Showing 63001 words to 66000 words out of 85942 words

Chapter 22 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt

26 Oct 2025

373

ubanki ne ya sai gidan sai ki sani na fita. Allah ya kwashe miki"

"Ya kwashe maka albarka dai. Ba kai aure aure ba. Ana zugaka kana dashare fuska. To ka aurowa kanka. Gida ya badu. Sai a rankaya a koma kauye. Don kuwa ni gaba nayi. Jammu Allah ya dasa mata kwandon arziki tayi aurenta na arziki . Shar da su itada yaranta. "

"Banason wasa Rumalle. Na shika ki sau daya. Kar ki tunzuro na Kara wani shikan akan wani."

"Kara 100 ma. Gida ya zama nawa. Daren farkon mu ka gayamun naje dakin Modibbo na dakko acikin jaka."

"Banda haukan ki a ina ake kyautar gidah sukutum?"

Kafin Rumalle tayi magana. Atuwa ta dire tsallen albarka hade da daga hannu sama ta kwakwaso rantsuwa kai kace ita aka bawa gidan. Ta nanawa cinyar ta duka. Hadi da rangada guda. Ta sauke aiyiriri a kunnen Ardo. Hade da cewa

" A hayye landantsan tsan. Allah mai alheri. Wabillahil Rumalle taci gidah. Kyauta ta badu. Ba Kai zamudin.aure ba. Daren farko ka yiwa amaryar ma kyautar gidan ka jallin jal da Allah ya baka. Hau ta hau Arddo. Mijin Atuwa sahibin jimmamman. Ubansu Zaraah angon Rumalle mai gidah. Kayya kaiiiiiiiiiii"



Masu tambaya. Duk books Dina Banda paid suna wattpad: missxoxo00

Instagram: @yerwaincense_and_more


XOXOWRITES 💯❣️
2/12/22, 11:37 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SO DA ZUCIYA*

*NANA HAFSATU*


*34*


Ardo takaicin Atuwa da ke zakalkalewa yasa shi jan dogon tsaki. Hade da kutuntumo ashariya ya 'dure akan Atuwa.

"Bak'ar munafuka. Allah ya kwashe miki albarka Atuwa."

Atuwa ta sheke da dariya. Kafin ta rangada guda ta saki. Jimmamman na daga tagar wundo tana leken su.

"Ba kai uban aure ba. Kana yiwa Allah shisshigi kan haihuwa. Bakayi maraba da yara matan da kake dasu ba. Ka dau kaunar son yaya maza tamkar su din martabar su daban ce. 'Dayan da Allah ya albarkance ka dashi ka dau son duniya ka dora masa. Ka tsani sauran yaranka mata. Har fada kake a baya kan cewar idan Modibbo ya tashi aure zaka dau gidan nan ka bashi. Mu kuma mu koma kauye ko ka shika mu. Toh gashi nan yanzu hau ta hau kan k..."

"Idan kika kuskura kika karasa magana. Wabillahil sai na hau kan ki da bugu. Munafuka. Yauwa ke kuma Rumalle tsaf zan kai karar ki kotu akan wannan iskar zancen. Mahaukacin ina ne ni da zan dauki kadarata daya a duniya na baki? Ni ba sakarai bane."

Rumalle ta tabe baki. Hade da zaro rake cikin kullin gyalenta tashiga gabtara kada kai.

"Ni ba irin ka ba ce Ardo. Zan iya maka afuwar shikan da ka mun na kyaleka ka cigaba da zaman matan ka har nan da sati biyu kafin ka nemi wani muhallin ku kara gaba."

Ardo cikeda takaicin yadda Rumalle ke magana cikin gadara da isa. Ya zare raken hannunta ya take shi a kasan takalmin sa yana huci. Hade da kokawar zare rigar yar sharar dake jikin sa.

Jimmamman ta sheko a guje ganin zai yi tabargaza agaban yaran sa.

