Showing 48001 words to 51000 words out of 86122 words
qofa bare ko kaya tasama jikinta baran tasannayi
Juhaina ina Alamin yake kekuma meya sameki naganki haka
Gagara magana tayi sai da hannu ta nuna masa qofar falo
Tura qofar yayi ya jita gam akulle bubbugawa yafara da iyaka qarfinsa dan abin yaqara bashi tsoro
Papa yanajin bugun qofa gakuma wayar TJ tashigo masa yasa ya taso ya fito falo ya bude qofar
Yanaganin TJ kawai saiya fada jikinsa yaqara saka kuka mai tsuma zuciya
Cikin rudani TJ yace waime ke faruwane man kamin bayani mana kozanji sauqin abinda nakeji
Sake qanqame TJ yayi yana cewa na cuci kaina na biyema san zuciyata na cutar da matata ta gaskiya na baqanta ran mahaifana yaugashi naga abinda bazan taba mantawaba
TJ ma kawai saiyafara hawaye nafarko tausayin papa dikda baisan meya faruba amma yadda yaganshi a hargitse yana kuka da idanunsa tabbas babban abune
Sannan murnan abokinsa ya gane gaskiya
Share hawayen fiskansa yayi yafara lallashin papa da kalamai masu dadi har papa yayi shiru
Sannan yafara bawa TJ labarin abinda ya faru yana furta abinda yagani sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo masa
Cikin tashin hankali TJ yakejin abin kamarca mafarki
Nan ya fara tausan papa da banbaki akan ya kwantar da hankalinsa komai zai wuce
Papa yace hankalina bazai kwantaba har sai ka kaini asibiti anmin test na HIV tukunna
TJ yace insha Allahu babu abinda zaisameka ka kwantar da hankalinka
Taya hankalina zai kwanta matuqar ina dauke da wani mugun ciwo wlh jujaina ta cuceni ta shiga tsakanina da fauziyyah dan bayadda fauziyyah zata dawo gareni ina halin jinya
Tj yace ya isa haka muje asibitin inhar hankalinka zai kwanta dan yaga har numfashinsa yana samasama
Amma kabar juhaina ta suturta jikinta kafin ta tafi
Da kyar ya yarda yace amma kada yadawo ya sameta
Nan suka fito TJ ya kalleta yace kitashi kije kisuturta jikinki amma yace kada yadawo yasameki gidansa yanafadin haka ya wuce abinsa dan dama papa ya riga da ya wuce
Sai bayan sunfito TJ yace wanne hospital zamujene
Ka kaini asibitin daddy shine kawai abinda ya iya fada
Suna isa asibiti lab suka wuce
Maaikatan wajen suna gaisheshi baiko amsaba yace subashi abin gwajin HIV kawai
Damamaki kowa ke kallonsa cikin tsawa ya maimaita masu nan take suka miqo masa
Alluraya dauka ya caka wa hannunsa nan take sai jini yazuba yafara zaman zullumi
Bada jimaba saka mako ya nuna negetalive
TJ dake tsaye agefe yace Alhamdulillah bana fada makaba gashi ai d answer is negetive dafatan hankalinka ya kwanta
Shiru kawai yayi ya miqe dan baijin zai iya magana
Tashin da zaiyi ya yanki jiki ya fadi sumamme
Cikin razana TJ ya sumkuya yana kiransa amma ina baimasan yana yiba
Cikin sauri aka kawo abin daukar marar lfy aka turashi sai emergency
Nan suka bashi taimakon gaggawa har Allah yasa numfashinsa ya daidaita sannan aka maidashi dakin hutu amma dai bai farka ba tukun
In hankalin TJ yayi dubu to atashe suke
Sai a lokacin ya tuna yadauki wayar papa dake aljihunsa ya fara kiran momcy
Bugu uku ta dauka tana cewa hello son
