Showing 15001 words to 18000 words out of 86122 words

Chapter 6 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt

26 Nov 2024

4807

kwanciyaba qarar wayanta ya tasheta


Jawo wayar tayi idanunta alumshe dan baqaramun dad'in baccin tafara jiba


Duba sunan mai kiran tayi, cikin sauri ta zauna tare da kara wayar akunnenta




Assalamu alaikum mama na, shine abinda tafad'a


Waalaikumussalam, yar mama, mama tafad'a ad'ayan bangaren


Ina kwana mama, mama tace lfy lau, ya gidan naki Komai lfy ko?


Lfy lau mama ya Abba na?


Mama tace lfynsa qalau, yama fita abinsa, mama tasake cewa inafata kina lfy kuma ba matsala ko


Wannan tambayar da mama tamata ita ta sake tuno mata da nasihan da Abba yamata akan ta riqe sirrin mijinta kada ta bari wani yaji tsakaninta da mijinta


Hakan yasa tace lfy qalau mama me kika gani


Mama tace bakomai kawai natambaye kine


Ayyah mama lfy qalau nake baccima nake, wayar ce ta tasheni


Toh shikenan sai anjima, daman nakira naji yaykika kwana, toh mama nagode kigaida Abba idan yadawo




Toh zaiji nan sukayi sallama mama ta kashe wayan


Sauqe wayar tayi, ta ajiye ta agefenta




Shiru tai tayi tagumi tana tunanin, ko dai Abba yasan halin ya Alamin ne yasa yaita mata wasu kalan nasiha


Girgiza kanta tayi tace aa kam tabbas da Abba yasan haka halin ya Alamin yake da bazai fara had'ani da shiba




Tashi tsaye tayi kamar ta fita waje taga yanayin gidan Amma sai tsoro yasa ta fasa, dan batasan yadda zata kasanceba idan sukayi 4eyes da papa


Amma tino da maganar aunty niima da tayi shiya sa tace kumafa gaskiyarta ne wlh barin iya yini da kwana ad'akiba


Toma wade namun girki, matuqar zan yini akulle, wani kwarin guiwa ne yazo mata ta miqe ta nufi toilet




Alwala tayi ganin qarfe 1 saura, sai da tayi sallah sannan tasake gyara fiskanta, nan tayi fes da ita dan yanzun idanunta sun washe sunyi haske kamar yadda suke


Wasu flat shoes yellow ta saka tayi har fita har tazo qofar falo data fito, sai kuma tafasa lokacin da zuciyarta ya tuno mata yanayin dataga papa jiya gaba daya baya cikin hankalinsa


Tace umm gara nakoma kada nafita ya shaqeni, sai wata zuciyar tace haba dai ai zuwa yanzu ya wartsake kuma ma inya tabbatar ina tsoronsa zansha wahala gara kawai na gwada masa nafishi hauka




Cikin qarfin hali ta bud'e qofar, wani sirrin corridor tagani yayi gabar da yamma, inda take tsaye shine ta b'angaren gabar sai can daga gefen yamma wata qoface akulle kuma tana da tabbacin nan ne side na ya Alamin


Ahankali ta tako har bakin steps, nan tafara sauqa cikin sand'a kamar munafuka, tana sauqa taganta awani qaton falo wadda yasha kayan duniya abin birgewa


Qarema falon kallo take, tabbas gidan ya had'u kuma ya birgeta dan bata tab'a zaton shiga irin wannan gidanba


Wani cuttain ne ya d'auki hankalinta, takawa tayi har wajen, hannu tasaka ta yaye labulen wani sanyi da qamshine suka daki fiskanta da illahirin jikinta, lumshe idanunta tayi dan nan take taji yanayin yamata aranta


Wasu steps ta taka ta sauqa qasa har cikin falon, amma kasancewa ba hasken wuta awajen sai duhu wajen


Juyawa tayi zata fita, kawai ta sule suuu, dasauri ta dafa wall din cikin falon sai hannunta yasauqa akan switch din wutan falon


Nan take wani haske ya gauraye wajen, nanfa taga ashe da bata ga komaiba dan wannan wajen yafi ko ina haduwa




Daga kanta tayi nan idanunta suka sauqa akan wani tangamemen photon papa


Yana sanye cikin wasu baqaqen suit, rigar cikin sky blue sun matuqar yimasa kyau, fiskannan dauke da murmushi