"Cika ni jimmamman. Kyale ni na chasa tah. Har ni zata kawo wa zancen banza. Agidan uwar ubanta na bata gidah?".Ardo ya shiga kokarin zare hannuwan jimmamman dake rike hannayansa. Bayan a zahiri idan an barshi da Rumalle kadai sai ta hallaka shi.

"Cika shi . Kafin na hade da ke na zaune. Agidan uwar ubanka borkindo dake Fanda ka ke. Banda tarin tsiya da abun kunya me ahalin ku ke da shi? Kaf banda ciki da waje dangin ku ne matsiyata. Wanda shanu hudu gare ku duk yawan ku. Wallahi banda kaddara meyasa zan aure ka Ardo?.wallahi ni ba sa'ar auren ka bace. Gidah Kuma ko ana ha maza ha mata sittin ta ubangiji ya zama nawa."

"Jar uban can kai. A hayye landantsan. Allah mai alheri. Yau ana wata ga wata. J"

Kasan gwiwar hannun sa Ardo ya sa kai wa Atuwa bugu a makoshi. Ta rike wuyanta tana kurma ihun zafi.

"Wato ga mareniyar wayon ka ko? Shine daga magana saboda ita tafi karfin ka daketa. Sai ni mareniyar wayon ka. Burbudin kashin duwaiwukan ka ko! Toh wallahi ban yafewa. Kuma Allah ya kwashe maka albarka. " Atuwa ta karasa fada tana mulma wuyan ta da Ardo ya kai mata bugu.

Rumalle ta mike daga zaman da tayi. Ta dau buta tayi hanyar bandaki tana yan wak'e wak'e. Tashige bandaki ba addua ba komai. Ta kwaye mazaunai tashiga kasayarwa tana waka.

" A hayye sama ruwa kasa kudi. A hayye sama kudi kasa ruwa. Wahabu wahidin lillahi. Sama ruwa kasa kudi. Katsina ta dikko ma ana maka ruwa. Sama kudi kasa ruwa. Kaduna ma ana maka r......"

Bata karasa wake waken data ke aciki ba. Ardo ya shigaa cikin bandakin ya janyota ..ko tsarki batayi ba... Domin wakar da take raira baitin ta ta karasa harzuka shi.

"Ba sama ruwa kasa kudi ba. Wallahi yau zakisan ainihin sama ruwa kasa kudi. Baki isa ba kinyi kadan ki cinye mun dukiya dan malafar kan na tsoho me allura na gangaren litiya fanda. Uban kakanki kenan. "

"Cika ni nayi tsarki kai dai kamar sabon tab'i."

"Kin gama kasayarwa acikin gidan nan tunda ba naki bane. Almura da idanu yan kanana a ciki."

Atuwa dake mulmula wuya ta kece da dariya. Kafin ta janyo gallan da Farillatu ta tsinto a shara. Ta shiga kidi tana rausaya kai.

"A hayye landantsan tsan tsan. Durama a gidan Ardo. Akan me? Akan gidan Ardo. Meya faru. Ardodo. Daren farkon su yayi kyauta. A hayye landantsan. Allah me alheri. Ku chasu bamban ku chasu. Ku chasu bame rabaku. "

Rumalle duk Ardo ya gama tukwikwiye ta yana neman bugata da kasa. Rashin wanke duwaiwukan ta da batayi ba shi yafi kona mata rai. Shysa ta kasa kokawa dashi. Atuwa ta ajiye gallon din hannunta tamike.

"Ka chikata ta wanke bahayar mana. Fisabilillahi mata tana kasayarwa kaje ka cafkota. KO kyankyami bakkai Ardo? Allah ya kyauta."

Rumalle data gaji cikin zafin nama ta tattaro kafafun Ardo ta nanashi da kasa.

"Allah me alheri " Atuwa ta fada tana sarawa Rumalle.

