Showing 36001 words to 39000 words out of 86122 words

Chapter 13 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt

26 Nov 2024

4811

wanke aka goge mata


Taji sallamar momcy tana amsawa taga daddy ma ya shigo ,dasauri ta miqe sai taji zuciyarta na bugawa ganin daddy har dakinta


Murmushin dole daddy yayi yace aa daugther kiyi zamanki muma zama zamuyi


Komawa qasa tayi ta zauna tana sauraronsu


Shiru sukayi nadan lokaci kafin daddy yayi gyaran murya yace Fauziyyah


Dagowa kanta tayi tace naam daddy


Yace kinsan cewa yana daga cikin rukunnan imani yarda da kaddara alkhairi ko sharri ko


Qirjintane ya tsananta bugawa dakai ta iya amsawa dan sai taji magana ta gagareta


Yace Alhamdulillah ,toh abinda zanfadamaki kidaukeshi kaddarace kuma mai wucewa


Sannan yaci gaba da fadin kwanakin baya Alamin yazomun da wata magana wai yanason yaqara aure


Cikin sauri ta dago kanta tana maimata aure azuciyarta


Daddy yace toh nan nace banyardaba daganan baikuma tada zancenba sai yau dinnan yasake dawowa da maganar


Fauziyyah dai tunani take aranta itakuwa me tayima ya Alamin ya tsaneta har haka baicin yayi watsi da ita baikuma isheshiba har kuma wani maganar aure zai tsiro


Maganar daddy ce ta dawo da ita daga tunanin dake


Yana cewa nikuma nace inhar bazai gaquraba sai dai ya sakeki inyaso yayi auren amma dake dan yaune shine ya furtamun kalmar ya sakeki


Wani razana da tayi yasa momcy tayi saurin riqota


Momcy tace kiyi haquri Fauziyyah tabbas papa ya cutar dake amma Allah zai saka maki kiyi haquri kinji


Shiru tayi batace komaiba sai take ganin kamar amafarkine ko ido biyune


Cikin dauriya tace sagaske kenan ya Alamin ya sakeni momcy tace kansa ya yima kiyi haquri


Aifa nan taji wasu hawaye masu zafi suna mata zarya afuska


Nan su daddy suka ta rarrashinta har suka samu tayi shiru


Washegari ta tashi da matsanancin zazzabi wanda yasa daddy ya fasa zuwa dambam dan tare yake son sutafi da ita


Kwananta biyu da taimakon Allah da rarrashi har suka samu ta sami natsuwa ta kuma dangana tunda har abinci ta karba taci sosai bakaman kwanaki biyun da suka wuceba




Ranan kwana na uku da faruwar alamarin daddy yace fauziyyah ta shirya sutafi dambam




Hakan ko akayi suna isa direct gidansu fauziyyah suka wuce




Agida yasami Abba dan yamasa awaya akan yana tafe


Afalon Abba dik sunyi shiru shida daddy dan maganar tazoma Abba abazata


Cikin damuwa daddy yace wlh nibansanma wacce kalma zanyi amfani da itaba wajen baku haquri


Abba ya nisa yace kada damu nafahimce komai kuma wlh ni bandauki zafi da maganar nanba bakomai Allah yasa haka shiyafi alkhairi ka kwantar da hankalinka aminina maganar yara bazata raba tsakanina da kaiba


Daddy yace nagode nagode Allaha bar zumunci sai dai kuma ina neman alfarma awajenka


Abba yace tsakaninmu kawuci haka fadi komeneneshi inhar baifi qarfinaba


Daddy yace inason nakoma da fauziyyah amma baxata cigaba da zama awajenaba sai nan da wani lokaci kafinnan nacika alqawarin dana daukarma zuciyata


Nan da kwana hudu mabarukha zata zo kuma sati daya kacal zatayi ta koma dan mijinta zaiyi tafiya zuwa Australia


Toh inso sutafi tare da fauziyyah ta koma makaranta acan wajenta


Shiru Abba yayi kafin yace bakomai Allah ya shige mana gaba damacan ai baa gabana takeba


Cikin farinciki daddy yayi tayiwa Abba godia sannan suka shiga ciki ya gaisa da mama


Sannan yafito ya nufi fada akan bayan sallan laasar zai dawo sutafi




Fauziyyah kuwa tun zuwanta mama take kwakwarta akan anya kuwa lfyrta kalau amma haka taqi fada mama maike faruwa dan har yanzun sai tanaga kamar bahaka bane yayane itama dai batasan yadda zata kwatanta abinba


Abbama daya shigo shiru yayi baice komaiba har daddy ya dawo Abba ya kira fauziyyah ya mata nasiha sosai sannan yace kuma tare zasu koma da daddy


