ta wuce gida tana fitowa.


Koda su anty Amina suka shiga gida Naj dakin ummansu take neman shigewa anty Amina ta jawota Bata tsaya koina ba sai gaban Dattijo dake zaune tareda Dadah suna maganar auren Asmau da za'a zo tambaya.


Dattijo ya dago yana kallon Naj din dake kuka har lokacin kafin ya kalli Anty Amina yace"


Ita Kuma wannan ya akai da itane?
Tasake gudowar ne batason auren?


Numfashin takaici anty Amina tasaki kafin tace"


Cikine da ita shine taje cirewa batareda sanin mijintaba yau dai harta Kai qarshen hakurinsa sai daya bayyanar.


Wani irin kallo Dattijo yayiwa Naj din Yana Dan gyara zama ya maida hankalinsa Kan Anty Aminar Yana sake tambaya cikin rashin gane bayaninta na farko yace"


ta samu cikine kokuwa?sake mun bayanin.


Dattijo cikine ajikin zata zubar bada sanin mijinba hakama bada sanin su hajjo ba......


Wani irin salati me qarfi Dadah tasaki tana kallon Naj da idanuwanta waje cikin daga murya da mamaki yagama suqeta tace"


'yar Nan ciki gareki?
dama Ashe kingama daidaitawa da mijin kike zuwa Nan Dan kin Gama rainamu kike zuba Mana hauka kullum bakyaso bakyaso to uban waye yayi Miki cikin?
Kokuwa shima mune mukai Miki Dole?yau ga 'yar banzar yarinya.


Hajjo data iso takuma ji abinda ake fada tayi saurin janye Naj tana kallon Dattijo daya Gama siqewa da wani irin mummunan baqin ciki da takaicin Naj din ta kallesu su dukan tace"


Haba Hana Dattijo wannan ba abun daza'aita tonawa bane Dan Allah abar maganar har asamu zuciyoyi su lafa Najma muje gida.
##MAMUH#




*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*




*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107






*_DM 42_*
Kasa motsawa Naj tayi sbd tsananin nauyin da kunyar dasuka riqe qafafun nata,ta sake soke Kai hawayenta dake tsiyaya masu yawa suna qara gudu Akan fusakarta datai jajir tarasa ta Yaya zata dago ta kalli hajjo.
Miqewa tsaye Dadah tayi tana sake kallonta har lokacin da bayyananen mamakine a cikeda da ita Bata iyayin shiru da magana ta matso gaban Naj din tana Mata kallon kinci Amanata tace"


Da tuni da kike bori da yamutse yamutsen bakyason mijin da auren,qanin qawarki dama Ashe kingama daidaicewa da abinki Kika barni inata faman lallabaki Ina ranqwafar da duk masifata sai abinda kikaso nake Miki Dan kawai musamu ki hakura Ashe duk kallon Mai saman ruwa uwa kike Mana har kinsamu Dan rakiyarki a dakin hajjoΒΏ


Kallon hajjo Dadahn tayi tana cewa"


Kinada labarin wannan salalar da akai Miki kokuwa kema bakida labarin Raina Miki wayon take?
Dattijo maza wanke fuskar Nan tata me Kama da wankakken karas da Marikanda saita nema hanyar asibitin makafi da kanta,
Dukan Yanda taci Amanar rarrashi da kwantar da Kan danake Mata zakamin Dan kuwa ta Jima tana zambatata,
Yarinya ido a kafe amma ta....


Cikin damuwa da Dan takaicin maganganun Dadah hajjo ta kalli Dattijo da baqin cikin duniya da takaicinsa yasashi qamewa gefe Yana kallon Naj din Dan kuwa dukan wankin bargo yakeson Mata Amma hajjo ta tareta shiyasa yakejin tafarfasar zuciya da kunyar yanda zai kalla su hajjon musamman Alhaji Alfa akan wannan mugun tunanin da niyar data shiga Naj din.


