Showing 60001 words to 63000 words out of 92879 words
yayi Yana sauke ajiyar zuciya a fili tareda gyara zama cikin nutsuwa yace"
Ciwonta ba komai bane face laulayi na ciki datake dauke dashi Wanda dama Dole zata ringa irin wainnan qananun ciwon kafin cikin yafara qwari.
Rufe idanuwa yasake Yi ya bude ahankali yanajin wani irin yanayi na shigarsa ya sake kallon Dr sa'id zaiyi mgna text din Sarah yashigo wayarsa Kamar hakan"
_please kana buqatan zuwa wannan address din Naj tanason aikata abinda yake hadari ga rayuwarta._
Sake karanta saqon yayi zuciyarsa na kasa fahimtar zancenta duka ya dago ya kalli Dr sa'id cikin yanayi na ransa dake neman baci yace"
Tasan cewa tana daukeda ciki ne?
Eh munyi mganar da ita saidai gskia zancen cikin kamar Bai kwanta Mata.
Ta maka maganar cire cikin kenan????"" Yafada Yana kafe kallonsa kan Dr sa'id din daya fara kame kamen boye zancen da yayi.
No,yes I mean ta nuna bataso Amma ai na Mata mgn Kuma inaga tabar zancen.....
Miqewa yayi idanuwansa na sauyawa ya fice daga office din ya nufi motarsa Yana kokarin shiga idanuwansa a juye da wani irin mummunan yanayi saiga motar Isma'eel yashigo asibitin da gudu Yana Kiran nurses saiga dr sa'id yafito take sukai kansu sbd Hanifa da ake kokarin fitarwa motar jini ya balle Mata gabaki daya Bata hayyacinta.
Wayar Isma'eel dayaketa Kiran Marshal Bai dagaba itace tashigo wayarta daidai lokacinda zata saka hannu a takardar abortion din tana dauka cikin tsananin tashin hankali yafada Mata mugun labarin dayasata sakin takardar tana miqewa cikin tsananin tashin hankali ta fice da sauri Sarah tabita tana tambayar lafiya Amma Bata tsayaba ta karba keys din motar da kanta taja cikin tsananin gudu sukabar asibitin zuwa asibitin su Dr sa'id.
Suna parking taga motar marshal agurin Bata tsayaba sukai ciki da sauri tana Jin qafafuwanta na neman sagewa da tunanin halinda kowa zai Shiga idan Hanifa ta rasa cikinta.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
*_DM 40_*
Isarta bakin gurin yayi daidai da isowar anty Amina itama hankalinta tashe,
Idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin damuwa da tsoron halinda Hanifa zata shiga ta juyo ahankali tana kallon Isma'eel da duk yagama ficewa hayyacinsa sbd damuwa saidai tawakkalinsa yasa yaketa kokarin natsar da kansa ya kalli Naj din kafin ya juya ya kalli Marshal dake magana da Dr sa'id cikin wani irin yanayi na tsananin zafi biyu daya hadu akansa fuskarsa amatuqar hade Babu rahama ko daya akai.
Shigewa Dr sa'id yayi da sauri yana cewa su Dan kwantar da hankalinsu Inshallah zasuyi iya kokarinsu.
Kasa zama tayi sbd tsananin tsalle da bugawar da zuciyarta keyi ta rintse ido cikin yanayi na sagewa Dan Bata fatan wani Abu ya samu Hanifa ko babyn,
Tana roqon Allah yasa Hanifa cikin Nan rabonta ne Dan tafi shaidar yanda take tsananin son haihuwa da samun baby Amma wannan ne karo na uku Wanda dagashi idan har ta rasa batajin za'a Kuma yimata wani dashen.
Matsowa Sarah tayi qafafunta a sanyaye ta kalli Naj cikin kulawa da Dan qaramin sauti tace"
Naj ki zauna Kuma ki Dan kwantar da hankalinki kema kinsan ba'a son kishiga damuwa sbd yanayinki please.
