Showing 45001 words to 48000 words out of 86122 words
har yadan sami natsuwa
Amma da TJ ya tambayi khairy hanya hanya tamasa kawai taqi fada masa gaskiaya
Shima haka dai yayima walawala ya qi sanar masa khairy taqi fada masa dan kada yaji haushinta
Haka rayuwa tayi ta tafiya inda papa yake cikin wani hali yakumayi dana sanin abinda ya aikata abaya kuma har gobe fatansa Allah ya nuna masa fauxiyyah ya roqi gafararta dan yanxu yagane cewar alhakinta ya ke bibiyarsa
Ba abinda ke qara daga masa hankali kamar yarda kullum sonta yake qaruwa acikin zuciyarsa
Watarana ankawo wata yarinya asibitinsu tasamu matsala a guiwarta daga faduwa
Aifa tun dayaji sunanta fauziyyah shikenan haka yaringa hidima da ita har aka sallamesu sabida yarda yake qaunar mai sunan
Kuma yasama ransa dik ranada yasan inda fauziyyah take kuma bata da aure tabbas koza ayi yaqi sai an maida masa da matarsa idan kuma basu sake haduwaba yasan sontane zaiyi ajalinsa
*****
Fauziyyah ta sauqa lfy, inda tasamu tarba na mutunchi awajen mr khan da matarsa da yaransa yan mata guda biyu
Kwanan ta biyu da zuwa tafara xuwa makaranta tanajin dadin karatunta sosai gashi Amisha tana taimaka sosai akan abinda bata ganeba
Cikin ikon Allah karatunta yana tafiya yadda akeso
Da haka har tacinye shekarar farko
*Bayan shekara biyu*
Fauziyyah ce zaune tana hada kayanta cikin farin cikin sabida gobe zata koma gida nigeria cikin nasarar uban giji ta kammala karatunta da saka mako mai kyau
Yanzu tazama cikakkiyar *PAMACIEST*
Cikin shekaru ukun datayi sau biyu kawai taje nigeria
Washegari jirgin qarfe 9 nasafe ta biyo sai gida
Acan nigeria kuwa su daddy ne da momcy da su aunty mabarukha harda aunty niima sukazo taronta dan akwai liyafar da daddy ya shirya mata a nan abuja
Jirgin na sauqa na hangota cikin jerin fasinjoji amma zaka rantse da Allah baquwace tazo daga india kuma zata koma sabida yadda fatarta ta murje tayi wani haske na musamman kyanta yasake fitowa
Kallo daya zaka mata kafimci zallan wayewa atare da ita dan tana daga cikin jerin mata masu class
Ko yadda take saqqowa cikin natsuwa kawai ya isa ya tabbatar maka cewa lalle wannan mace ce mai jida kanta
Daddy kuwa murmushi kawai yakeyi
Cikin sauri aunty ta qarasa ta rungumeta tana mata oyoyo
Wani daddan murya naji ya daki dodon kunnena hausa takeyi amma kamar maiyin indianci sabida yadda harshenta ya juye
Cikin farin ciki ta gaisa da kowa sannan suka nufi gida
Da yamma aka gabatar da liyafa mai kyau acikin gida
Sunsha hira sosai da daddare daddy ya kirata yace washe gari zasu wuce bh tare amma ita zata wuce dambam gida dagacan zai tura driver ya maidata abuja sai service nata ya fito sai tadawo bh tayi acan
Haka koh akayi watanta daya a dambam ta koma Abuja
Watanta biyu a Abuja service dinta ya fito amma jos aka turata nan daddy yamata cukucuku amaida ta bh
Tsabar tanada daurin gindi ko camp bata shiga ba
Sai byan an musu posting aka duba nata anturata teaching hospital na bh
Ana saura sati daya ta dawo bh uncle salim qanin mijin aunty yazo da abokinsa Barrister Nabil Abdullahi gidan aunty mabarukha
Wajen aikinsu daya a bh yanzuma wani aikine ya kawo su abuja kuma babansa shine commissioner for works n houses na bh
Tunda ya kyalla idanu yaganta ya nacewa uncle salim shifa yaga wata balarabiya kuma tamasa
Har saida ya kira aunty awaya yafada mata abokinsa dasuka zo tare yaga fauziyyah yana so kuma ya fada masa ta taba aure yace ko dik yaran duniya ita ta haifa yaji ya gani
Aunty kuwa hakan yamata dadi nan take ta tura masa phone no fauziyyah
Tunda yasamu no shikenan waya ba dare ba rana text ne meyene amma sam fauziyyah bata kulashi dan ba namiji aranta sam