Har lokacin tana rakube Kai a soke takasa dagowa ta kalla kowa sai zuciyarta dake raunana da girman kunya da kukan kunyar Dan kuwa tonon asirin da Dadah ke Mata yasa kusan duk sauran jama'ar gidan suka fito tanaji Umma habiba data iso gurin da mamakin hayaniyar fadan Dadah daya dayake tashi cikin mamaki take kallon bakin Dadah dake fadar ciki ajikin Naj,ta Dan fito da idanuwa cikin kaduwa da mamakinta itama daya kasa bayyanuwa tace"


Najman ce da ciki?
ToΒΏLallai aure yayi albarka tunda har ansamu rabo kafin tarewa.


Da wani sabon takaici Dadah ta kalleta tana Mata mugun kallo tace"


Bar Nan tunda daman ke bakya fadar alkhairi.


Juyawa tayi ta tana barin gurin tana cewa"


ALLAH dai yasa a sauka lafiya tunda Naga kamar cikin ya kwana biyu da Samu.


Kamo hannun Naj hajjo tayi tareda kanta Kai tsaye suka wuce tana cewa"


Sai da safenku" suka wuce.


Tunda suka fito gidan hajjo ta saketa ahankali tana gaba Naj din na bayanta qafafunta na tafiyar da kyar sbd yanda takeji a zuciya da jikinta.


Suna fitowa waje motar Marshal na tsayawa da Umma aciki tafito fuskarta a matuqar daure hajjo na ganin hakan ta waiwayo ta kalli Naj da har lokacin kanta a qasa yake takasa dagosa a natse tace"


Najma wuce gidan Ina zuwa.


Daqyar ta daga kafafu ta taka ahankali ta wuce ta nufi gate din gidan securities na wangale Mata tashige.


Sai data Shiga harabar gate na biyu na gidan tasamu ta Dan dakata tareda Dan dagowa tana share hawayenta dasuka cika Mata ido ko gani Sosai batayi.
Wucewa zatayi ta qarasa ciki hancinta ya shaqo Mata qamshin turarensa ta dakata ahankali tareda Dan juyowa gabaki daya ta zuba Masa idanuwa Yana tahowa ya fito daga motarsa fuskarsa amatuqar kame Kuma da alama Baigada tsayuwarta agurinba Dan ko kallon gurin datake baiyiba ya wuceta kadan saiga Hannah ta fito tana ganinsa ta qarasa gurinsa da sauri tana wani irin karya jikinta da shape dinta yake bayyane cikin wata straight English gown data kwana jikinta sosai sai qamshi takeyi cikin kashe murya da kulawa tace"


Kasa hankalina ya tashi tun Rana nake kiranka baka dagawa asibiti ma ko danaje duba Hanifa bakacan duk sai ahankali na yasake tashi,Yaya kake?


Wucewa yayi tana binsa a gefensa ahankali ya furta" Hannah kaina na ciwo bana buqatan abin dazai qaramin ciwon kan ok???


Ahankali Naj data dauke idanuwanta daga kansu ta daga qafafunta tafara tafiyarta ta wucesu batareda taji abinda suke fada ba Kai tsaye sashen hajjo ta nufa ta shige,


Shima hanyar nasa sashen ya nufi yabar Hannah tsaye agurin tana binsa da kallo zuciyarta fal farin ciki ahankali tace"


Koma dai menene Kai nawane tunda nasan yanzu kowa yasan da maganar cikin zanjira gobe naji sakamakon inda cikin yafito.
Juyawa Tai itama ta wucewarta.


Naj na Isa palo Bata tsayaba Kai tsaye dakinta ta wuce tareda rufowa ta qarasa Kan kujera ta zauna sai alokacin yasake sakin sabon kuka Mara sauti tana dafe zuciyarta dake tsananin zafi da bugawa.
Sai datai kukan hartaji sauran qarfinta ya qare ta share hawayenta tareda miqewa ahankali ta nufa toilet ta shige bayan ta cire kayanta.
Wanka tayo sosai tasamu jikinta ya Dan sake taji qarfi qarfi Bata shafa komaiba ta saka riga da wandon bacci masu kauri da hula tana sallame sallar ishai ruqayyat na shigowa daukeda abinci ajere harda orange juice da kwanakin akaga ta maqalewa Sha sai yanzu da zancen cikin ya fita suka fahimci dalilin Shansa kenan.
Ajiyewa ruqayyat tayi tana gaidata kafin ta juya ta fice.


