Showing 15001 words to 18000 words out of 85942 words

Chapter 6 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt

26 Oct 2025

369

amaka auren dole.?

Dan dariya kawai sudeis yayi. Wanda hakoran sa farare suka bayyana. Bai ce masa komai ba, Sai ma rufe akwatunsa da yayi. Ya gama shirya kayansa na koma wa gidah tsaf.

“Allah ya shrya mun kai Sudeis.?

“Aamin...? Ya amsa Hammad, Hade da yin gaba. Hammad yabi bayan sa suka nufi dakin taron da za’a basu sakamakon karatun su na doctorate degree.


**KING FAHAD TWIN THEATRE**

Sannu a hankali aka fara gudanar da shirye shrye, Addu’oin fara taro, Gudanar da manyan bak’i, sauraron karatu daga manyan dalibai, Refreshments (Lemo da sauran su) sai kuma awarding na certificates.

Sannu ahankali karatu yazo kan sudeis ibn Harith. Ahankali cikin zazzakar murya tamkar ana busa sarewa yafara karatu bil tartil wal tajwid. Lamarin sai wanda ke sauraro. Nutsuwa da wani Irin dad’i ne ke shiga zukatan masu sauraro. A haka ya cigaba da karatun har ya kai ayar karshe ta cikin suratul-Al-Baqrah.

‎“لا? يُكَلِّفُ

‎اللّه? نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ

‎رَبَّنَ? لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلاَ تَحْمِلْ

‎عَلَيْنَ? إِصْراً كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلاَ

‎تُحَمِّلْنَ? مَا لاَ طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا

‎أَنت? مَوْلاَنَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ {286

Duk wasu haruffan tajweed sai da Sudeis ya fitar da su. Cikeda nutsuwa ya karasa har k’arshen ayah. Sannan yayi sallama ya ajiye. Wuri ya dau tafi da kabbara.

Kusan mai karatu yasan cewar dole akwai kyauta ta musanman da zaa yiwa Sudeis sakamakon kasancewar sa dalibin daya kere sauran dalibai ‘kwazo, Da kananun shekarun sa ya sami mallakar certificate na digiri na biyu a fannin islama da shari’ah, gurbin matakin karatun sa na masta kuma yayi shine akan Fiqhu da tajweedi, Sai matakin digiri na farko akan fannin zallar ingilishi, Sai professional diploma akan zane da fikira.

Anci ansha anyi hani’an kuma. Kyaututtuka da sudeis ya samu kuwa har bayar dasu yayi don tsabar yawa. Da dare aka shirya liyafar abinci.

Washe gari da safe, SUDEIS Ibn Harith ya biyo jirgi zuwa ‘kasaarmu ta gado........


#Ayi hak’uri dai, Muna shimfidar labarin ne, Zamu shiga gundarin labarin In Shaa Allah!💯❤️
Afuwan da rashin post akai akai, Yawanci kunsan uzurin. Idoooooo😹👏🏼💯 AFUWAN #ONE LOVE🥰😍

#pls follow/like and refer my scented product to your beloved ones🥰🔥💯🍓
Instagram:yerwaincense_and_more
Muna sales. Tun daga 4 ga December zuwa 10 ga watan sabuwar shekarar 2022 watan janairu/January Insha Allahu. Mun cire kaso 30 na kudin kayayyakin mu. Akwai kuma kyauta ta musanman ga wanda suka saya kaya daga dubu 7 zuwa sama.

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
1/31/22, 18:36 - Buhainat: Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SDZ*

*NANA HAFSATU*

*9*

*RIMIN KEBE*
(GADA MAI DOYI)

**A bakin titi motar tai parking sakamakon kwatocin da suka cika dan karamin layin, gashi idan motar ta shiga ma babu isasshiyar hanyar wucewa dole tasa su tsayawa daga bakin titi. Matar ta fito ita da wata yar budurwa da baza ta gaza shekara goma ba, sai wani matashi da shine ya tuko su ga kuma mugun kamanni da suke yi da matar alamar dai danta ne na cikin ta.

Kai tsaye suka shiga longun suna ta yar hirar su mutane na ta binsu da kallo. Kalle-kalle matar ta shiga yi tana kuma yiwa saurayin tana cewa.