Cikin natsuwa TJ yace ba Alamin bane Tijjani ne
Momcy tace ayya ya khairy da mubeen (dansune wadda bai wuce shekara biyuba)
Lfy qalau umm dama Alamin dinne bashida lfy yanzu haka muna asibiti
Salati momcy ta fara tace mai yasamu papa kuna wanne asibiti
Asibitin daddy muke naje wajensama bayanan
Momcy tace eh yau bai fita ba amma muna zuwa yanzu
Daddy ne ya dubeta yana cewa wai meya sami Alamin din
Cikin damuwa momcy tace nima bansaniba kam
Toh dauko mayafinki muje
Suna zuwa suka shige inda aka kwantar dashi
TJ suka sami yayi shiru yana zaune
Bayan yamasu sannu da zuwa daddy yace wai meke faruwane kam
Nan TJ yafada masu abinda yafaru yace shine dai sanadin sumansa
Sannan TJ yace dan Allah daddy kuyafe masa wlh yayi nadama kuma yanzu damuwarsa qaruwa zatayi matuqar baku yafe masa ba
Daddy yace hakane Allah ya yafemu gaba daya ya kuma kiyaye na gaba
Dik suka amsa da amin
Suna nan zaune ahankali ya fara motsi
Kadankadan idanunsa suka washe yafara ganin komai tass
Aiko yana ganin su momcy sai yafara hawaye zaiyi magana
Daddy ya kamo hannunsa yace kada kace komai Alamin munyafe maka duniya da lahira saifatan wannan yazama darasi agareka
Momcy ta matso kusa dashi tana shafa kansa tace ya wuce papa ka kwantar da hankalinka sannan matakin daka dauka akanta yayi daidai Allah yasaka maka sukuma Allah ya shiryesu
Cikin jin dadi ya yunqura zaune yace nagode daddy na gode momcy nagode sosai
Momcy tace sai mutafi gida tunda yasami sauqi
Daddy yace muje amaidaka gida sai muwuce
Girgiza kansa yayi yace bazan iya zama acikin wannan gidanba ni gida zan koma
Momcy tace toh shikenan kutaho a motar tijjani inyaso sai kuje kadauko kayanka
Ahankali ya miqe TJ na riqe da hannunsa har mota
Momcyma gida suka wuce Sukuma suna zuwa gida basu tarar da juhaina ba
Nan TJ ya hada masa kayansa suka fito sai anan yayi magana yabawa maigai key yace idan tazo kwasan kayanta ya bude idan tagama ya kulle ya ajiye key din awajensa
Suna tafiya a mota ba mai magana acikinsu
Papa ya kwanta ajikin kujera ya tallafe fiskarsa da hannunsa yayi nisa cikin tunani
TJ yace haba man karage tunanin nan mana haka yanzu ai saidai ka godema Allah tunda kagane gaskiya sannan Allah ya toni asirin munafukai
Cikin damuwa yake kallon TJ yace man damuwata fauziyyah tafi qarfina ta wuce tinanina fauziyyah ta nuna batama sanniba yazanyi wlh idan ban auri fauziyyah ba mutuwa zanyi sabida ina sonta sonda bantaba jin inayima wata ya maceba aduniya ashe juhaina ma ba sonta nakeba fauziyyah nakeso na yaudari kaina nan idanunsa suka sake kadawa sukayi jajur
Cikin mamaki TJ yacecfauziyyah kuma a ina ka ganta
Nan yafada masa iya abinda yasani da haduwarsu
Tirqashi shine abinda TJ yafada dan yasan tabbas zaayi haka rananda papa ya komwa fauziyyah da sunan so
Papa cikin damuwa yace komai ya jagulemun man,kyiu wati hai bahaa??? Kyiu kyiu (mai yasa wannan canjin yanayin maiyasa maiyasa) ya qarashe maganar kamar zaiyi kuka
TJ yace komai zaidaidaita kaci gaba da addu a kakuma kwantar da hankalinka
Maganar fauziyyah zamu zauna muga yadda zamu bullowa abin
Da haka har suka qaraso gida...