Tsananin yunwar datakeji tasata cin abincin sosai bawai Dan tanada appetite na comes din ba Tasha orange juice din ta miqe ta nufi gado ta Haye ta kwanta tanason fita Amma bazata iya kallon hajjo ba ta kwanta tareda rufe idanuwanta bayan ta rufa.
Tanaji ruqayyat tayi Knocking kafin tashigo ta tattara kayan abincin ta gyare gurin ta fice bayan ta kashe Mata wuta.




Washe gari tun da wuri ta tashi tayi sallah Takoma bakin gado ta zauna tana tunanin yanda zata iya fitowa Palo ta nufa kicin neman abinda zataci sbd cikinta dake wani irin kukan yunwa,batasan da wane ido zata kalla su hajjo ba.


Daurewa tayi takoma ta kwanta bayan taci wani short bread biscuit dake cikin handbag dinta wani sabon baccin wuya yakuma dauketa.
Bata Farkaba sai qarfe Tara shima yunwarce takuma tada ita ta sauko gado nufi toilet takuma yin brush ta fito Kai tsaye ta nufi kofa ta bude ta fito palon sbd tunanin zuwa lokacin hajjo tana asibiti taje.


Dining ta nufa Kai tsaye ta zauna babu kowa a palon da dining din duk saitaji jikinta yaqarayin sanyi ta zuba abincin ahankali tafara ci wayarta na hannunta tanason Kiran Hanifa taji Yaya jikin nata Amma takasa sbd Jin nauyi da kunyar,
Ita yanzu shikenan abin daya sameta kenan na kayan kunya da to Nan asiri.


Kofar dakin hajjo aka bude gabanta ya buga da qarfi jikinta na mutuwa ta dago ahankali tareda waiwayowa idanuwanta suka sauka Kan kyakkyawar fuskarsa dakeda cika ido yafito dakin hajjon ta dauke Kai ahankali daga kansa ganin Babu alamar zai nuna yaganta kokuma yasan da ita a palon ya nufa kofa ya fice yabar palon da qamshinsa daya sanyata Dan rufe ido tanajin cikintama yacika da abincin ta miqe tabaro dining din takawo tsakiyar palon saiga hajjo ta fito fuskarta ba wani alama na bacin Rai ko fushi ta kalli Naj din cikin kulawa tace"


Najma kinci abinci kuwa?


Batareda ta dagoba ta bude Baki bayan ta sauke Yar ajiyar zuciya tace"


Eh.


Ok kije ki kwanta ki huta Babu maganar sake fita gareki umarnin mijinki ne daya gindaya Wanda Nima na Aminta da hakan Dan Haka ki nutsu hutu kawai Zakiyi.


Komai bataceba bayan gyada Kai datai tana wucewa dakinta sbd ita kunya da wannan tunanin da kowa keyi akan cire cikin yagama dama Mata lissafin Kai sbd batasan ta Yaya zata iya sanar dasu cewan tariga tafasa cire cikin,zata bar abunta tun kafin komai ya faru,
Shi takeson ya fahimci hakan Amma batajin zata iya yimasa wannan bayanin na bafa zubar da cikin zataiba yanzu sbd da alama baya buqatan bayani ko iya sauraran wani abun.