"Kai Usmanu ku rikemun shi kafin na fito." Rumalle ta fada hade da komawa cikin bandaki tashiga karasawa tana jan tsaki.

Su Usmanu suka hau Ardo da kokawa. Ga gam suka rike Ardo. Baya da damar kwacewa saboda tsananin yadda suka tamke shi. Idrisu kuwa ya haye saman kafafun Ardo ya zaune

"Charanchas Ardodo. Allah me alheri."

Duk kuwa da a daddaure yake. Ardo bai fasa daga kai ya dankarawa Atuwa harara ba..

"Allah ya kwashe miki albarka Atuwa. "

Atuwa ta ja yar yarkaccacciyar kujerar ta ta zauna. Sam taki tarewa Ardo saboda tsananin yadda zuciyar ta ke 'kullace da shi. Ya cire su ya ajiye a matsayin matan sa. Bayan kowacce da igiyoyi biyu akanta. Ya shika su sau 'dad daya. Yadda ya yakice al'amuran yaran sa da yaran nasa baki daya tamkar ba shine ubansu ba. Cin su. Shan su. Tufatar da su, Makaranta kai dama dik wani hakkin su da ke kansa ya tattara ya ajiye a gefe. Tun wasu na jinjirai wasu kuma tun kan a haife su ya dora tsanar su a kambun zuciyar sa.

Rumalle tafuto daga bandaki tashige daki ko takan Ardo dake mutsimutsi da hannuwa bata bi ba. Kaya ta sauya ta zura hijabi ta fice. Kai tsaye ta wuce gidan mai unguwa. Bata jima ba ta fito ta dawo. Tabarmarta ta dakko ta shimfida a tsakiyar gidan. Atuwa na ganin haka ta sake gyara zaman da tayi akan yar kujerar ta. jimmamman daii na daga kuryar dakinta a rakube.

"Ku cika shi. Ga me unguwa Nan zuwa." Rumalle tabawa su Usmanu umanrni.

Ardo cikin takaici ya fashe da kuka yana kwashewa Yan gidan baki daya albarka .. Ba jimawa sai ga zagin mai unguwa na doka sallama

"Mai unguwa Yana neman iso. Assalamu Alaikum. Mai unguwa na neman iso. "

"Shigo zagi. Ku shigo. "

Mai unguwa da zagi suka shigaa. Nan Ardo ya fesa musu komai. Rumalle ma tafadi yadda akayi. Mai unguwa ya nisa kafin yace,

"Abu na farko dai shine an kafa.maka dokar hana shikan da kake wa matan ka. Da Kuma kara karen auren da kake yi. Bayan gida bata koshi ba. Iyali ba suturar kirki da sauran su. Dole ire iren matsalolin nan su yi maka yawa. Kuma zahirin gaskia inada masaniyar kyautar gida daka yiwa matar ka Rumalle . Domin a satin auren KU. Ta kawo mun takardar shedar mallaka ta gidan nan. Ta Kuma gayan yadda akayi.

"Zahirin gaskia banidaa ta cewa anan. Domin sheda de ta jima a hannu na. Kuma bazan iya cewa kyauta ta badu ko bata badu ba. Wannan sai dai sharia tashigo ciki. Amma kafin sannan inason ka san kai ne silar faruwar komai Ardo. Yawa yawan auren ka. Shi yake sa kake shiga cikin matsaloli. Sam yaran ka mata basa gaban ka. 'Da daya tal da Allah ya baka ka dorawa kulaficin so Allah ya dauke abinsa ya bar ka da halin ka. Yanzu kai wannan kadai bai isheka ishara ba? Matar ka kuna zaune da dadi ba dadi da yaran ku a tsakani. Haka kawai akan wata figalalliyar tinkiya ka shika ta. Sai gashi ta auri wanda yafi ka komai. Itada yaranta shar da su sun bar halin rashi sun koma na samu.