Ranan sunday ta taho bh dan monday zata fara fita aikinta na service
Isowan yamma tayi lis dan basu taso da wuri ba hakan yasa tayi bacci da wuri
****
Papa kuwa yau tun daya tashi yakejin zuciyarsa wani iri kuncine meye ne baima saniba gashi yana da aiki a office gashi akwai maganar da zasuyi da daddy kafin ya fita office
Dolee yasa da wuri ya shirya ya taho gida daga can ya wuce office
Fauziyyah kuma qarfe bakwai ta tashi tayi wanka ta shirya amma tayi ligh make up sai pink jambaki data goga a lips nata
Kayan su na coppers tasaka ajikinta nan naqare mata kallo da kyau
Rigat ta kamata sosai inda na fulaninta da suke a cike dam gasu atsaye suka cika mata gaban rigan hakama wandon hips nata da bayanta sunfito sosai dan ya kamata sosai
Gaskiya wadda yasan fauziyyah lokacin tana gidan papa yaganta yanzu bazi ganeta sabida yadda tacanza komai najikinta ya canza ga wani kyau na musamman data qara
Kallon kanta tayi tsaf a madubi sai taji kunya bazata iya fita waje ahakaba
farar qaramar hijab ta dauka iya guiwa amma bata saka ba sai ta riqo ahannunta
Nima sake kallonta nayi da kyau nan naga zallan kaman datake da *Arti matar Yash na cikin film din married again*
Cikin natsuwa ta dakko yar qaramar jakarta mai kamar purse ta rataya hannuntabriqe da hijab
Tana fitowa falo da momcy tafara haduwa bayan tagaisheta momcy tayi murmushi tace masha Allah kiyi maza kije wajen daddy sai kizo kiyi break ko
Cikin muryarta mai dadi tace ok sannan ta mufi bangaren daddy
Da sallama ta shiga cikin faraa ya amsa bayan ta gaidashi
Yadan mata nasiha sannan ya miqo mata key din motarta sabuwa dal daya saya mata yace motarki tana waje Allah ya kiaye hanya ki kula da tuki
Nan taringa godia sabisa baqaramin dadi taji ba
Daddy yace kada kidamu jeki abinki kada kimakara
Papa kuwa yana zuwa gida afalo ya samu momcy bayan sungaisa yace bari yaje wajen daddy
Tace toh sannan ya wuce
Momcy kuwa jin fauziyyah shiru gashi kada time ya wure mata yasa ta kwala mata kira
Dauther kiyi sauri kizo kiyi break kada kimakara
Fauziyyah kuwa ta fito tazo daidai kan steps da zata sakko falo taji kiran momcy
Dama sauri take taxo ta nuna ma momcyn kyautar da daddy yamata
Itama cikin daddan voice nata mai dadin sauri tace yess me arihoo momcy(ina zuwa momcy)
Daidai papa yasaka qafarsa zai haura kan steps da zai kaishi side din daddy yaji wata murya mai dadin gaske cikin harshen indianci tana magana
Saida yadan matsa baya data bugeshi dan cikin sauri ta wuce batama lura da mutum ba
Papa kuwa ganin kyakykyawar mace kuma ba india yasa yabi bayanta da kallo amma dake tariga da wuce sai bayanta daya kallah
Wadda hips nata yake masa gwaliyo
Lumshe idanu yayi ya bude gashi ta buleshi da qamshin turarenta
Cikin sauri ya riqe gini dan baisan yayi missing step ba
Jiki a mace ya shige dakin dadi amma muryarta sai yawo yake masa akwanyarsa
Bayan sun gaisa gagara haqura yayi yace daddy baquwa akayi agidanne
Daddy yace baquwa kuma
Papa yace eh kamar ma ba india ce kuma daga nan ta fito
Wani murmushi daddy yayi yace aa kam indai wacce tabar nan yanzune sai dai qanwarka
Papa yace qanwata kuma wacce qanwata nikuma inada qanwace
Daddy yace qanwarka fauziyyah mana yar gidan Abbanku na dambam
Cikin sauri ya dubi daddy yace Fauziyyah kuma itace ta fita anan
Daddy yace yawuce wai itace mana amma bar wannan maganar ina jinka yadda abin zai kasance yasa na ce kazo da safe
Ina papa hankali yayi gaba baimasan daddy yana yiba
Saida daddy ya lura baima tare dashi sannan ya tabashi yace kana jina Alamin
Cikin sauri ya firgita yace me kace daddy
Wani murmushi daddy yayi wanda shikadai yasan maanarsa........