*****
Fauziyyah kuwa tana wucewa awajen tamanta da shafinsa dan sam baya gabanta sannan tunaninsa tsabar tsanan data masa batayi
Qarfe uku ta iso gida sai dai bakowa su momcy basa nan
Wanka tayi ta daura alwala
Sai datayi sallan laasar sannan tayi kwalliya ta shirya cikin wata doguwar riga yar kanti lokacin da zata dawo nigeria tasayeta
Coppee da milk tasha ado mai kyau
Bata saka dankwaliba sai gashinta data kama da milk ribbon ta fesa turare tafito
Tana zuwa falo taga momcy tadawo tace sannu da dawowa momcy
Momcy tace yawwa kindawo baki samemuba munje asibiti ne papa bayada lfy amma ansallamesa ma
Allah ya sauwaqa shine abinda ta furta albarkacin momcy
Momcy tace naga motarki shine na leqa dakinki kina wanka
Tace eh wlh sai danayi sallah tukun nafito
Momcy tace kinci abinci kuwa
Yanzu zanci ta amsa
Kai daugther bakyason cin abinci ko mai yasa toh kije kici
Toh ta amsa sannan ta wuce dinning taci abinci
Falo ta dawo ta zauna kenan su papa suka shigo
Aiko yana kyalla idonsa akan fauziyyah yaji wani sanyi aransa dan baqaramin kyau tamasa ba
TJ ma haka yake kallonta da mamaki ya kuma jinjina abin lalle akwai aiki agaban abokinsa dan yada ko kanta bata dagoba bare tasan da shigowarsu saima wayarta dataketa latsawa
Momcy tace sannu tijjani Allah yabar zumunci papa kushiga mana katsaya anan
Wajema yasamu yazauna yana cewa aa zansha iska kadan anan
Fauziyyah kuwa kamar ta bar wajen amma sai taga kada ya rainata kawai ta matse abinta
Acikinsu ba maimagana dan shi papa kallonta ma yasashi farin ciki sai yaji tsoro kada yamata magana tama bar wajen shiyasa yaja bakinsa ya tsuke
TJ kuwa shakkar mata magana yake kada shima tace bata ganeshiba
Wayarta ce tafara ringing dubawa tayi taja tsaki axuciyarta ganin no Brr.Nabil ne
Yau batasan iya adadin kiran daya mataba kuma bata dauka ba shikuma bai haqura ba
Harta katse bata daukaba sake kira yayi sai taji shaawar ta dauka kodan tasamu hanyar barin wajen
Momcy kuwa miqewa tayi tace barin turo muku da abinci
Fauziyyah cikin daddar muryarta tadau wayar da sallama jin muryarta mai sanyi yasa papa lumshe idanu.....
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
*Wai maiyasa mutane bakwa uzuri ma mutum ne? Idan kukaji shiru kunsan aidai da dalili kuma dai bazanyi typing ban turoshiba idan kuwa har hakane saikuyima mutum kyakykyawan zato masu cewa wai dan andamu nake masu yanga toh ai mai sauqine tinda ku kuka dami kanku ba nina saku ba, sabida haka saiku daina karantawa tunda ba wanda nasaka saiya karanta dole*
4โฃ8โฃ
Murmushi yayi sannan ya amsa sallaman
Cikin natsuwa tace ina yini
Fara arsa ya fadada yace lfy dan wani dadine ya lillibesa jin yadda ta amsa da faraa sannan yau har gaisuwa ya samu
Cikin murya mai sanyi yace gimbiyar mata asassautamun mana aidai ko haka na wahala
Juya idanuwa tayi cikin murya mai jan hankali tace namefa
Murmushi yayi sannan yace tinsafe nake kira baki dau wayata ba pls ko shiruma nikiyi amma dai kidauka sai hankalina ya kwanta
Hakan daya fada shiyasa ta wani qayattacen murmushi wadda ya qawata face nata tace ayyah aifa ba dagangan bane ba bani kusane kuma yanzun bagashi nadauka ba
Cikin murmushi yace hakane nagode da kika bani lokacinki amma da zaa taimakamun abani dama nazo gida mugaisa
Shiru tadanyi dan harga Allah bata san takuri amma kuma yau sai takejin nauyinsa sosai
Maganarsa ce ta katse mata tunani yana cewa ya kikayi shiru pls fauziyyah kibani dama na bayyana maki irin sonda nake maki wlh tunda nake arayuwana bantaba jin son wata mace aduniya kamar yadda nake sonkiba kuma ni inkika amince mun insha Allah zan zamar maki alheri arayuwa amma kibani dama domin kitabbatar da maganata
Jikintane taji ya mutu murus kuma ya tuno mata da wasu kalaman da papa ya taba fada mata abaya
Cikin sanyin murya tace bakomai ur always wellcome
Wani dadine ya lillibeshi yace thanks a lot my life insha Allah gobe da yamma zanzo
Cikin murya mai kamada shagwaba tace gobe kuma gaskiya is to early
Cikin rarrashi yace haba my life ai da zafi2 akan bugi qarfe amin haquri dai nazo goben kinji my life