Harga Allah ranta baisoba amma haka ta haqura ta bishi


Bayan suntafi sannan Abba ya mayarma mama abinda ya faru


Nan mama tace batasan zancenba ita atafam saidai adawo mata da yarta tunda abin walaqancine


Ita dama tajima jikinta yana bata ba lafy fauziyyah takeba


Da kyar da nasiha Abba yashawo kanta ta haqura dan yasan zuciyar iyaye mata da rauni take shiyasa bai fada mata ba sai bayan sun tafi ya kuma godema Allah daya bashi ya mai jin maganarsa




Bayan dawowarsu fauziyyah da kwana hudu aunty mabarukha ta zo bauchi ita da yaranta uku dik maza




Ranta ya matuqar baci da taji labarin abinda ya faru


Daddy yace sabida haka nakeso kitafi da fauziyyah wajenki kisama mata makaranta ta koma daga naira 1 zuwa biliyan 1 zan kashe dan fauziyyah tasami ingantaccen ilmi


Aunty mabarukha tace tace insha Allahu daddy namaka alqawarin kula da fauziyyah yadda ko kai idan kaganta sai kasan lalle mace ce mai ilmi


Kuma gashi dama yanzun ne zaa koma first term so kafin hutun ya qare zaa sama mata lesson teacher


Shikuma yaje Allah ya shiryeshi amma saiya ga sakayyah


Cikin jin daddy yace haka nakeso Allah ya taimakemu


Momcy ta shigo nan suka cigaba da tattunawa




Sannan ta kira fauziyyah tafada mata tare da aunty mabarukha zasu tafi


Taji dadin hakan dan gaba daya zaman bauchi ya fita aranta




Ana gobe zasu tafi taroqi momcy tabarta taje gidan aunty niima da kuma gidan khairy


Momcy tace sai dai driver yakaiki gidan khairy amma niima kanma zataxo anjima


Sai dayamma sannan ta shirya ta tafi gidan khairy




Agida tasamu TJ sai taji kamar ta koma dan bata qaunar abinda zai kuma hadata da ya Alamin so dataga TJ sai taga kamar tare data gansu


Bayan sun gaisa TJ yace ashe abinda yafaru kenan Allah yasa haka shiyafi alkhairi amma gaskiya Dr bai kyautaba sam


Murmushi tayi tace lah bakomaifa nihakanma yafimun


TJ yace idan da rabo saiku sasanta kuma shimuke fata


Fauziyyah tace hmmm kaidai mubar maganan nan kawai kada na furta abunda ba kyau


Shiryawa yayi ya fice nan yabarsu da khairy suna tada abinda ya wuce


Sai gab da magriba driver ya dawo daukarta


Sai anan take fadama khairy tazo mata sallama ne amma ta roqeta ko mujinta kada tafadawa gashi gashi


Khairy tamata fatan alkhairy ta rakota har bakin mota sannan ta tafi




Washegari sukabi jirgi sai birnin tarayya Abuja




*****
*2weeks later*
Papa yana kwance yana tunanin sati biyun da yayima juhaina alqawari ya cika kuma har yau daddy bai nemeshiba sai yaji qarar wayarsa


Sai daya tashi zaune ganin sunan maikiransa amma haka ya bude idanunsa da toka ya dau wayar yana cewa


Barka da yamma Abba


Yawwa Alamin ya aiki


Yace lfy lau Abba


Abba yace batun yarinyar da kake so nakira inji awanne gari ko unguwa take dan insha Allahu jibi zamuje maka tambayar


Dik iskancinsa dayaji kunya ta kamashi cikin sanyin murya yace akaduna take


Abba yace toh inyaso kashirya gobe zamu shigo bauchi nida Alhaji Sabo qanin daddyne inyaso jibin sai mu wuce tare dakai harda daddynma


Toh nagode Abba Allah ya qara girma




Abba yace bakomai nan sukayi sallama ya kashe wayar kuma yayi hakane dan jin irin furucin da daddy yayi akan shi baruwansa da wannan auren


Da kyar su Abba suka shawo kan daddy ya amince suka tafi kaduna tare


Atare da papa suka tafi kaduna kuma anmasu tarba ta mutunci nan suka tsaida magana maganar aure nan da wata 1 kacal dan ko wani fanni ashirye suke


Papa da juhaina suna zaune acikin garden din gidansu juhaina ta dubi papa cikin shagwaba tace my king


Naama my queen ya amsa


Tace umm ya maganar dakace kowa gidansa da banne ko inace bakacanzaba


Murmushi yayi ya riqo hannunta yana duban idanunta yace ki kwantar da hankalinki Alamin nakine kekadanki


Cikin rashin fahimta tace kamarya likitana fahimtar dani bakacemun kanada mata ba




Yes amma dakenan yanzu single nake cos na yanka mata red card nata so kinga ni nakine ke kadanki




Nan taji wani dadi ya mamayeta koba komai yanzu aikin dake gabanta ya ragu sai dai tayi qoqarin ganin bai dawo da itaba dan gaskiya batajin zata iya zama da Dr Alamin tana ganinsa da wata mata.....




โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
[3:01PM, 8/19/2017] โ€ช+98 903 074 3573โ€ฌ: ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017




3โƒฃ9โƒฃ
Washegari dasafe suka biyo jirgi suka dawo bh


Gida papa ya wuce dan Abdu yazo daukarsa


Bayan yayi wanka ya kwanta dan ya huta amma sai da yajima yana waya da queen nasa kafin yayi bacci


Bashi ya tashiba sai wajen5 tukunna


Cikin sauri ya gabatar da sallan laasar sannan kira TJ awaya ya sanar masa yana zuwa gidansa anjima kadan


Sake wanka yayi ya shirya tsaf abinsa ya nufi gidan TJ


Afalo yasamesa shida amarya suna zaune suna kallon wani film a setlite


Fiskannan ba yabo ba fallasa ya qaraso ya zauna


Nan suka kashe hannu


TJ yana cewa ashe kana kusa kenan mutumin


Yace no inafa gida nakira ka kawai dai ban biya ko ina bane


Khairy ce tace ina yini ya Alamin


Lfy lau ya amsa mata


Tashi tayi ta fice kitche ta kawo masa ruwa da juice ,tana ajiyewa ta juya abinta daki dan ita haushi papa yake bata ko yaushe fiska kamar an aiko masa da saqon mutuwa




Ya hanya toh TJ ya tambayesa


Umm normal fa kuma albishirinka


Toh goro fari tass ma kuwa


Papa yace anfa tsaida magana nan da 1 months juhaina tazama mallakina


Kashe hannu sukayi TJ yace shege mutumina kace kawai komai ya kankama


Atare sukayi dariya papa yace kai dai yanzu kawai shiri zamu fara dan kasan dole muyi party kalakala sabida baqin da zasu zo


TJ yace tabbas yanzu dai muje kaci abinci dan nasan kyar inkayi lunch ma inyaso sai muduba muga yadda abin zai kasance dan bama da enough time


Papa yace wlh kuwa kaman zanbiya Eatry sai nace barindai fara zuwa nan sai mufita tare


TJ yace ai zanci abinci saiga wayarka nace toh barin bari saika zo sai muci


Ok muje to,dinning suka qarisa


Ya bubbude masu wamers yace bismillah Dr


Aroma ne yaji ya bugi hancinsa ga kuma ya birgesa a ido nan yadauki plate ya debi white rice wadda taji vegetables da chips sai stew wadda tasha naman dajajatun


Spoon 1 yakai bakinsa yaji abincin yamasa 100๐Ÿ’ฏ


Shiru yayi kawai yanacin abincin dan har yamafi na resturant dayake zuwa cin abinci


Gagara haqura yayi yace man wai a ina kuka sami mai aiki wadda ta iya girki haka


Murmushi TJ yayi yace haba wuce nan nayi aure kuma nazo inacin abincin mai girki never


Papa cikin mamaki yace kana nufin wife nakace tayi wannan girkin


TJ yace yeah itace dan bamuma da mai aiki agidannan komai ita takeyi


Shiru papa yayi yana tunanin wannan yarinyan itace ta iya abinci haka sannan gidan ko ina tsaf sai qamshi kawai , da atunaninsa mai aikice ta gyara gidan dan wannan tayi qanqanta tayi haka sannan kuma yar qauye inama tasan wani gyara haka


Maganar TJ ce ta katse masa tunani yana cewa aikasan Allah nifa kullum sake godema Allah nakeyi


Dan wlh bani da matsalar komai , gata da haquri ga tsafta dik abinda dik abinda nakeso shitakemun


Shiyasa na shafama kaina ruwa na tattara dik wata sabga nafakata a gefe dan wlh yadda yarinyarnan takemun biyayya har kunya nakeji tasan halayena nada kuma kullum inaroqon Allah ya yafemun zunubaina dan da dan hali nane bazan samu ta gariba


Papa yayi shiru yana sauraronsa axuciyarsa yace lalle ashe shima zai more tinda wadda ya auri qaramar yarinya ma gashi dik ya canza sabida kwanciyar hankali baran shida matarsa wayayya wadda ta mallaki hankalin kanta