βπ»Faty Mmn Faty
[7:13PM, 8/26/2017] βͺ+234 803 082 4581β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
4β£6β£
Daddy yace maganar bude asibitin nan ne dama najika shiru haryanzu baka fadi wani suna zaa sama ba sannan wacce rana ya dace sabida buga IV
Papa dai yayi shiru yana jin dadi amma harga Allah dakyar ya tsinci kadan daga abinda yake fada masa
Sabida hankalinsa da tunaninsa baya tare da daddy
Cikin wani yanayi yace zanyi tunani akai zuwa gobe zan sanar maka
Yafadi hakan ne kawai dan yasamu ya tashi awajen dan ya tabbata bazai samu natsuwa ba har sai yayi tozali da farin cikin rayuwarsa dan yana da good assurance batayi aure ba tinda ya ganta agida da wannan lokacin
Daddy yace is ok sai najika toh
Aiko daddy na rufe bakinsa ya miqe cikin sauri yana cewa barinje office
Daddy yace Allah ya kiyaye hanya
Yana tafiya ya amsa da Amin
*****
Fauziyyah kuwa cikin sauri ta nufi wajen momcy tana murna
Rungume momcy tayi tana cewa dekho momcy meri gari key (kalli momcy key din motata) daddy ne ya bani kitayani godia
Cikin faraa momcy tace masha Allah, Allahu ya tsare hanya
Amin ya Allah ta Amsa
Momcy tace kije kiyi break kada kimakara
Toh ta amsa sannan ta wuce dinning, dan kadan ta iya ci sabida murna tadawo falo tace zata wuce
Har bakin qofa momcy ta rakota tana cewa ganan motar taki jiya dare aka kawota Allah ya tsare sai kindawo sannan ta juya ta koma ciki
Itakuma qarasa wajen motar tayi sannan ta bude ta shiga tana jin wani dadi aranta
Ahankali tamata key sannan tafara tafiya cikin natsuwa har bakin gate inda mai gadi ya bude mata gate ta fice
Direct NYSC office ta wuce sabida akwai abinda zatayi acan kafin ta wuce asibiti
*****
Papa yana fitowa yaga wayam bakowa afalo sai motsi dayaji acikin kitchen
Leqawa yayi sai yaga momcy ce itakadai
Ziciyarsa ce yaji ba dadi dan fauziyyah yaso yasake kallo
Asanyaye yace na wuce office amma idan nadawo zan biyo
Toh adawo lfy tace dashi sannan ya fice
Motarsa ya shiga ya wuce asibiti driving yake amma hankalinsa na wani waje
Tinani yake yanzu fauziyyah ce tadawo haka yarinyar da ya raina yanzu itace tazama big girl haka
Ikon Allah ne kawai ya kawoshi lfy yana parking ya wuce office nasa
Zaune yake amma yakasa tabuka komai tunani kawai ya addabi zuciyarsa har yafarajin yarasa maike masa dadi
Ya jima azaune amma ko file daya baigama dubawa cikin sauri ya ture su gefe ya miqe
Dan jin kansa yakeyi yamasa nauyi ga wani irin faduwar gaba da kunci dake damunsa
Gara ya tafi gida ya kwanta kawai
Wayoyinsa da key nasa ya zara ya fito
Cleaners da masinja suna gaisheshima amma hannu kawai yake daga masu
Yana fitowa ya nufi parking space sai yaga wata mota mai kyau kalar mata ta tsaya agefen motarsa
Kafin ya qaraso sai yaga ta fito tana rataya jakarta
Sake zuba mata idanu yayi tabbas fauziyyah ce amma badan daddy yafada masa ba bazai ganetaba
Sai alokacin ya lura ashe kayan NYSC ne ajikinta tambayar kansa yake yaushe kenan haka tafaru
Fauziyyah kuwa dago kanta dazatayi wazata hango yana nufota ya Alamin
Tabbas shine dan bazai taba bace mata ba dik da yadan canza yaqara kyau yadanyi qiba kadan sannan daganinsa naira tazauna masa fiye da da
Ahankali tasauqe idanunta tanajin zuciyarta tana bugawa da sauri sauri