“Tambayo mana kace gidan Ardo dan tabbas nan ne layin gidan na kasa gane wanene ne kawai.?

Ibrahim ya juya bayan ya zuba hannuwa a cikin aljihunsa ya isa wajan wasu samari dake shan rake, sallama yayi musu tare da basu hannu suka yi musabaha ya kuma tambayesu gidan Ardo daya daga cikin samarin ya nuna masa da hannu. Ibrahim yayi godiya ya koma wajan mahaifiyar su suka karasa har cikin gidan Ardo.

“Assalamu alaikum.?

Duk matan suka amsa tare da zubawa kofar ido suna jiran ganin mai sallamar.

“Shigo.? Atuwa ta fada tana gyara kujerar kusa da ita.

Shiga suka yi banda Ibrahim shi sai ya tsaya a zaure, ganin wata matar daban ba wacce suka zo nema ba yasa matar tsayawa daga kofa tana gaishe da Atuwa tare da gaishe da Jimmamman dake wanki a kofar dakinta.

“Dan Allah ba nan bane gidan Ardo.??

“Kwarai kuwa nan ne, ai gidan nan ba boyayye bane indai kika zo gada mai doyi kika ce gidan Ardo aure-aure sai an kawo ki gidan nan.?

“Allah sarki, Jammu fa bata nan??

Jin ba gurinta aka zo ba yasa Atuwa komawa kan kujerarta tai zamanta tare da ci gaba da tankadenta da take yi. Sai Jimmamman ce tace.

“Tana dakinta.?

Dada dake cikin daki tana dinkewa yan biyun ta kayan su da suka yage da zare da allura, jin an ambaci sunanta yasa ta saurin tashi ta leko dan ganin ko waye.

“A'ah lale marhabun Hajiya ku shigo daga ciki.?

“Oh Jammu ashe dai kina cikin gidan nan har yanzu??

Tayi maganar tana cire takalminta ita da yarinyar da suke tare.

Atuwa ta dinga tabe baki tana mamakin yadda akai Jammu tasan irin wadannan hadaddun hajiyoyin. Gabaki daya ita kuma ta rasa abinda zata shimfida musu wanda zata fita kunya ta rasa, dole yar yaloluwar tabarmarta ta shimfida tana faman sosa kanta. Zama tayi ba tare da ta nuna jin kyankyami ba sai ma kallon dakin da take yi ganin duk babu kaya sai tarkacen bakkuna kamar dakin tara bololi. Babu abinda take tunawa irin yadda suka kawota tana amarya daki cike da samiru, kwallaye da jeran combo manya da kananu amman yanzu duk babu ko ya tayi dasu oho.

“Hajiya barka da zuwa, ina yini?"

“Lafiya lau Jammu, ya bayan rabuwa?"

“Sai godiya Hajiya."Dada ta fada tana tunanin kofin da zata zuba mata ruwa.

“Rabon da nasaki a idona tun ranar arba'in ɗin mahaifiyarku, lokacin kina goyan yarki ta farko Zaarah, wai kuwa tana ina??

“Allah sarki, tana nan taje nan makota yo aikin gida (Home work) da aka basu a makaranta.?

“Allah sarki nasan yanzu ta zama budurwa ko Jammu??

Kafin Dadaa tayi magana Zaarah tayi sallama.

“Kin ganta nan ma ta dawo yar halak.?

Hajiya Amina tabi kofar da kallo fuskarta kushe da fara'a har Zaarah ta shiga dakin da sallama. Tana shiga har kasa ta gashe da matar cike da ladabi da biyayya.

“Masha Allah Tubarkallah Jammu wannan ce Zaarahn? Lallai ko a hanya bazan ce ita bace masha Allah kyakkyawa da ita.?

Duka daga Dada har Zaarah babu wanda yace komai saboda nauyi, kuma idan da sabo sun saba jin haka yadda mutane da yawa basa yadda cewa itace ta haife ta saboda tsananin kyawunta tamkar ba haifaffiyar gidan ba.