Wuni tayi a daki ko palon takasa fitowa saidai ruqayyat dake yawon Kai Mata abinci da fruits wanda hajjo tace aringa Kai Mata dakin tunda bazata iya fitowarba tana sane da tsananin kunya komaice ke dawainiya da Naj din Wanda itama har cikin ranta Bata daina mamakin yaushe har suka samu wani kusanci da fahimtar data kaisu har ga mu'amalar aureba saidai sukaji ciki suna Nan suna jiran saukowar Naj din Ashe tuni suka San yanda sukai suka kebewarsu kilama Kamar yanda Dadah tafada acikin sashenta aka samu cikin tana Nan tana dakon bin dare da adduar Allah ya kawo kusancinsu ga wannan aure.,
Lurada tsananin kunya da girman kunyar dake dawainiya da Naj harta yanke shawaran cire cikin dakuma yanzu da kowa yasani yasa ta bar nata fadan da zancen cikin ranta ba yanzuba sbd Kar abin yayiwa Naj din yawa damuwa ta shigeta ga juna biyu a tareda ita badan hakan ba na Dadah zatai Mata taji suna Ina akai wannan babban aikin ga Marshal din yadauki zafi gabaki daya yakoma Marshal dinsa ko maganar yace Kar kowa yayi Masa baya buqatan ji.


Har dare Haka ta wuni Babu wani doguwar walwala sbd daga daki sai daki asibitin ma takasa Kiran kowa nauyi da kunyar kowa takeji qarshe Sarah takira a waya ta tura asibitin ta dubo Mata jikin Hanifan.
Dukkaninsu wainda Sarah ta tarar a asibitin suna ganinta suka San Naj ce ta aikota Amma Babu Wanda yayi maganar saima Hanifa data kalleta cikin kulawa tace"


Sarah Yaya uwar dakinki?


Murmushi Sarah tayi tana Dan satar kallon inda Marshal yake zaune Hannah na gefensa sai wani basarwa takeyi itama tunda tasamu Marshal din ya taho tareda ita bayan ta nace Masa akan motarta nada matsala.


Kallon kyakkyawar fuskarsa dake Kan wayarsa tayi tareda dauke idon ta maida Kan Hannah dake gefensa tamkar wata sabuwar amaryarsa ta dauke Kai tanajin zafin Hannan ta Dan kalli Hanifa tana miqewa tsaye tareda qaqalo murmushi tace"


Tana gida Ina saka ran Kuma tana Lafiya sbd banje ba saidai gobe kila zanje nadubota,
Zan tafi, Allah yaqaro lafiya.


Amin anty Amina tace tana cewa" ki gaida umma Jamila.


Zataji." Juyawa tayi ta fice batareda ta sake kallon inda Marshal din yakeba Dan har cikin ranta take jiwa Naj dinta kishin Hannah da kusancin datake samu dashi.


Da maraicen ranar aka sallami Hanifa suka tattara suka dawo gidan sbd taqarasa warwarewa a gida kafin Takoma duk da dai Isma'eel din tafiya zaikuma Yi idan yadawo zai fara Mata Shirin su koma gabaki daya can qasar da yake tare kowa ya huta.


Tana daki taji dawowarsu gabaki daya harda ummanta da anty Amina sai hanifar da Isma'eel daya fice bayan shigowarsu.
Fuskewa tayi ta fito sanye cikin doguwar riga Mara nauyi sosai ta wani English material fuskarta tayi fayau kowa yabita da kallo sbd zuwa yanzu da zancen cikin ya fito kowa yasani sai dukkanin alamomin cikin suka bayyana da kyau tanajin zuciyarta na narkewa cikin kunya me girma da tsanani Amma ta fuske ta qaraso tsakiyar palon ta nufi gefen Hanifan ta zauna tana satar kallon ummanta data miqe tana cewa"


Zata shige gida.


Anty Amina ce ta kalleta bayan tafiyan umman tace"


Uwar biyu angama kukan borin kunyar?
Yanzu kowa ya daina biyewa kukanki da borinki tunda angano kukanki da borinki daban aikin da kike dabam.


Qaramar dariya Hanifa tayi Mara sauti tana kallon Anty Amina tace"


Please Anty Amina karki saka tafasa zaman Takoma daki Mana.
Kallon Naj tayi a natse cikin kulawa tace"


Maman baby Yaya?ya jiki jikin?


Banza tayi musu duk su dukan tana sake daurewa tana Hana kanta komawa daki,
Hajjo ta katse zancen da cewa"


Kar Wanda yakuma yimata maganar daba ita takesoba,
Kubarta taji da laulayi daya dameta.