Nidai Mmn Faty nace lalle dasauranka papa dan abin badaga nan takeba wai andanne ma bodari kai


Suna cikin hiransu wayar daddy ta shigo masa


Hello daddy yafada bayan ya dau wayar


Inaon ganinka yanzun shine abinda daddy yafada masa ya kashecwayarsa


Alamin ya dubi TJ yace man zan wuce yanzun daddyne ya kira kuma yanason ganina


Ok sai gobe insha Allahu zan shigo gida


Harka fara fita kenan


TJ yace no sai nanda two weeks zanje sayama khairy form din school ne


Tabe baki yayi yace ok saika shigo na wuce


Harbakin mota ya rakashi sannan ya tafi




*****
Daddy da momcy suna zaune afalo inda papa yake gefensu azaune yayi shiru yana sauraron daddy


Alamin ya kira sunansa


Naam daddy ya amsa yana kallon daddy


Daddy yace toh nakirakane dan inmaka godia ka kyauta sosai akan abindakayi


Kaci nasara ko ,great ,welldone amma kasani wannan auren tinda kai kaga zaka iya toh kasani ba nairana ko daya da zai shiga ciki


Saika hada masu lefe sannan ka tanadi wajen ajiye matar dan ina buqatar gidana


Papa yace ok daddy wannan bamatsala bace zaayi komai yadda ya dace shikenan zan iya tafiya


Daddy yace eh kana iya tafiya


Bayan ya fita daddy ya dubi momcy yace saudah anya kuwa yaronnan yana cikin hankalinsa


Momcy tace mekagani




Yace gashi baiko damuwa da fushinmu baran yagane abinda yakeyi ba daidai bane


Momcy tace Alhaji nifa abinda yasa kaga nayi shiru bana magana wlh nafiganin laifinmu akan na papa


Daddy yace kamar ya laifinmu kuma


Tace toh icce tun yana qarami ake tankwarashi amma mu dik abinda papa zaiyi bama tsawatar masa baran mu nuna masa kuskurensa




Yanzu gashi yaxo yafi qsrfinmu tunda bamu isa dashiba


Daddy yace wannan gaskiyane amma yanzukam lokaci yaqure sai dai muyi ta masa addua Allah ya shiryesa




*****
Kwanan Fauziyyah biyar da zuwa abuja aka kawo mata lesson teacher


Cikin ikon Allah kuwa tana gane karatun sosai dan dama fauziyya tana da ilmi


Hankalinta akwance batada matsalan komai dan Aunty mabarukha ta maidata kamar qanwatta ciki 1


Cikin wata guda tayi wani kyau ta qara haske


Gashi tasamu admission nan da sati biyu zata fara zuwa makaranta


Yanzu bikin papa ya rage saura sati 1 hakan yasa aunty mabarukha ta shirya ta tafi bauchi amma ita kadai tatafi tabar su fauziyyah a gida


A bangaren papa kuwa yagama dik wani shirin biki ,gidansa dake sokoto road ya dauki kamfani ya basu contract su ronobeting gidan


Lefe kuwa nagani nafada aunty niima ta hada masa a dubai


Aunty mabarukha nazuwa suka wuce kd suka kai lefe


Biki ya rage saura kwana biyar aka fara hidima ta alfarma


Ango da abokansa da yan uwansa kwanamsu biyu a kd ana shagali sai da aka daura aure aka dawo bh


Nan aka dora daga inda aka tsaya


Gidan amarya idan kashiga kamar kada ka fita dan kyau da tsari gashi anzuba kaya na alfarma




Kwanan mutanen kd biyu suma suka tattara suka koma aka bar amarya daga iya sai halinta


Papa kuwa kai na rawa yau gashi ga juhaina amatsayin mata sa miji


Qarfe tara abokai suka rako ango gidansa .......




โœ๐ŸปFaty Mmm Faty
[3:02PM, 8/19/2017] โ€ช+98 903 074 3573โ€ฌ: ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017




4โƒฃ0โƒฃ
Shiru bakowa afalo sai qarar AC hadi da daddan qamshi


Wani lumshe idanu papa yayi yana hasashen yanayin da zai tsinci kansa acikin daren yau


Zama sukayi afalon farko yace bari ya dubo ta aciki


Sai da ya wuce wani falo daganan yabi wani corridor ya shiga room nata


Tana zaune adaki ya sameta , tasha lillbi daga kanta har qafanta


Shigowa yayi yana wani murmushi na musamman dahaka ya qaraso har gabanta


Cikin murya mai taushi yace my queen bazaki dago fuskarki naganiba baran ki amsa mun sallamar da nayi ko dai saina biya ne