Nan take taji wani zafi azuciyarta dan bata qaunar abinda zai hada ta papa ko ahanyane
Daidai da ya qaraso jikin motarsa amma ya qudira aransa zai mata magana dan bazai iyah ganinta ya wuceba
Itakuma yitayi kamar bata ganshiba zata wuce kamar daga sama taji muryarsa wadda kodaga bacci tafarka bazata manceba
Yan mata shine abinda ya furta yana kallonta
Cak ta tsaya dan jitayi kamar ya caka mata wuqa wai yan mata
Dagoda kanta tayi ta sauqe dara2n idanuwanta farare tas masu kamar madara akansa
Nan yaji wani abu wadda bai san mene ne ba kawai yasamu kansa da lumshe idanuwansa yana tasbihi ga ubangijin halitta dan fauziyyah ta tafi dashi gaba daya
Muryarta ta dawo dashi daga duniyar tunani daya tafi
Cikin halin ko inkula da rashin damuwa tayi kamar bata sanshiba
Ya tsina fiskanta tayi tana masa duban rashin sani tace konhei tum(wane ne kai)
Kutt dan zaro idanu kadan yayi sabida mamaki wai harshine fauziyyah zatace bata ganeshiba
Amma sai yadaure yayi wani qayataccen murmushi yace mera naam Dr Muhammad Alamin Abubakar(suna na Muhammad Alamin Abubakar)
Ya tsina fuska tayi ta wani juya idanuwanta tace eyyerh sowwie am not talking with people that i dont know
Tana fadin haka ta wuce abinta bata sake koda kallonsa ba
Shiru kawai yayi yabi bayanta da kallo
Cikin qunan rai ya bude motarsa ya fada yana tuna irin walaqancin da fauziyyah tamasa ta yankwanashi
Afusace yafigi motar wadda dakyar yataka birki yabawa scurity pass sannan ya wuce
*****
Juhaina ce ta dubi munnir tace wai saurin me kakeyi ne kamar wadda ba agidan zaka kwana ba
Yace kinsan najima bangankiba wlh ina kewarki sosai muje ciki narage zafi
Murmushi tayi sannan tace haba dai kaida zakayi 1 week me zai dameka kuma Dr sai yamma shida yadawo
Yace ai har tunani nke next idan zanzo wacce qarya zamu masa tunda munce nazo gyara carry over ne
Dariya tayi tace wannan mai sauqine tunda shi baho ne inba hakaba sai kace ba mutumin daya shiga ajin ABCD ba
Komai aka fada masa sai ya yadda
Shima dariya yayi yace nidai muje toh pls mana
Riqe hannunta yayi suka shige bedroom nata
Nan suka fara mashaarsu da suka saba
Tsabar sunyi nisa basa cikin hankalinsu ko jin shigowar mota basuyiba
Papa kuwa ko parking mai kyau baiyiba haka ya fito ya nufi cikin gida
Ahargitse ya shigo falo dakinsa ya nufa
Yazo daidai dakin juhaina harzai wuce sao yaji kamar nishi
Saurarawa yayi da kyau sai yaji tabbas ba kunnensabane nishintane
Cikin sauri ya bude dakin dan atunaninsa ko batada lfy ne
Yana shiga yayi turus wani jirine yaji ya debeshi yayi saurin riqe qofar sabida abinda idanunsa ya gane masa
Juhaina da munnir kwance haihuwar uwarsu suna aikata zinah
Abinda bai taba tunaninba juhaina zataci amanarsa kuma ma da dan uwanta
Su juhaina kuwa jin anbude qofa yasa cikin sauri suka juyo ganin papa atsaye yana musu wani kallo cike da baqin ciki har idanunsa sukoma jajaye kamar gaunta bushashshe
Dasauri munnir ya tashi akanta itakuma cikin razana ta tashi zaune tanajan mayafi tana kare jikinta
Ahankali yasamu nutsuwarsa ta dawo maida qofar yayi ya rufe da key sannan ya nufo su gadangadan
tsabar tsoro ba juhaina ba hatta munnir jikinsa rawa yake
Yana zuwa ya shaqo wuyan juhaina yace cikin kakkausan murya kifadamun wane ne munnir kuma meye atsakaninku
Aifa cikin tsoro da firgita tace dan Allah kayi....