"Dan mijin Kuma shike auren diyar ka . Ko wannan bai isheka ishara ba? Ko kuwa su Hajara yaran Atuwa ba auren sukayi ba? Kowacce kuma tana zaune gidanta cikin koshin lapia. Dadin aure ya sa ka bawa matar da kayi sabuwa gidan ka kacokam shi kadai daka mallaka a duniya. Nan bangaren babu abunda ya shafeni. Na tura zagi da takardar ya kai kotin gangare. Muje can ayi shari'ah

"Amma kafin sannan inason jan hankalin ka Ardo kana saurara ko?"

Ardo ya fyace hancin ssa da kasan rigar sa kafin yace,

"Ni ban bata gidah ba Mai unguwa. Mahaukacin ina ne ni ?"

"Mahaukacin rimin kebe mana. Shashasha, sakarai, Sauna. Wanda kaf rimin kebe ba Wanda aka dauka wawa gara irin ka. Kayi haihuwa tayi 10 amma gaba daya bakada hankali. Hankalin ka daya ne wajen neman aure kawai. Gaba daya bakasan falalar haihuwar 'ya'ya mata ba. Toh ka saurara kaji:

"Bincike ta bangaren tarihi da zamantakewa duk sun tabbatar
da cewar 'ya'ya mata sunfi 'ya'ya maza tausayin iyaye da yin
biyayya garesu.
Zaka iya tarar da mutum ya haifi 'ya'ya maza guda biyar ko
sama da haka duk sun girma amma abin da zai ci ma ya
gagareshi saboda duk cikinsu babu mai tsayawa ya kula da
rayuwarsa bayan tsufansa. Amma duk wanda ya haifi 'ya'ya
mata koda kwaya biyu ne sai kaga sun taimakeshi, sun tallafi
rayuwarsa komai tsananin talaucin da suke ciki.
Haihuwar 'ya'ya mata babbar falala ce daga Allah wacce ke
samar da farin ciki anan duniya, sannan ga babban sakamako
a lahira kamar yadda hadisai da yawa suka tabbatar.
Misali yazo acikin hadisi cewa Manzon Allah (sallal Lahu
alaihi wa aalihi wa sallam) yace "Duk wanda aka bashi 'ya'ya
mata guda biyu ya kula dasu kuma ya tarbiyyantar dasu, to
sune suturarsa (wato zasu kareshi) daga shiga wuta"
Koda Manzon Allah (saww) zamu ga cewa acikin jumlar
"ya'yan da Allah ya bashi, matan sunfi yawa. Kuma zuriyarsa
ma ta hanyar yarsa mace suka wanzu.
"Ya mace rahama ce, jin qai ce, baiwa ce, daukaka ce,
mutunci ce, hutu ce, farin ciki ce, albarka ce, falala ce, kuma
alfarma ce.
Kuma hadisi ya tabbatar mana da cewa:
•Amatsayinta na 'ya ('diya) tana samar wa mahaifanta dalilin
shiga aljannah.
- Amatsayinta na uwa, tana samar wa 'ya'yanta Qofar shiga
Aljannah.
? Amatsayinta na 'yar uwa tana samar wa 'dan uwanta hanyar
shiga Aljannah.
- Mace ce ta fara gaskata Annabi Muhammad (sallal Lahu
alaihi wa aalihi wa sallam) alokacin da Allah ya aikoshi.
Nana Khadijah.
- Mace ce ta fara samun darajar yin shahada (rasa rai ta
dalikin kare addini). - Sayyidah Sumayyah.
- Ta dalilin mace ne al'ummar Musulmai muka samu falalar
yin taimama idan larura ta kamamu. - Nana A'ishah.

