Showing 78001 words to 81000 words out of 85942 words

Chapter 27 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt

26 Oct 2025

382

yayi gaskiya. Abin ba a shekaru bane ko kankantar jiki rahama ce kawai da ga Allah.

Tausayinta da yanda jikinta ke tsuma ya sashi daukarta gaba dayanta yayi toilet. Dan yasan babu abinda tafi bukata a halin yanzu sama da ruwan zafi. Wani irin kankamesa Zaraah tayi da cusa kanta cikin kirjinsa dan sam bata bukatar ya ganar mata jiki. Tsabar wahala ma kukan nata ya gagara fidda sauti sai jan ajiyar zuciya kawai take.

Duk yanda yaso rabata da jikinsa a toilet din ma danya hada ruwa taki. Ya hadiye dariyar dake taso masa da kyar yana murmushi.

"Duk fa abinda ba'aso na gani din na gansa harma yayimin amfani madam, Ina rokon mahalicci dare da kuma safiya ya kwaranyo miki albarka. Ya wanke dukan damuwa da tsoron da ke ranki,Ya wadatar dake da yawan hakuri da kuma wadatuwar zuci,Ya ni'imtaki daga tsoro da dukan abinda kike shakka,Ya cika miki burin ki,Ya wanke damuwarki,Ya miki sutura,Ya sanya farko da karshen wannan rana sanadin wadatuwarki da dukan alkhairi a rayuwarki.

"Batoul, kin zame min komi arayuwata.kece kaddarata kuma kece manufa ta..Nagoda Allah kuma nagode fadi tashin daya zamo alkhairi har ya zuwa yau da na sameki." Yana magana yana kai mata sumba a dukkanin gabbanta.

Babu shiri Zaraah tai azabar sakinsa da son barin jikin nasa duk da azabar dake ratsa mata jiki. Duk yanda yaso danne dariyarsa kasawa yayi dole ta fito. Yasan ya gama sake jefata a cikin kunya, dan haka bai sake magana ba ya fara hada ruwan dumin. Zai taimaka mata tace zata iya. Badan ya yarda ba ya koma gefe ya bata damar yi amma ta saka masa kuka akan ita dai ya fita zatayi.

Dole ya fito ya barta yana faman murmushi. Jinsa yake wani sakayau tamkar an sauke masa wasu kaya masu nauyin gaske a kansa. Ga wani yalwataccen farin ciki da ke ratsa zuciyarsa da fargonsa. Bazai taba manta wannan ranar ba a rayuwarsa. Kamar yanda baya fatan ya taba manta Zaraaj da alkairin data shayar da shi a wannan rana. Lalle SO DA ZUCIYA sun zama abu daya.

Saurin bude idanunsa daya lumshe yayi jin ta saki yar kara. Dama yasan bazata iyaba shiyyasa ya tsaya a kofar toilet din. Komawa yayi ciki, sai ko ya sameta tana hawaye zata karama ruwan daya hada matan ruwan sanyi wai yayi zafi da yawa. Bai wani zauna jan zancen ba ya dauketa cak ya tsulma a ruwan. Duk yanda taso tashi ya hanata saboda karfin ba daya ba.

Tana kuka yana lallashinta har ruwan ya huce ya sake hada mata wani. Sai ko gashi taji dadinsa har tana sakin tagwayen ajiyar zuciya a jajjere.

Tare sukai wankan tsarki a karshe. Tana nokewa shiko ka'a jikinsa. koda suka kammala sotai ta rigashi fitowa. Sai dai yanayin tafiyar tata yasa suka fito ataren da bata so.

Shi da kansa ya shiryata cikin kayan barci, dan ya fahimci sanyi takeji ga kamar zazzabi-zazzani nason kamata na shiga sabuwar rayuwa.

Maganin daya tanada dama dan irin haka ya dakko mata. Harta kwanta ya tadata ya bata. Da kyar tasha tana zirarar da hawayen da bayason gani.

Sauri-sauri ya shirya shima ya hawo gadon dan ya fahimci dumin jikinsa tafi bukata fiye da komai a halin yanzun. Yana rungumeta kuwa ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya shima haka.

