Showing 21001 words to 24000 words out of 92879 words

Chapter 8 - DEEN MARSHALL COMPLETE DOCUMENT .txt

27 Nov 2024

5664

da kanta tunda ba itace me ikon kanta da yanda takeso ba,
Idan Kika biyeta tunda ba tunani cikakke akantaba da Haka zata qare rayuwar auren bare tana ganin cewan ta girmesa Wanda girmewar ta zama ta banza da wofi dankuwa yanzu a qasanshi kike.


Murmushi manya hajjo tayi tana kallon Najman dake gefenta zuru tace"


Bazata tareba saita buqata hakan da kanta inshallah,
Ina Kuma da tabbacin zata buqaci hakan Inshallah.


Kasa wata magana Dadah tayi sbd takaicin Najman datai shiru alamar hakan shine yayi Mata daidai ta miqe tana cewa"


To na tafi Ni Saida safenku Allah ya bamu alheri Dan dai Naga alamar a sashenki kila za'a haif....katseta hajjo tayi da cewa"


Amin ya Allah Dadah Saida safe" saboda sanin Dadah zata iya yanko zancenta tsakani da Allah.
##MAMUH#






*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107








*_DM 14_*
Bayan tafiyar dadah hajjo ta kalli Najma da kallo daya zakai Mata kasan Kuka ta kwana ta yini tanayi duk da hakan fuskarta is so fresh sbd wankan da Bata Jima dayiba ga qamshinta tunda tafito ta zauna yake gauraye palon maida kallonta kan hanyar dining da jalal ke gurin har lokacin yanacin abinci Kamar wani sarki Wanda har lokacin Naj batasan da Yana palon ba ta miqe tana nufar hanyar dakinta tace"


Jeki ki kawomin ruwan dumi daki da Zuma zansha na kwanta 'yar gajiya nakeji.
Shigewa dakinta tayi tabar Naj na lumshe ido ahankali cikin sanyin jiki ta miqe ta nufi dining hanyar dining Dan dauko zuman tana tafiya a natse har saidata shiga dining area din da kyau taga Wanda ke tsaye agurin hannuwansa sanye cikin aljihun guntayen qananun kayan dake jikinsa zai bar gurin tana isowa.


Mayun fararen idanuwansa ya 'dan zuba Mata sbd yaji maganar Dadah ta banbancin shekarunsu data kawo Wanda yasashima 'dan kallon nata Dan ganin abinda ake ikirarin ya girmesa a jikin nata Wanda a iya ganinsa baiga komaiba sai kayan baccin dake jikinta riga da wando ba bra ajikinta sai idanuwanta dasukai nuni da kukan datai ya kalli iya tsayinta da shafaffen cikinta ya dauke Kai ahankali Yana barin gurin yabarta tsaye tanajin wani irin damuwa da 'dacin zuciya me qarfi duba da kallon tsaf sama sama da yayi Mata ya dauke Kai ya wuce yabar gurin da qamshinsa na _Tom Ford, Tobacco vanille_ daya zama Kamar maita tasan qamshim kamar me sbd shikadai tasani me amfani da turaren Dan tsadarsa.


Numfashi me zafi ta sauke tareda shaqaqqen tsokin dabai fitoba taji duk komai ya fice Mata a sukwane ta hadowa hajjo ruwan takai Mata ta fito ta wuce daki ta kwanta tanajin wani Abu toshe a maqogoranta da qyar tasamu bacci ya dauketa.


Qarfe Tara na safe ta fito Palo sanyeda doguwar straight gown ta atampar super exclusive maroon dataiwa farar fatarta kyau fuskarta fayau ko kwalli Bata sakaba saidai qamshinta daya zama na koyaushe dayake tashi jikinta idan ta kusantoka.
Da slippers a qafarta ta nufi kicin ta hado tea me zafi sosai tadawo Palo ta nufi dakin hajjo tana sha ta zauna kujerar dakin tana cewa"


Ina kwana hajjo.


Amsawa hajjon tayi tana cewa"


Kinyi waya da Hanifa kuwa?
Tun jiya Isma'eel yakira batajin Dadi Wai hannunta na dama ya riqe Yana ciwo kamarma yakira wayarki a kashe yace.


Miqewa tayi tana cewa"


Bari na dauko wayar tun jiya na kunna inaga Banda caji ne Bari nasaka nasamu ko kadan ne saina kirasu kafin na Isa.


Kallonta hajjo tayi tana cewa"


Ki Isa Ina da sabon aurenki akai NajmaΒΏ
Kinga hakuri Zakiyi tunda Isma'eel din na Nan Kuma Dr sa'id ma yaje tun jiyan Dan Haka basai kinjeba yanxu Bari a kwana biyu tukuna.


