Showing 42001 words to 45000 words out of 86122 words
abinsa ya farru
Juhaina sosai takeson munnir dan araayinta idan ta tashiyin aure shidata aura haka shima ya amince da batun aurenta tinda shikam ya samu tana masa komai
Bayan ta qare karatunta ta dawo nan suka dora daga inda suka tsaya itada munnir
Lokacin da papa yazo mata da maganar aure bata boyewa munnir ba
Amma shi saiya ce sam baisan zancen ba kuma ba auren da zatayi ta barshi
Nan tace masa wane shi harya isa ya hanata aure dama itace tace data aureshi kuma tafasa sai yaya
Duban bakida wayo yamata yace wlh intayi aure sai da yardarsa dan zaije ya samu saurayin nata yafada masa gaskiyar abinda ke takaninsu inyaso yaga yanda zatayi
Sanin munnir zai iya bin diddigi ya samu inda papa yake yasa ta lallaba shi dan tana matuqar son papa sosai
Dakyar tashawo kan munnir ya amince amma da sharadin suna tare koda tayi aure
Haka ta amince akan bayan bikinta zata sama masa koda gidane inda zai zauna saiya dawo bh da zama harma ya fara karatu
Wannan kenan
*****
Bayan sallar magribah papa da juhaina suka fita basu jimaba suka dawo dama abinci sukaje sayowa
Bayan sunyi parking Abdu yazo dasauri ko da akwai abinda zai shiga dashi ciki
Cikin girmamawa yace barka da dawowa oga
Aha Abdu shine abinda yafada yana miqo masa abincinsu adaqike yace gashi na hutar dakai fita
Juhaina ta fito da leda guda uku ahannunta yayinda uban gayyar shima ya fito
Har zata wuce sai papa yace my queen
Juyowa tayi ta amsa da yess my king
Inaga mu miqama munnir abincinsa idan munshiga ciki basai munfitoba ko
Ok muje to tashi dashi
Munnir kuwa tunda suka shigo yake tsaye ajikin window yana kallonsu cikin baqin ciki
Dan wani haushin papa yakeji cos y rage masa jin dadi ganin sun nufo wajensa yasa cikin sauri yasauqe curtain ya koma kan cussion ya zauna yana latsa wayarsa
Norcking suka masa
Daga ciki yace yess come in
Suna shigowa dasauri ya tashi cikin murmushin dole yace barkanku da shigowa
Papa yace yawwa amma yana tsaye cos baxama zaiyiba
Miqomasa take away nasa tayi tace bross ga abincinka sai da safe
Allah ya kaimu yafada yana bin bayanta da kallo
Nace sai kayi ai matar wani ceπ
Bayan sun ci abinci papa ya dubi juhaina amma bada wasa ba yace my queen yakamata kifara dafa mana abinci tunda kinga yanzu ga munnir ma bai dace kullum muriqa bashi abincin wajeba
Ganin yadda yayi maganar bada wasa ba ya kuma sha murr yasa tace shikenan Allah ya kaimu
Washegari da safe ta dafa masu indomie
Sai dai satisfactory haka sukaci dan bai wani test ba
Da rana kuma haka aka kwaba white rice da stew dikda kajin dake ciki amma sam kasa ci sukayi dagashi har ita
Sauran mutanen gidan kuwa banbi takansuba
Ai daga kan dinning yace mata kada tamasu dinner tabari kawai dan yafahimci bata iya girkiba
Haka sukaci gaba da zama ahaka inda azuwa yanzu yafara gajiya da halayenta sam
Gashi bata kunyar idan yace tamasa abu tace bayanzuba
Satin bikinsu biyu TJ ya kwanta rashin lfy fever mai tsanani har saida papa yaje ya saka masa ruwa agida da allurai
Amma abinda ya birgeshi da gidan TJ shine tsaftar matarsa ko ina kyalkyal kamar baa takawa sai qamshi kawai dake tashi ta ko ina
Gashi ya lura da tana son TJ sosai ba irin sonda juhaina kemasa ba tinda dik abinda yakeso shi take masa
Agidan ya wuni ranan bayan tagama abinci ta kawo masu amma TJ sai ya gagara ci
Papa kuwa haka yaci yaqoshi yana santi aransa har yana inama ace matarsa haka take
Ganin yakasa cin abinci dik ta damu sai tambayarsa take mezaici adafa masa
Yace tamasa faten irish potatoe da hanta da alayyahu