? Mace ce ta samu darajar samun sakon gaisuwa daga Allah
(SWT) - Nana Khadijah.
- Mace ce tayi jinyar Annabi (saww) a karshen rayuwarsa ta
nan duniya, kuma a hannunta ya koma ga Allah.
- Nana
A'ishah.
- Mace ce ta haifi Shugabannin samarin Aljannah, kuma ita ta
tarbiyyantar das - Nana Fatimah.
Wani Alkali yace "Acikin shekaru ashirin da biyar (25) da nayi
ina alkalanci, ba'a ta'ba kawo min shari'ar 'ya mace wacce ta
bijire wa mahaifinta ba. Amma nasha gain 'ya'ya matan dake
barowa gidan aurensu domin suyi jinyar mahaifansu"
Nagode wa Allah, yanzu haka ina da: A'ishah, Aminah, Fatima
Mukarramah, Fatimah Munawwarah, da Ramlat.
Fatana Allah ya rayasu, ya kula min da sha'aninsu ya tsaresu
daga dukkan abun Qi, tare da dukkan 'ya'yan musulmai baki
daya. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (10/06/1441)

"ka ji manazarta suka ce. Saboda haka ka zauna Kayi tunani. Domin arzikin da kake matukar son samu a 'yayaa mazan ta iya yiwuwa ajikin 'yaya matan zaka samu ninkin fiye da yadda kake muradin so. Toh Allah ya zabi abunda yafi alheri. Yasa abunda hukuma ko ince shari'ah zata zartar ya zama shine mafificin alkhairi. Gobe da yardar Allah sai muje muji yadda zasu yanke komi. Ni bari na tashi zanje ta'aziyya can kasan mil tara."

Ardo ya mike yabi bayan Mai unguwa. Ya rakashi har kofar gidah. Mai unguwar ya sake bashi shawara hade da neman fatan alkhairi abisa abinda zai wakana a kotu. Ardo ya gangara can karshen layi ya takure. Gaba daya ya rasa meke masa dadi a duniya. SOn ZUCIYA ta kai shi ta baro shi.


×××××××××.

Bayan sallar ishai. Haj Mari . Da hajia Amina sune suka yiwa Zaraah rakiyar kai amarya. Zuwa sashen su itada Maheer. Dake can karshen gidan an sake kawata shi. Bayan sun kaita ta gaggaysa dasu Haj Jidda da Iklima da suke a matsayin mahaifan sa Mata. Dukkan su suka kasa boye hassadar su.

Kuka kam Zaraah ta shashi kamar Wadda zaa dauke daga garin.. Sun kaita dakinta tare da sake bata shawarwari akan sabuwar rayuwar data shigaa na makarantar aure.

Sun jima suna ja mata kunne. Kafin su mata sallama su tafi. Maheer dake cikin mota tun dazu. Sai a sannan ya futo ya rufe motar. Hannunsa dauke da ledoji. Ya Sha ado cikin manyan kaya kalar sararin samaniya. Ya mjrza hula zanna bukar.. yanata tashin kamshin baccarat rouge. Ya jefa mint flavored gum a bakin sa. Yana taunawa ahankali .

Ya bude kofar ya sshiga ciki. Bakinsa dauke da sallama. Tafiya yake cikin takun kasaita. Ado da kamshi sun dabaibaye ilahirin gidan dake turare da turaren wutar yerwa incense and more.. Ya bude hanci ya shaki kamshin yana lumshe idanu .

A haka ya karasa dakin Zaraah . Tana lullube cikin laffaya. Sai kamshi ke tashi hade da shesshekar kuka. Ya karasa ciki yana sallama a hankali cikin wata iriyar murya mai tattare da nutsuwa da cikar Kamala .

Ajiye ledojin yayi a bedside drawer ya karasa kusa da ita. Taja can gefe tana kara sautin kukanta sosai.

Maheer ya samu kansa da janyota jikin sa. Wata nutsuwa ta rufe su a take. Duk shure shuren da take Maheer yaki cikata. Ahankali cikin muryar lallashi ya shjga rad'a mata a kunnenta,

"Haba Zaraah . Sarauniyar mata. Kukan ya isa dan Allah. Saurare ni da kyau kiji,.Ni fa yayan ki ne. Kuma nanda lokaci kalilan zan roki su Bappah su warware auren mu tunda ba ma son....juna KO ?" Ya karashe ahankali yana danne dariyar dake son fashewa.