"Allah yayi miki albarka, yanda kika shayar dani zumar nan kema Allah ya shayar dake ruwan alkausara Zarah. Allah ya azurtamu da zuri'a mai albarka ya bawa rayuwarki kariya a duk inda kika tsinta kanki. Tabbas SO halittane Burin ZUCIYA na bai wuce namallakeki ba. Alhamdulillah kuma yau na mallake ki. Burin kafafuna suzo gareki. Burin Idanuwana shine sukalli kyakkywar fukarki,

"Batoul dina....I love you to the moon and back. I think of you daily. I think of you and you alone. You are my dream girl and treasure. My day is beautiful because of you. The only thing I care for now is you. I’m never lonely when you are around. I feel a spark connecting us from afar. I love you more than roses need the rain. A ship is lost in the sea if it loses its captain. I will prove you my love for eternity. You hold the key to my heart. I hope these words make you happy, I love you. I want to spend forever with you. You have filled the void in my heart. There are no words to describe what you mean to me. Your happiness and joy are my best priorities. I will stop loving you the day the ocean turns into a desert. It took me a moment to like you and an eternity of loving. Yau Maheer ya mallake ZUCIYAr zaraahn sa. Da SON ta dake dawainiya dashi. Ina kaunar ki Zaraah na. Allah ya miki albarka. Ya Kara miki ni'ima da sutura duniya da lahira."

Duk da halin da take aciki taji dadin addu'ar tasa. Harta saki tattausan murmushi da kai hannu ta share hawayenta...

××
Charanchas Mr and Mrs Maheer
Malami da dalibar sa.
Kaga yaya da kanwar sa.
Zazzafar kiyayya ta koma kauna🤗💯
SO DA ZUCIYA🥰❣️💯



XOXOWRITES
,🥰
2/24/22, 08:07 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p

PLS FOLLOW US ON IG🥰🙏JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO



SO DA ZUCIYA!!

ZAFAFA 5 PAID BOOKS❣️

PG: 42


×××A hankali Maheer ya sa lallausan hannun sa a fuskar Zaraah ya shigaa goge mata hawayen nata da tafukan hannayen sa.

Temaka mata yayi . Ta karasa tsaftace jikin nata. Hade da dauro alwala suka koma daki. Maheer din yana temaka mata ta hanyar kwantar da kanta a kafadar sa suka karasa shigaa cikin dakin..

Cikin ikon Allah kuwa aka kira sallah. Maheer ya jasu sallar. Wanda Zaraah tayi a zaune kasancewar yadda jikinta gabaki daya yayi tsami. Ga wani zazzabi dake neman sake lullube ta.

Suna idarwa. Maheer ya koma kusa da ita. Ya janyota jikin sa. Zaraah ta fashe da hawayen da ta kasa sanin na menene .

Ahankali cikin muryar rad'a. Hannun sa daya na karakaina a bayanta yana shafawa ahankali cikin sigar ban hakuri da rarrashi. Mai dauke da luntsumemiyar kauna maras algus. Ya Shiga yi mata magana a kunnenta yana mai busa mata iskar bakinsa dake fitar da wani turirin zafi mai sanyaya zuciya .

"Batoul!!! Inama a ce zan zamo hawaye ta yadda zanke kwanciya a cikin idanun ki, kumatunki ya zamo babbar farfajiyar da zanke rayuwa a bisan su, labbanki su kasance nanne wajen da da zasuyi bakina kyakkyawa masauki .

"Batoul, Kalmomi uku na yin sanadin karuwar bugun da zuciyata ke yi, kalmomi uku na sanya kafata karkarwa, kalmomi uku na sanya kaina ya yi ta faman rangaji, bari dai na furta su yau a gare ki ko na huta da azalzalar da zuciyata take yi mini a dangane da hakan, kalmomi uku: Ina son ki .....

Zaraah ta dan yi kokarin janye jikinta .Maheer ya hanata ta hanyar sake rungumota gaba daya ya dureta akan gado. Kafin ta sake cewa wani abu ya rage wutar dakin zuwa dimlight.

"Dole na nuna godiata agare ki Zaraah. Hakika kin jefa malamin naki jiya a kogin zumar dadi. Narasa tantance wacce irin duniya ta sinadarai na tsinci kaina ajiya. Allah ya miki albarka . Domin na same ki fiye da tunanin mai tunani. Nagode da adana darajar ki da kikayi , kimarki, martabar ki na ya mace. Kin adana komai a kammalance izuwa gidan auren ki. Bakina yayi kadan wajen zayyano godiata ag...."