Nan da nan ta daho ta kawo masa balaifi yadanci kuwa sai anan hankalinta ya kwanta
Sai gab da magriba ya tafi yana fitowa wayar juhaina ta shigowa
Doguwar tsuka yaja kafin yadau wayar dan
Tun bayan laasar juhaina take kiransa awaya yaushe zai dawo
Cikin jin haushi yace wai meyene kika dameni aidai zandawo ko ko ancemaki bata zanyi yana fadin haka ya kashe wayar dan wani haushinta yakeji yanzu dayaga yarinya qarama yadda ta iya komai da kula da miji
Ita kuwa banda abiya mata buqta batada aiki
Yana tafiya yana tunanin gaskiya dole dasake inma makarantar koyan girki da gyaran gida zata shiga sai dai tashiga dan zamansu ahaka bazai yiyuba
Itakuwa tasamu dama suna sheqe ayarsu da munnir shiyasa ajima kadan ta kira taji koya kusa dawowa kada ya dawo yasamesu atare
Amurtuqe ya shigo gida direct room nasa ya shige sai bayan yayi wanka sannan ya fito
Juhaina ta dubeshi tana zaune afalo tana kallo tace wai lfy kuwa hooney kaketa bata rai
Nakira ka awaya kana wasu magana gashi kadawo kuma ranka abace
Yace eh kawai zamanmu ne yakamata mu gyara
Gyara zama tayi tace toh kamar me kenan
Yace yanxu ace ko girki baza ki iya yimana ba komai idan inason nagani da kyau sai dai inni nayi haba
Kawai nayanke shawara zan maki register a school na koyan girki da kula da gida
Dubansa tayi nan taji ranta ya baci wato raini ne yasa zai zo yana fada mata haka
So kawai gobe zanje na mak........
Hannu ta daga masa tace heeyheey ya isa haka Alamin kul karkasoma wannan maganar
Da mamaki ya dubeta yace ni kikecema hey har kina dagamun hannu
Tace anfada maka din so what
Kuma ko cemaka akayi mai aikice ni da zaka fara tsiro da wani abu aidai ciyar dani dolenkane
Ko ance maka agidanmu inayin girkine har zakazo kanamun wasu surutai da shouting
Cikin bacin rai ya dubeta yace lalle juhaina nikike fadama haka ba kunya
Tace nice ma kai kajiko
Hannu ya daga zai mareta sai yafasa
Wata dariya ta sheqe dashi tace ya kafasa lalle da kamari mai tsada dan wlh ramawa zanyi tsaf ni banza bazata shani ba
Ko ashaye kazo kada ka taba kwatanta dukana dan ni bazan tolarating nonsense ba
Dubanta yatsaya yi dan baitaba tunanin tasan yana shan wani abu ba tunda boye mata yake
Itama dubansa tayi ido cikin ido tace yess ko ka dauka bansan kana shayeshaye bane kawai kallonka nake so kada kafara abinda zai dameka kaji nafada maka tana fadin haka ta wuce shi tabarshi awajen
Tsabar mamaki da bacin rai yakasa koda motsi kamar wadda aka dasa......
Wai ina labarin mutan Abujane kamπ€
Kubiyoni a next page domin jin labarin *Swt Fauzy*
βπ»Faty Mmn Faty
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
4β£4β£
Ahankali ya wuce ya nufi room nasa yama rasa wanne irin tunani zaiyi guda daya
Tun daga ranan ya shareta ya fita aharkarta shi atunaninsa zatazo ta basa haquri
Amma har sukayi 5days ahaka itama bata kulashi kamar yadda bai kulata
Abincima sai dai ta tura asayo mata
Papa kuwa abin ya masa yawa wai suna yana da mata amma babu abu daya dayake amfanuwa dashi ata bangarenta
Dan abinda yake samunma yanzu baisamu tunda sun kancake
Gajiya yayi yaje yasameta ya lallaba ta suka shirya
2weeks later
Yanzu hutun daya dauka awajen aiki ya qare hakan yasa juhaina ta bude sabon babin walawanta
Sassafe kafin papa ya tafi aiki munnir yake fita amma yana fita zata kirashi awaya ya dawo
Ta back door yake shiga wajenta yadda bawanda yake sanin shigarsa
Kullum suna shan shagalinsu da munnir hakan yasa yanzu ko papa bako yaushe yake samun biyan buqatarsa
Dan taringa masa hanya2 kenan aa daga tace batajin dadi sai tace bacci takeji