Murmushi mai dan sauti tace ok Allah ya kaimu
Papa dayakai har wuya dan takaici dan tini ya fahimci da wani take waya
Jiyake kamar ya shige cikin wayar yazugamasa rashin mutunci dan wani kishine ya tirniqeshi dan ya fahimci ya samu waje tinda taketa zuba murmushi
Cikin qunar rai ya miqe afusace yayi side nasa
Ganin yadda ya tashi afuce nan danan fiskarsa ta canja hakan yasa TJ ya tashi yabi bayansa
Adaki yasameshi sai safa da marwa dayakeyi acikin daki
TJ yana shiga yace yadai man lfy kuwa lokaci daya kacanza
Cikin damuwa yace badole nacanba kana kallo cin fuskan da fauziyyah tamun
TJ yace haba man kada wannan ya dameka kabi ahankli mana kadaina bata ranka
Cikin fushi yace wani irin kada na damu bayan fauziyyah ta nuna batasanniba then gashi tana hira da wani awaya harda yimasa murmushi haba haba
Ya qarashe maganar kamar zaiyi kuka
TJ yace pls man cool down ur temper komai zaizo dasauqi da yardar Allah ammafa saikabi komai ahankali kuma daki2
Cikin sauri yace kamar me kenan pls tell me abokina wlh ruwan kaina ya qare i dont know what to do
TJ yace zauna kaji yadda zamu bullo wa lamarin
Zama yayi ya paying full attention nasa akan TJ
TJ yace dafarko abinda nakeso dakai kasauqe dik wani abinda kakeji dashi agefe sannan ka cire saurin fushi kadau hakuri kasa ma ranka
Wannan shine matakin farko dan dole sai kayi haquri
Sannan kasameta anatse kabata haquri akan abinda kamata kanemi yafiyarta dan inba hakaba bazaka taba samun fiska awajentaba matuqar tanajin haushinka tana kuma tuna abinda ya faru abaya
Amma idan har tayafe maka ta haqura to komai zaizo dasauqi
Papa yace wlh nima inada niyyar bata haquri saidai bansan ta ina zan fara ba tunda lokacin data gannima cewa tayi bata sanniba kuma wlh abin yacimun rai ya dameni kuma ya dagamun hankali
TJ yace tafada ne kawai sabida tanajin haushin abinda kamata shiyasa nace kafara bata haquri tukunna
Sannan katattara dik wani halin banza ka zubarshi agefe wannan shaye shayen banza da wofin ka haqura dashi dan ba macen arziqi da zataso mijinta da wannan halin
Papa yaja wani dogon numfashi yace hakane kamtunba yauba dama komai ya ficemun arai kuma dayardar Allah nabar shan komai tinda suma basa qaran mutum da komai
TJ yace good abokina naji dadin yadda ka yadda da shawarina da haka harya kwantar masa da hankali kafin yamasa sallama ya wuce
Fauziyyah kuwa cikin qunan rai bayan takashe wayar ta nufi dakinta dan aduniya ta tsani abinda zai tuno mata da papa baran tasashi a idanunta
Washe gari da safe papa baiko tashiba ta wuce hospital abinta sai 3 kafin ta dawo gida
Bayan tayi sallah taci abinci sannan ta tsantsara kwalliya sosai
Wajen qarfe biyar saiga wayar Brr. Nabil kan cewar ya iso fa
Mayafinta ta dauka sannan ta fice
Wani murmushi tasake sabida yadda yamatuqar birgeta
Yana jingine jikin motarsa fara tass , sanye yake cikin wani danyen boyel mai kyau da tsada farare sol wanda sin matuqar amsanshi
Fularsa ta dace da kayan jikinsa haka takalnan qafarsa farare sol, hannunsa daure da agogon azurfa sai kyalli yake
Haka kurum taji ya matuqar birgeta dan harga Allah tana matuqar son mutum mai kamala da shiga ta mutunci
Ahankali cikin takunta mai natsuwa harta qaraso wajensa sallama tamasa cikin siririyar muryarta mai dadin sauraro
Lumshe idanunsa yayi ya bude ahankali dan ta tafi da dikkan tunaninsa kwalliyarta kyan fiskanta uwa uba dirinta sannan daddadan muryanta su suka qara narkar masa da zuciya
Waalaikumussalam barka da fitowa sarauniyar mata
Murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta ahankaki tace ina yini
Lfy lau ya gida da aiki
Tace dik lfy lau ya naka
Yace well um gaskiya aikinmu ba dadi sai dai shukrah
Tace ayyah Allah ya taimaka, Amin ya amsa
Gyara tsayuwarsa yayi yana cewa yau gani ga gimbiyata dafatan zan samu mazauni acikin zuciyarki
Murmushi kawai tayi batace komaiba dan nauyinsa takeji sosai
Nan yasake gabatar mata da kansa ya kuma tabbatar mata ba dawasa yakeba kuma bashida mata dan baitaba aureba