Satar kallon Marshal Sarah tayi taji gabanta yasake bugawa cikinta na Dan kadawa ta dauke Kai sbd ganin wani irin mummunan hadewar fuska da wani boyayyan fushi dayake cikin idanuwansa Yana zaune ya harde qafa Babu Wanda yacewa kala sai jiran tsammani dasukeyi.
Qin zama Naj tayi tana Dan kaida kawo ahankali idanuwanta na neman kuka Amma yaqi zuwa sbd tashin hankalinta biyu ya kasu tanajin tashin hankalin halinda Hanifa ke ciki ga nata tashin hankalin sbd sosai take sake jin tsoro da shakkar cire cikinta dayake neman mamayarta Wanda ke sake cusar Mata da kai gabaki daya ta rasa wane tunani zatai,ta rintse ido tana dafa bango sbd sarawar da kanta ke dauka Yana neman sakar Mata da jiri.
Anty Amina dake kallonta cikin kulawa tace"
Naj ki zauna Mana tunda kema zazzabin da kikai Ba gama sakinki duka yayiba karki qara Mana wata damuwa Anan idan Kika shiga cikin wani hali.
Sai alokacin ta kalli Anty Amina tanason fashewa da kuka yaqi zuwa ta Dan sake dafa bango Sarah na kamata ahankali ta qarasa kujerar kusada Marshal ta zauna tana sunkuyar da Kai har lokacin hankalinta duka baya jikinta.
Gabaki daya Babu wata alamar data nuna Marshal dake gurin yasan da wanzuwar dukkaninsu a gurin bayan anty Amina data Dan basa bakin komai zai daidaita inshallah Akan Hanifa itama bayan Kai daya gyada Mata ahankali bai samu cewa komaiba sbd a yanayinda yake ciki idan ya fitarda fushinsa da tsananin bacin ran dayake ciki kowa bazai iya tsayawa agurinba.
Ismail ma miqewa yayi yafara safa da marwa yana Dan bubbuga hannayensa dake nade a kirjinsa,
Yanason Kiran Yan gidansu ya sanar musu Amma bayason tayar musu da hankali tukuna sai ansamu Kan matsalar.
Hannuwan Naj rawa suke ta damqesu tana Dan rintse idonta daketa cikowa da hawaye Amma kuka da hawayen sun kasa saukowa tsoro ne fal aranta,
Hannu ta daga ahankali takai Kan cikinta ta dafe tana sake Shiga wani sabon yanayi,anty Amina dake lure da ita ta matso ta dafata Anatse tana kallon fuskarta da duk take bayyanarda damuwarta a natse tace"
Naj,kina Lafiya dai?
Kasa mgn tayi ta sauke Kai ahankali tana sake dafe cikin ta gyadawa anty Aminan Kai.
Dr sa'id ne ya bude kofa yafito ahankali tareda wani Dr Adebayo
Dukkaninsu suka kallesa suna kallon idonsa da bakinsa jiran Jin abinda zai fada Dr Adebayo kuwa wucewa yayi zuwa office dinsa.
Kallon Marshal Dr Sa'id yayi Yana sauke numfashi tareda ajiyar zuciya ahankali kafin ya maida kallonsa kan Isma'eel a natse yace"
Hanifa ta rasa cikin sbd ta haifi babyn da Bai Isa haihuwaba kwata kwata hakan ne yasa babyn baizo da raiba sbd baima Gama zama cikakkiyar halittaba,
Jinin ya tsaya duk da ta zubarda jini sosai Amma bama buqatan qara Mata wani jinin sbd munduba pcv dinta is normal,
ayi hakuri Haka Allah ya nufa,wannan jarabawa ce idan anyi tawakkali za'a cinyeta Kuma za'a ga ribar hakan, Allah yabata lafiya,an bi kofar baya anfita da ita zuwa dakin hutawa zaku iya samunta acan.