Idan ya matsa mata sai tace toh bata cikin mood din wannan abin
Gashi yanzu tamaidashi kamar ATM mashen sabida kullum acikin ya bata kudi take
Ga yawon tsiya da koyaushe sai dai ta dauki motarta ta shiga gari
Sau da dama haka zai dawo bai sameta ba
Yau dama tun bai fita ba yamata kashedin kada ta fita ko ina idan yadawo office zasuje gida sugaida daddy baiji daddy ba
Bayan ya dawo suka shirya sukaje basu jima ba ta dameshi da sutafi sabida yadda bata samu fuska awajen momcy ba haka aunty niima bata sake mata ba
Bayan sun tafi aunty niima ta dibi momcy tace momcy wlh matar papa ashe bayarinya bace yanzu naqare mata kallo da kyau
Cikin takaici momcy tace wannan ai idan bata girme masa ba toh saidai suzo saanni dan bai isah ya girmetaba
Aunty niima tace wai ya labarin fauziyya ne kam nakai 3days banyi waya dasuba
Momcy lfyrta qalau dazunma munyi waya da mabarukha tacemun tatafi makaranta
Aunty niima tace Allah sarki Allah ya bata miji nagari yarinya mai haquri
Momcy tace insha Allahu Allah zai canza mata da mutumin kirki
Haka sukayita hiransu suna jajanta abinda ya wuce
*****
Juhaina ce tsaye gaban papa ta riqe qugu ranta abace
Fiska a tsuke tace wai Alamin maeke damunka ne dannace kabani kudi shikenan sai kafaramun kididdiga kuma kana dashi bawai baka dashiba
Shima cikin fada yace ai banace bazan bakiba but i just want to know mezakiyi da kudinne ke kullum cikin abaki kudi kuma banga me kikeyi dasuba
Ahasale tace idan bazaka bani bane kawai kafadamum bawai kana wani kwana ba
Kallonta yayi dakyau sannan yace toh bazan bayarba ki kwata
Ok is that what u said tace dashi tana wani turo qirji
Yeah haka nace kin wani tsareni kamar wani danki kina turomun tsumma
Kutt qirjinawa ne tsumma ta fada cike da bacin rai
Adaqile yace toh meye acikin ido banda ruwa ni bani hanya kiga ina da abinyi
Naqi nabaka hanyan marar mutunchi kawai kuma ahakan kake kwantar da kwadayinka ba
Ya tsina fiska yayi yace eh arashin uwa ba
Nan sukayi tsiya tsiya kamar zasu daki junansu
Da kyar yasamu ya shige dakinsa ya kulle dan shakkar juhaina yake kuma ya tabbata idan ya daketa zata iya ramawa shiyasa bayi attempting dukanta
Kwanaki na tafiya, watanni sun shude
Haka rayuwa yaci gaba da tafiya tsakanin papa da juhaina
Zaman lfy da kwanciyar hankali sun qauracem papa kullum yana yawon wajen cin abinci kuma itama dole ya kawo mata nata inba haka ba bayi da kwanciyar hankali
Kudi kuwa ko yaso ko yaqi dolensa ya bata
Abunda yafi daminsa yanzu yawo da ta qara couse akai yakuma rasa inda take zuwa tunda bata da yan uwa bauchi amma kusan kullum bata yini agida
Munnir kuwa yanzu yayi sabuwar budurwa
Dazaran juhaina ta bashi kudi ita yaje zuwa ya kashewa shiyasa kullum acikin tambayarta kudi yake
Time to time kuwa yana zuwa kd yayi two weeks harma fiye da haka
Yanzu haka mota juhaina tamasa alqawarin zata canza masa
Itama can wajen yawonta tayi sabon kwarto shiyasa yanzu bata damu da mumnir ba
Ita yanzu hanyar da zata samu ta koreshi take nema shiyasa takeson tacanza masa mota ta lallaba shi ya koma kd
Wasa gaske yanzu aurensu ya doshi shekara amma shiru ko batan wata bata tabayiba sabida kwayoyin hana daukar ciki datakesha
Dan bata shirya haihuwa yanzuba acewarta zata tsufa da wuri kuma ma ita bata shaawar yara dan wai takura garesu
Ya zuwa yanzu dik wadda yake tare da papa zai fahimci akwai abinda ke daminsa kawai dai bai fito ya fada bane
Amma acikin zuciyarsa yafara danasanin auren juhaina tunda bai qareshi d komaiba
*****
Aunty mabarukha nagani tsaye ajikin mota da alamu fita zatayi unguwa sai dai kamar jiran wani abu take