"Dan Allah Ya Maheer kayi shi...'

Bata karasa ba ya samu nasarar hade bakunan su waje daya. Sunbatar ta yake cikin kwarewa da jefa mata salon tayi shiru ta cigaba da karbar sak'on zuciyar sa.

Hannun sa daya yasa ya tallafo kanta. Yayinda hannun sa daya ke zagaye ilahirin jikinta. Kauna yake nuna mata tamkar zai mada ita cikin sa.

Ta shiga ture hannun sa ahankali. Hade da zame bakinta daga cikin nasa. Ta juya kanta daya bangaren

"Batoul! Juyo ki fuskance ni. Karki bari na maimaita dan tsaf zan sake second round dan ba k. .."

Bai karasa ba tayi saurin juyawa ta fuskance shi tana hawaye daya nabin daya..

Ya sanya tattausan labbansa yana goge mata hawayen cikin wani irin salo' A hankali cikin kasa da muryar sa. Ya shiga ce mata,

" A tsananin so da kaunar ki bayan da kika samu nasarar sace zuciyata. Wannan zuciyar da ta kasance mallakina, ina mai farin cikin na mallaka miki ita a matsayin wata kyauta ta musamman. Na zama mallakin ki. Ki kasance mai ririta soyayyar mu kamar yadda na kasance. Na baki amanar kaina ki amince mu damke amanar juna. Kinji Batoul dina?"

Kasa magana tayi. Kalaman sa na matukar zagaye mata dukkanin jikinta. Jin sa take cikin zuciyar ta. Ta rasa ya akai hakan ta faru lokaci daya.

"Baki ce komai ba!!! Batoul ... Uhm? Kinyi shiru. "

Hannunta tasa ta rufe fuskar ta. Cike da jin kunyar sa . Yanayin tafiyar tsutsar da yake mata ne yasata ture shi ahankali.

"Ka bari Dan Allah. "

"Wai ka bari. Shikenan ni banda wani suna? Na gaya miki bana wani son yaya ehe. "

"Allah kai yayana ne"

"Ki dena cewa Allah. Muna kwance gado daya. Manne da juna . A canzamun gaskia. "

"Jon wuro.... "

"Jon wuro as in meke nan?"

"Yana nufin mai gidah da fulatanci."

"Na amince. Amman dai nan gaba zaki sauya wani dole "

Lakuce Mata kumatunta yayi. Ya mata kyakkyawan masauki a kirjin sa. Yana shafa jikinta. Hade da sumbatir gashin kanta Wanda ke tashin scented hair spray na yerwa incense and more.

"Nasan zaki mamaki.... Lokaci daya na fito na nuna miki ina son ki. Bazan karya ba Zaraah . Tun ranar da Allah ya qaddara aurena dake na tabbatar hakanne mafificin alkhairi. Na tsinci kaina cikin matsanancin kishin ki. Ashe soyayyar ki ce keta taruwa acikin zuciyatah . Don haka ba wani cigaba da dogon turanci da zanyi domin da har na fara rubuta miki labarin zuciata a dan wani littafi danai masa laqabi da SO DA ZUCIYA!! Wanda Zan danka miki shi yanzu kuwa don ki tabbatar. "

"SO DA ZUCIYA Kuma? "

"Eh mana SO na DA ZUCIYAr ki ne suka hadu waje guda zasu fara gudanar da ginin tsanin soyayyar su. Zaraah na ki amince mu gina rayuwar mu cikin aminci da kaunar juna . I promise to be an excellent lover, best friend and favorite life partner . Ki amince mu gina rayuwar auren mu tamkar yadda iyayen mu ke fata. Ni Kuma nake muradin buri. Ki amince mu tabbatar mu Kuma wanzar da A LOVE SOO BEAUTIFUL!! Zaraah I love you pass my mind beyond my soul. Ina kaunar ki. Kauna marar algus. Kauna marar gushewa da izinin Allah.. Kin amince ? Kin amince? Umm? Zaraateey? Say something please. "

Fashewa Zaraah tayi da kuka. Ita din gaban banza zataki amincewa da soyayyar sa? Mutum Mai tarin ilimi, dattako da sanin yakamata. Gashi dan manya mai jini a jika. Maheer ya mike da sauri ya kamota yana kallon idanunta

"Kuka Zaraateey? Bar kuka please. Nayi shiru. Bazan k ...."