Shiru tayi yanayinta ba Dadi idanuwanta na sauyawa da ciko hawaye kafin Tai magana Hannah tashigo dakin da sallama muryarta a shaqe,hajjo na ganin fuskarta tasan itama kwana tayi kukan Dan kuwa a kumbure idanuwanta suke jajir.


Naj ta qurawa ido zuciyarta na wani irin harbawa da zafin radadin kishinta me qarfi saidai kamar yanda mum Malika ta hudubar da ita akan danne fushi da boye bacin Rai shine matakin nasarar komai tunda dai kowa yasan daga Naj din har marshal ba son juna sukeba aurene kawai na Hadi na huce takaici da fita kunya Dan Haka fushi da qunci ba nasu bane samun zama Matar JALAL da rabuwarsa da Naj ba wani Abune dazai Basu wuyaba ko daga musu hankali Dan Haka dole zasu danne 'dacin zuciyarsu.


Dan yaqen dole tayi tana qarasowa ciki ta zauna kusada Naj tana cewa"


Hajjo Ina kwana?
Ya gajiyan taro?
Allah yasanya alkhairi.


Hawayen datake dannewa suka gangaro ta qarasa gaban hajjo ta durqusa tana sake siririn kuka ahankali tace"


Dan Allah karkiga laifin kukana hajjo zuciyatace ke zafi bansan yazanyiba naji sauki bayan kukan sbd abin yazomin a bazatane.


'dan tausayinta hajjo taji Kuma tasan Kam Dole hannah zataji damuwar abin musamman datasan ayanzu Kam babu ranar auren Hannah din da jalal sai taga Najmanta tasamu zama dakyau tukuna Dan Hakan takejin tausayin Hannah ta dafa kanta tana cewa"


Kiyi hkr shi aure muqaddarine Kuma Allah yayi itace zata zama Matar ayanzu Amma kadaki daga hankalinki Matar mutum kabarinsace kema lokacin ne baiyiba ki kwantar da hankalinki kinji.


Shiru tayi tanajin wani qaton takaicin tsohuwar Yana tsaya Mata a maqoshi datake Mata zancen wani lokaci bayan ba Haka takeson ji ba.


Share hawayenta tayi tana miqewa a sanyaye ta juyo gurin Naj datake Shan tea dinta batareda ta maida hankalinta kan zancensuba ta Dan saki yaqen murmushi tace"


Naj Allah ya Sanya alkhairi da fatan bazaki ringa Jin damuwar alaqata da Marshal ba.


'dan kallonta Naj tayi kafin Kai tsaye tace"


Thank you" kawai taci gaba da Shan tea dinta Dan ita abundama zai ringa alaqantata da Marshal din Bata buqata Dan Haka Hannah ma na cikin abinda zata nesa kanta dasu.


Kallon tsaf Hannah taqare Mata tana ayyana wannan shariyar ta Naj datake Kamar wulaqantawa gareta kafin ta juya ta fice idanuwanta na sake kadawa da Jan baqin ciki da takaicin hajjo da Naj din.


Cajin wayarta Takoma daki tayi takira Hanifa sukahau wayarsu duk da taqi Bari Hanifan tayi Mata maganar auren itama Hanifan data fahimci Haka saita bar yimata maganar suka hau zantukansu.


Saida tayi sallar azahar ta 'dan ci abinci kafin taje gurin gaida Dad Alfa datun jiya Basu haduba tafara zuwa gurin mum Malika ta gaidata Kamar yanda suka Saba Babu komai a fuska mum din ta tarbeta suka gaisa Tai Mata addua da fatan alkhairi Hannah na daki tanajinsu taqi fitowa sbd ayanzu kyakkyawan fuskar Naj tafasa zuciyarta yake itakuwa Naj Kai tsaye palon Dad din ta nufa tana duba wayarta ahankali tashiga da sallama ta tura kofar palon tana kashe wayarta Yana zaune kuwa a palon suna magana da jalal dake gefensa sanye cikin farar jallabiyar datasa takasa ganesa sosai Dan kuwa hardasu qaramar farar hular tabani kaji hadisi datai Masa wani irin kyau sbd kayane dabai cika sawaba sai yazo Nan Dan acan kayansa idan ba suit ba sai uniform din aikinsa sai kuwa qananun kayan Shan iska dayafi sakawa idan baya aiki komai Wanda suna cikin kayan dasuke Masa kyau sbd kyan fatar jikinsa.