Fauziyyah ce ta fito cikin shiga ta alfarma wadda sai danayi da gaske naganeta
Taqara haske taqara girma
Wata arabian gown ce pusher pink wacce ta matuqar shan adon duwarwatsu masu kyallin gaske
Ta rolling veil din rigan akanta hannunta riqe da wata waya mai dan banzan kyau
Cikin sauri ta qaraso wajen aunty
Tana cewa am sorry aunty nabarki kina jirana
Aunty tayi murmushi tace no badai kin gamaba muje bazama mujima ba zamu dawo sabida kada su daddy sudawo daga islamiyya
Ok ta fada tana shiga mota
Gidan wata qawar aunty sukaje suka karbo wasu kaya tadawo daga dubai
Bayan sundawo yara ma sundawo daga islamiyya suna hira afalo
Aunty ta dubi fauziyyah tace Fauziyyah inaga tinda yanzu kina SS2 kawai kizana SSCE inyaso bazaki fasa zuwa school ba
Idan paper yayi kyau sai munemi admission kawai
Fauziyyah tace toh Allah ya kaimu
Aunty tace inyaso idan anyi hutu bazuwa dambam sabida kisamu kiyi karatu sosai
Cikin ikon Allah fauziyyah tana cikin shekaranta na biyu da komawa makaranta ta zana SSCE
Kuma da ikon Allah papers nata sukayi kyau dan fauziyyah dagaske take karatu idan kuna magana da ita zaka dauka tagama university sabida yadda takware a turanci
Kuma tana daukar shawara da nasihar da aunty take mata akan karatu
Takan cemata kiqara maida hankali akan karatunki sabida kizama wani abu kema arayuwa kinga dai abinda namiji yamaki akan rashin karatu
Hakan yasa ita kuma tayi alwashin sai tayi karatu mai zurfi
Lokacin da paper suka fito dikkansu suka taho bh
Daddy yayi murna sosai
Sannan yace meye shawarin aunty
Aunty tace yanzu dama sun sayi jamb form sun kuma sayi form na gwagwalada university
Daddu yayi shiru yace jiya sunyi magana da mr khan wani friend nasa dake india
Kuma yamasa magana akan asamawa fauziyyah gurbin karatu a jami'ar new delhi
Kuma ya tabbatar masa wannan badamuwa zai trying best nasa yace atura masa takardunta
Sosai sunji dadin shawaran da daddy ya yanke
Kwanansu daya ta wuce dambam abinta dan bata kaunar abinda zai hada ta da papa
Cikin watanni uku komai ya kankama na tafiyar fauziyya dan tasamu admission kuma agidan mr khan zata zauna dan abokin daddy ne sosai
Ranan talata su daddy suka kaita airport dake lagos dan tacan zasu tashi
Qarfe uku na rana jirgin su fauziyyah ya bar nigeria ya nufi india...[truncated by WhatsApp]
[7:12PM, 8/26/2017] βͺ+234 803 082 4581β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
*I dedicated this page to Zainab Abdulmumini(Mmn Samha) n My Swt Sis Fauzy, Allahu ya barni daku Mmn Faty ππ*
4β£5β£
Dawuri ya dawo gida cos yana da sugery da yamma a asibitin daddy
Akwai wani mutum da zaamasa aiki a spinal cord nasa
Yana shigowa tin daga parking space ya gane juhaina bata nan sabida he did not see her car
Key nasa ya bude qofa ya shiga ciki dan inda sabo ya saba da hakan
Dik randa ya kuskure ya bar key nasa kuwa to zai zauna a gate jiranta
Sabida rana daddaya ne zai dawo yasameta agida
Room nasa ya shiga ya kwanta nan bacci ya kwasheshi sai pass 3 ya tashi
Cikin dauri ya shirya ya fito sabida 4:30pm zai shiga aikin
Fitowa yayi ya kulle dakinsa dan ya kuskura ya bari abude sai tamasa barna
Amma ga mamakinsa bata dawoba ficewarsa yayi kawai abinsa
Bashi ya fitoba sai wajen 7 sallah yayi sannan ya nufi gida amma sai daya tsaya a resturant yaci abincinsa sannan ya wuce gida
Dagangan yaqi saya mata yace taci yawon taqoshi yau bazai saya ba
Har lokacin daya koma gida nanma bata dawoba
Tabe bakinsa yayi yaje yayi wankansa yayi sallah sannan ya fito ya kunna press tv yana kallon wani program da sukeyi