"kai ne masoyina na hakika tunda har ZUCIYOYIN mu sun aminta da juna. Ina son ka kaima kana sona ina yi maka albishir din ka samu makullin bude daular zuciyata, ina kuma fatan zaka kara shiri domin fantsama a cikin kogin soyayya mai dadi. Ina yi maka fatan samun nasara a dukkan al’amuran ka, Na amince Jon wuro. Na mallaka maka ZUCIYATA, na kuma amshi SOYAYYAR ka da hannu dubu. Tabbas SO DA ZUCIYoyinmu sun qulla aminta mai dorewa ta har gaban abadan..."

Maheer bai jira tasake cewa komai ba. Ya rungumeta tsam a jikin sa. Dukkanin su suka shigaa zubar da hawaye. Kafin Maheer yai nasarar hade bakunan su waje daya. Suna hawaye suna nuna bajintar kaunar sumba mai ratsa jiki da bargo. Kowanne yana nunawa dan uwansa yafi shi son sa.

Daganan suka sake tsunduma wajen bude wata fagen soyayyar. Mai gardi da bada kala. Alkalami yayi kadan wajen zayyano maku yadda masoyan suke gurzar soyayya tamkar cin kwan makauniya.

💯❣️

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
2/25/22, 18:16 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p

PLS FOLLOW US ON IG🥰🙏JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO



SO DA ZUCIYA!!

ZAFAFA 5 PAID BOOKS❣️

PG: 43

×××Ardo na cikin baccin sa daddada. Mai hade da mafarkin yayi kudi ya auro mata yan nijar kyawawa. Sun haifa masa yara maza yan dagwai dagwai. Ya kuma zama hamshakin malami. Gashi nan dik inda ya zaga ana kiransa da gwani Ardo borkindo.

Lallausan jikakken abu yaji acikin kunnen sa. A mafarkin kuwa gani yake wai dan da aka haifa masa ne yake wasa. Ashe wata kandararriyar akuya ceta makota da yunwa taci tacinye ta. Itace kunnen Ardo mai rufe da rigar yar sharar sa koriya da alama kama da ganye tai mata kama

Jikake lubus. Ta laso kunnen Ardo . Da sauri Ardo ya mike. Gumi sharkaf ya kamashi. Dama a dakin marigayi Modibbo yake kwance ya dan saye kofar dakin. Ta haka akuyar ta shiga.

"Wayyo Allah na. Wannan algungumar akuya matsiyaciya . Allah ya kwashe miki albarka. Dan tsabar reni. Saboda kowa da komai ya renani. Ace kina dabba ki kere duk ciyawoyin lungunan. Ki rasa inda zakije sai ki shigo mun makwanci ki gwaigwayi kunne na. Dan kan uban uwar ki? Wannan tsinanniyar akuya daga gani ta gidan lantai ce itace ke sasakar dabbobi suna abunda sukaga dama. Ina mafarkina mai dadi. Wannan tinkiya wannan tinkiya Allah ya kwashe miki albarka."

Ardo ya karasa yana kokarin riko akuyar tayi waje da gudu tana kukan

"Mb'eee, B'eee "

"Allah ya kwashe miki albarka. Zakici gidan ku.".

Ya kwasa aguje yai Kan akuya saiga Ardo zube a kwata yafada. Dai dai lokacin da Atuwa tafito sanye cikin atamfar ta da mayafi data sayo a kasuwar tsaye. (Kuncen kaya da ake sayarwa. Wanda Allah ya horewa niimar kaya. Dan Allah ya dinga bada tsofi ga mabukata ko gidan marayu. Akwai dubunnai dake neman kayan tsummokaran da zasu saka ajikin su. Wanda kai Kuma awajenka gani kake tsummane na goge goge. )

Sai dadura gyatuma radau din jambakin ta take a labbanta. Tanata sauri . Taja ta tsaya ganin Ardo face face da kwata

"Ardo uban iyali. Kwal landantsan. Allah me alheri. Ardodo yanaganka a kwata? KO kifi kake nema mana? Sahibin raina. Dan Allah ban..."