Sake kallon Isma'eel yayi Yana cewa"
Zaka jira mu hado maka babyn sai aje a rufe ko.
Kallon Marshal da idanuwansa suka qarasa sauyawa gabaki yayi cikin kulawa yace"
Sorry Marshal,Allah yabada hakuri yabada rayayye,
Ita Hanifan kwata kwata Babu wata matsala atareda ita yanzu saidai damuwa Dan Haka tana buqatan ku dukan.
Juyawa yayi ciki yakoma Dan hado gawar 'dan babyn yakawo.
Kowa agurin kasa kuka yayi sai Naj dakejin kukan nason taso Mata Amma yaqi fitowa ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Isma'eel da qarfin imaninsa yasa ya daurewa zancen sosai Yana jiran fitowar Dr sa'id
Kasa kallon gefen Marshal tayi tanajin nauyin zuciyarta na qaruwa ta miqe Kai tsaye ta bar gurin ta nufi hanyar dakin datasan can za'a Kai Hanifan a Amenity Sarah na bayanta anty Amina kuwa matsowa tayi cikin kulawa da tsananin tausayawa tana sake bawa Marshal hakurin wannan rashin shida Isma'eel dake gyada Kai cikin wani yanayi Yana cewa"
Bakomai anty Amina nagode.
Marshal kuwa Kai kawai ya gyada Mata har lokacin Yana zaune a inda yake idanuwan Nan tamkar zasuyi Aman wuta sbd baqin ciki,bacin Rai dakuma damuwar Hanifa.
Tsayawa tayi itama har akawo babyn.
Da tsananin sanyin qafa Naj ta tura dakin tashiga fuskarta na narkewa da ganin hanifar wadda tana ganin Naj din ta sauke Kai wani irin gigitaccen kuka na zuwar Mata da sauri Naj din ta qaraso ta zauna tana rungumeta itama Bata hawayen na gangarowa alokacin.
Kuka Hanifa keyi Sosai Wanda yake fitowa daga tsakiyar ranta tareda dibbin 'daci da ciwon rashi na cikinta,
Sosai takejin wani irin radadi da zafi dama ciwo Wanda takeson kokesa idan zai fito shiyasa take kukan sosai zafin zuciyar Amma yakasa raguwa saima tsananta da quncin keyi.
Kukan Hanifan har cikin zuciyarta Naj ke jinsa sbd kukane da Bata taba irinsaba,kukane me cin Rai na Shiga zuciya,tanason Bata hakuri Amma takasa bude Baki sbd tanajin ciwon da Hanifan keji,tasake rungumeta nata hawayen na sake gudu.
Kukan datakeyi tuni yafara daga hankalin Naj din ta dago tana kallonta ta bude Baki murya a yamutse taka cewa"
Hanifa Dan Allah kiyi hkr ki daina kuka Haka Inshallah Zaki samu wani babyn,
Dan Allah ki daina kuka Haka Kinga Baki Gama warwarewa kada wata damuwar ta shigeki.......
Wani kukan me qaramin sauti yakuma zuwar Mata tana girgiza Kai cikin dasashiyar murya tace"
Naj Ina tsananin son babyna Amma Allah baiyi Zan zama uwaba.
Hanifa karki cire Rai daga rahamar ubangiji Dan Allah..."Naj tafada hawaye na gangarowa idanuwanta dasukai jajir.
Naj bakowane yakeda rabo da Sa'ar zamowa uwa ba kila Ina cikinsu duk da na dandana zamowa uwa me renon ciki ko ahakan na godewa Allah
Amma zafi nakeji da qunci cikin zuciyata sosai......kakane yaci qarfinta ta sunkuyar da Kai tanayi.