Nan Fauziyyah taji ya matuqar birgeta dan baqarya photon yayi


Kuma wannan shine karo na farko dataga murmushi afiskansa


Nan taji wannan Alamin d'in photon ya birgeta amma wancan Alamin d'in koson ganinsa batasonyi


Murmushi tayi lokacin data sake kallon photon, kome ta tuna kuma oho sai ta juya ta kashe hasken wutan falon ta fito


Lelleqa ko ina tayi,sannan ta qarasa dinning area, wajen ya birgeta shima sosai dan aqawata wajen bana wasa ba, qofar dake cikin wajen shiya tabbatar mata nanne kitchen dan bataga kitchen ba awajen




Harta riqe handle din qofar data shiga sai taji qarar mota anshigo


Falo ta dawo ta tsaya dan ganin waye mai shigowa, dan atunaninta baqi sukayi dan bataji fitan ya Alamin ba


Gamm taji anbud'e falon anshigo, cikin sauri ta d'ago kanta tana qare masa kallo, wani tsoro ne ya dirar mata lokaci guda dan yadda taga fiskansannan babu annuri


Daurewa tayi, ta juya tayi zamanta akan 1 daga cikin kujerun falon


Fiska a murtuqe ya qaraso ya tsaya akanta, wani kallon rainin hankali da zallar tsana ya ke mata


Yitayi kamar batasan da tsayuwarsaba


Afusace yace keh yar qauye nazo kashe maki warning ne akan kada kifara abinda zai dameki


Ke waye daga zuwanki tinma bakiji matsayinki da sharud'an da zan kafa maki agiddannan ba har kina da bakin kai qarata


Sai anan ta d'ago ta kallesa, ganin irin kallon walaqancin dayake mata yasa itama ta watsa masa wata uwar harara


Tace nakai qarar ina?




Au tambayata ma kike, ke har kin isa kitsayarmun da tambaya


Cikin tsiwa tace haba yanzu na gane kacemun tabarmar kunya kazo nad'ewa


Ganin irin kallon rashin kunyar datake masa, da tsiwa yaqara harzuqashi


Hannunsa ya d'aga, bata tsammaniba taji sauqar mari afiskarta


Dasauri ta dafe wajen da hannunta, ta miqe tsaye tace Allah ya isa banyafe maka ba, kuma qarya nayi ba tabarmar kunyan kazo nad'ewa inba haka a ina nakai qarar ka, saika fad'a ai




Cikin masifa yace dan ubanki ke har kin isa kitsareni, wlh am warning u this is the first n last da wani zaizo gidannan kiyi maganata dashi, idan kuma kinki jikinki zai fad'a maki




Tace Sannu ubana, inba ka kasheniba wlh baka cika sunanka ba, nadauka da dare kake shaye2n, ashe harda ranama yi kake


Aiko daya wani fincikota sai data fad'o jikinsa, lokaci guda yaji wani irin shork ajikinsa wane wuta ce takamashi ai baisan sanda ya hankad'ata ta bugu da kujeraba




Wani irin ihuu ta kwala lokacin da kanta ya bugu amma ko ajikinsa saima qoqarin cire belt d'insa dayake yana cewa bari kiga aikin yan shaye2


Tinda bakida kunya sai naga qarshen rashin kunya....




✍🏻Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] β€ͺ+234 703 448 8635‬: 🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾






🌾🌾🌾




Budurwar Qauye πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


July, 2017




1⃣7⃣
Fauziyyah data riqe kanta dan azaban datakeji aiko sai takuma jin yayyafin bulala ta ko ina


Dukanta yake tsakaninsa da Allah, bako tausayi, haka yake zabga mata belt d'inanan


Ga zafin da kanta kamata ga kuma belt dayake zuba mata amma hakan baisa bakinta ya mutu ba


Allah ya isa ta jamasa yafi cikin kwando, tana kuka tana cewa wlh sai Allah yamun sakayya tinda ban maka komaiba, mugu azzalumi kawai


Sai daya tabbatar ta daku kafin ya kyaleta


Sai huci yake kamar wani kumurci, hannunsa ya nuna ta dashi yace kibud'e kunnenki da kyau kijini




Nafarko kisani bani bake, bana sonki haka bana qaunar ganinki bare zama tare dake


Sabida haka kitabbatar kin kiyaye abinda zan fad'a maki, kinganninan bana qazanta haka bani qaunarsa