Dauke Kai tayi daga gefensa tanajin idanuwansa na yawo a jikinta ta qaraso ta zauna a qasa tana gaida Dad din cikin nutsuwa.


Amsawa yayi Yana Mata barka da gajiyar biki cikin farin ciki kafin ya Dora da yimusu nasiha musamman ita akan dole tabi umarni da hukunci JALAL kowane irine cikin biyayya.


Shiru kawai tayi batareda ta dagoba har yagama ta Dan dago tace"


Nagode Dad" ta miqe ta fice batareda Tama nuna tasan da akwai wanzuwar wani a palonba bayan su.


Bayan fitarta waiwayowa dad yayi ya kallesa batareda yace komaiba ya Dan saki gajeran murmushi Yana mamakin qarfin girman Kai irin nasu su duka biyun Wanda bazai taimakesuba.
##MAMUH#










*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107






*_DM 15_*
Washe gari sanin a daki ta wuni taqi fitowa sbd fahimtar dai a sashen hajjon yakecin abinci abinda Bata saniba shine baya fitowa zuwa cin abincin Rana acan ake Kai Masa sbd baya fitowa da ranar sai dare yake fitowa cin abincin Daren Dan masallaci kawai yake iya fita cikin Rana Amma bayan sallah Babu abinda yake sakashi fitowa cikin Rana Wanda hakan ne yasa skin dinsa yake fresh koyaushe.


Hajjo na sane da dalilin qin fitowar tata Dan Haka itama Bata damuba tunda lallabata takeson Yi Dan Haka Bata dametaba ta qyaleta,
Sai dare ta fito sanye da riga da wando na bacci farare masu tsantsi kanta sanye da qaramar hular da Bata Gama rufe gashintaba hannunta riqe da waya tana sai qamshi takeyi me sanyi ta nufi kicin ta dauko fresh milk Mara sanyi sosai tafito tanasha ta nufi dining tana shiga idanuwanta suka sauka kansa Yana zaune cikin fararen qananun Kaya hannunsa riqe da cup din ruwa marasa sanyi yanasha ahankali.


Dauke kanta tayi tana kokarin juyawa hajjo dake zaune taredashi tace"


Zoki zauna.


Dakatawa tayi tareda Dan rufe idanuwanta kafin ta bude ta juyo tareda kallon hajjon fuskarta Babu wani sauyi daga straight din datake cikin muryarta me nutsuwa Kai tsaye tace"


Banajin yunwa freshi milk din ya isheni bacci zanyi Dan natashi da wuri gobe zankoma aiki office.


Dan kallon Marshal hajjo tayi taga ko dagowa baiyiba bare yanuna yasan da zuwan wani agurin saidai tasan yanajinsu,
Ta maida kallonta kan Najma cikin kulawa da tausasawa tace"


Wane aiki bayan Baki Gama hutawa daga hidimar biki ba Kuma saikun zauna da mijinki kunyi magana akan aikin idan yaji zai Bari kici gaba.


Dagowa Najma tayi da idanuwanta dasuka sauya Nan take da maganar ta kalli hajjo sai Kuma takasa magana tayi shiru tana hadiye wani daci daya danne zuciyarta ta Dan rufe ido tabude ahankali tace"


Kaina Yana ciwo zanje na kwanta Saida safe hajjo.


Juyawa tayi zata wuce hajjo tace"


Dawo Najma zoki zauna.


Dakatawa tayi tafara sauke numfashi kadan kafin ta juyo tadawo taja kujera ta zauna batareda tace komaiba sbd Jin numfashinta ma takeyi Kamar siqe zamanta agurin da Wanda har lokacin Bai nuna yasan da wanzuwar wata halittar Dan Adam agurinba Wanda Kamar Ana sake sukar martabartane na mace dakuma girmanta.


Ahankali ya dauka tissue yana goge bakinsa Dan yagama cin abincin sai alokacin ya dago ya kalleta Yana kallon hajjo datake lallabata da alama zatai taurin Kai da taurin zuciya
Ya dauke Kai ahankali tareda miqewa tsaye ya zuba hannuwa a aljihun wandonsa ya bude Baki Kai tsaye a gajarce yace"


Saida safe hajjo" ya juya ya wuce yabar gurin harya fice itama Bata dagoba bare ta nuna tasan dashi,


Kallonta hajjo keyi tana Jin qaunarta da tausayinta tareda jinjina taurin zuciyarta Dan kuwa sosai ta hango tsanar auren da qinsa cikin idanuwan Najma da zuciyarta,
Bataji dadin hakan ba Amma Kuma Dole za'a dubawa Najma din tunda aurene na Babu shiri Babu sanarwa Babu amincewa musamman yanda take yiwa auren jalal din auren ci baya qarara amatsayinsa na qanin qawarta Wanda Kuma takejin bazata iya russunawaba ya juyata kamar yanda maza ke juya matayensu.