Gabaki daya jikin Naj mutuwa yayi da Tsananin tausayin Hanifan Dan kuwa ko Hanifan Bata fadaba kowa yasan zatai qunci sbd tsananin soyayyarta da son haihuwa Amma Allah ya qaddara hakan,
Sake mutuwa jikinta yayi da wannan yanayin na Hanifa ta dafa cikinta tanajin shin idan ta cire cikinta zata iya Shiga irin wannan halin na Hanifa na kuka da baqin cikin rasa nata babyn¿
Dafata Sarah tayi ahankali,Bata dagoba ta rufe idanuwanta hawayenta na gangarowa akaro na farko taji kamar qaunar cikinta ta motsa aranta tasake kallon yanayin quncin dake Kan fuskar Hanifa ta rufe ido tanajin qaunar cikinta amatsayinta na uwa,
Uwa mahaifiya zata zama,idan ta cire cikin tazo kukanta yafi na Hanifa.
Dafe kanta tayi tana rasa tunanin Yi sai tazama kamar Hanifan ta zuru zuru da ita sbd rashin sukunin zuci Dana fili ga na Hanifa.
Bude Baki takuma Yi a kasalance tana son rarrashin Hanifan Amma takasa sai shafa Mata bayanta take tana gyada Mata Kai alamar tausayawa har lokacin hannunta daya na Kan cikinta datakejin Kamar zai zube sbd tsoro da firgicin datake ciki,
Tunanin hakan Kuma shiyafi komai sakata rudu a daidai yanzu a wannan lokacin.
Shigowan marshal ne yasata dagowa ahankali ta kalli kofar sbd Jin qamshinsa daya fara Shiga hancinta ta sauke idanuwanta akansa zuciyarta na harbawa da wani irin bugu tana qure kallonta akansa akaro na farko tunanin wannan shine mahaifin cikin jikinta,
Shine uban 'da ko yarta,
Wasu irin zafafan hawayene suka gangaro Mata,ita tata qaddarar kenan kuma ta abun kunya cikin qanin qawarta ajikinta,
Tayaya zata iya kallon kowa da wannan cikin bayan kullum cikin tashin hankalin ta qi Aminta da auren ake,
Duniya ta shaida rashin yardarta da Aminta da auren ta Yaya zata iya kallonsu da cikinsa ajikinta bayan ko tarewa bataiba, ta ina?ta Yaya suka samu kebewar data samu cikin?
Da wane ido zata kalla hajjo da ma Dadah datasan bazatai shiru ba,harma ummanta da Hanifa duk batasan ta Yaya zata iya kallonsu da wannan cikinba gashi Kuma yanzu bazata iya cutatar da kantaba ta cire cikin sbd jinsa data farayi ayau akuma Nan asibitin sbd gani ga wane datai.
Yanayin fuskarsa da Babu wani sauki acikinta kamar dai ayanda yake kame koyaushe saidai yau muguwar kamewar tafi ta kullum Wanda takewa kallon yanayinda Hanifa take ciki ta dauke idanuwanta ahankali daga kansa din ta sauke Kai tana miqewa daga gefen hanifar ya qaraso Yana kallon Hanifa da ganinsa keson dawo da kukanta Wanda yafi komai cin ransa ganin hawayenta Dana wadda yanzu yafi komai takaicin kansa daya Bata lokacinsa.
Riqeda hannun Hanifa yake Yana kallonta da idanuwansa cikin kulawa yace"
Soon Zaki Kuma samun wani Inshallah just have faith ki dauka wannan jarabawa Allah zai duba zuciyanki ya Baki wani ok????stop this tears now.
Handkerchief dinsa yaciro daga aljihun wandonsa ahankali ya fara share Mata hawaye Yana Dan kokarin sake kwantar Mata da hankali fuska kame.