Itadai har lokacin Bata ce komaiba saima sake fuskewa datai tana tambayar Hanifan Yaya jikin.


Anan gidan Anty Amina ta wuni sunata firarsu itadai Bata wani saka Baki sbd gabaki daya bakinta ya mutu a gidan,
Ko dataji Dadah tashigo sulalewa tayi ta shige dakin hajjo sbd Kar Dadah taqara Mata wani tonan asirin Dan kuwa tasan Dadah tafara kenan daga yanzu.


Da daddare su kadai Sukaci abinci batareda Shiba Hanifa Kuma duk wani abinda tasan Naj din ta nacewa ci a kwanakin Haka tasa aka kawo Mata duk da tana cikin radadi na rashin nata cikin Amma tana farin ciki dana 'dan uwanta da Aminyarta.


Washe gari ma Haka suka wuni tana ta kokarin kawar da Jin nauyinta sbd ganin hajjo ta share maganar laifinta na maganar cire cikin Kuma ta Hana kowa tada maganar,
Kwana biyu tana Jin nauyi zuwa gaida Dad Alfa qarshe dai Haka ta hakura taje har palonsa gaishesa jiki ba nauyi ta fito
Tana fitowa taci Karo da Hannah tafito sashen Marshal suna tare fuskarsa tayi wani irin fresh sbd hutun dayake samu kwana biyun da baya fita koina Yana part dinsa gabaki daya skin dinsa yasake kyau,Yana sanyeda fararen Kaya qafafunsa sanyeda slippers na gucci
Hannah na ganinta ta sake matsowa kusadashi sosai tana sake karya murya tana cewa"


Marshal please zanbika Nima akwai program dazan attending acan tunda sati biyu ne zuwa uku zaka dawo I really want to go with you.


Dan kallonsa Naj tayi tayiwa fuskarsa kallon seconds kafin ta dauke idonta tana dauke kanta tana wucewa sukuma suna bayanta har cikin palon hajjon
Tana Shiga ta nufi hanyar dakinta batareda ta tsaya gurinsu Hanifa dake zaune palonba.
##MAMUH#




*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107








*_DM 43_*
Tana shiga dakin nata jin tayi numfashinta na toshewa ta nufa windows din dakin da ba'ata taba budewaba ta yaye curtains dinsu ta bude tana shaqar iska Dan Kamar zata sanqame takeji.


Iska ta shaqa sosai agurin har sai daya fara Mata yawa sbd Ana Dan iska sosai agarin da sanyi,
Shiru tayi tareda fadawa tunani me zurfi na yanda komai ya sauya a rayuwarta tadawo yanda take yanxu,
Ahankali takai hannu tana dafe cikinta bugun zuciyarta na sauyawa da tsananin so da qaunar jariri ko jaririyarta,
Tabbas tanajin shauqin kauna irin ta uwa ga cikinta ta lumshe idanuwanta dasuke ta cikowa da hawaye tana maidawa ahankali sbd qamshin turarensa daya shiga hancin nata ta bude idanun suka sauka akansa ya wucewa ta makeken windon kyakkyawar fuskarsa datafi komai cikawa mutane ido tana a Dan sake Hannah nataredashi har lokacin.


Dauke kanta tayi daga kallonsu tana rufe windows din Takoma Kan sofa zata zauna saikuma ta fasa ta nufi toilet tana wanke fuske fuskarta datake Jin idanuwanta na yaji yaji.


Da daddare Koda suka zauna cin abinci da wani irin yanayi na sanyi tafito sbd gabaki dayama zazzabi taji tanaji me qarfin gaske Amma ta daure ta fito sbd abinda aka tambaya tanason ci shi aka dafa
Cikeda kulawa hajjo ta kalleta tana cewa"


Najma Lafiyanki kalau ko?
Banason ganinki wani iri,akwai abinda kikeji ba daidai ba?


Dan qaqalo murmushi tayi tana Hana kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login