Hajjo da kanta ta janyo plate ta zubawa Najman abinci kadan iya Wanda tasan tana iya ci ta turo Mata gabanta cikin kulawa tace"


Ci abinci kafin kije ki kwanta din karki kwanta Babu wani Abu me Dan nauyi a cikinki kinji.


Bata iya gardamaba Sam musamman a yanzu da zuciyarta ke cikin wani hali Dan Haka ahankali tadauki spoon tafara cin abincin hajjo na kallonta tana sake Bata Baki akan karta damu Babu Wanda zai takurata akan komai.


Daqyar tayi spoon shida ta dauki ruwa Tasha ta ajiye ta kalli hajjo cikin nutsuwa tace"


Na koshi zanshiga daga ciki.


Tare suka miqe saidata raka hajjo har dakinta ta sake gyara Mata gadon kwanciyarta kafin Tai Mata Saida safe ta fice.


Tana Shiga daki toilet ta wuce tayi brush tafito ta hau gado ta kwanta tana rufa da bargo wasu hawaye suka gangaro Mata saiga kuka ya kufce Mata ahankali ta rufe idanuwanta tana sakin kukan ahankali tanajin wani irin radadi a zuciyarta,
Bayan qaddarar rashin aure data fasawa qarshe dai qaddarar irin wannan aurence take jiranta,
Auren Wanda ta girma,Wanda ko kallo Bata isarsa bare ya nuna sanin da ita a duk haduwar dazasuyi tayaya zatai rayuwa ahaka a gurin Wanda tafi Amma agurinsa ita ba komai bace face ta qarqashinsa,
Bata buqatar soyayya Amma dai tayi fatar yin aure inda zatai rayuwar 'yanci da mutuntawa tareda Bata kulawa da qaunar data rasa samu tun tashinta,
Batada shaquwa da mahaifiyarta sosai sbd miskilancinta,batada shaquwa da 'yan uwanta da kowa nata face Hanifa wadda itama itace me kokarin riqe shaquwar tasu sbd miskilancinta Dan Haka tayi fatar jinkiranta ya zamar Mata alkhairi tasamu mijin dazai rusa miskilancinta ya cike gurbinsa da soyayyarsa da qaunarsa Amma Haka qaddara tazo Mata Wanda ta gwammaci zamanta Babu me aurenta da wannan auren dazai ringa quntata rayuwarta a zahiri da boye.


Washe gari Haka takuma wuni a daki Bata fito ba a dakin ruqayyat takai Mata abinci Wanda hajjo tasa akai matan.
Koda daddare Bata fitoba saidata tabbatarda ya bar sashen ta fito taje tayiwa hajjo Saida safe Takoma takwanta.


Saidatayi kwanaki tana kiyaye duk wani Abu dazai hadata dashi ko a hanya ne dan ko Dad Alfa idan zataje gurinsa saita Gama tabbatarda Rana tagama tsagowa lokacinda taji baya fitowa kenan a bakin hanifa take zuwa gurin gaidashi su mum Malika ma tana Dan shiga sama sama sbd lurada Hannah Kamar tana Dan Jin zafinta Wanda Sam gabaki daya daga Hannan har Wanda takeyi dominsa basa gabanta Bata Kuma buqatan su shiga gaban nata.


Daqyar taga sati biyu tacika Isma'eel ya koma Hanifa tadawo gidan sai alokacin taji hankalinta yadan dawo Mata musamman yanzu da Bata ganinsa Babu me Mata maganar auren saitake mantawa tana fitar da abin a kanta ta tattara maganar auren ta watsar gefe tafara kokarin son komawa aikinta Amma Kuma Bata buqatan kowa yasake tada mata maganar Saida izinin wani ko damar wani zata fara fita aiki hakan yasa taketa dannewa.


Ta bangaren Marshal kuwa kamar yafita mantawa da maganar auren Dan kuwa gabaki dayama ya daina shigowa ko cin abincin akai akai wani lokacin Hanifa ce ke kaimasa suyo firarsu da maganganunsu dasuka shafesu acan duk da yawanci nasa sauraro ne sai kadan kadan yake saka doguwar magana tanason sako Masa maganar Naj Amma tana Hana kanta kamar yanda suka yanke da hajjo bazasu takuraba akan zancen ahankali komai zai daidaita.