Anty Amina ce ta qaraso itama tana sake Bata nata rarrashin suna cikin hakan saigasu umma da hajjo sun iso motarsu daban ta dad Alfa da mum Malika dabam sai 'yan gidansu Isma'eel dasuka iso mum dinsa da qannanesu biyu sai qaninsa namiji daya na dakin ya cike da Yan uwa kowa Yana fidda kalar jimaminsa sbd Babu wanda abun Bai taba zuciyarsa Dan dukkaninsu sun qwallafa Rai a cikin bama kamar hajjo da Dad Alfa sbd rashin 'yaya a familyn Alfa din sunason 'yaya su hayayyafa a cikin zuriar ko Dan a morewa dukiyar da aketa tarawa.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
*_DM 41_*
Yanda kowa ya damu yake Kuma bayyanarda damuwarsa yasa Hanifa daina kukan saidai fuskarta Kam Bata dubuwa ta kumbura sosai tayi jajir daqyar mumyn Isma'eel tasata Dole lallabata Tasha tea dasu magani aka hada ruwan zafi sosai anty Amina ta taimaka Mata tayi wanka ta gasa Mata jikinta suka fito tasaka doguwar riga Mara nauyi lokacin maraice yayi sosai kusan kowa ya tafi sai anty Aminah da Naj din sai Sarah Yar hannun damar Naj Isma'eel ma lokacin yasake dawowa daga gida dayaje ya sake kintsowa cikin wasu kayan sbd waincan sun baci.
Kallon Naj da idanuwanta sukai laushi Sarah tayi ta kalli Anty Amina tace"
Anty Amina kice tazo na maidata gida Mana ko abinci taci itama ba isashiyar lafiya ne da itaba gashi idanuwanta sun nuna ta galabaita Amma taqi zuwa
Hanifan ma gatanan alhmdlh taji sauki ki daure muje gidan kici abinci kiyi wanka ki Dan nutsu saiki dawo asibitin.
Kallonta Hanifa tayi da idanuwanta dasukai mugun nauyin kumburi ta bude Baki ahankali cikin kulawa a natse tace"
Naj kije gida Mana ki huta gaba daya kinyi na kyan gani sbd damuwa da gajiya,naji sauki banajin komai yanxu kije banson ganinki ahaka zanji ba dadi.
Dagowa Naj din tayi tana kallon Hanifa jikinta na sake sanyi ta dauke idanuwanta daga kanta tun yanzu tanajin kunyar hada Idanuwa da kowama kafin aji aikin dake jikinta cikin sanyin murya tace"
No banajin yunwa ko naje gidan bazan samu nutsuwaba zan zauna din anan...
Naj karki kamanta fa tunda safe Kika fita ba daga gida kikayo Nan ba Dole kina buqatan samun hutawa....
Sarah please nace Zan zaunsa Anan...
Anty Amina ce ta katseta da cewa"
Akace kije ki dawo mana.
Marshal ne ya shigo dakin tareda Isma'eel da Dr sa'id lokacin har anyi sallar magriba kowannensu Yana zuba nasa kalar qamshin turaren Amma gabaki daya nasa ya take nasu qamshin ya cika dakin Yana sanyeda jallabiya fara qal da alama wankan maraice yayi ya nufa masallaci dagacan yayo asibitin idanuwansa na Kan Hanifa datake zaune Kan gado duk jikinta a mace tayi sanyi.
Wasu maganunan Dr sa'id yakuma rubutawa cikin folder dinta tareda Masa wasu tambayoyin yana rubutawa cikin folder din yayi signing ya rufe Yana ajiyewa ya kalleta cikin kulawa da Bata qwarin gwiwa yace"
Ki sake Inshallah rabo na zuwa agaba,ki qara hakurine Hanifa okay???
Gyada Masa Kai tayi ahankali tana cewa"
Thank you Dr sa'id.
Dan murmushi yayi Mata kafin ya maida kallonsa kan Naj datai mugun laushi sbd har wani irin jiri me qarfi take gani daga zaunen cikin kulawa da mamaki yace"
Naj yakamata fa kije gida kisamu hutawa da abinci,you don't you look good kinsan Kuma yanayinki kema masu ciki ba'a son suna saka damuwa irin haka,"""kallon Marshal yayi Yana cewa"
Inaga yakamata ka kaita gida yanayinta ya nuna ta galabaitu sosai.