Har wajen 9 sannan yaji shigowarta
Gyalenta a hannu ta shigo falo
Ganinsa azaune sai tayi kamar bata ganshiba zata wuce
Keh daga ina kike da wannan daran yafada yana kallonta
Ko cikanka bata ce dashiba zata wuce ta gefensa
Cikin sauri ya riqo hannunta yace bada ke nake maganaba nace daga ina kike
Hannunta zata fisge yayi saurin sake riqeta sosai sannan ya miqe tsaye
Yace juhaina wai me kika maidanine dan iskanci ina maki magana sai kiqikulani toh inkinga kinbar wajennan sai kinfada mun daga gidan ubanwa kike at this time
Wani walaqantaccen kallo ta wurga masa sannan tace daga gidan uban mai tambayar nake
Nan take yaji xuciya ta debeshi watoma harshi zata zaga
Aiko nan take ya daga hannu ya wanka mata mari mai kyau
Yana sauqe hannunsa itama ta daga hannunta ta zabga masa mari tana huci tace kai har ka isa kadakeni to ko ubana bai dukana baran kai banza a banza ta fisge hannunta ta wucectabarshi
Shikuwa mamaki ne da baqinci suka hanashi cewa komai ko ya tanka mata
Wani zafi ne kawai yakeji yana taso masa daga kasan zuciyarsa kamarshi ace matarsa har tadaga hannu ta mareshi
Tsabar bakin ciki nan take idanunsa suka caza launi suka qanqance
Dakinsa ya nufa ya bude fridge ya dakko wine nasa ko takan cup baibi ba
Ya dannan bakin kwalbar amma maimakon tamasa dadin sha sai yaji wani daci sabida yadda zucitarsa ke tafasa
Nan take sai tunanin fauziyyah ya fado masa
Yaune rana tafarko daya fara tunota tinda ya saketa
Tunanin yadda yake nada mata duka yakeyi amma koda wasa bata taba tunanin fada masa magana mai muniba baran tarama
Ya walaqanqanta ta son ransa amma yarinyar nan haka zata haqura sai dai tayi kukanta tayi shiru bata taba fada ma waniba
Anya kuwa yamata adalci kuwa nan yaji xuciyarsa tasake quntata
Kotana ina yanzu ko wani hali ta shiga lokacin daya saketa bada haqqinta ba
Nan take zuciyarsa tafara bugawa da sauri sauri
Nan yafara tuno irin yanayinta kyan fuskarta yanayin jikinta
Tuno rananda yafara ganin qirjinta yayi nan take yaji wani kewanta marar misaltuwa yana shigansa
Zuciyarsa take raya masa inama har yanzun itace matarsa ba juhainaba daya rungumeta tsakani da Allah da bai cutar da ita ba
Nan ya tuno qamshin girkinta idan tana dafa abinci amma zuciyarsa ta cuceshi ta hanshi aminta da ita
Cikin qunan rai yake zargin kansa da mai yasa tunda baiga wannan abubuwanba sai yanxu da bai masan inda takeba
Nan wata zuciyar tace wataqilanma tayi aure abinta
Damm yaji zuciysrsa ta buga wani zafi yasakejin yana mamayeshi har yana zufa dikda sanyin AC dake bugawa
Haka ya ajiye kwalbar giyar dan bazai iyama shaba
Yadda yaga rana haka yaga dare sabida tunani daya addabeshi ya kuma tabbatar ma kansa zuciya takaishi tabaro tunda gashi yau yarasa tudun dafawa
Tundaga wannan ranan tsanan juhaina ya dasu a azuciyarsa amma haka yake zaune da ita ya kuma kasa saketa
Hakadai suke zama marar dadi
Sai abinda yafi daminsa wato yadda tunanin fauziyyah ya addabi rayuwarsa ba dare ba rana
Wani matsanancin son kasancewa tare da ita yakeji
At last ya tabbatar ma kansa sonta yakeyi
Rasa mafita yayi yaje yasami TJ ya fada masa abinda ke faruwa
TJ yaso yayi masa dariya amma ganin halin dayake ciki sai ya danne
Yace toh wai bakada labarinta ne
Papa yace banma san inda takeba ko agidan momcy ban sake ganintaba
TJ ya nisa yace toh yanzu shawarn da zan baka kadage da addu a idan rabon kace tadawo gareka
Nikuma zan tambayi khairy tunda yar uwartace dole nasan tana da labarinta inma aure tayi inma ko me nene zamuji
Godia yayi ma TJ sosai dan