Lokacinda tasamu labarin komawarsa abakin hajjo da Hanifa Sam Bata nunama tajiba Dan ba abune daya shafetaba Dan ita yanzu tabar auren akan hanyar data sauya Mata na uzzurawarsu Dattijo dasu Dadah da ummanta ma hakama dai tana gidane bawai wani gurinba hakama Wanda ake Kira da mijin da auren duk basa gabanta itama Bata gabansu Dan Haka hakanma is okay tunda tasamu yancinta ta wani bangaren.




Yau ciwon baya Hanifa ta tashi dashi me 'dan qarfi Dan Haka bayan zuwan Dr sa'id yadubata yabata wasu magani da wasu treatment dayasa sukai mata na Nan gida tasamu sauki Sosai ba laifi musamman datai bacci Sosai har yamma kodata farka alhmdlh taji sauki saidai Dan sanyin jiki na rashin qwari na wuni datai kwance Dan Haka wanka Naj ta taimakata Mata tayi tayi salloli taci abinci sai alokacin ta dan sakewa ta dauki wayar mijinta dake Kira tun dazu yanajin Yaya jikin.


Sai alokacin Naj tasamu nutsuwa tafito taje taci abinci tadawo tayi sallar ishai da aka Kira tana idarwa ta tube ta shige toilet wanka Dan bacci takeji Sosai.


Tun safe baya gida Yana gurin wani sabon company da Dad Alfa zai bude rashensa anan Wanda Marshal din zai sake zuba hannun jarinsa me kauri kamar yanda shares dinsa sukafi yawa a wancan company din da Naj take gudanarwa.
Sai kusan magriba suka dawo Dan Haka sallar magriba yayi ya shige Saida ya huta yayi wanka yayi ishai kafin ya nufo sashen hajjon qamshin TF tbc daya Gama Kama jikinsa Yana tashi jikinsa Hannah datakai Masa fruits salad daya 'danci kadan suka fito tare zuwa sashen hajjon tana gefensa tana Masa fira cikin wayewarta da sonsa daya Gama cire Mata kunyar kowa itama sai qamshi takeyi tana sanye da doguwar free grown me guntun hannu dayake bayyanarda tattoo dinta me dauke da sunansa a gefen kafadarta.


Babu kowa a Palo sai qatuwar LG TV dake aiko Dan hajjo na dakinta Kai tsaye suka nufi dakinsu Hanifan hannah na daukeda sauran fruits salad din dazata kawowa Hanifan Dan nuna kulawarta da damuwarta.
##MAMUH#








*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107






*_DM 16_*
Hannah ce tayi Dan knocking dakin so biyu kafin ya tura kofar suka shigo tana Dan nuna kulawa ta qarasa gurin hanifan tana ajiye bowl din hannunta kan table tana cewa"


Ohh sister in-law sannu da jiki tun dazu naso shigowa kaina Yana Dan ciwone shiyasa ban shigoba ya jikin?


Gyada Kai Hanifa tayi tana cewa"


Alhmdlh naji sauki thank you.


Dagowa tayi ta kalla Marshal din Yana tsaye da hannu cikin aljihu ganin hanifance kawai a dakin yasashi zaunawa ahankali kan sofa Yana kallonta da fararen idanuwansa ya bude Baki cikin kulawa yace"


Yaya jikin?
Ina tare da dad yau duka sai yamma nasamu kaina,
Dr sa'id yamun bayanin komai Yace hadda sanyi yana Miki yawa meyasa bazaki daina kwana da AC ba?


Murmushi ta 'dan saki tana kallonsa yanda koyaushe yake tamkar shine yayan sbd irin tasa kulawar.


Gyara zama tayi tana kallonsa da sauran rashin kuzari a muryarta tace"


Ina kiyayewa Marshal.


Jeho kanta Hannah tayi cikin zancen da cewa"


Sister in-law Allah yabaki lafiya duk mundamu dake bamason ganinki cikin irin yanayina ciwo musamman Marshal he cares for you so.......katsewa zancenta yayi yawu na neman zubo Mata daga Baki tayi saurin hadiyewa sbd idanuwanta dasuka sauka Kan kofar toilet da aka bude Naj ta fito daureda towel sky blue me haske cinyoyinta dasukafi komai tada hankalin Hannan sai daukan ido sukeyi tayi sama da idanuwanta kan qirjinta dasuka fito Dan fito ta saman koina jikinta daukan ido yakeyi gashinta daure a tsakiyar kanta ta dauresa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login