Wani sanyi taji har cikin ranta yadda yakirata cikin soyayya


Ahankali ta dago kanta tanacewa aa my king barka da shigowa


Nan papa yayi suman tsaye cos tasha kwalliya ta alfarma , wani yadine ajikinta mai kyallin gaske da kyau da tsada golding colour


Ya mutuqar karbarta, face nata anqawatashi da kyakykyawar kwalliya ta musamman


Ganin yadda yake binta da wani mayen kallo yasa ta jefeshi da wani shuumin murmushi


Wadda yasa dakyar ya lalimo natsuwarsa yace my drling muje falo atare dasu TJ nake


Cikin wata siririyar murya tace ok sannan tafara qoqarin tashi


Hannunsa yasaka ya dagota inda itakuma dagantan tasake jikinta tafado akan chest nasa qirjinta ya mannu ajikinsa


Sai ya gagara dagota yasake ma manna ta ajikinsa cos arayuwarsa yanason mace mai manyan booms


Kuma yafison wannan abin fiye da komai ajikin mace hakan yasa juhaina take burgesa dan yaga tanada wannan kayan


Sunkai 5mins ahaka yana wani shashshafata


Itakuma sai wani ahh take hadi da wani irin numfashi mai sauti wadda yasake sauqeshi a network out of service


Cikin wata murya qasa2 tace my king munbar baqifa afalo


Sai anan yadawo duniyar zahiriyyah dan yama manta sam da wasu wai afalo


Dagota yayi ya lakaci hancinta yana cewa it is not my fault,dik kece kika rudani


Ashagwabe tace toh kayi haquri muje aidai yanzunkam muna tare ko


Baice komaiba sai hannunta daya riqe suka fice


TJ kuwa har yafara qulewa dan ajima kadan ya duba wach na hannunsa cos yanason komawa gida sabida babynsa ita kadaice danma basu da nisa sosai


Yana cikin shawarin ko ya taboshi awayane yaji idan bazai iya fitowa ba su qara mai kawai sai yaji takun tafiyansu


Qarasowa sukayi suka zauna akan kujera guda sun wani mnne ma juna kamar wani zai rabasu


Nan suka gaisa hade da dan barkwanci agurguje sukayi addua kowa yacika ma rigarsa iska dan sun lura da angon ahannu yake




Binbayansu yayi zai kulle falo nan yadan tsaya shida TJ bandaiji mai suka fadaba sai naga sun kashe hannu suna dariya


Kulle falon yayi ya dawo ciki sai dai baigantaba


Daukar ledar daya shigo da ita yayi ya koma dakinta


Nanma baigantaba sai yaji qaran ruwa a toilet hakan yasa ya ajiye abin hannunsa ya fice dakinsa


Wanka yayi ya shirya cikin wasu kayan bacci na alfarma farare tass dasu


Sannan ya dawo dakinta ,azaune yasameta agaban mirror tana shafa turare ajikinta, sanye take da wata shegiyar rigar bacci milk colour iyaka cinyanta


Tamatuqar yimata kyau sosai


Juyowa tayi tasakar masa wani murmushi mai kashe zuciya


Shima mayar mata yayi sannan ya tako ahankali har indabtake


Rungumeta yayi ta baya cikin murya mai kama da rada


Yace rigarnan tamaki kyau sosai yana yasa hannunsa yana wasa da hannun rigar


Hannunsa ta riqe takai bakinta tana lashewa ahankali tace kaima kayi kyau harma ka fini


Yadda tayi maganar irin dagaskennan shiya bashi dariya


Yace kai darling wayace maki maza suna da kyau


Juya idanuwa tayi tace umm gaskiya mafi yawancin maza basa da kyau but kai nadabanne king of my hrt


Cikin murmushi yace hakane


Nodding kanta tayi tace yeah


Yace thanks my luvely wife muje muci abinci ko


Dagota yayi tamiqe sannan suka nufi darduman dake gaban gado suka zauna


Jawo ledar yayi kafin yace ah my darling pls helf us mana ki kawo mana plates n cups


Shagwabe fiska tayi tace haba hooney nifa amarya ce ai yau ranan hidimanka ne


Fiskanta ya shafa yace gaskiiya fa yakamata nizan feeding nakima barinzo


Baijima ba ya shigo ya zauna a inda ya tashi


Wasu gasassun kaji ne wadda suka gane kurensu acikin oven guda uku sai ya ciro daya ya saka akan plate


Sannan ya zuba masu fresh milk a cikin cups


Dubanta yayi yace my baby matso muci abinci ko


Ashagwabe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login