Cikin gamsuwa da baya nansa tace bakomai amma yabata time tadanyi nazari
Yace badamuwa ya bata kwana biyu ammafa zai ringa kiranta suna gaisawa awaya tace badamuwa
Papa ne ya shigo gida kamar wadda akace ya duba gefensa kawai yaga fauziyyah da wani mutum atsaye sai faman kallonta yake yana murmushi kamar zai cinyeta
Nan take yaji qirjinsa ya buga wani kishi ya taso masa,jiyake kamar yaje shaqesa
Da kyar ya lallami zuciyarsa yayi parkin motarsa ya fito
Cikin gida ya wuce zuciyarsa adagule
Brr Nabil yace to madam nizan wuce naga kamarma na takureki kinyi shiru bakiyin ko magana
Dubansa tayi aa nibaka takurenba kawai dai nagajine yau awajen aiki
Yace eyyerh kishiga gida kihuta toh inyaso da daddre zankiraki
Tace toh nagode sosai Allah ya kiyaye hanya agaida gida
Insha Allahu zasuji bude mota yayi ya miqo mata wata shopping bag mai kyau baby pink colour yace ga wannan bayawa kisha swt
Aa nikam kabarshi nagode
Bata fiska yayi da sigan lallashi yace haba dai pls kikarba badanniba
Yadda ya tsareta da idanuwansa yasa tasa hannu biyu ta amsa tace nagode
Yawwa dear saikin jini yafada yana tada motar
Itakuma juyawa tayi ta nufi cikin gida tana bude qofar falo zata wuce taji anjawo veil nata hakan yasa tayi saurin juyowa
Papa kuwa tunda ya shigo ya gagara shiga ciki dan gaba daya jiyake kamar yaje shaqe wanda yaganshi yana tsaye da fauzinsa
Ganin papa ne yasa ta tsuke fuska tace lfy malam wani abu kake nema
Dubanta yayi da kyau cikin shan mur yace wayene waccan dana ganku tare
Kallon uku saura kwata ta watsa masa tace mene damuwarka da son sanin wayeshi kumama kaidin wayene dazaka tsareni kanamun wasu silly question
Cikin zafin zuciya yace au bakisan niba kikecewa ma
Tace eh banma taba ganinka tunda kadamu kaji wayeshi mijin dazan aurane ar u satisfied now
Yace lalle kinyaudari kanki barin fada maki bakida miji saini kuma ke matata tace sabida haka da kin daiba yaudarin kanki
Wani murmushi tayi na takaici tace Allah ya sauwaqa ni nazama matarka kuma ma kaga mundace dakai ne
Kadubi yanayin Brr. da shigarsa ta mutunci da kamala shine yadace da mijina ba kai wadda ko shigar mutunci baka iyaba dan shayeshaye kawai mazinaci Allah ya mun katangar qarfe tsakani na da kai kuma ni kadaina iqirarin matarka ce bansankaba bantaba saninkaba arayuwata tana fadin haka ta wucesa abinta .........
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
August, 2017
4โฃ9โฃ
Jikinsane yayi sanyi jin yadda take fadan munanan halayensa wadda ashe tana riqe dasu acikin ranta
Yadan jima kafin ya nufi side nasa cikin tunani kalakala
Zama yayi yana nazarin hanyar da zaibi ya wanke kansa awajen fauziyyah
Yanason ya shafe dik wani tunanin dake akansa na halayen banza ta daukeshi a mutumin kirki
Shiru yayi yana nazarin hanyar da zaibi kuma tabbas dole ya dauki shawaran da TJ yabasa idan yanason gane kanta tinda haryanzu tana riqe dashi da abinda ya mata acikin zuciyarta
Cikin sanyin jiki ya dauko wayarsa ya lalimo layin TJ yafa kira
Bayan sun gaisa papa yace TJ pls gobe irin 10am inason karakani wani waje mana
Ok Allah ya kaimu ya jikin dai
Dasauqi sosai thanks saimun hadun
Yana ajiye wayar yafara tunanin gara yafara shigan mutanen kirki wataqil fauziyyah tacanza tunaninta akansa tunda har take kwatance da wani
******
Itakuwa tana wucewa dakinta ta shige zuciyarta namata zafi cos tunawa da irin azaban da papa ya mata abaya
Allah ya qara ta furta afili dan momcy ta bata labarin matar papa
Tunani take wani irin mataki zata dauka akan katsalandan dayakeson ya mata arayuwarta
Shiru tayi kafin ta miqe ta shige toilet dan kanta harya mata nauyi gashi dama a gajiye take
Washegari bayan papa ya fita office ya dan duba patients nasa ten thirty ya fito ya nufi office din su TJ
A office ya sameshi yace ya zamuje ne ko kana da ayyuka mubari sai da yamma
TJ yace ina zamuje ne kam
Papa yace inda kake sayan kaya daka rakani saimuje wajen tailor naka dinki nakeso amun
TJ yace lalle nayarda abokina kacanza
Papa yace wlh jiya fauziyyah tafadamun abinda