Kitabbatar dik randa naga datti agiddannan wlh sai jikinki ya gaya maki, sannan dik abinda kike idan kinji qarar motana kafin nashigo kisan Inda dare yamaki sai nafita, kada ki kuskura nadawo ina zaune afalo kifito, ko ahanya bana qaunar kallon fiskan kinnan mai dauke da shegun idanuwa kamar na mayu




Idan kika kuskura kika aikata 1 acikin wad'annan zakisha mamaki dan wannan flashing na maki


Banziya jaka, yar qauye kawai, yana kaiwa nan ya wuce ta ya haura sama abinshi




Wani kukan takaici da baqin ciki ta fashe dashi, ga kanta sai zafi yake mata, illahirin jikinta rad'ad'i yake mata dan ba dukan wasa yamataba




Wani tsanarsa ce ya sake shiga zuciyarta, afili tace sai dai ka kasheni wlh ko 1 bazan aikataba kuma wlh ka daki bashi daganan zuwa shekara 100 sai na maka abinda zan qunta tamaka fiye da abinda kamun




Da kyar ta miqe tahaura b'angarenta, toilet ta shiga ta had'a ruwa mai zafi sannan tayi wanka


Dik jikinta yayi pink shatin duka abinka da farin mutum


Wata sabuwar yunwa taji ta taso mata, kitchen ta wuce ta dakko sauran abincinta nasafe tafara ci


Door bell taji ya karad'e ko ina, hijab dinta ta jawo tasaka sannan ta fito


Jikin main Door din tazo ta tsaya tana kallon wane ne yazo


Ganin wata matashiyar mace ce dauke da basket na abinci a hannunta yasa ta bude mata



Sannu da zuwa, tace mata Bayan tashigo
Yawwa, ina yini tacema Fauziyyah, lfy lau ya gida, ta amsa mata


Lfy lau, hajiya ce tace nakawo maki abinci


Karban basket din tayi tace nagode sosai, ki qaraso mana


Asabe mai aikin momcy tace aa driver yana jirana zan koma


Toh kigaida momcy nagode


Side nata ta koma, Tattara wancan abincin tayi ta zuba wadda aka kawo mata taci abinta


D'aki ta koma ta kwanta dan kanta ciwo yake mata har yafara daminta




*******
Papa kuwa yana haurawa d'akinsa ya wuce, kayan jikinsa ya rage sannan ya shige toilet, ruwa ya sakanma kansa ko zaiji sanyi azuciyarsa amma ina, maganganunta su suke masa yawo akansa, shaye2 harda ranama yi kake shine abinda ya ke daminsa


Inba rainiba ba wanda ya tab'a furta masa wannan kalmar iya tsawon rayuwarsa, sai qaramar yarinya lalle zan d'au mataki akanta


Next time da kud'i aka bata bazata kuma cakamun abinda taga damaba


Fitowa yayi d'aure da towel aqugunsa, sai anan ya tuna ashe ko breakfast baiyiba




Tsaki ya kuma ja, sabida wata yar qauye Komai nasa ya jagule Wayarsa yajawo ganin time ya qure ya sake jan wani tsakin




Ajiye wayar yayi, ya dauko white jallabiyarsa yasaka, tada sallah yayi, yana cikin sallah aka fara kiran Wayarsa


Sai bayan ya idar, yana dubawa yaga TJ ne ya kirashi




Kiransa ya fara bada jimawa ba ya picking, hello ango kasha mai abinda ya fada kenan ya daga wayar




Tsuke fiska yayi kamar yana ganinsa, yace wlh TJ inajin kunyanka fa


TJ yace kadaina jin kunyar tawa dan namaka kirari sai kawani fara dojewa bayan nasan iyanzu Komai normal


Papa yace to tinda ba maganar arziqi yasa kanemeniba sai anjima


Haba dakata mana mutumin yafad'a cikin sauri, me yayi zafi haba wasanefa


Toh inajinka meke happening, TJ yace laufa daman inason leqowa gidane kasan tin rabibin biki rabona da amarya


Aiki nad'auma wani abu mai muhimmancine to waya riqeka yanzuma




TJ yace idan kana gida zuwa 4 haka zan shigo, papa yace inanan bana nan mene damuwarka tinda ba wajena zakazo ba


Eh amma dai ai inason nasameka, dan akwai error fa, error name? Yatambayesa


Wlh surry ta dameni da waya wai atafir saina kawota gidanki tinda baka daukan call nata