Wani gigitaccen mari daya zabga mata saida taga wuta shiya katseta
Cikin tsawa yace wane ne munnir zaki fadamun da bakinki kosaina kasheki shegiya tsinanniyah macucuciya Allah ya isa tsakanina da keh wlh kinci amanata
Ganin yadda kamanninsa suka sauya fiskarsa tayi jajur tsabar bacin rai
Murya na rawa tafada masa tsakaninta da munnir tace amma kayafemun wlh bazan sake ba
Bata gama rufe bakintaba ya saka hannunsa ya makata da gini nan tafadi a asume
Munnir kuwa tsabar tsoro ganin yadda yayima juhaina saida ya saki fitsari ajikinsa
Aikuwa da papa ya damqoshi yafara dukansa yana cewa munafiki kana zaune agidana kana zaluntata ashe ina tare da kwarto bansaniba
Mari duka harbi haka yake masa saida kansa bakinsa hancinsa ko ina jini yake amma zuciya ta hana papa ya kyaleshi
Hannunsa yasa yakamo gabansa da iyah qsrfinsa ya jawota ya murde wadda saida ya saki kashin azaba
Hannunsa ya kama ya buga da jikin drower ji kake kass kass ya karyashi
Axaba iya azaba saida yakasa motsi sannan ya kyaleshi ya nufi toilet ya debo ruwa a bucket
Zuwa kan juhaina yayi wacce ke kwance asume ya sheqa mata
Nan ta firgita ta farka aiko itama nan yahau jibgarta da waya yana harbinta
Saida jikinta ya faffashe fiskarta ta kumbura tayi sumtum tsabar duka
Tsabar azaba har saida ta kasa kuka cikin baqin ciki ya jawota har waje tana nade acikin zanin gado amma saida kamanninta ya canza dan ba dukan wasa ya mata ba
Sannan yace tsinanniyah kada nafito nasameki kificemun agida na sakeki saki uku muna fuka
Itadai batada bakin kuka ma bare bashi haquri
Mai gadi ya kira yace suzo suna biye dashi har dakin juhaina yace su fitar masa da munnir agida su kaishi can waje
Haka suka jawoshi kamar har sun kai qofa paoa yace ganan haqorinsa biyu kuhada dashi kufitamun dasu
Suna fita ya nufi dakinsa yafada agado ya fashe da kuka....
βπ»Faty Mmn Faty
πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
*Gaisuwa mai tarin yawa musamman zuwaga Members na Mmn Faty Novel Group, Ina matuqar jin dadin yadda kuke bada gudumawarku da nuna jindadin ku akan littafin BUDURWAR QAUYE nagode sosai Allah ya bar qauna ππ*
4β£7β£
Kuka yake mai cike da nadama, hawaye wani nabin wani haka suke zuba akan face nasa
Zuciyarsa cunkushe da zallar dana sani akan abinda ya aikata abaya
Tabbas yau ya tabbar alhakin iyayensa ne dana fauziyyah ke bibiyarsa
Kuma ya qara daukan darasi akan bijirema iyaye ba abune mai kyauba tunda gashi yaga saka makon abinda bai taba tunani ba
Wani irin nauyi yaji qirjinsa yamasa
Kuka yake sosai har abin tausayi domin dik abinda mutun ya aika matuqar yagane kuskurensa har yayi nadama nagaske ba tuban baqin muzuru ba dole ya baka tausayi
Sambatu kawai yakeyi yana cewa daddy, momcy, fauziyyah kuyafemun ashe gata kukamun na auramun yarinya yar mutunci kuma mai mutunci
Amma son zuciya yasa na bijire muku yau gashi abinda yasameni wayyo kaicona kaicon halina dama duk masu hali irin nawa...
Maganarce tasarqe qirjinsa ya cushe numafashi yafara masa wahalar fita
Dakyar ya dauki wayarsa yafara kiran layin TJ
TJ yana office saiya ga kiran abokinsa
Hello man shine abinda ya fada yana daukar wayar
Cikin wata raunanniyar murya datake nuna mai ita yana cikin wani hali
Yace pls kazo gida kasameni ina cikin wani hali
TJ baisan sanda ya miqe tsayeba cikin razana jin yadda muryar abokinsa take a hargitse
Meyasameka??? Shine abinda ya maimaita harsau uku
Ahankali papa yace TJ banida lfy juhaina zata kasheni kazo pls kataimakeni
Afirgice TJ yace ganinan zuwa ganinan zuwa am on my way yana fadin haka ya suri key din motarsa ya fito cikin sauri yacema scretery nasa idan bandawoba zuwa 2 ka kulle office kawai
Baijira amsar shiba ya fice cikin sauri da tashin hankali dan baisan yadda zai sameshiba
Cikin gudun balai har ya iso gidan papa wani mahaukacin horn yake dannawa
Maigadima saida ya tsorata dajin irin horn dake masa
Aiko baibata lokaciba ya bude
TJ yana shigowa ko cikkakken parking baiyiba ya hnyar cikin gida daidai qofar falo yayi turus ya tsaya ganin juhaina lullube da zanin gado tana rizgar kuka dan sai alokacin tasamu kuka yaxo mata gashi ya kulle