Zaraah tasamu kanta da daga kai. Yasaka hannun sa daya yana shafa bayanta alamar rarrashi.

"Yauwa Zaraah.. Ko kefa? Yanzu dai bari na gaya miki abunda nakeso da wanda banaso ko?"

Ta daga kai. Tayi luf tana shakar kamshin sa. Munafuka🙄

Ahankali cikin wani salo da kwarewa. Maheer ya tsinci kansa da fadawa Zaraah abubuwan da yakeso da Wanda bayaso ..ya karkare da,

"Inada wani cuta...Ana ce dashi sleepwalking a turance. Yauwa saboda kakkiga wataa rana nazo dakin ki na kwanta cikin dare. KO na Miki na wani abun daban .Ba a hayyaci na nake ba. " Ya karasa fada cikin muryar umarni Kai kace gaske ne.

"Zaraah! Kinji ko?"

"Na ji. "

"Yauwa. Kuma ta yadda su Bappah zasu yarda a raba aurenmu shine idan sukaga muna kyautawa junan mu. Bama nuna kiyayya da sauran su..zakiga lokaci daya da mun same su da maganar zasu amince. Kin gane ko?"

Ta sake daga kai tamkar gaula.. Maheer ya saki murmushi kafin ya sake cewa,

"Zamu cigaba da karasa karatun ki na islamiyya a gidah. Kafin ki koma makarantar bayan wani dan lokaci . Kinji ko?"

"Eh"

"Yauwa yar kanwata Zaraah. Allahumma Bareek!!" Ya karasa fada hade da samun kansa da sakarwa Zaraah zazzafar sumba a goshinta. Ya tabbatar wa kansa a yan kwanakin nan yafara jin wani abu game da Zaraah .

Ta janye jikinta da sauri. Murmushi ya yi ..kafin ya janyo ledojin ya bubbude su,

"Gashi kamar yadda al'ada ta tanadar. Kici ki koshi Yar kanwata . Bari Yayan naki ya tafi dakin sa. Sai da safe ko?"

Ta samu kanta da girgiza kai da sauri. Maheer ya fuce yana murmushi. Ita kuwa dama kamshin kazar ya mata dadi. Nan danan ta wanko hannu a bandaki tayi bisimilla tana ci tana korawa da yogoberry.

Ta nannade sauran ta ajiye .Ta yo wanka ta zura kayan bacci ta haye gado bayan tayi alwala. Ta tottofe jikinta da addu'oi tayi kwanciyarta.

Cikin bacci tafara jiyo kyakkyawar rungumar da akayi mata. Tamkar wani zai kwace ta. Da sauri ta yunkura ta janyo wayarta ta kunna fitila .wa zata gani in ba Maheer ba👩‍?

Har zata tashe shi sai ta tuna maganar da yace mata akan cutar sleepwalking da yakeda ita. Dake batada man Kai saita koma ta kwanta. Dama abunda Maheer keso kenan. Ya sake kankame ta. Bayan kallo daya zakayiwa fuskar sa kasan shirya zancen sa yayi da sani.


Asubah ta gari. SO DA ZUCIYA dake Shirin Zama abu daya💯🤣


Unedited 😭
2/12/22, 11:37 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*SO DA ZUCIYA*

*NANA HAFSATU*


*35*

Maheer na ganin ta kwanta bayan ta kashe fitilar. Ya samu zuciyar sa da jin dadi da kuma nutsuwa. Ya sake rungumota sosai. Tamkar za'a kwace masa ita.

Zaraah gaba daya ba yadda zata yi ne. Don bil haqqi gani take ciwon sleepwalking din nasa ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login