Tsit dakin sukai kowa wuta na dauke Masa musamman Hanifa da anty Amina dasu kadaine Basu San da cikinba sai Isma'eel Amma shi me cikin yasani yau din sai Sarah datafi kowa sanin komai.
Batareda anty Amina tasaniba tace"
Waye me cikin??
Kallonta Dr sa'id yayi sai alokacin ya lura da yanayin kowa yake fahimtar ba kowane kenan yasan da maganar cikin ba ya Dan juyo Yana kallon Naj datai zuru takasa dagowa jikinta amatuqar sake yayi Dan gyaran murya Yana kallon Anty Amina yace"
Tana buqatan zuwa gida koma yayane."ya juya ya nufi kofa zai fice Marshal ya dago sai alokacin ya kalleta lokacinda take bude Baki jiki ba nauyi tace"
Lafiyata kalau banajin komai Zan zaun.....
Akaro na farko da kowa yaji tsawar Marshal Da ba Naj din kawaiba Hanifa ma da anty Amina Saida suka Sha jinin jikinsu suna kallonsa cikin tsananin mamakin ganin bacin ransa shima akaro na farko da wani irin kallo dake sake saka Mata shakkar halinda take ciki Yana dauke Kai daga kallonta yace"
Kitashi ki koma gida yanzu,
Anty Amina ku maidata gida karta sake dawowa asibitin ta zauna gida.
Yana fadar hakan ya miqe ya nufi kofa ta dago tanabin bayansa da kallo zuciyarta na tsalle ahankali ta bude Baki zatai mgana Anty Amina ta tareta da cewa"
Tashi muje kinji abinda yace.
Hanifa kuwa kasa shiru tayi ta kalli Naj din data miqe Tasha gabansa zatai magana jiri ya dibeta tayi baya zata Fadi anty Amina da Sarah suka zaburo zasu tareta Amma yariga ya tareta ta hanyar riqota yana Mata wani kallon Yana sake boye fushinsa akanta yace"
Ke kanki baya daukan magana daya me sauki?
Ki aje wannan shirmen kije gida idan kuma kina shirin komawane gurin cire cikin daganan toh let me be very clear with you,
Idan wani Abu yasamu cikin Nan zakisan wayeni,nayi tunanin banzan tunaninki baikai kiyi tunanin cire ciko ajikinki ba Amma har Zaki iya zuwa wani asibitin daban tunda Nan Dr sa'id yaqi yarda da manufarki sbd kece Kika fi kowa shekara a duniyan Dan Haka kisa aranki wani Abu yasamu cikin Nan zakiga abinda bakyaso now get out of my sight.
Cikin rudu da mamaki Anty Amina take kallon Naj data Gama jiqa fuskarta da hawayen baqin cikin tayaya yasan da cikin har yasan tayi niyar zubar a hasale anty Amina tace"
Naj cikine dake kike son zubarwa?????
Cikin tsananin hawaye ta dago tana kallon fuskarsa dake a hade Babu sauki tako Ina ta bude Baki tace"
Ban aikata......wani wanan Mari ne ya sauka fuskarta Wanda yasata faduwa zaune da sauri hanifa ta sauko gado ta qaraso ta riqe ummu da basusan da isowarta ba Saida tayi Marin.
Dr sa'id ma da Isma'eel matsowa sukai suna bawa umman hakuri duk da kowa yashiga mamakin jin abinda Naj din taso aikatawa.
Wasu sabbin hawayene suka tsinkewa Naj takasa dagowa tana sake qaramin kuka ahankali
Ya rintse idanuwansa tareda Dan sake kame fuska ya kamo hannuta daya ya damqa cikin na anty Amina Yana cewa"
Ki kaita gida kawai.
Baiso zancen yafita Haka ba yaso yabarshi a tsakaninsu Amma