“Oh Jammu haka kika bi kika lalace? Duk ina soyayyar da Ardo ya dinga zuba miki lokacin da yana zuwa tadi? Wallahi yauma wucewa zamuyi ta nan, nace da Ibrahim akwai wata yata a nan ya kawo ni mu gaisa tunda ke bakya neman mu. Kuma kinsan tsakanin mu da Iyami bata da aminyar da ta wuce ni, tsakanina da Iyami babu bye-bye hakan yasa ma ban manta dake a nan wajejan ba.?

Dada tayi kasa da kanta tana jin kamar tayi kuka, Hajiya Amina aminiya ce a gurin mahaifiyarta, duk wani kaya na aure rabinta Hajiya Amina ce ta yiwa Dada saboda amincin dake tsakanin su. Ita kuma abinda yasa bata nemanta dalili ne mai yawa, ita tana rimin keb'e yayin da hajiyar take Nasarawa babu ta yadda za'ai ace tana zuwa, dan bata son shiga cikin irin wanda suka fita arziki gudun rai ni da wulakanci. Amman tunda gashi yanzu tazo itama kila wata rana taje mata ziyara matsayinta na uwa a gare ta.

“Zaarah ya karatun??

“Lafiya lau.l

“Kin sanni??

“A'a.? Cewar Zarah cike da jin kunya tana rufe ido.

“Kinji ko Jammu, jikar tawa guda amman bata sanni ba.”Dada ta kalli Zaarah kafin ta kalli Hajiyan tana cewa.

“Wallahi Hajiya ta sanki ganinki ne kawai batai ba sai yau.? Ta sake kallon Zarah.

“Zaarah ba nace akwai wata kakarku ba a unguwar Nasarawa?? Cikin tunawa da nuna tabbaci Zarah ta zaro ido tana bude baki tace.

“Au lahhhh Dada daman itace Hajiyan Nasarawa??

Jin haka ya tabbatarwa da Hajiya Amina cewa Jammu tana bawa yaranta labarin su.

“Eh itace gashi har tazo ina ta cewa zamu je ku ganta.?

“Yau kam gani nazo jekalle, tunda babu rayuwar Iyami ai kamata yayi ni a maida ni gurbinta, amman sai kuka watsar dani Jammu, to banyi fushi ba ina Ardon yake??

“Baya nan Hajiya.? Cewar Dada.

“Wadancan matan kuma fa Jammu?? Hajiya ta tambaya dan ita bata san kowa ba a cikin su.

“Abokan zama na ne.?

“Oh ai mun gaisa dasu, sai dai ban gane uwar gidan ba, kinsan lokacin da muka kawoki bata gidan aka ce taje kauye.”Dada tayi kasa da murya gudun tada fitina.

“Ta zaune a kofar dakin tsakiya itace Atuwa sai dayar da yayo kwanan nan, kinsan akwai wace ta rasu matarsa ta farko wace bayan ita ne ya auro Atuwa sannan ni sai kuma wadanda yake aura suna rabuwa.?

Daga nan fa hira ta balle Zaarah ta ja Badiyya yarinyar da Hajiya Amina tazo da ita wacce jika ce a gurinta suka fito tsakar gida. Su Dadah sun jima suna maganar rayuwa da yadda komai ya lalace musamman yadda mata ke rayuwa da irin su Ardo. Hajiya Amina tace da Dadah.

“Idan Zaarah ta kammala J.S 3 din zan aiko a dauke ta taje tayi S.S 1 to 3 a guri na, duk da nasan a dai dai wannan lokacin kinfi kowa don ganinta a gurinki. Amman karatunta ingantacce shine dadin dad'awar jin dadi da kwanciyar hankali, kuma idan Allah ya taimaka kafin tai aure kin fara cin moriyar hakan. Kici gaba da yi mata addu'a Allah ya tsare miki su a duk inda suke.?

Hawaye suka zubowa Dada ganin tsantsar halacci irin na Hajiya Amina, mace mai yi dan Allah ba dan ace tayi ba. Kasa koda motsi Dada tayi har sai da taga Hajiya Amina ta mike tana yi mata sallama, cike da jin nauyi Dada tace.

“Gashi ko ruwa baki sha ba Hajiya.?

“Karki damu, ai da zan sha zan sanar dake. Idan mai gidan ya dawo ace ina gaishe shi, ga wannan.? Ta bada dubu biyu tace.