"Idan Kika karasa Atuwa na rantse da malafar kan uban borkindo sai na chasa ki. Banda wulakanci irin na yan lungun nan ace kamar ni Ardo akuya tazo tana sudar kunnena s"

Bai karasa ba Atuwa taja guda ta saki tana dariya .

"Allah me alheri. Yau ana kwal landantsan. Ardo uban iyali ne a kwata charanchas haka? Ina a"

"Atuwa Allah ya kwashe m"

"Karka karasa Ardodo yau a farin ciki nake . Don haka bazan bata lokaci na ba gidan lantai z. "

"Lantai dai matar balalle?"

"Eh ita"
Cewar Atuwa tafada tana kallon kanta a mudubin fashashshiyar yar hodar dake hannun ta . Sai dashare hakoran take tana jujjuya fuskarta gefe da gefe.

"Wabillahil lazi kikaje gidan nan na shika ki?"

"Shika wane iri Ardo? Dan duwala zan sayo na shafa kayan nan sai warin ruma suke. "

"Nide na gayan ki.  Don narantse da Allah idan na sake saka akuyar nan a idanu na sai na Mata dukan kawo wuka. Kana ganin akuyar nan kuranin Allah kasan son abun duniya ne da ita irin na uwar dakinta Lantai. Na hada su dika na kwashe musu albarka"

Harara ta watsa masa hade da yamutsa fuska. Cikin gatsine gatsine hade da buga tsakiyar zaninta tace.

"Bari naje gidan mai unguwa . Uwalliya na sayar wa." Tayi gaba tana watsa hannu sama. Da alama dai kwashewa Ardo albarka take.

Yayinda ya shige gida bayan ya leka yaga ta dau hanyar gidan mai unguwa. Kaya ya sauya Kai tsaye ya wuce shagon Muhsina mai kayan kwalam da makulashe.

"Muhsinsin,,,"

"Na'am Ardodo. Cincin din zaa baka ko sifuringiroyis (spring rolls) ko samusa (samosa)? Akwai mitifayif (meatpie) "

"Ban cincin din da mitifayi na wazobia shima sai zobo."

Ta dakko ta mika masa ta taga. Hadi da cigaba da tuyar awararta akan dan risho.

Ardo ya samu waje ya zauna ya shiga ci yana korawa da zobon.

Atuwa taje ta dawo tanata zabga sauri. Daga bakin kofa ta tsaya tana kwalawa su Rumalle Kira

"Dan Allah kuzo mu tafi." Ta fada tana goye Farillatu data fito itama an shirya ta .

Fitowar sukayi kowanne da dan kayansa gwanin sha'awa. Suka nufi titi kai tsaye.

"Tsaya Dan sahu"

"Ina zan kai ku?"

"Nasarawa."

"Nasarawa ina? Sashen hotoro ko su lamido kiristen🥺? KO kofar nasarawa"

Atuwa tayi shiru tana kallon sa. Shima kallonta yake yana jiran amsa

"Haka dai da maka makan gidaje. Amman dai unguwar sharbebiya ce da gidaje masu kyawu harda famfu .."

"Basai kin karasa ba. Ina kike nufi wai?"

"Kai mu nasarawa kai dai."

"Nawa zaku biya"

"Dari hudu."

"Gaskia bazanje ba idan ba zaku bada dubu daya ba. "

"Dubu dannan? Ina mukai maka kalar dubu?"

"Zamu baka dari bibiyu." Cewar Rumalle hade da zaro tata ta bayar. Jimmmamman ma ta bata tata yan goma da ashirin. Atuwa ta dakko tata acikin bra yan dari guda 2 ta bayar.

Dan adaidaita ya kwashe su sukayi gaba. Sai zagaye suke. Sai da dan adaidaitan ya karbu number Dadan ya kira tukun sannan tace ya ajiyesu zata tura a daukesu.

Hakan kuwa akayi cikin rawar jiki tasa direba ya tafi ya dakkosu a bakin durbar hotel a titi .

Sai kallen unguwar sukeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login