Papa yace aida ka kawota, naci uwarta tukun gobe ko ahanya taganni bata nuna tasanniba, niba irin yan iskanta bane ba


TJ yace aa kam taya zan kawota gidan matar aure, idan kun had'u dai ka d'aye mata amma ba agidankaba




Toh naji sai zuwa jimawa zamu had'u ko kanada wani eh umm


Sheqewa sukayi da dariya gaba d'ayansu


TJ yace aa wlh kawai dai yau ina gida dan full house muke


Ok nikam yanzuma fita zanyi, ina da wajen zuwa




Toh ba yawaa, gobe insha Allah zan shigo




Ok, sai munhad'u nan sukayi sallama


Fitowa yayi tsaf cikin shirinsa na blue jins n red shirt, yayi kyau abinsa


Canza mota yayi, yadau farar Rio ya fice, kai tsaye banila resturant ya shiga nan yaci abincinsa sannan ya wuce ya had'o wine nasa cotton cotton


Bashi yadawo gida ba sai gabda magriba




Yana shigowa side nasa ya shiga dasu, wasu yasa a fridge wasu ya ajiyesu haka, sai bayan ishai sannan yaci kazar daya saka aka sayo masa nan ya zauna yana kallon news yana shan wine nasa


Sai wajen 12 sannan ya kwanta






Washegari tun safe Fauziyyah bata fito ba sai 11 nanma kawo mata abinci akayi, nan tace Wa Asabe tafadawa momcy kada a turo mata na rana wannan ma ya isheta




Ba ita ta fitoba sai wajen pass 4, nanma kitchen take da niyyar shiga taga ko akwai kayan tea dan tanason shan tea yau




Saqqowa tayi qasa, tana zuwa tsakiyar falo tajiyo kamar muryan papa, matsawa tayi kusada falonsa sai taji kuma kamar shida wasu ne, ahankali ta matso ta leqa sai taganshi shida TJ dama wani wanda batasanshiba amma sunje wajen kamun aurenta da TJ




Shiru tayi tana tunanin ta wuce kota koma, nan take tayi wani murmushi tace yau saina nuna maka tsiyar dan qauye




Sad'af2 ta juya, d'aki takoma ta sake kwalliya, wata doguwar riga fitedgown tasaka ta shadda, dark ash, anmata aikin surfani daga sama har qasa


Rigan tad'an kamata, idan kaganta tayi kyau sai dai kamar yar baby dan Fauziyyah ba jiki ko kadan ga girjinnan kamar yayan goruba, yarinta zalla kawai daka ganta zaka gani dan babu wani abu mai auki ajikinta


Daurin dan kwalinnan yamata kyau dan Fauziyyah kyakykyawace sosai, fitowa tayi zuciyarta sai bugawa take, tana zuwa bakin steps sai data dai dai ta natsuwarta sannan tafara saqqowa dasdas kake jin qarar takalmin ta


Falon papa ta wuce direct, tana yaye curtain d'in da sallama ta shiga dik suka juyo TJ da kb suka amsa sallaman


Inda papa ya tsaya ganin mai yakawo yarinyannan yana tare da baqi Bayan dik kashedin daya mata


Gunsa yaga ta nufo kadan2, idanu ya zuba mata dan ganin iyaka gudun ruwanta........






✍🏻Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] β€ͺ+234 703 448 8635‬: 🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾






Budurwar Qauye πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


July, 2017






*This page goes to my swt sis Aunty Hadiza, thanks 4 ur luv n support 😘😍*




1⃣8⃣
Cikin taku mai natsuwa harta iso wajen dayake zaune


Kan hannun kujeran dayake ta zauna, hannayenta dik biyu tasa tasaqalo wuyansa


Fiskanta ta kwanta jikin nasa, cikin wata murya dabai san tana dashiba mai tattare da shagwab'a tace


Dear, ashe sun qaraso nikam inacan sai yanzun nagama


Papa nan yayi mutuwar zaune, abu uku su suka hanashi magana




Nafarko wannan shegen shork dayaji jiya lokacin da ta tab'a jikinsa, dik da yana huld'a da mata amma bai tab'a jin irin wannan abinba dan ya tab'a mace, amma karo na biyu kenan da Jikinsu ya had'u amma sai yaji wannan abin




Na biyu kuma wani fitinannen qamshi dake fita daga dikkannin jikinta su suka kashe masa jiki




Na uku shine haushi da baqin ciki yarfashi da tayi agaban su TJ, shi TJ baima damesa kamar kb ba