“Ki bashi ba yawa abin ne sai a hankali. Wannan kuma naki ne.? Ta mika mata dubu biyar tana nuna mata yan dari biyar-biyar tare da cewa.

“Wannan idan zan fita zan bawa kishiyoyin naki, Allah ya baku zaman lafiya.?

Dadaa ta dinga godiya kamar zata hadiye ta dan jin dadi, suka fito tare Hajiya Amina ta bawa Atuwa dari biyar ta bawa Zaarah ta mikawa Jimmamman na ta, suka dinga zabga godiya kai kace ranar suka fara taba kudi a rayuwarsu. Sosai suka yi sallama Dada ta koma ciki Zaarah kuma ta raka su har mota, daman tun dazu Ibrahim ya koma da yaji basu da niyar fitowa.

Gashe shi Zaarah tayi tare da yiwa Hajiya godiya suka ja mota ita kuma ta koma gida. Daman suna fita Atuwa ta kalli Dada tana washe baki tace.

“Jammu mu an bamu dari har biyar, ke kuwa nasan kin samu kusan dubu goma ko??

Dadaa tayi murmushi kawai ta shiga daki bata ga dalilin jin ba'asin nawa aka ba ta tunda itama ba tambayarta take yi ba. Ranar sunci abinci me dadi sun kuma siyo abinda suka fi bukata na amfaninsu.

#pls follow/like and refer my scented product to your beloved ones🥰🔥💯🍓
Instagram:yerwaincense_and_more
Muna sales. Tun daga 4 ga December zuwa 10 ga watan sabuwar shekarar 2022 watan janairu/January Insha Allahu. Mun cire kaso 30 na kudin kayayyakin mu. Akwai kuma kyauta ta musanman ga wanda suka saya kaya daga dubu 7 zuwa sama.

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
1/31/22, 18:36 - Buhainat: _*Mierah's dukkan_*
_*Mierah’s dukkan_*
_*Mierah’s dukkan_*

_(Palace of exotic scent and more)💯❤️_

_MD: is ur plug! Muna siyarda kaya kala2 kamar jaka da takalmi kamfanin lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers 'yan yyi dominku da yaranku,Muna order kaya dga kasashe daban-daban,Muna siyarda da kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr suratti,Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria. Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi ku tuntube mu awannan nmbr kamar haka wa.me/07039773001 Muna turawa ko Ina afadin Nigeria da wasu kasashen ketare ngd_

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SDZ*

*NANA HAFSATU*


*10*


*AMINU KANO INT. AIRPORT*

***Jirgi na gama saisaita kansa, Su Sudeis da sauran fasinjoji suka fara fitowa daga ciki. Sudeis ya shaki iskar Allah yana sake lumshe idanun sa. Ya sakko daga matattakalar benen jirgin bakinsa dauke da addu’oin godia ga Allah daya kawo su lapia. Sanye yake cikin jallabiya kalar royal blue. Da dishi’dishin kalar toka a hannayen. Sai ya zamto yar hular kansa da takalmin sa kai dama agogon dake daure a wutsiyar hannun sa duk kalar tokan ne. Idanun sa saqale cikin wani farin gilashi daya karawa fuskar sa kyau da cikar kamala.

Sai bulala kamshi yake yi. Haka ya karasa cike ciken takardu, Tukun sannan ya janyo akwatin sa da kuma wata yar jaka mai dauke da littattafan sa. Yana tafe bakinsa dauke da addua, Har ya karasa fita zuwa waje. Wani mai taxi na gefe yana ‘barar gyada yana afawa a baka.

“Yallabai tafiya ne?? Ya tambayi Sudeis yana mai tafiya zuwa inda yake.

“E...Eh?

“Toh muje ko. Kawo kayan a saka a baya.? Ya fada hade da d’aukar akwatin gaba d’aya ya zura a booth. Kafin ma sudeis din ya bashi umarni.

“Yauwa to abokina shigo mu wuce ko??

Bayadda Sudeis ya iya. Haka ya bude kofar gaba ya shiga. Mai motar sai jansa yake da hira. Shi dai ya shiga amsa shi dakyar. Saboda shi mutum ne da baya da son magana, Bashida hayaniya kwata kwata. Ko da yana karami bashida abokin fad’a.

“Yallabai ina zamu je ne..?? Cewar direban, Hannun sa d’aya akan sitiyari, Dayan kuma yana gwaiwayar dafaffiyar masarar daya siya a hold-off.

“Suleiman crescent...? Ya karasa fada yana mai jan kasan leben sa ahankali.

“Heda ka fada na hango kamar ka da yan unguwar. Alkur’an. Hyar da ku. Kai alaji kudi yayi.?

Shi dai Sudeis kanzil baice ba. Sai ma kambama kokarin zubar zancen direben da yake. Tamkar ‘ya’yan kanya. Tunda ya hau motar direben ke fetsa masa zance. Dai dai da sakan d’aya bai yi shiru ba. Kuma ko kadan ‘kin amsa shin da sudeis yake, Hakan bai kwab’ar da bakin sa ba. Sai ma kara sautin muryar sa da yayi. Ya shiga ratattakowa sudeis din tambaya.

“Aboki na ni kuwa ya labarin tsohon dan siyasar yankin unguwar ku da efcc ta kame??

“Wa....??

“Aban nan, Uhm... Kaji sunan sa, Kai mts! Allah ya tsinewa mantuwa. Kaji sunan mutumin nan daya handame kudade. Yauwa Hannafi Na Galluwa.?

“Ban...San.. Bansan shi ba.?

“Kai haba dai? Na galluwan. Yo ai ko a cikin karkara ba maraya ba. Ba wanda baisan hi ba. Domin na galluwa yayi nisa. Amma aboki na ka jima baka kasar ko??

“Eh.....”Ya amsa shi can kasan mak’oshi.

Duk da haka direban bai daddara ba, Yai ta kwararawa Sudeis zance ba kakkautawa, Tundaga airport road har nassarawa GRA (suleiman crescent). Dai dai wani katon gidah mai shudin fenti Sudeis yace direban ya tsaya.

Chanjin kudin najeriyar da Hammad ya bashi jiya ya ebo masu kauri ya mikawa direban.

“Du ni d’aya Yallabai??

Sudeis ya kad’a masa kai alamun Eh. Yai saurin shigewa cikin gate din gidan bakinsa dauke da sallama, Don bayason ma ya tsaya yi masa godia...


**GIDAN ARDO (AURE-AURE)**
(BAYAN SHUDEWAR WASU WATANNI)

Jimmamman na daga tsaye akan Ardo yana wanke mata kayan ciki. (Undies) Atuwa na daga gefen dakinta, Ta dora Farillatu akan po tana kashi. Ta kece da dariya tana bubbuga kafafu.

“Allahu Akbar kabeeran! Bana su o’o an debo ruwan dafa kai. Ahhaha caran chasss.?

Jimmamman taja tsaki tana mai zama a kofar d’akinta.

“Mace tafita a idanu na wallahi. Gayyar tsiya.?

“A hayye landantsan. Wai mai cikon duwaiwaice zata jefe ni da kalmar tsiya. Nafi karfin mai ciko billahil lazi. Yanzu sai na yage zani na caskala ‘ya.?

Haka dai sukayita jefawa juna maganganu. Ardo na duke yana wanke kayan cikin Jimmamman.

“Aina zan shanya ne?? Ya tambayi Jimmamman yana katse gumin dake sharara a fuskar sa. Sakamakon ranar da ake.

“Sannu Nawan. Allah dai ya bamu ikon sauke cikin nan lapia. Kai ma ka samu ‘da namiji a karo na biyu, ka huta..?

Ardo ya dashare baki, Jin ta sake tuno masa da samun karuwar namiji da zata haife masa. Haka ya tattaya Jimmamman gyare koina tas. Sannan suka shirya zuwa asibiti awo.

“Jammu mun fita. Idan nayi bak’i kice musu munje awon jaririn mu..?

“Toh auntyn su? Cewar Dada dake daga cikin dakinta tana sauraron shirin da ake a rediyo.

“Toh Maman mata mun fita ko.?
Cewar Jimmamman ta datsawa Atuwa magana.

Atuwa tayo kanta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login