Sanin bazai yi maganaba yasa ta juyo tana kallon su kb, da murmushi afiskanta tace sannunku da malam TJ, wlh kunzo ina ciki




TJ da mamakin ashe shi Ameen yake, zagayawa soyayya suke sha da amarya fal zuciyarsa amma sai ya share




Yace haba bakomai ai amarya bakya laifi ko da kinkashe d'an masu gida




Dariya tayi ta sake maqale papa, tana kallon idanunsa, cikin shagwab'a tace wai haka ne swt




Wani qululun baqin cikine ya sashi lumshe idanunsa yana tunanin mai zaima yarinyar nan ya huce abinda tamasa




Hakan da yayi sai ya bada kamar amsa mata yayi




TJ azuciyarsa yace shere Dr ashe kawai harka ya bud'e sabuwa yasamu yar shila yana morewa, sai wani pretending yake




Ina yini tace da kb, lfy lau amarya ya amarci?




Wani shuumin murmushi tayi wadda yasake qawata face nata tace sai dai katambayi swt




TJ yace tabbas Ameen keda wannan amasan, aikaga yayi shiru baiko magana


TJ yasake cewa wannan abokinmune yana nuna kb sunansa




Malam kb ko tayi saurin fad'i




Au kinsan sunansama ashe TJ ya fad'a




Dear yacemun zakuzo tareda kb ko namanta sunan, alhalin lokacin data lab'e taga suwayene a lokacin taji TJ ya kira sunansa yace kb




Nan TJ yasake tabbatar da lalle shi Alamin yake rainawa hankali




Miqewa tayi barin kawo maku ruwa, bata jira amsan suba ta wuce abinta


Kitchen ta shiga, tana shiga ta dafe qirji tace hmm lalle yau nayi jarumta irin wannan rashin kunyan bantab'a yin irintaba




Wani dariya kuma tayi dan tasan tabbas yau ta qonawa ya Alamin zuciya




Cikin sauri takama bud'e2 dan taga mene damene akwai dan wannan shine shiganta na farko




Aiko nan taga ba abinda babu, freezer ma shaqare yake da nama, kifi, kaji




Wata qofa tagani, tana bud'ewa taga store ne nanma ba abinda babu, dankali, doya, kwai ma ga wasu banda wadda tagani acikin fridge




Aifa nan tafara jido tana kaiwa falon ta tana ajiyewa, sai da ta d'ebi dik abinda take buqata sannan ta d'auki tire ta cikashi da drinks kala daban2, cups ta wanke sannan ta d'auko ta nufi falon papa




Yanda ta barshi haka tadawo tasamesa fiskarnan babu annuri




Ko d'agowa baiyiba baran ya kalleta, lokacin data fita kamar ya bita amma sai yafasa tinda ai zasu tafi su barsu agidan






Kuma idan har ya bita, tabbas wani tunani nadaban zasu sake tinda tagama zubarmasa da class agaban kb, shi bayajin ta TJ ma




Zubawa tayi ta ajiye masu tace bismilla kusha ruwa






Kb yace godia muke amarya thanks so much




Bakomai ta fad'a, wajen papa ta koma ta zauna, sai dataga sunsha ruwa sannan






Ta matso jikin papa tace swt nikam barin shiga ciki, na daura mana dinner




Maida kallonta wajen su TJ tayi sannan tace toh nikam barin shiga ciki




Saina fito




TJ yace mukam ma tfy zamuyi




Tace haba dai bazaku tsaya kuci abinciba




TJ yace inaa kinaga yadda ango ya had'e fiska alamun mumtakuresa, gara mu wuce tin bai koramuba




Suka kashe hannu shida kb, kb yace gaskiya kam




Mungode madam sai wani lokaci kawai




Tace to mungode Allah yasaka ya bada ladan ziyara




Dik suka amsa da amin


wani hot kiss ta danna masa a chicks dinsa tace Dear sai ka shigo


Cikin sauri ta wuce kada cafkota, aiko tana zuwa bakin steps da gudu ta haura ta nufi side d'inta




Tana shiga ta saka key, ta kulle dik wata maqata najikin qofar sannan ta zauna tana Maida numfashi




Papa kuwa jiyake kamar ya fashe da kuka dan baqin cikin abinda yarinyar nan tamasa




TJ ne yace ango mu zamu wuce sai munhad'u kawai




Da kyar ya iya furta ok man sai munhad'u, thanks kb sai n

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login